Showing 69001 words to 72000 words out of 82398 words
ta dau mataki akansa saidai kasancewarsa tareda ita yasa take iya control din yanda takeji saidai kamar abin nason yafara mata yawa.
Cikin nutsuwa sukaci abincin duk da kadan taci tasha maganinda aka aje kan dining din daga negasi.
Harsuka gama cin abincin idonsa nakanta sbd sosai ya lurada sauyi atareda ita saidai zuciyarsa naqara jaddadawa kanta arayuwa babu abinda zai rabata sonta.
Kasancewar bata fara sallah ba yasa yakaita daki yasake kwantar da ita ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa yace,
Inason sanin abinda yafaru tsakaninki da ammy.
Kallonsa tayi kafin ta dauke kai tana sake sawa zuciyarta qin ganin laifin ammyn kai tsaye tace,
Sultan ya kashe iyayena da taimakon ammy da jakadiya.
Cikin wani irin mugun yanayi na mamaki yake kallonta
Ta zame ta sauka gadon ta nufi bakin window ta tsaya.
Gabanta ya zagayo ya tsaya yana kallon cikin idonta ta rintse idon tana dauke kai.
Ahankali ya bude baki zaiyi magana ta bude idanuwanta dasukai ja ta katsesa cikin sanyin murya da cewa,
Bana maka wani kallo na daban a zuciyata bayan Wanda nake maka na mahadinta ko Allah baya kama wani da laifin wani....
Shiru tayi tana tauna Kalmar dazata fada cikin qarfin hali tace,
Na yafewa ammy sbd Allah da soyayyarta gareni da kasancewarta mahaifiya kuma kaka ga mutane biyu danafiso ayanxu fiyeda rayuwata dakomai,kai YARIMA MAHEER ABDULSHAMS da ABEEL HASSAN......
Cikin sanyin murya dake nuna baqin cikin dayake ciki ya furta,
Sultan f....
Bai qarasaba tace,
Kayi hakuri.
Ta juya masa baya cikin wani irin zafi datakeji a zuciyarta ta rintse ido tasake cewa,
Kayi hakuri.
Kasa motsi yayi sai idanuwansa dasukai jajir yana jujuya kalmarta ta yayi hakuri....zata dauki mataki akan mahaifinsa kenan.... No not possible...tokuma ko Ba itace akan mulkiba tana buqatar justice.....
Ficewa yayi sbd jin kamar numfashi na masa wuyar ja ko gani sosai bayayi sbd tashin hankalin dayake ciki.
Suhailat dake tsaye gaban windonta taga fitowarsa daga sashen na rumanah ta 'dauke kai tareda barin jikin windon sbd gujewa ganin damuwa.
Yana fita ta zauna bakin gado tareda dafe kanta ta rintse idanuwanta kanta na mata wani irin ciwo.
Koda dare yayi duk yanda taso bacci kasawa tayi sbd kewar iyayenta da 'yayanta.
Koda gari ya waye qarfe goma wata zungureriyar takardar saqo daga alqalamin sauraniyar mineelik ummu-rumanah bulama ta isa hannun sarkin fada haroun inda saqon yake cewa ayau angama karbar duk wani bayani akan asalin sarauniya ummu-rumanah daga baiwa mamani dan haka ayau za'a yanke mata hukunci.
Atake aka buga sanarwa koina ya dauka qarfe goma sha daya jama'a suka taru ana jiran isowar assultana.
Cikin wata irin royal gown tafito red mai adon golden gashinta koina rufe da adon sarqar farin zinari wasu irin samudawan guards ne maza da mata taredasu Jakadiya a bayanta ta fito suka nufi fada.
Cikin nutsuwa na wani irin miskilanci ya yasha gabanta yana kallonta guards din bayanta suka nufosa ta 'daga musu hannu tareda juyowa cikin nutsuwa ta kalli Jakadiya tace,
Duk Wanda yasake gangancin tare mijina aduk lokacinda yakeda buqatar magana dani yana ganganci da rayuwarsane a sanarda kowa.
Cikin tsananin ladabi dukkaninsu suka sauke kai suna tuba.
