Showing 69001 words to 72000 words out of 110071 words
ya fito"
Ran Dr Tani yayi baki da maganarsa ta shige fuu yayi dariya kawai.
Falon baki taje ta tarar da kaya baja baja a kasa ga dishi dishin jini. Sama tayi cikin sauri tana kiran Qareeba taji motsi daga dakinta da kukan Qareeban amma kofa a rufe. A guje ta fito ta kirawo Dahiru.
Shi tsoro ma ta bashi amma ya kula ba lafiya don da takalmi daya ta fito ma. Binta yayi da sauri tayi sama tana kiransa da ya taimaka. Suna jiyo kukan Qareeba yayin da BB yake dukanta.
Dahiru baiyi wata wata ba ya kaiwa kofar wani irin duka sai ta bude.
Abinda suka gani ne yasa Dr Tani sumewa shi kuwa Dahiru yayi kan BB kamar zaki ya ga nama.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰18
*Batul Mamman*💖
Haj Mara duniya tayi zafi ta rasa ina BB ya shiga. Ta kira wayarsa har ta gaji.
Bata sanshi da wasu abokai ba yanzu balle ta neme su. 'Ya'yanta mata ta fadawa halin da ake ciki kowacce ta zuke saboda sun gama gajiya da halinsa.
Ta san Dr Tani akan 'ya'yanta da kowa ma fada take balle an taba Qareeba.
*****
Kano kuma Dr Auwal ya debo 'yan sanda ya shigar da kara. Cikin gidansa suka shiga aka dauki hotuna da za'a gabatar shaida. Komai a ilimance don yasan me yake yi shiyasa ko tsinke bai yarda an taba ba. Bayan sauraron bayanan maigadi suka ce suna son ganin wanda ya kaisu asibitin wato Dahiru.
Basu jima da fita ba Dr Auwal ya kira Alh Sule. Yana ofishinsa dake Lagos. Yayi zaton magana zasu yi da ta shafi auren 'ya'yansu sai yaji sabanin haka. Fada Dr Auwal yake yi cikin kunar rai.
"Alh Sule ina Babawo yake?"
"Dakata Dacta meya faru ko gaisawa bamu yi ba"
"Gaisuwa? Gaisuwa ai a gidan mutumci ake yinta. Saboda ku nuna hali an fada muku abinda yaron nan yayi amma daga kai har iyalinka babu wanda yazo yau kwana uku. Wallahi duk inda Babawo yake ku fito dashi domin na riga na hada da 'yan sanda sai munyi shari'a da ku"
Kan Alh Sule ne ya daure ya dai ce masa yayi hakuri sannan ya katse kiran ya nemi Haj Mara.
Tana dauka yace mata "me yake faruwa da Babawo yanzu Dr Auwal ya kirani"
Kuka tasa masa "Na shiga ukuna Alhaji Babawo fyade ya yiwa 'yarsu na rasa yadda zanyi bansan inda yake ba shi kansa"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Marakisiyya kin kasheni" ya harzuka matuka ya fita da kansa ya kira drebansa. Ko gida bai koma ba ya wuce airport. Jiran awa biyu yayi kafin ya sami jirgi zuwa Kaduna.
Kai kawo Haj Mara take yi ya shigo rai a bace.
Tasowa tayi tana ganinsa "Alhaji."
"Marakisiyya kinga abinda nake gudu ko? Banda lalacewa yarinyar da zai aura nan da 'yan kwanaki ace yayi mata fyade. Wannan wane irin bala'i ne."
"Alhaji ba ta wannan nake ba yanzu shi kanshi bansan inda yake ba. Na kira wayarsa kullum a kashe."
Cikin takaici ya rike kafadunta yana jijjigata "ina tsammanin Babawo mahaukaci ne kuma a jikinki ya tsotso haukan. Ya za'ayi ina fada miki yayiwa yarinya fyade kice ba"a ganshi ba shi allura ne? 'Yar mutane tana gadon asibiti kin kasa fada min gashi har iyayenta sun shigar da kara"
"Kara??? Na bani na lalace Babawo wace irin rayuwa ka zabarwa kanka" tace tana zama dabas akan kujera.
