Showing 45001 words to 48000 words out of 82398 words
rumanah kuwa tun 'yanxu yanajinsa cikin azuciyarsa sbd shine abinda yake nunawa duniya gabaki 'daya rumanah tasace shikadai shiyasa yake tsananin qaunar cikin tunkafin yazo duniya.
Fuskarsa ta shafo tana Murmushi tace,
Kana tunanin mezan Haifa ne?
Kallonta yayi yakalli cikin ya riqo hannunta cikin nasa cikin yanayi na sanyin murya yace,
Bana tunanin mezaki Haifa ta 6angaren jinsi sbd agurina ko me zaki haifa shine babban abinda zai cigaba da sakani farin ciki har abada sbd shine fitilarda take haskomin abu mafi soyuwa azuciyata.
Sanyi jikinta yayi takallesa da idanuwanta dasuka ciko da hawaye tasake riqe hannunsa cikin sanyin murya tace,
Ko agurin haihuwarsa na mutu ayanzu nasan bazaiyi maraici kamar niba,
Abinda yake cikina shine hasken rayuwata sbd shine cikakkiyar shaidar soyayyata da batada mahadi,
Shine abu mafi soyuwa a zuciya da rayuwata sbd shi tsotsonkane saidai bansaniba ko zan cigaba da zama uwa agaresa kamar yanda nake mafarki.....
Rufe mata baki yayi yana kallon idonta yace,
Har abada kece zaki zauna amatsayinki na mahaifiyarsa babu Wanda zai rabaki da abinda zaki Haifa....
Mutuwa ko qaddara "" tafada muryarta na rawa sbd tsoro da fargabar dake shigarta.
Girgiza mata kai yayi da sauri tareda Rungumeta cikin wani irin yanayi daya bata mamaki yace,
Ina roqon Allah daya cigaba da azurtani da 'yaya mata daga dukkanin matana.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali ta furta amin saidai hankalinta yariga yatashi sbd ganin shima bayason ta haifi namijin sbd guje mata arabata da 'danta da mijinta.
Shiru sukayi tsawon mintuna saida suka samu nutsuwa kafin yatashi suka fito ya nufi dakinsa ya shiryo yana saukowa suhailat tashigo agajiye sbd cikinta dayayi girma itama.
Cikeda tausayinta ya ware mata hannu ta rungumesa yayi kissing goshinta batareda yace komaiba.
Cikin kulawa tace masa,
Thank you baby"" sbd tasan sannu yake mata da gajiyar dayaga ta debo koda baiyi maganar ba.
'Dauke kai rumanah tayi tareda juyowa ta nufi cikin ahankali zuciyarta na bugawa da sauri sauri.
Bayanta yabi da kallo jikinsa na sanyi
Ganin yanda yayi yasa suhailat juyawa taga rumanah ce harta kusa shigewa kicin
Ta juyo takalli idanuwansa taga yanda yanxu soyayyar rumanah bata 6oyuwa acikinsu duk kuwa da iya qoqarinda yakeyi dan boyewar amma soyayyarta tafaracin qarfinsa sai kawai taji yabata tausayi tasaki murmushi qarfin hali ta dafasa cikin sanyi tace,
I will go and freshen up.
Tana fada ta wuce idanuwanta na cikowa da hawayen tausayin kanta da rayuwarta nan gaba sbd.
Ya lurada halinda itama tashiga yabi bayanta da kallo tausayinta nasake kama zuciyarsa ya zauna sofa yana sake kallon qofar kicin cikin damuwa.
Da daddare gurin dinner kowa nacin abinci cikin nutsuwa da rashin sukunin zuciya ya 'dago ya kalli rumanah dake cin fruits kawai yaji damuwar hakan sbd batason cin abinci saiya sakata dole idan suna sukadai kenan sbd lurada hakan yasa wani lokacin suhailat ke qin cin abinci a dining taredasu sbd su sake saitace akai mata daki.
Bayan sungama harzai bar dining din yacewa Carolina data qaro drink taje ta dafo masa noodles kadan a plate.
Suhailat najin haka tasaki murmushi tace,
Ok baby nizanje na kwanta bacci nakeji sosai so gud night.
