Showing 45001 words to 48000 words out of 110071 words
don yasan dalilin fushin "matar Yaya kinsan babban wa uba ne matarsa kinga ta zama uwa. Fushin me kike yi dani kuma yau"
Ta kula wani nishadi ma yake yi tayi kwafa "nagode da wulakanci Dahiru. Wai kai kayi kudi kana nuna min iyakata"
"Assha me kuma ya kawo wannan maganar don Allah" ya fada murmushi na bayyana a fuskarsa mai nuni da rashin damuwa da fushin nata.
Hakan ya kara kular da ita "ba laifinka bane, laifina Hansa'u ne da ta dage sai kai. Tukwicin da ka ga ya dace ka bani kenan duk wahalar da muka yi da kai lokacin karatunka ka guji kanwata ko"
Hakuri ya bata don wannan rigimar kullum ya shigo sai anyi. Saboda shi kanwarta gidan ma ta dawo amma idan ka cire gaisuwa baya yarda wata hira ta hadasu. Ya tabbatar baya sonta bai ga dalilin sanya mata burin karya ba.
Tare da yayansa suka yi sallar magariba sannan yaci abinci ya tafi gida.
A daren yayi ta kiran Mawadda wayarta chaji ya kare kuma da ta dawo gida ta nemi chaja ta rasa. Haka nan taji babu dadi don tana tunanin da wuya idan Dahiru bazai nemeta ba. Yadda ta damu da rashin chajin har Ade sai da tayi magana tace ko akwai kiran wanda take jira ne. Wannan maganar ce tasa ta jin kunya ta hakura ganin an soma yi mata dan biki.
*****
Washegari ta kama lahadi Dahiru bazai je office ba. Baba Prof ne ya gayyace shi rakiyar daurin aure suna dawowa yace masa lallai ya wuce gidan Dr Auwal yau su gaisa da mutan gidan.
Bazai taba iya ketare maganar Prof ba shiyasa bayan ya kaishi gida ya tsaya. Horn yayi maigadi ya bude suka gaisa ya fada masa yazo wurin masu gidan ne. Maigadi ya ga babban mutum irin wannan ba wata-wata ya bude masa.
Shigarsa ke da wuya wata motar ta shigo. Matsawa yayi wurin mutumin da ya fito daga ciki ya mika masa hannu suka gaisa.
"Kamar nasan fuskar nan"
Dahiru yace "Safwan ko? Dahiru ne mai wanki da shara"
Idanu Safwan ya ware ya shiga zagaye Dahiru sannan ya saki ihu "Ahirin kaine? Tabdi, muje ciki"
Sun shiga korido da zai sada su da kofar falon Safwan ya rike masa hannu yana ta zuba surutu Dahiru ya tsaya daga bakin kofar.
"Ya haka muje mana"
"Ka shiga ka fara sanar dasu. Bai dace na shigo kai tsaye ba"
Safwan yace hakane ya shige da sauri yana ta mamakin ganinsa.
Dr. Tani tana yanke farce da nailcutter ya shigo ya zauna a gefenta.
"Mummyna..."
Dadin ganin autanta tayi yayi fes dashi ga uwar kiba yana ta hadawa.
"Ka ci abinci kuwa?" Ta tambaya don tasan matarsa da kyuyar girki ita kuma bata yarda danta ya wahala ba.
Kamar wani wawa irin maganar shagwababbu yace "Kai Mummy kema kinsan naci. Tun ranar da ki ka fada mata idan bata soya min chips da kwai yadda nake so zaki sa nayi mata kishiya ta canza. Yau ma shi tayi min da safe"
Dahiru yana jinsu ya girgigiza kai "ana jika har yanzu"
Kamar Safwan ya jiyo shi ya buga tsalle ya mike "Mummy albishirinki"
Murmushi tayi a zatonta ko jika zata samu "goro fari kal"
"Tare muke da Dahiru. Dahiru mai shara da wanki!"
Wani uban tsaki ta ja har zuciyar Dahiru.