Ta juyo ta kallesa cikin nutsuwa tace,
Ina kwana?
Kallonta yayi kafin ya watsawa su jakadiya wani mugun kallo atake suka ja baya sukai 'dan nesa kadan dasu.
Ya kalleta cikin ido yace,
Bazaki yankewa mamani hukuncin kisaba that's an order amatsayin na mijinki
Ba mamaniba har kowama bazaki yankewa hukuncin kisaba nin......
Sultan ne bakason a kashe ba mamani ba"""ta fada tana kallonsa cikeda fargabar abinda zaice.
#mamuhgee
Sorry manage.
*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationš”_
*40*
_Not edited_
Kallonta yayi yana sake kafeta da manyan idanuwansa ransa na qoqarin 6aci da zancenta zuciyarsa na qoqarin hana faruwar hakan ya bude baki zaiyi magana ya fasa ya kama hannunta da qarfi ya jata part din ammy dake kusa
Tsakiyar palon ya saketa tareda kallonta cikin sautin dake nuna bacin ransa yace,
Me kika fada yanxu?
'Dauke kai tayi kai tsaye tace,
Kana qoqarin kare sultan ne akan laifukanda yariga ya aikatasu ne cikin son rai da ganganci saidai kuma nariga nayi alqawarin duk Wanda ya cutatar da wani sai anbi masa haqqinsa sbd wannan shine adalcin assultana,wannan shine banbancin mulkin son rai da adalci....duk Wanda ya kashe a kashesa wannan shine hukuncin a musulunce.....
Riqota yayi da qarfi ransa na qarasa 6aci yace,
Kina tunanin na hanaki hakane sbd sultan yana nahaifina?
Kisa dai matuqar ina raye kuma da aurena akanki bazan ta6a bari kiyiba ko adama kin kashetane a lokacinda bana kusa da bazan taba bari ki kashetaba and da.....
Qwacewa tayi tana kallonsa tace,
Nice na kashe adama kana qoqarin cemin mai kisa ne????
Bayan kasan mutanen nan sun cancanci kisa tako wane sashe na sharia,
Anyiwa iyayena kisan wulaqanci da son rai,
Anyiwa 'dana kisar son rai da ganin dama duk basune masu laifiba nice danake shirin qaddamar da adalci wa kaina amma y.......
Idan kina maganar abeel Hussain ne ni mahaifinsa nabarwa Allah duk Wanda keda saka hannu nabarsa shida ubangijinsa maganar iyayenki kuma amatsayina na mijinki nake baki umarnin kibarwa Allah bazaki qara yankewa kowa kisar wulaqanciba ki tabbatarda idan kika sake hakan ni maheer abdulshams mungama zama tare abakin aurenki gabak......
Cikin tashin hankali suhailat dake palon basusan da itaba tayi saurin katsesa da cewa,
Abu abeel ka.....
Shut up and stay out of this suhailat"""""yafada ransa a matuqar 6ace.
Rumanah datai mutuwar tsaye tana kallonsa idanuwanta sun kada jajir suna zubo hawaye zuciyarta takai qololuwa gurin tashin hankali da baqin ciki ta bude baki cikin baqin ciki tace,
Basaika datse alaqar dake tsakaninmuba nasan bana ranka ko gabanka kayi qoqarin barina da aurenka har zuwa yanzu da baka sallameni bayan haihuwataba sbd itace amfanina daman shiyasa kace haka sbd sanin sirrin zuciyata saidai........
Fixgoto yayi da qarfi zaiyi magana ta fixge jikinta tana sakin wani irin kuka mai qarfi da ciwo sbd zancensa ya girgiza duniyarta gabaki 'daya ya kasheta jitake zuciyarta kamar zata babbake ta kama da wuta sbd masifar dake ci mata zuciya.
Cikin tsananin damuwa suhailat ta dauki abeel ta nufi palon qurya tafadawa ammy dake zaune cikin tunani abinda yake faruwa.
Da sauri ta taso tana shigowa palon ya juya zai fice ammy tayi saurin riqo rumanah dake kuka kamar ranta zai fita takira sunansa ya tsaya cak batareda ya juyowa sbd qaran kukan dake sake hargitsa nutsuwarsa da tafasa zuciyarsa.