Riqo hannunta yayi yana kallonta yace,
Zamu koma mineelik this weekend so idan kinje office kiyi magana dasu.
Ok tace gabanta na faduwa akaro na farko taji ankirama sunan mineelik hankalinta yatashi bare dataji zasu, asanyaye ta nufi dakinta tashige dama yau take fita girki.
Kallon qofar dakin rumanah yayi yanufa yashige lokacin harta gama shirin bacci.
Da mamaki takallesa ya qaraso bakin gadon ya hau ya kwanta yana lumshe ido.
Ranar asabar suka wuce Libya dukkaninsu sbd lahadi zasu isa mineelik gashi lokacin cikin rumanah yashiga wata na takwas suhailat kuma wata shida kuma sosai yake bata matsala sbd cs dinta shiru kawai tayi sbd batason dagawa maheer hankali saidai Sam batajin wannan karon cikin nada lafiya kamar sauran cikin datai tayi nasu amah.
Lokacinda ammy tayi ido biyu da rumanah da cikinta jin tayi hawayen farin ciki sun ciko idanuwanta sbd Allah ne kawai yasan iya adadin qaunar datakewa rumanah gashi tana 'daukeda cikin maheer 'dinta datafi kaf cikin 'yayanta.
Rungumeta tayi cikeda farin cikinta daya kasa 6oyuwa
Rumanah ma batasan haka tayi kewar ammynba saidata ganta hawaye suka ciko idanuwanta ta rungume ammyn tana cewa,
Ammy nayi kewarki sosai.
Cikin farin ciki sosai ammy ta zaunar da ita tana cewa,
Rumanah babu ranarda ammynki bata kewar kulawar dakike bata.
Murmushi tayi tace,
To ammy aigashi nadawo.
Kallon maheer daya shigo lokacin tayi tace,
Ko kindawo babu ruwan ammy dasaka matar mutane aiki bayan ga yanayinda ma take ciki.
Yagane ammy dashi take yayi kamarma baijiba ya qaraso gurinta suka rungume juna yace,
Nafekushy ya Ammy.
I miss you too maheer""tafada tana sakinsa takamo hannun suhailat dake tsaye bayansa tana Murmushi ahankali
Tace,
Suhailat yakuke?da yaran duka.
Lafiya klau ammy munsameku lfy?
Alhmdllh zoki zauna suhailat kinji sannunki.
Zama sukayi rumanah kuwa sashen s salma ta nufa acan s salma ba qaramin farin cikin ganin rumanah tayiba harda tsokanarta tayi da cewa,
Yanzu bada dadewaba zansa akira aarib yazo dalibarsa tadawo.
'Yar qaramar dariya tayi tace,
Idan yazoma babu ruwanah da abinda zai samesa.
Dariya s salma tayi tace,
Eh mana tunda miskilin mijinki nanan dole zakice haka.
Tsayawa yayi bakin qofar yana kallon yanda tasake take magana sosai da s salma baitaba ganin tayi surutu sosai hakaba musammanma dariyar datake tayi hankali kwance cikin farin ciki kamar ta dauwama cikin farin ciki haka harwarshen rayuwarta.
Qamshinsa yashiga hancinta ta juyo ahankali takalli qofar suka hada ido murmushin dake fuskarta bai daukeba taci gaba da kallonsa soyayyarsa mai qarfi nasake shigarta musamman irin kallon dataga yana jefota dashi,
Ahankali yaqaraso cikin babban palon yazo gabanta ya zauna kusada ita yana sake kallon Murmushi da farin cikin dake kwance fuskarta.
Cikin tsananin farin ciki s salma ke kallonsu tace,
Allah yadauwamarda farin ciki mai darewa a rayuwarku da abinda zaku haifa.
Kallonta sukayi atare suna amsawa da amin acikin xuciyarsu.
Sake kallonta yayi sosai zuciyarsa ke tsumayin son sake ganin dariyarta data dauki hankalinsa fiyeda komai.
Ganin irin kallon da yake mata ta fara qoqarin miqewa ya riqe hannunta ta zame ta miqe ta nufi dakin s salma tashigewarta tana Murmushi.