"Me kuma ya kawo shi? Shi kadai ne ko an rakito iyali daga kauye a fake da zuwa gaishemu nan kuwa yawon maula ne"
Safwan ya kece da dariya "Hmmm baki ganshi bane tare muke yana bakin kofa bari na shigo dashi"
Rai a bace ta kai masa duka "kai meyasa kake abu kamar wawa ne. Ya zaka kawo min shi nan. Yana shigowa falon nan zai soma tashin warin rana kuma kasan Daddynku yana gida yanzu zai hau fada. Kace ya koma daga waje gani nan zuwa"
Ran Dahiru yayi bakikkirin. Da Allah bai daga shi ba yau baisan inda zaisa ransa ba wannan wulakanci. Wato kallon da masu kudi suke yiwa talakawa 'yan kauye kenan. Idan sun zo ba'a taba zaton alkhairi ya kawo su sai maula. Ficewa yayi ya koma mota abinsa kamar ya tafi sai wata zuciyar tace ya zauna. AC ya kunna ya rufe kansa ya dauko waya yana kallon numbar Mawadda. Kiranta yake son yi ta bashi dama yaje gidansu su gaisa yaji yadda rayuwarsu ta kasance.
Dr Tani tare da Safwan suka fito tana ta yatsina hanci. Idonta ne ya sauka akan motar tana cikin cewa ina Dahirun yake. Bata ankara ba ta ga wani mutum ya fito daga motar da ta dauke mata hankali. Kallonsa tayi daga sama har kasa babu abu mara tsada cikin suturarsa.
Yadi ne a jikinsa ruwan madara sai hula da takalmi ruwan toka. Kamshin turarensa har inda take tsaye.
Dahiru ya tako har kusa da ita ya duka "Hajiya barka da rana"
Wayyo dadi jiki na rawa tace "Safwan jeka ka taso Qareeba tayi bako"
Dariya ce ta kama Dahiru yadda yaga tana yi duk ta rude halinta bai chanja ba na son aurar da 'yarta . Ganin haka ta dan nutsu tana kallonsa. Sai ya wayance "Hajiya dadin ganinku ne kawai. Baki ganeni ba ko. Dahiru ne mai wanki"
"Laaaaaaaa" ta hangame baki cike da tsananin mamaki mara misaltuwa. Sai kuma ta sake kallonsa ta kalli motar "shine ka tsaya a waje Dahiru kamar wani bako kai da gidanku? Safwan ma dai wani lokacin ba ya aiki da tunani. Me zai sa ya barka a waje"
Ba don da kunnensa yaji ba kila da shikenan sai ya zata har zuciyarta hakan ne.
"Nan ma yayi Hajiya dama nace bari nazo mu gaisa ne zan wuce"
Dan shan kunu tayi "haba Dahiru ka shigo ku gaisa da Daddynku mana"
Mutum mai fuskoki ya fada a ransa. Bayanta ya bi duk ta gigice saboda yadda ta ganshi. Mai aiki ta kira tace maza a soya kaza a hado masa fruitsalad da juice mai sanyi. Ta nuna masa kujera tace ya zauna yace kasa ma yayi ya zauna a kan kafet.
"Dahiru shiru kuma shekara da shekaru ka manta damu" a matse take taji yadda akayi ya sami wannan cigaba amma ta daure kada ta nuna hali.
Gudu suka ji daga bene Qareeba da Safwan suna rige rigen saukowa. Daga ita sai riga da wando na bacci domin kuwa shigar Safwan ya tayar da ita sai hula da ta saka.
"Dashiru Ahirin!"
Ai kuwa sai da gabansa ya fadi saboda tunawa yayi da yadda take matsantawa rayuwarsa a baya.
Kusa dashi taje ta zauna tana ta tafa hannu.
"Ahirin kaine haka? Mummy kin gani"
Dr Tani tayi murmushi "na gani bari na taso Daddy yazo ku gaisa".
Tana tashi su Qareeba suka shiga bugawa 'yan uwansu waya wai ga Ahirin yazo ance mata da mota. Sai da ta leka ma ta ganewa idonta ta dawo tana ta damunsa. Shi kuwa kallo daya yayi mata tun saukkwarta ya sunkuyar da kai. Idan ba ballagaza ba ga kiba ta soma yi ta fito da kaya irin wannan duk motsinta jiki na rawa. Kuma a haka mahaifiyarta ta gani amma ko a jikinta.
Ba jimawa sai ga Daddy da Dr Tani. Shima ya nuna farincikin ganinsa har yake tambayarsa me yake yi yanzu. Kunnuwa Dr Tani a nbude taji yace yana aiki da kamfanin sadarwa na Etisalat.