Rungume rumanah tayi tana qoqarin rarrashinta saidai kukane takeyi sosai Wanda ke nuna tsananin ciwo da baqin cikin da zuciyarta ke ciki.
Kasa tsayawa yayi ya rintse ido da qarfi ya fice yanajin baqin cikin kukanta da maganganunta.
Suhailat dake tsaye ji tayi jikinta ya qara wani irin sanyi da kukan da rumanah keyi ahankali ta fice daga sashen sbd ganin suna buqatar tattaunawa tsakanin 'ya da uwa dan jin tayi tazama baquwa acikinsu su duka din har maheer 'din.
Shiru ammy tayi da ita rungume a jikinta batareda tace mata komaiba sbd halinda take ciki tana buqatar tayi kukan ko dan ta rage nauyin dake zuciyarta,
Maganar gskia ko ita bazataso rumanah ta zubar da jiniba sbd sauyi suke fatar samu daga gareta...
Itace sarauniya ta farko a tarihin qasar gabaki 'daya data hau sarauta batareda jinin sarauta a jininta ba bama 'yar qasarba baquwar haure daga wata qasar,
Qaddara ta koro iyayenta daga gida suka fada wani gari inda daganan Allah yasake jefasu hannun masu kamun bayi aka kamosu zuwa nan qasar aka haifeta amatsayin baiwa
Wata qaddarar tasa ta auri yariman masarautar,
duk wannan qaddarar data koro iyayenta ta zamtowarta cikin lissafin masu mulkin qasar ne wannan kawai ya tabbatarda akwai abinda Allah ke nufi da hakan Wanda suke fatar sauyine na alkhairi mezaisa suso ganinta tana aikata abinda sauran sarakunan suka aikata.
Tasan tabbas maheer yayi hakan ne dan bazai iya bari ya rasataba dan idan ta cigaba da zubarda jinin karagar mineelik zata shiga jikintane sosai ta yanda zasu rasata har abada.
Dakinta tashigarda ita ta kwantarda ita kan gadonta ta rufeta tareda shafa kanta ta fice taje palo ta zauna tareda kallon Jakadiya data shigo duba assultana jin shiru dan tuni aka zagaye sashen ammyn da tsaro kasancewar tana cikin.
Dafe goshi ammy tayi cikin tsananin damuwa da rashin sanin mafita tace,
Kije kisanarda sarkin fada haroun assultana ta 'daga hukuncin zuwa wani lokaci batajin dadi yanxu.
Cikin girmamawa da jimami tace,
To""ta fice taje ta sanar atake akai sanarwar aka watse tareda tsananta tsaro sashen ammy.
Har dare tana sashen ammy kwance ko motsi bata yi
tayi wani irin sanyi idanuwanta sunyi jajir.
Shigowa ammy tayi cikin nutsuwa ta zauna bakin gadon tareda sauke numfashi ahankali cikin kulawa da sanyin murya takira sunanta.
Bata motsaba ta bude idanuwanta dasuka kumbura batareda ta amsaba.
Duk wani 'da na halak bazai iya kallon makasan mahaifansa ya qyalesuba matuqar yanada halin daukar mataki ko fansa akansuba..
Saidai kuma dangana da bariga Allah ta wata hanyar shine sasanci da kawo qarshe ga kashe kashen.,
Ummu-rumanah har abada haqqin asma'u da bulama bazai bar ko 'dayanmuba koda kin yafe mana saidai kuma ina sake roqon yafiyarki a maimakon mu duka 'din,
Wlh rumanah ina kallonki amatsayin 'yar dana haifa,
Ina qaunarki da sonki har cikin zuciyata fiyeda wasu daga cikin 'yayan dana haifa shiyasa bazan iya bari naganki cikin wata muguwar rayuwa.
Kisan bashine mafitaba bashine zaisa kiji sanyi a mutuwarsuba saima lalata rayuwarki dazakiyi ta hakan sbd har abada bazaki yafewa kanki abinda kikayiba zaki tsinci kanki cikin baqin ciki da damuwar da muma muke ciki ayanxu,
Mijinki yana miki sonda bazai iya bari ki fada wani mummunan haliba bawai yanayi ne dan karki kashe mahaifinsa saidan yana tsoron hakan zai qarasa gusarda imaninki ne.