Da kallo yabita itakuma s salma nabinsa da kallo tana tausaya masa da irin soyayyar data hango yana yiwa rumanah sbd tasan atarihin mineelik soyayya itace mugun makamin dazai kashe mai ita ko tabarbare rayuwarsa sbd tana cikin asalin asalin masifar datake bibiyar masarautar musamman data hada da haqqin mutenan 6oye dabasa yafiya musamman ita rumanah dasukewa gujewar haihuwar namiji sbd nesantata da kujerar mulkin mineelik.
Wani 6oyayyan murmushi yasaki Wanda zaiyi wuya ga gani ya miqe bayan sun 'dan taba magana da s salma Wanda gabaki dayan Rabin hankalinsa na cikin dakin s salma Wanda duk tana lure saikuma taji jikinta yayi sanyi sbd tausayinsa.
Dakinsa yaje yayi wanka yayi sallah ya nufi gurin sultan jalaluddeen.
Suhailat agurin ammy tayi zamanta tayi wanka itada yara da Carolina sukaci abinci tana gama sallolinta baccin gajiya yayi gaba da ita.
Ammy Palon s salma ta nufa sbd ganin rumanah ta qaurace masu takoma can wanda tasan qila sbd suhailat su samu sakewa tabar nan din.
Acan abinci sosai s salma tasa taci sbd maheer daya bar mata saqon ta tabbarda rumanah din taci abinci.
Ammy data shigo kuyanga daya a bayanta daukeda qaton tray cikeda abinci masu qara lafiya kala kala tace a ajiye gaban rumanah dake zaune tana cin boiled vegetables.
Cikin kulawa ammy tace,
Rumanah saurake suhailat taci abinci hanacan tana hutawa.
Kallon ammy tayi kamar zatayi kuka tace,
Ammy gashi naci abinci naqoshi amma anjima zanci insha Allah.
Sam ammy bazataso takurataba tace to ki tabbatarda anjima kinci.
To ammy insha Allah.
Har dare tana gurin s salma bata komaba ammy so biyu tana dawowa kawo mata abinci da samuwar dafaffiyar madara mai zafi Wanda suke famar dirka mata da wasu maganin haihuwa lokacinda ammy tagama bata saida hawaye suka gangaro mata ta riqe hannun ammyn cikin wani irin yanayi na tsananin qaunar ammyn tace,
Nagode ammy sbd kinzamo uwar data kasa bawa maraicinah damar juya rayuwata,
Kin maye duk wani gurbi da uwa take dashi arayuwata sbd kin qaunaceni tun ina a tsumman 'yar baiwa harna girma amatsayin baiwa nazamo mutum mai 'yanci ayanxu,
Bazan taba sakamiki da soyayyar dakikeminba amma nayi miki alqawari bazan ta6a zama butulu mai manta akhairinki agareniba zan cigaba da zama tamkar baiwa agareki har qarshen rayuwata sbd kece kikabani abu biyu danafi so arayuwata 'yanci da......
Kasa fada tayi sbd nauyin ammyn saidai ko bata fadaba ammyn tasan maheer take nufi
Tausayinta da sabuwar qaunarta tareda zancenta yasa jikin ammy mutuwa matuqa cikin sanyin murya tace,
Rumanah ina qaunarki ne aranarda kika fado duniya tamkar 'yar dana Haifa nakejinki shiyasa nakeso kiyimin alqawarin komai zai faru har abada bazaki daina kallona kina tuno matsayina na uwa agarekiba wadda bazata taba yin wani abu dan cutatarwa agarekiba.
Da hawaye a idanuwanta tace,
Ammy nayi miki alqawarin har abada zan kare martabarki ta uwa dakike da ita agareni.
Rungumeta ammy tayi tashin hankalinta da fargabarta tareda tausayin rumanah nasake ninkar mata.
Har dakin dake palon s salma ammy taraka rumanah ta kwanta sukai saida safe ta fito ko tsayawa gurin s salma data shiru cikin jimamin zancensu ta fice.