Kasa daurewa tayi tace "amma kace mana zaka tafi munyi zaton kana kauye Qareeba kusan kullum sai tayi min zancenka"
Daddy ne ya take mata kafa don ya soma fahimtar daga nan ina ta dosa.
Dahiru yace "lokacin scholarship na samu na tafi Turkey masters"
"Wow! Ahirin Turkey fa kace. Can birnin Turkiya dai da na sani? Wowwww gaskiya big wowww ni Ghana Daddy ya turani ba rabon mu zauna wuri daya. Kasan nima can na nemi admission da farko" inji Safwan
Qareeba abu ya burgeta cewa take "tun haduwarmu ta farko nasan kai na daban ne. Shiyasa fa nake cewa Mummy ta dena maka wula...."
"Toh, toh, toh a tashi haka ku barshi ya sha iska" Daddy yace ganin za'a fara rashin hankali. Dr Tani tana kitchen ita ta karasa suyar kazar.
Ana kawowa ga su fruitsalad tray cike taf da kayan alatu na tarar bako Dahiru ya mike abinsa ko ruwa bai sha ba.
"Hajiya nagode amma cikina a cike yake"
Duk yadda taso yaki zama. Ba fariya yake son yi ba amma irin wulakancin da ya kunsa a zama dasu shi kadai ya sani. Kuma nata yafi masa ciwo tunda ita duk a cikin kyamar talaka ne. Yau daya komai ya chanja saboda ya zama wani.
Abin mamaki har waje ta rako shi tare da yaranta suna ta daga masa hannu ta ce ya rinka zuwa don Allah zumunci dadi ne dashi.
******
Tun asubar fari Haj Mara ta tashi ita da masu aikinta biyu ana ta gyaran gida Alhaji zai zo weekend. Ya sake samun budi fiye da shekarun baya yayi suna a Nigeria sosai ta fanin sana'arsa ta chanji.
Tsakaninsa da Haj Mara ba yabo ba fallasa. Kudi dai da sauran nauyin da yake kansa yana matukar kokarin saukewa amma fa sai yayi wata biyu bai zo Kaduna ba. Gida daga ita sai masu aiki bata jindadi ko kadan tace zata dawo Lagos yaki amincewa. Wata rana tayi masa zuwan bazata a tunaninta kadagarun bariki yake ajiyewa ta ga babu kowa don ba zama yake sosai ba a nan din amaryarsa tana Abuja. Tafiye tafiye ne dai ta rasa gane ina yake yawan zuwa kullum ka taba shi yace baya nan. Tayi fadan tayi mitar har ta gaji. Shi kuma yace idan tana son gida ya dawo daidai ta dawo da BB daga inda ta tura shi taki amincewa.
Anyi girke girke gida yasha turaren wuta taci ado ana jiran mijin da ta dade tana kewa kusan wata uku.
Tana zaune taji horn ta tashi ta koma dakinsa ta hada masa ruwan wanka tare da fesa airfreshner mai dadi. Bude kofar dakin tayi zata sauko kasa shi kuma ya shigo rike da hannun wata ga yara uku maza a bayansu.
Zaro idanu tayi ta ja da baya ta ga iya gudun ruwansu sai gani tayi ya taimakawa matar ta kwanta akan gadon da ta gyara da kanta ya rufa mata bargo.
Ya juyo "Hajiya ashe kina nan "
Yaran ya nunawa kofa yace su koma kasa su bar Mama tayi bacci yana zuwa. Babban cikinsu ya kama sauran biyu suka fita.
Haj Mara fa jin kanta take kamar ba ita ba. Me yake faruwa ko mafarki ne take yi?
Alh Sule ya katse mata tunani "Hajiya sauko kasa muyi magana"
"Kana son ganin haukana ne a gaban wadancan yaran ko me? Malam idan kana da abin fada ka fada min a nan kafin ka ga ba daidai ba"
Matar dake kwance akan gadon tayi juyi tare da mikewa a guje ta shige inda take tunanin bandaki ne tana kwara amai.
Bayanta Haj Mara ta bi "ni zaki yiwa bariki a cikin gidana? Kinsan a ina kike kuwa?Alhaji kalma daya nake son ji daga gareka indai ba ka fara shaye shaye bane wace 'yar....din ce wannan?"
"Matata ce" ya fada a takaice sannan ya wuce cikin bandakin yana yi mata sannu. Ruwan wankan ya taba yaji bai huce ba yace tayi wanka. Yana rufe kofar bandakin Haj Mara tana cakumar wuyansa.