Amatsayina na uwa ba sultana matar sultan mahaifiyar maheer ba nake baki shawarar karki kashe mahaifin mijinki ki bar iyayensa da haqqin ran iyayenki wlh Allah zai kamasu sbd baya taba barin haqqin wani akan wani dan haka kiyiwa magana nazari.
Miqewa tayi jiki asanyaye tabar dakin tana fatar rumanar tayiwa zancenta kyakkyawan fahimta.
Qofar da ammy ta fita ta qurawa ido idanuwanta nasake kadawa sbd zancen ya shigeta saidai fadanta da maheer ya kasa barin zuciyarta ta nutsu da daga bakinsa wainnan kalaman suka fito tabbas zuciyarta bazata tsaya wasi wasin daukarsu ba,,
Meyasa zai fada mata kalaman dasukafi dalma zafi gurin tarwatsa kunnuwanta da zuciyarta?????
Meyasa zaiyi fushi ya iya furta mata kalaman rabuwa da ita bayan alqawarin dayayi mata badan mutuwaba dashi da ita bazasu rabeba????
Wasu irin hawaye masu radadi suka gangaro mata ta rintse ido tana qoqarin danne kukan dake qoqarin zuwar mata.
A cikin daren takoma sashenta tareda guards inda ta bada gargadi mai qarfi akan batason ganin kowa.
Kwana biyu tayi bata fito ko qofar part dinta ba..
Abincin safe rana dare haka ake kwashesa bata fitowa saidai ammy tazo dakanta har bedroom tasata cin abinci dole.
Duk iya yanda take jin kewa da soyayyarsa na cin zuciyarta dannewa tayi sbd har lokacin zuciyarta cike takeda zafi da radadin kalamansa shima kwana biyun bai nemeta ba hakan yaqara quntata yanayinta.
Nuratu data rungumi qaddara da hannu bibbiyu akan mahaifiyarta still itace ke kulada rumanar amintacciyar baiwarta duk da da farko anso hanata ko kusantar inda rumanah take saidai rumanar ta hana sbd tasan suna tsananin buqatar juna sbd sukadai suke ganin junansu amatsayin jininsu tunda mamani sunanta matacciya.
Sultan kuwa a rubuce ta aikawa harooun da takardar a tsananta tsaro a sashensa kowama yanxu ta hana yashiga gurinsa
Hakan kuwa akayi nan take aka cika umarninta tareda bada gargadi ga duk Wanda yaje kar abari yashiga.
Kwance take kan doguwar royal chair 'din shaqatawa dake qaramin palonta dakeda manyan qofofi guda biyar dasuke ta bayan garden din shashaqatawarta,
A rufe idanuwanta suke saidai Sam ba baccin takeba iskar gurin mai sanyi take kado mata ta shara sharen labulayen winduna da qofofin palon dan ragewa kanta zafi da quncin datake ciki.
Ahankali ta jiyo kukan jariri na shiga kunnenta ta bude idanuwanta a hankali sbd tasan kukan abeel ne tunda kaf masarautar babu jariri bayanshi.
Tashi zaune tayi cikeda kewar 'danta da tausayinsa na rashin 'dan uwansa dakuma 'dumin jikin mahaifiyarsa
Miqewa tayi ta nufi qofar bakin window ta tsaya tana hango cikin bedroom din suhailat da itama ta iska ke daga farin labulenta....
Rungume take dashi a tsaye tana jijjigasa cikin tsananin kulawa da damuwar kukan nasa
Ta 'dagosa tafa duba fuskarsa cikin qaunarsa tayi kissing kumatunsa tana cewa,
Abeel please kayi hakuri mummy bazata sake baka maganin zazzabi ba kaji pls my little prince forgive mummy......
Hawayen datake ruqewane suka gangaro mata na tsananin soyayyar 'danta da qaunarsa saidai kuma bazata iya karbarsa daga suhailat na....