A palon ammy yaci abincin dare yana gamawa ya wuce dakinsa ya kwanta duk da zuciyarsa na kwadayin ganin 'daya daga cikin matansa.
Washe gari qarfe goma na safe masarautar tacika da baqin mineelik Ethiopia sbd daukar matan yarima maheer uwayen magajin mineelik tareda sultana zaarah da aka mayar mata da matsayinta lokacinda labarin cikin rumanah ya isa ga sultan.
Harda jakadiya da itace zata karbi ragamar kulada cikin rumanah tun daganan Libya harzuwa haihuwarta.
Lokacinda aka fito da rumanah cikin wani irin shiri na adon doguwar royal gown cikinta yafito sosai tana tafe kusan bayi da guards goma zuwa sama Suna bayanta.
Kallonta ammy tayi jikinta na sanyi
Jakadiya ma cikin ta qarawa ido numfashinta na fita da sauri tasaki ajiyar zuciya.
Gogan kuwa tunda yaga abubuwa sunfara canxa masa daga yanxu ya rintse ido tareda budesu yayiwa Jakadiya kallo 'daya tagano manufarsa ta qarasa ta tarbi rumanah din ta suka nufi motar da zaishiga aka bude mata tashige nan kowa yashiga motocin suka nufi airport.
Tunda suka shigo motar hannunsu suke sarqe dana juna saidai babu mai iya magana acikinsu dan kowanne da halinda zuciyarsa take ciki.
Ko acikin jirgi tafiyar babu Wanda yake iya magana acikinsu sbd kowa da abinda yake kai kawo acikin zuciyarsa.
Suhailat dama tuntuni tasan ita farin ciki yaqare arayuwarta daga ranar da mijinta yafara son rumanah musamman yanxu datakejin duniyar dakomai ya fice mata arai gashi ciwon dakecinta yafara fin qarfinta musamman yanxu datake yawan ciwon mara mai tsanani.
Qarfe hudun asuba jirginsu ya sauka a Ethiopia.
Matse hannunta dake cikin nasa yayi ta juyo takallesa da idonta dasukai ja sbd tsananin damuwar dake ziciyarta.
Ahankali ta zare hannunta ta miqe ta wuce gaba su Jakadiya da sauran suka mara mata baya tana qoqarin maida hawayen dake qoqarin zubo mata.
Bayanta yabi da kallo idanuwansa na canxawa
Hannunsa suhailat ta riqo idanuwanta cikeda hawaye cikin rawar murya da kulawa tace,
Zan zamo bangon jinginarka aduk lokacinda kake buqatar hakan.
Rintse ido yayi idanuwansa naqara canxawa suka fito jirgin.
Motar rumanah daban ita kadai da masu tsaronta kuma itace agaba sai sauran nasu lokacin gari baigama haskeba.
Ruwa yaji ankelaya masa yayi saurin bude ido yatashi a matuqar zafafe saiyaga jini kaca kaca a jikinsa da sauri yatashi tsaye aka mayar dashi zaune da qarfi tareda dora masa wata doguwar takobi mai tsananin kyallin sbd kaifinta tsoro bai kamasa sbd dama yasan hakan zata iya faruwa ko yau ko gobe....
Cikin wata irin murya data amsa amo har cikin qwaqwalwarsa yaji ance"""asauke kansa Daga gangar jikinsa a qawata qofar shigowa masarautata dashi kowa ya 'dan'dana kalar mulkin assultana the redblood Queen.
Daga takobin akayi da qarfi za'a sare kansa yayi wani irin yunquri yana hada mugun zufan daya jiqa dukkanin jikinsa yakalli adama dake gefensa itama ta farko tana hada nata zufan da alama itama wani mugun mafarki tayi kamar shi sbd harma tafisa rudewa sbd rawar da jikinta keyi.
Saukowa yayi kan lafiyayyan qaton gadonsa yanajin wani irin tashin hankali na shigarsa busar data cika masarautar tashigo kunnensa kenan su maheer sun iso.
#mamuhgee
_*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_
*31*
Not edited.