"Wadancan shegun 'ya'yanka ne?"
Hannuwanta ya kama ya yarfar ya nunata da yatsa "jinina ne kada ki sake zagin kowa a nan. Ki wuce muje nace ina da magana dake"
Har wani haki take yi na tsananin bacin rai ta sauko nan ta sami 'ya'yanta mata zaune tare da yaran da Alh Sule ya shigo dasu.
Sun gaishe da mahaifinsu yana tambayar kowacce iyalinta sannan ya fara musu jawabi.
"Nasan zakuyi matukar mamaki idan nace muku yaran nan kannenku ne mahaifiyarsu tana sama mun taho bata jindadi. Kuyi hakuri da rashin sanar daku da nayi hakan ya biyo bayan fushin da nayi lokacin da Babawo ya yiwa yarinyar nan fyade ku kuma duka kuka biyewa mahaifiyarku akan marawa karya baya. Duk da haka nasan ban kyauta ba amma ina so don Allah ku bani hadin kai wurin ganin na hada iyalina yadda ya dace"
To su dinma sun dade da dawowa daga rakiyar Hajiyan tasu shiyasa suka bashi hakuri tare da nuna masa in sha Allahu zasu rike kannensu.
"Hajiya baki ce komai ba" ya waiga inda Haj Mara ta zauna sai dai babu ita babu alamunta.
Hayaniya suka ji daga sama ya tashi da sauri yace su jira yana zuwa.
Haj Mara tunda yace yayi auren nan ta koma dakin. Matar na fitowa daga bandaki ta daga hannu ta wanka mata mari sannan tace
"idan ma wani salon karuwancin ne ya hadaku kizo ki fita tun wuri. Nasan Alhaji bazai taba aure bai fada min ba don ban bashi wannan damar ba"
Murmushin gefen baki matar tayi tace "ashe?"
Sannan ta wuce ta zauna kan kujerar gaban madubi ta janyo man da hannunta ya fara tabawa ta soma shafawa.
Haj Mara ta daka mata tsawa "ba dake nake ba?"
"Bana son ihu kinga ba lafiya gareni ba"
"Eyyeeee sannu kwankwararriya ke nifa wanda ya ajiyeki ma bai isa ba"
Tashi tayi ta mikewa Haj Mara tsayinta "wanda ya ajiyeni ya isa kuma idan kika nemi tayar masa da hankali wallahi zan baki mamaki. Yanzu ma ra'ayin kaina ne naga ya dace yarana su san 'yan uwansu har ki ka ganmu. Kinyi sa'a laulayi ya sakani a gaba kuma bani da burin da ya wuce farantawa mijina da na nuna miki matsayinki a gidan nan"
Zuciya ce ta debi Haj Mara tana ihu ta kai mata duka irin na mahaukatan nan. Zata rama Alh Sule ya shigo kawai sai ta bage a kasa harda kwance tawul ta soma kuka.
Alhaji na zuwa ya ture Haj Mara ya janyo matarsa ya rungume.
"Sannu Yasmin babu inda ke miki ciwo? kwanta bari na dauko miki jakar kayanki."
Sakato Haj Mara tayi ganin wannan abu yarinyar da bata fi sa'ar 'yarta ta biyu ba ta wani lafe a jikinsa ga tawul dinta yana reto ya kusa faduwa sai karairaya take shi kuma duk ya gigice.
Yana juyowa marin Haj Mara yayi "idan wani abu ya sami cikin nan sai na bata miki rai. Wannan rashin hankalin na gaji da dauka. Duk da nima nasan da laifina akan kyaleki da na rinka yi amma ki sani wallahi baki fi karfina ba"
Bayan Yasmin ta shirya ya sake hadasu duka a falo. Haj Mara sai kukan zuci ta rasa me yake mata dadi.
"Kamar yadda ku ka sani shekaru takwas rabon Babawo da kasar nan. Hajiya ta tura shi kasar waje nayi nayi harda ku nasa ku tambayeta amma tana ganin kamar cutar da dan cikina nake son yi taki fada mana inda yake. To Alhamdulillah Allah Yasa nasa an nemo min shi ta hanyar binciken account din da kika rinka tura masa kudi. Duk abinda Babawo ya zama a yau sai muyi hakuri mu rungume shi tare da fatan shiriya"
Haj Mara na jin haka ta mike tsaye "yana ina?"