Alh Sule yace "irin wadda ki ka zabar masa mana. Da ace kin bari mun gyara waccan barakar da abubuwa sunyi mana sauki tunda da bakinsa yace yana son yarinyar zai gyara barnar da yayi"
Hararar Alh Sule tayi rai a bace "kai babu dama ayi zancen Babawo sai ka sako wannan yarinyar. Mawadda, Mawadda dai kamar autar mata. Ana maganar 'yar mutane kana kiran 'yar aiki kazama 'yar kauye"
Hade bakinsa da ya saki yayi cikin mamaki "wato Qareeba 'yar mutane tunda iyayenta suna da kudi. Waccan yarinya Mawadda kuma ba mutum bace saboda 'yar aiki ce? Gaskiya kina da matsala da ke da duk masu yiwa 'yan aiki kallon bayi. Bawa ma Marakisiyya akwai hakki tsakaninsa da ubangida ballantana wadda tazo neman halak da guminta"
"Maganar yarinyar nan ta riga ta wuce da wanne zanji kuma? Yaro ya bata ga kuma wata a asibiti ka tsaya kana dauko min wani zance mara tushe. Har yau bana nadamar kashe maganar Mawadda domin tayi tsararo rayuwar dana ta gurbace saboda ita"
"Da kyau matar Alh Sule Chanji" yace yana tafa hannuwa "sai dai ina son tuna miki dukiya da duk wani abu da kike tunkaho dashi nawa ne ba na uban kowa ba"
Juyowa tayi jiki a sanyaye "Alhaji zagina ka ke yi ko gori?"
"Duk wanda ki ka dauka a ciki daidai ne. Kinga Malama na baki minti shabiyar ki shirya Kano zamu tafi yanzu"
******
Bayan sallama sai da aka bashi izinin shiga sannan Dahiru ya bude kofar dakin da aka nuna masa an mayar da Qareeba.
Tana kwance Dr Tani na bata tea gefe kuma yayunta ne. Najib ya matso kusa dashi fuskarsa dauke da murmushi "Dahiru bamu da bakin gode maka. Allah Ya saka da alkhairi"
Hannu ya mika masa Dahiru ya dago nasa da yake nannade da bandeji babu halin gaisawa.
Faisal da Safwan ma duka sunyi masa godiya Dr Tani ta tambaye shi me ya sami hannun cike da kulawa. Banda 'ya'yan cikinta duk duniya babu wanda ta taba jin ya kwanta mata tamkar ita ta haife shi kamar Dahiru.
Murmushi yayi "Targade ne amma an gyara. Zazzabi ne ya rikeni ban sami dawowa ba. Yaya jikin naku?"
Sakin fuska tayi "da sauki Dahiru"
Ya mayar da kallonsa ga Qareeba da ta kafe shi da idanunta daya da rabi "Anti Qareeba ya naki jikin?"
"Da sauki. Dahiru ba don kai ba da rayuwata ta zo karshe...."
Faisal yace "shhh Sis ki dena irin wannan magana"
Kuka ta soma yi har lokacin Dahiru take kallo "you are my hero Dahiru bazan taba mantawa da kai ba. Tun da na farfado nake neman me zance idan kazo na godiya na rasa"
Murmushi Dahiru yayi ya kalleta da tausayawa "gashi kin kirani Dahiru har sau biyu, ina ganin babu sauran godiya a tsakaninmu"
"Kuskure ne Ahirin my hero nake nufi" ta sake cewa itama tana dariya.
Gabadaya dakin suka sa dariya Dr Tani tana ta jan shi da hira anyi sabon da kuma wannan karon har ranta take nufi don Dahiru yayi mata abin da dole ne ma ta kaunace shi.
Zuwan Dr Auwal hirar ta chanja zuwa karar da ya shigar da kuma neman BB da 'yan sanda suke yi. Dahiru yayi alkawarin tsaya musu shaida a duk lokacin da aka neme shi.
Yadda ya dauki zafi sosai akan lamarin ya sanya Dr Tani tunanin ko dai da gaske yana son Qareeba din ne. Idan kuwa hasashenta gaskiya ne ta kuduri niyar Dahiru ko matansa uku zata bashi 'yarta. Ashe hakan take a wurin itama Qareeban. Soyayyar da bata taba sanin ana yi ba mai zafi ita ce ta kamata akan Dahiru. Kallo daban take yi masa yanzu. Kuma kamar Dr Tani ta ta'allaka taimakon da jin zafinsa da soyayya wanda shi kuma duk yana yi ne idan ya tuna Mawadda ta taba shiga wannan halin kuma tsaninsu ta karshe da zata taimaka musu taci amanarsu a kotu. Bashi da wannan burin, tunda Allah Ya dawo masa da ita har ana kirgen kwanakin aurensu dole ne ya nuna godiyarsa ta hanyar taimakon masu bukata.