Kallon adama dake qoqarin saukowa gado yayi yaga yanda jikinta ke rawa saidai Sam bata tata yakeyiba mafarkinsa ya girgiza tunaninsa da zuciyarsa matuqa sbd su mutane ne dasuka yarda da mafarki,
Basason 'yaya mata sbd muguwar aqidar dasuke ciki ta wani irin mulki da ake gudanarwa na tsantsar iko kowa yasan mulkin mace a mineelik masifa ce dabaza'aso maimaitawaba sbd jinin matansu bazai iya controlling na abinda yake tareda throne dinba kamar namiji shiyasa mulkinsu yake zama tamkar masifa ko annoba sbd mulkine na tsantsar zubarda jini Wanda babu yaro ba babba bare mata bare maza,ba tsoho ba tsohuwa.
Alqawarine yadauka bazai taba bari mace ta mulki mineelik ba koda zai rasa ransane sbd yasan duk macen dazata hau zaiyi wuya basuyi ajalin junaba dayaga haka ya roqi Allah yayi gaggawar daukar ransa.
Cikeda rudu adama takallesa tana goge fuskarta dahar lokacin take gumi tace,
Sultan nayi mugun mafarkinda gwara nayi mutuwar qasqanci a hannun 6arayi dana fuskanci irin abinda Nagani a mafarkin.
Bai kalletaba bare yatsaya sauraran abinda take fada sbd tunanin daya cika zuciyarsa akaro na farko arayuwarsa dayaji mulki yafara fita ransa sbd duba da irin mutuwar da sarakunan mineelik keyi yayi tunanin zai iya tsallakewa ya sauka mulkin salin alin batareda fuskantar irin qarshen sauran sarakunan ba shiyasa ya tattara duk dagewarsa akan ganin maheer ya karbi mulkin amma yaqi gashi matarsama ta haifi namiji arabasa da wannan masifar abu yaqi yiyuwa ta wani 6angare ga daular shiefffs na jiran rashin magajinsu su zamo bayi a qarqashinsu Wanda yafison ya sare kansa daga gangar jikinsa dayaga wannan baqar ranar yanzu kuma ga wata masifar nason 6ullowa sbd baisan me mafarkinsa na assultana yake nufi ba.
Hannunsa ya daga ahankali ya shafo fuskarsa cikin mamaki saiyaga zufa ne ke tsatsafo masa,
Rabon da yayi zufa a rayuwarsa harya manta.
Irin tarbarda akayiwa isowarsu ta qara sanyaya jikin rumanah sbd tafara fargabar itama me zata Haifa sbd ganin irin dubban jama'ar dasuka dogara da abinda zata haifa.
Lokacinda mamani tayi ido biyu da rumanah da cikin dake jikinta wani mugun jiri mai qarfi ya 'dibeta nuratu tayi saurin tareta tana kallon idanuwanta dake cikowa da qwallar baqin ciki tace,
Mamani lafiya?
Kasa riqe hawayenta tayi sbd baqin cikin daya rufe zuciyarta tace,
Har abada bazanyi lafiyar zuciya ba sbd bulama da asma'u har bayan barinsu duniya basu bar kurwata ta zauna lafiya ba bayan duk balain dasuka sako rayuwata aciki dan haka wlh bazan zauna nashaqi numfashi mai dadiba sai ranar dana gama lalata dukkanin zuriar da suka bari aduniya....
Sakinta nuratu tayi cikeda mamaki da baqin cikin halin mahaifiyar tata muryarta na rawa tace,
Mamani dazaki cire abinda yake ranki gameda rumanah dakin cire sbd zai kaikine matakin halaka sbd yanxu tariga ta taka wani matsayinda duk Wanda yayi mata wani ganganci zai iya rasa rayuwarsa sbd dukkanin burin daular nan da zagayenta akanta da cikinta yake dan haka ki nesanta kanki da ita sbd gujewa rasa rayuwarki..ke mahaifiyatace ina sonki fiyeda komai amma bazan iya kallo ki cuci rumanah ba dan haka karkiyi abinda zai barni da rashin zabi face na fadi gaskiyar dazaki rasa rayuwarki.