Tunda ta shigo rayuwarta ta sanadinta ta rasa komai,
Ta rasa jin dadi,kwanciyar hankali da soyayyar mijinta sbd ita,
Ta rasa babynta sbd jin mijinta ya aureta,
A yanxuma ta rasa jemal ne sbd ita Dan 'yayanta akaso kashewa duka tsautsayi yasa aka kashe mata jemal kuma gashi ta rasa mahaifarta har abada...
Gashi ta riqe 'dan kishiyar datai sanadin rabata da komai da zuciya 'daya tana qaunarsa tamkar itace ta haifesa,,,
Wace irin soyayyace takewa maheer??sbd tasan tana tsananin qaunar abeel ne sbd shi 'din tsotson maheer ne.
Idan suhailat ce a matsayinta na yanxu zata iya kashe mahaifin maheer?
Duk wainnan abubuwan da suhailat ta rasa ta dangana bata riqe kowa araiba gashi tana rayuwarta gwargwadon iyawarta batareda tasaka damuwar duk Wanda ya cucetaba koya tauyeta.....meyasa ita takasa hakan?
Suhailat tafita son maheer ne???
Girgiza kai tayi tareda durqusawa a gurin tana zubarda sabbin hawaye masu radadi da ciwo gabaki 'daya ta rasa nutsuwarta da sukuninta rashinsa atareda ita jitake tanason zubarda jinin duk Wanda ya cutatar da ita da iyayenta da 'yayanta SBD kalamansa dasuke yawo cikin kanta suna qona zuciyarta...
Cikin kuka tace,
Bakasan rashinka taredaniba ha'darine dan zan iya aikata abinda bakason dan Allah kadawo gareni maheer.
Suhailat data shigo palon dan kawo mata abeel tagansa sbd ta hangota lokacinda take kallonsu tayi saurin tsayawa cak jin abinda rumanar tace.
Numfashinta taji yaqara gudu tayi saurin juyawa dan ficewa tun kafin rumanar taganta
Saidai tana juyowa tagansa tsaye bayanta idanuwansa sunyi wani irin zurfi ya qureta da ido.
Tsawon kwanaki kenan itama bata sakashi a idoba 6acin ran rumanah duk yashafesu saidai Sam bata damu sosai da rashin ganinsaba sbd tasan irin radadi da zafi da zuciyarsa ke ciki na fada da abinda kafiso fiyeda komai.
Rabasa tayi zata fice sbd ahankali ya kira sunanta ta tsaya cak
Rumanah kuwa tun shigowarsa taji qamshinsa saidai bata juyoba sbd wani irin bugawa da zuciyarta keyi.
Hannu ya miqa ya dawo da suhailat gabansa cikin murya mai bada umarni yace,
Miqa mata 'danta.
Arikice takallesa itama rumanah a firgicen ta juyo takallesa.
Fuskarsa a matuqar 'daure yace,
Kibata 'danta.
Wasu irin hawayen soyayyar abeel da qaunarsa suka gangarowa suhailat takalli abeel din takalli fuskar maheer din taga babu sakewa ko kadan ta juya tana tsiyayar hawaye qafafunta na rawa ta nufi rumanah datai mutuwar tsaye cikeda mamakinsa.
Siririn kuka suhailat tasaki tareda 'daga hannuwanta ta miqawa rumanah abeel.
Cikin rawar murya rumanah ta bude baki daqyar tace,
Nabar miki shi.
Girgiza mata kai suhailat tayi tana wani irin kuka mai ciwo da qaramin sauti.
A firgice tasake cewa,
Wlh na barmiki shi....
Girgiza mata kai suhailat tasakeyi tareda ajiye mata shi kan kujera ta nufi qofa da gudu tana toshe bakinta sbd kukan dayaci qarfinta.
Dawo ki daukesa.
Cak ta tsaya tareda juyowa takallesa da sauri
Ki daukesa nabakishi bar abada 'dankine.
Da sauri tadawo ta daukesa ta rungume tareda dawowa gaban maheer din ta rungumesa cikin tsananin farin ciki tace,
For a moment I thought na rabu da abeel har abada..nagode.