Zuwanta Dubai uku inda ta tura shi amma bata samunsa. Idan ta matsa masa da tambayar yana ina sai yace tafiya ce ta kama shi. Abinda bata sani ba shine ko wata shida baiyi a Dubai ba ya koma Italy.
Sai bayan kusan rabin awa BB ya iso gidan. Haj Mara ta manta da batun kishiya danta da take ta kewa take jira. Karar bude gate taji ta fito cikin sauri Alh Sule ya girgiza kai. Wannan makauniyar soyayyar da take yiwa danta ba gata bane gare shi ko kadan.
Motar bata gama tsayawa ba ya duro waje ya yo kan Hajiyar tasa yana ihun murna.
"Yooo, yooo Hajjaju meen.....see my Maama looking gorgeous"
"Na shiga uku" Haj Mara ta furta a hankali kwalla na sauko mata.
Wai yau Babawo da take mugun ji dashi ne haka sanye da wani mahaukacin jeans mai mugun fadi duk an gutsire kansa da kyar ya wuce gwiwa. Ga takalma kamar wanda zai shiga daji farauta manya manya. Rigar fara ce ta dame kwanjin da ya tara abin takaici da bakinciki yana sanye da sarkoki, dankunne ga gashi yayi kalba har kafada.
******
Kusan minti goma da zuwan Dahiru layin gidansu Mawadda yana ta tunanin kiranta zaiyi yace yazo ko kuwa ya tafi daga baya ya kira yace zai zo?
Can dai wata zuciyar tasa ya kirata. Gidan da sauran 'yan biki amma saboda gajiyar da suka yi tana daki a kwance kan gado. Yaya da Ade suna ware kayan gudunmawa saboda idan basu hadasu wuri daya ba wasu sai su salwanta gida na taro.
Tana jin waya tayi zumbur ta tashi zaune ta dauka tare da ficewa daga dakin ta koma kitchen.
Sallama tayi ya amsa mata sai kuma duk suka yi shiru sai bugun zuciyoyi.
"Ina cikin layinku fa. Zaki iya fitowa mu gaisa?" Ya katse shirun nasu.
Abin yazo mata a bazata sai kuma ta fara tunanin me zata ce a gida.
"Kunya nake ji Yayanmu"
Yayi 'yar dariya "nima haka Mawadda"
Suka sake yin shiru kamar wasu sabon shiga.
"Ina zuwa" taji yace sai ya kashe wayar.
Tunani ta fara me zaiyi ya kashe wayar sai ji tayi wani yaro yana cewa wai ana sallama da Baba inji Dahiru.
Gabanta ne ya fadi lokacin da Inna tace ace yana zuwa. Ita aka kira taje ta fadawa Baba ya fito yana cewa basuyi da kowa zai zo ba. Ita dai shiru tayi har ya fita. Yanzu jikinsa yayi lafiya sosai duk da shanyewar barin jikin amma yana zuwa gashi sosai yana iya tafiya da wasu abubuwan da kansa.
Daki Mawadda ta koma tana ta tunanin ya zata kasance.
Mal Fatihu yana fita Dahiru ya iso kofar gidan ya durkusa a gabansa. Har suka gaisa bai gane shi ba saboda kansa na kasa.
"Samari sai dai kuma ban waye ka ba"
Dahiru ya dago kai "Baba nine Da..."
"Dahiru? Laila ha illallahu kaine kuwa. Ikon Allah tashi tashi don Allah. Muje daga ciki"
Sosai mamaki ya kama Baba. Yana son Dahiru ko don yadda ya nuna soyayyarsa ga Mawadda a lokacin da ta rasa masoya.
Gyaran murya Baba yayi yana ce musu su gyara fa shi da bako ne. Ade ta kira Mawadda "yi sauri ki gyara dakin soro babanku yayi bako"
Dakin baya bukatar wani gyara saboda yau tun safe gyaran gida akeyi dama kujeru ne a ciki da dan tebur. Tana fita Baba ya shiga dashi yace ta kira su Iya su zo su ga bako.
Dahiru kunya ta rufe shi da ganin su Iya, Inna, Yaya da Ade. Dukkaninsu babu wanda ya nuna rashin jindadin ganinsa duk da yadda basu ji dadin irin rabuwar da