Tana gama fadar haka tabar gurin cikeda damuwa
Duk murnarta da farin cikin ganin rumanah din ya 6aci sbd mamani.
Kukan 6aqin ciki mamani tasake tana tsinewa bulama da asma'u ta juya ta nufi gurin adama da sai alokacin zata fito tarbon.
Kallo daya tayiwa cikin rumanah taji tari mai qarfi ya sarqeta kamar ranta zai fita
take ta gigice da gudu akaje aka kawo mata ruwa ta karba tasha idanuwanta dasuka firfito sukai jajir sbd tari numfashinta na fita da sauri ta juya tabar gurin nanma idonta ya sauka kan na suhailat dake tsaye gefen Maheer ai take taji qaramar hauka na neman kama zuciyarta tana isa palonta na farko dukkanin bayi da kuyangin part din suka fice sbd gudun laifi lurada halinda take ciki.
Mamani data sake biyota da ruwa ta miqa mata har lokacin itama jitake kamar ta cinnawa mineelik wuta kowa ya babbake ya mutu ko zataji abinda ya tsaya mata a maqoshi ya fada.
Karbar ruwan tayi tasake sha tana cewa,
Burina dana gina tun ina budurwa bazai taba rushewaba kan baiwa 'yar bayi,
Babu Wanda bazan iya raba gangar jikinsa da kansaba kan burina sbd burina shine burin karagar mineelik..
Cikin tsananin damuwa da baqin cikin mamani daya kasa dannuwa aranta tace,
Duk inda bulama da asma'u suka sauka saisun bar masifar data addabi kowa awajen
Shiyasa bazan numfasaba saina tabbarda na tarwatsa rayuwar rumanah da abinda ke cikinta.
Kallonta adama tayi da jajayen idanuwanta baqin cikinta na ninkuwa tace,
Ko bulama ne aduniya bai isa ya shiga tsakanina da hawa throne din mineelik ba bare 'yarsa dan haka ni adama ayau ina sake daukarwa kaina alqawarin kawarda ko wanene ya shiga hanyata ta cimma burina
Idan nace ko wanene ina nufin ko wanene ciki bancire kowaba.
Cikin takaici mamani tace,
Allah yasa gurin haihuwa ta mutu daga ita har abinda zata haifa kowama ya huta.
Kobata mutu gurin haihuwa ba ta haifi namiji saiya mutu kozan rasa rayuwatane"""adama ta fada tana miqewa tsaye.
Tsayawa tayi tareda juyowa takalli mamani itama mamani ita takalla sai alokacin kowannensu yadawo nutsuwarsa jiki na rawa mamani ta zube tana sunkuyar dakai
Adama fuskewa tayi sbd duk duniya daga ita sai bokanta ne suka San da sirrinta sai yanzu da 6acin rai yasata fadar abinda ke ranta saidai kuma ga alama tasamu wadda zata riqa amfani da ita Dan cimma burinta musamman da kusancinsu da rumanar zasuyi amfani tunda tana yiwa mamani kallon uwa.
Wani irin babban sabon sashe da aka zubawa tsaro na musamman aka kaita Wanda yake gefen part din yarima maheer duk wani abin jin dadi da hutawa anxuba mata shi ga kuyangi na musamman da aka kawo mata.
Bayan duk wata aladar tarbonsu anyi angama da daddare bayan tayi wanka ta saka kayan bacci ta kwanta bakin gado tareda lumshe idanuwanta ta bude ahankali tareda kiran sunansa cikin zuciyarta.
Suhailat kuwa sbd yanayin jikinta da gajiya yasa tana kwantawa bacci ya dauketa cikin tsananin gajiya.
Abincin da aka aikawa kowaccensu daga part din sultana zaarah babu wadda tasamu damar ci har gwara suhailat tasha madara mai zafi sbd sanyi datakeji kamar zai kamata.
Rumanah kuwa kwance take tayi lamo cikin zurfi a tunani da tsananin son ganinsa sbd har lokacin takasa daina tuno yanayin dasuka rabu 'dazun hakan na raunana zuciyarta da kuzarinta ahaka bacci yadan 'dauketa tanayi tana farkowa hardai akai