*******
Yana barin asibitin Alh Sule da Haj Mara suka iso. An nuna musu dakin suka tafi jiki a sanyaye.
Haj Mara ce a gaba ta tura kofar Dr Tani ta hayayyako mata cikin bacin rai "Marakisiyya kada ki shigo dakin nan don baki da abinda zaki fada min"
Alh Sule ya biyo bayanta ya nufi Dr Auwal ya mika masa hannu yaki mika nasa sai ma kallon banza da yake binsu dashi. Jikin Alh Sule ya sake mutuwa, da mutumcinsa da komai da guda daya ya zame masa wake daya bata gari. Bai daddara ba yace "Dacta don Allah..."
"Kalli 'yata Alh Sule. Dubi yadda Qareeba ta koma a dalilin danka"
Daga shi har Haj Mara sun tsorata da ganin Qareeba. Jikinta ya sha bandeji fuska kuwa sai kayi mata farin sani zaka ganeta saboda kumburi.
Gaban Haj Mara ya fadi har wani jiri ta soma ji saboda yadda ganin Qareeba ya tuna mata da maiaikin da ta tsani jin sunanta da labari a kanta.
Matsawa tayi jikin gadon "sannu Qareeba"
"ALLAH YA ISA ANTI MARA"
Kowa sai da ya kalli Qareeba yadda ta daga murya ta sake cewa "bazan taba yafe miki kuma ina addua duk wata masifa ta duniya ta fadawa Babawo"
Turus ta tsaya tana bin mutanen dakin da kallo "Tani kina jin Qareeba za ta yi min rashin kunya"
"Rashin kunya ta wuce wannan dan akuyan da yazo ya kaita har gadon mahaifiyarta zaiyi mata fyade? Idan baki fita daga dakin nan ba zaki ga rashin mutumci irin wanda baki taba tsammani ba"
Ja da baya tayi wai yau ita Haj Mara wadda maza da mata suke tsoro itace matar da ta rainawa wayo a baya take fadawa magana haka.
Alh Sule zai yi magana Dr Auwal yace dashi "kaga ka dauki matarka ku tafi kawai zamu hadu a kotu idan an kamo shi."
"Ba don wayarka ba ko da wasa bansan abinda yake faruwa ba Dacta kayi hakuri muyi magana"
"Babu fa abinda zaku ce da zai sa mu janye karar nan"
Haj Mara tace "Allah ko? To bari kaji in fada maka idan baku janye ba Dr Tani sai ta rasa wannan aikin da asibitin saboda shaidar karya da tayi a kotu."
Tsananin bakinciki ya kama Alh Sule "yanzu ina kokarin shawo kan matsalar kina kawo wani zancen banza daban"
Ido a soye tace "Yo me ya rage min Alhaji? Ka tsaneni ka tsani dana. Gara tun wuri na fada mata idan tana son ganin bayana ne sai dai mu ga bayan juna."
Dr Tani ta tako gabanta kamar me neman wani abu sai ji suka yi ta taske Haj Mara da mari dakin gabadaya ya dauka. Dago kai tayi a kufale Dr Tani ta sake kara mata a dayan kumatun
"Marakisiyya ni dake shege ka fasa. Da kika ganni nan ko zanyi bara na rantse da Allah sai naga karshen dan mahaukacin yaron nan naki. Kudi ne dai kike takama dashi ko? Kin dade da sanin daga gidan da na fito nafi karfin tunkaho da dukiyar gaibu dukiyar miji. Idan kin cika ki tareni gaba da gaba in kudi ne zai bada nasara a kotu kin sani na fiki, idan kuma shaidu ne to dama a tafin hannuna kike."
Tsananin mamaki da gigitar mari yasa ta rike kumatun duka biyu "ni ki ka mara?"