Kallon rumanah data zuba masa ido yayi cikin kulawa yace,
Suhailat idan babu so biyayya na jawo soyayya fiyeda komai,
Idan akwai so rashin biyayya na rusashi komai qarfinsa..
Har abada suhailat matsayinki daban yake cikin zuciyata bazan ta6a daina ganin girma da qimarkiba.
Sanyi jikinta yayi masifar yi sbd gane amfani yayi da ita gurin isarda saqo ga rumanah...
Wani irin ciwo da radadi taji yana tasowa a zuciyarta akaro na farko data kasa riqe abinda yake zuciyarta tasaki wani irin kuka mai ciwo tareda ficewa tana dafe qirjinta dayake mata zafi sosai.
Gabanta ya qaraso ya tsaya yana kallon cikin idanuwanta dake zubard hawayen abinda yayi yanxu dan ta tabbarda ita yake fadawa magana bada suhailat din yake.
#mamuhgee.
*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationš”_
*41*
_Not edited_
_*Marubucin gskia baya rubuta abu acikin labarinsa batareda yayi bincike ko tambaya ba yayiwa abin cikakken sani kusani marubuci ba jahili bane sbd wata tambayar ko comment din tamkar wanka da jirwayene akewa marubuci dan haka kusani ni bana rubuta abinda banida sani akansa.*_
Juyawa tayi tabasa baya zuciyarta na wani irin bugu sbd zafin maganar daya gama fada mata,
Kobai fadaba tasani yafi ganin girma da qimar suhailat sbd ko babu komai itace uwar 'yayansa kuma macen data girmama dukkanin abinda zaizo mata dashi saidai tasan itama baza'ace bata masa biyayyaba,,,,
Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na sake jiyo mata zafin abin,
Da kishiyarta yake gaya mata maganar bata masa biyayya...sabon ciwon hakan taji ta rintse ido da qarfi tareda girgiza kai ta juya ta nufi qofa tana qoqarin maida kukanta.
Riqo hannunta yayi daidai lokacinda tazo wucesa ya dawo da ita gabansa yana kallon fuskarta data qi kallonsa saidai yanayinta ya nuna jin zafinsa ne cikin ranta.
Kujera ya nufa ya zaunar da ita ahankali kafin shima ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa da kulawa yace,
Kina tunanin wannan itace mafita???
Kina tunanin a halinda muke ciki yanxune lokacinda yakamata mu ringa samun matsala akan abinda nakeĀ buqata nakuma baki umarni?....
Kina tunanin sbd kare mahaifina nakeson dakatar dake daga abinda kike shirin aikatawa???
A musulince duk Wanda ya kashe a kashesa amma idan kashewar zata kawo kashe kashen bayin Allah da basujiba basu ganiba to an yarda abar Wanda yayi kisar sai ayi masa wani hukuncin kwatan kwacin zafin abinda ya aikata.
Kina tunanin sultan mahaifanki kawai ya kashe?
Sultan ya bada umarni ankashe mutanen da sukafi mahaifanki abin tausayi,
Ya maida yara qanana marayu babu adadi,
Ya saka mata zaman takaba babu adadi,
Duk kina tunanin yin kansa ne kokuma ra'ayin kansa ne???
Dana barki da tun a shrkaran jiyar kinzama abinda yafi sultan ha'dari dan kuwa da yanxu jinin mutanen da kika zubar yafara ta6a qwaqwalwarki...
Kinga abinda mu bamu ganiba labari kawai mukeji na asalin abinda ya faru har aka samu karagar kuma kinsan duk wata masifa dake bibiyar masarauta nan har yau ankasa samun Wanda zaiyi amfani da tunani da baairarsa domin kawo sauyi domin kuwa tun farko kisar cin amana ce ta samarda karagar kuma har yanxu kisar ce akeyi kina tunanin hakan shine mafita da sauyi tareda jin qan da talakawan qasar ke buqata bayan sune ake kashewa wainda basujiba basu ganiba.,
Kinason yankewa sultan hukuncin kisa bawai dan fadar musulunci ba saidan daukar fansar kisar iyayenka Wanda