Dr Auwal ya dubi Alh Sule "ka fitar da matarka daga asibitin nan haka Alhaji"
Matsawa yayi daga kusa da ita kamar wata abar kyama "Ina ganin lokaci ne yayi da zanyi abinda ya dace game da ita. Marakisiyya kin tuna lokacin da na fada miki akwai ranar da zaki girbe duk tsiyar da kika shuka? "
A matukar tsorace tace "Alhaji kada ka sakeni don Allah"
"Alfarma daya zanyi miki mu koma Kaduna tare ki kwashe kayanki zama dake bashi da wani amfani sai tarin bakinciki"
Kallonsa ta jima tana yi kafin ta hade rai sosai "a gaban makiyana ka wulakanta ni me zai sa na bika, sakina nawa kayi min?"
"Babu sauran zama tsakaninmu"
Su Safwan da suke gefe suka yi zuru zuru suna kallonsu. Dr Tani ta tabe baki ta koma ta zauna sai Dr Auwal ne ya iya cewa yayi hakuri su tafi tare.
Shima harara ta buga masa ta fice kamar zata tada kura. Alh Sule ya kwantar da kai duk da yadda yake ji ya cigaba da basu hakuri "idan rufe Babawo ne zai kawo karshen fitinarsa Dacta zan baka dukkan goyon baya. Dana ne kuma wallahi ina son sa amma bazan zuba masa ido ya cigaba da lalata 'ya'yan mutane ba."
Fita yayi bai tarar da Haj Mara ba ta sami tasi ta tafi tasha. Mota daya tayi shata sai da ta zauna ta shiga kuka sosai. Dreban yana ta tambayarta ko lafiya bata tanka masa ba ya gaji ya rabu da ita.
Har gida ya kaita ta ciro kudinsa ta bashi ta shige maigadi yace ina Alhaji harara ta bashi amsa. Kayanta taje ta hada wanda zata iya hadawa a lokacin ta duka karkashin gado ta dauko kit dinta. Komai mai mahimmanci kama daga kudade, gwal da takardu suna ciki.
Daukar mutumci tayi masa saboda tasan yana da nauyi sai taji abu sakayau. Zuciyarta ta harba ta dire shi akan gado hannu na rawa ta bude. Kasa ta fadi wanwar saboda tashin hankali. Fanko haka ta same shi ko kura babu.
"BABAWO!!!!"
******
Biki ya gabato inda Haj Mama da Baba Prof suka nuna bajinta sosai. Su wannan ne bikinsu na karshe saboda Attahir ne auta. Shima kuma Dahiru shine karshen aure a nasu gidan kannensa biyu sun riga shi. Saboda karamci da dattako ko a jikin katin Mother's Eve an rubuta sunayen angwaye biyu, Attahir da Dahiru. Wannan abu yasa masa kara son mutanen da jin nauyinsu. Yadda baya gajiya da yi musu godiya da addu'a haka ma su Inna da Baffa. Su kuwa sai dai su ce da na kowa ne baka san wanda zai ji kanka ba nan gaba.
Kowane ango an bashi katunan da zai kaiwa dangin amaryarsa saboda wurin taro sai da kati ne. Babbar 'yar Baba Prof ita ta dinka musu kayan da zasu saka iri daya. Karshe Dahiru har hawaye yayi yana ta addu'ar kada Allah Ya bashi ikon cutar dasu ko daidai da kwayar zarra. Ya san yadda zamani ya canja yanzu sai ka taimaki mutum ya zame maka alakakai. Ka nufe shi da kyakkyawar zuciya idan ya sami sukuni kaine mutum na farko da zai bakantawa musamman idan naka karfin ya kare. Wani ko labarinsa ma bazaka kara ji ba likkafa taci gaba. Saboda irin wannan hidima da ake yi musu Inna da Baffa suka ce ko bayan ransu idan Dahiru ya butulcewa wannan iyali basu yafe masa ba.
Sannan fa suma ba'a barsu a baya ba. Buhun wake uku, kwandunan tumatir da tattasai da albasa wanda kila har a gama bikin ba sai sun nema ba haka suka kawo musu. Ga su gero da kabewa tuli guda. Lallai kyautatawa abar so ce kuma babban tsani na samuwar farinciki ga mai yi. Babbar bukata ka nufi Allah da kyakkyawar zuciya babu gori ga wanda aka kyautatawa kuma babu saka tsammanin za'a ramawa kura aniyarta.
Zuwa yanzu Mawadda da Nawal sun kulla zumunci da juna duk da basu taba haduwa ba amma suna waya har hotunan juna sun gani. Su ma kowacce nata dangin suna ta shiri ne domin fita kunya.
Anje anyi jeren Mawadda kayanta babu karanta babu karya. Duk wani abu da ya kamata iyaye su yiwa 'yarsu mace nata iyayen sun kamanta. Idan ka duba 'yan uwanta dole kace Mawadda ta wuce zarra domin kuwa ita kusan da biyu ake mata komai. Wanda ya auri 'yarka da duniya take gudu saboda laifin da bai zama nata ba ya cancanci godiya. A wurinsu kuwa godiya idan ta wuce ja wa 'yarsu kunne akan ladabi da biyayya to fa sai fita kunyar juna su nunawa duniya bata wulakanta ba ko da aka juya mata baya Allah Ya tsare bayinSa.
Katin daurin aure bugun farko sunan wani masallaci a nan unguwar tasu aka saka. Sai kuma abin dadi abin mamaki kanin Mal Fatihu yazo gidan tare da wasu dattawa su uku da Maigari ya wakilta akan ya bada umarnin aje fadarsa a tsakiyar garin Tariwa a daurawa Mawadda da Dahiru aure. Suna fadin sakon Baba yasa kuka.
Guda cikin 'yan aiken yace "Mal Fatihu nayi zaton zaka yi farinciki da wannan abu"
Hankici yasa yana goge ido yana murmushi "Mal Uba burina ne ya cika. Ban damu da auren Rafi'a da nayi a nan ba. Amma kaga Mawadda, saboda Mawadda kowa ya tsanemu har ana ikirarin cinnawa gidana wuta. Saboda ita aka yi mana iyaka da mahaifarmu mu duka. Yau gashi saboda ita zamu koma. Kullum kukanta idan ta tuna da gida shine ta janyo an rabamu da 'yan uwanmu tana ganin ita ce silar komai."
Wani mai suna Muntari yace "ka godewa Allah kuma ka yafe mana. Maigari yace shine zai yiwa amarya walicci idan ka amince domin dinke barakar da aka samu a baya"
Shi kuwa Mal.Fatihu idan ba yasha giyar wake ba me zai cewa Maigarinsu. Mutumin da ya ceci rayuwarsu kuma ya basu muhalli harda yafe kudin haya na wata shida. Abinci yasa aka dafa musu aka karramasu karshe sannan yace a sanarwa Maigari ya bashi wuka da nama. Alfarma daya yake nema akwai dan uwan Dahiru wato Attahir da za'a fara daura nasa auren a ranar. Suna son a kara kamar awa hudu ko zuwa azahar ne ayi na Mawadda saboda kowa ya sami halarta.
Baki na tafiya ya sanar da iyalinsa. Kowa kuka musamman Innarsa wadda ta tuno rabonta da garin tunda ta fita takabar Malam mahaifinsa.
Daki Mawadda ta shige tayi sujjadar godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Wayar Dahiru ta kira cike da zumudi ta fada masa.
"Zan ajiye miki tukwici babba saboda na fiki farinciki. Burina dama na nunawa 'yan garinmu ina son Mawadda duk runtsi duk wuya"
"Nima ina son Dahiru duk runtsi duk wuya"
Wayar ya kankame kamar ita ce a gabansa "maimaita don Allah"
Tana murmushi tace "Me zan maimaita?"
"Mawadda manaaaa pleaseeee" yace yana jan kowane harafi a kasalance
Mawadda sai da taji bugun zuciyarta ya karu ta daure tace "Yayanmu mata ne ke shagwaba fa a iya sanina. Amma kai naga alama Inna tasha fama."
"Gara ma ki shirya tarihi yazo min ance kyuya ce dani da son jiki."
"Kada ka damu bazan rinka saka ka aiki ba kasha zamanka da son jikinka"
"Assha, ba kya ganewa. Son jiki fa irin wanda zanyi ta makale miki dinnan. Duk inda ki ka zauna ina kwance a jikinki"
Bata san Dahiru ya kware a iya bata kunya ba sai yanzu. Ta dan cije lebe tana tunani sannan tace
"Ban ma san me kake cewa ba. Kasan nakan kurmance lokaci zuwa lokaci sai abinda kunnen ya ga dama yake ji....hello, hello, Yayanmu bana ji ka sake kira"
Yana dariya yace "idan ki ka ajiye wayar nan zamu yi fada Mawadda. Ki saurareni kawai ki tsinci na tsinta ki bani amsa"
Turo baki tayi da nata salon shagwabar
"me yasa ma