Showing 42001 words to 45000 words out of 110071 words
sosai yace zata yi wata batare da wani magani ba domin su tabbatar da samun lafiyarta.
"Alhamdulillah Mawadda wannan sauki daga Allah ne da kuma dagewarki wurin shan magunguna da yin kegel exercise yadda ya kamata. To sauki ya samu sai maganar aurenmu ko?" Ya daga mata gira.
Kai ta girgiza tana murmushi "kayi ka gama. Tare muke da Baba yana wurin karbar magani na barka lafiya"
"Mawadda meyasa kike min haka ne?" Ya fada a sanyaye.
Dan hade fuska tayi "saboda kasan komai game da ni Dr Imran. Babu wani dalili da zaisa kai ko wani yayi sha'awar aurena. Sannan....kasan burina na rayuwa har yau bai cika ba"
Cewa yayi zai kirata kawai don idan suka fara wannan muhawarar zancen baya taba karewa. Kafiya ce da ita sai kace irin mutanen farkon nan. Akwai ranar da ya zolaye ta ma yace da a wancan zamanin tazo irinsu ne suke yin riko da manyan gumaka a kasa chanja musu ra'ayi. Baya mantawa ranar ne ta fara sakin jiki dashi saboda dariyar da ya sakata sai dai gashi har sun bawa shekara baya babu wani cigaba.
Wurin Baba taje ya gama karbar magani da Saifullahi suka fito suka tafi.
Mawadda Fatihu kenan matashiya yar kimanin shekaru ashirin da biyar. Taga rayuwa ita da gabadaya ahalin gidansu a dalilin fyade da akayi mata a gidan da take aiki.
Bayan dawowarsu Kano sunyi ta fadi tashi har Allah Ya buda musu da taimakon Anti Zahra mai gyaran jiki. Matar nan ta riketa da zuciya daya ta koya mata sana'ar gyaran jiki sosai. Da ita take biyanta idan sunyi aiki daga baya cikin ikon Allah ta kware Anti Zahra tace lokaci yayi taci gashin kanta. Sannan ita sun dade da barin unguwar ta koma tudun yola da zama. Suna zumunci sosai har yanzu. A lalace a wata Mawadda bata sami kudi ba ta rike dubu talatin. Budi suka samu na ban mamaki da tasbihi ga Allah. Matan manya da 'yan uwa bata taba rainawa har kasuwarta ta bude haka.
Idan an zo gyaran jiki tana yi Rafi'a na lalle Jamila na kitso. Mal Fatihu sai son barka don kuwa 'ya'ya matan da bai taba rainawa ba sun zame masa babban arziki. Hatta 'yan uwansu na kauye su Nana suna cin arzikinsu.
Shekaru biyar baya Malam kakansu ya rasu amma bai bar duniya ba sai da ya mayarda auren Ade da Baba. Itama ta dena aikatau yanzu sun hada kai da Yaya awara suke yi fin kwano biyar a rana. Marwanu da Saifullahi sun koma makaranta almajirai ke jigilar fita da awara mai sauce da ta sami karbuwa sosai.
Kanen Mawadda na wurin Ade suma bata barsu ba tana tura musu kudin makaranta. Gabadaya ta sauya ta koma Mawadda cikakkiyar mace mara tsoro wadda burinta daya yanzu a duniya shine tayi ido hudu da Haj Mara da rabin ranta BB.
Innar Fatihu da Iya sun kara tsufa amma duka gida daya suke. Gidan Mal Fatihu na kauye sunyi kakara da Maigari ya karba suka yi masa ciko suna biyansa a hankali yanzu gidan Tunga ya zama nasu.
******
Tun kafin ya fito daga motar yara sun yanyameta suna ta shafawa ana kiran sunansa. Wata leda ya dauko a gefensa cike da kayan kwalama na yara ya bude motar ya fito. Kamshin turarensa da sanyin ne suka biyo bayansa. Rufe motar yayi ya shiga rarraba musu suna karba ana murna.
Daga cikin gida Innarsa tana jinsu ta soma fara'a tasan ya iso. Shima sauri yayi ya shiga gidan wasu matasa biyu suka biyo shi da akwatinsa da wata katuwar jaka.
Inna ta tashi tana tafi farincikinta baya buya "marhabin lale lale da mutanen ya ma sunan kasar...?"
Dahiru yayi 'yar dariya yana durkusawa a gabanta "Inna na sameku lafiya?"
"Lafiya lau Dahiru....oh ni Indo tafiyar wata biyu shine ka sake cika haka duk ka zama wani basamuden kato."
Ai kuwa ta saka shi dariya sosai. Muryarsa ma ta kara zama ta manya baka ce Dahiru saurayin Mawadda bane mai aikin kubewa a gona.
Baffa ne ya shigo suna tsaye Inna tana ta yiwa Dahiru tsiya yace ta barshi ya huta mana.
Bayan Isha suna hira da iyayensa Inna ta soma mitar rashin aurensa.
"Sai dai kaci banza kaci wofi aje iyali ya gagara" cewar Baffa
Bangaren da aka gyara masa da sunan zama da Mawadda ya kurawa ido yana tunani. Inna ma wurin ta kalla wanda Danlami ne daga baya ya ajiye matarsa kafin su koma cikin gari suma.
"To....to an tabo inda yake masa kaikayi ya lula duniyar tunani" Inna tace tana nunawa Baffa yanayinsa.
Tashi yayi bai kara magana ba ya shige dakin da ya sauka zuciyarsa duk babu dadi. Ina Mawadda take? Ina zai kara ganinta? Kuma a wane yanayi.
Bayan tashinsa Baffa yayi ajiyar zuciya. Tsahon shekarun nan basu taba sanar dashi Maigari ne ya basu gida ba saboda haka za'a iya gano inda suka koma. Hana karya lokacin rasuwar Malam ance masa Mal Fatihu yazo jana'izar mahaifinsa amma ko kwana baiyi a kauyen ba. Shi kuma lokacin baya gari sunje Kano daurin auren 'yar Baba Prof ne.
Rayuwar Dahiru ta dade da sauyawa tun bayar hduwarsa da Prof Abdulhadi. Mutumin ya amsa sunansa mutum ta kowace sigar kwatancen halin kwarai. Bayan ya daukarwa kansa biyan kudin makarantar Dahiru yakan taimaka masa da ihsani. Shi kuma Dahirun sai ya mayar da hankali sosai kada ya bashi kunya. Anyi sa'a kuwa sakamakonsa ya rinka kyau yana gama aji biyar ko bautar kasa bai tafi ba Prof ya samar masa tallafi wato scholarship aka tura shi Turkey karo ilimi. Yaje yayi masters dinsa ya gama cikin shekara daya da rabi. Wannan kudi da ya samu dasu ne ya rinka taimakon iyayensa. Gidansu yanzu idan ka dade baka garin sai yayi maka wuyar gamewa. Yayi masa gyara dan gaske don ma Baffa ya dage bazasu bar garin ba.
Bilya shima likkafa taci gaba yana da nasa garejin har 'yar mota ya saya. Danlami kuma sana'ar busasshen kifi yake wanda yake zuwa kudu ya saro kala kala ya kawo. Yana nan da teburinsa har wuri biyu a kasuwar sabon gari. Ummiyo tayi aure harda yara uku. 'Yan uwanta maza sune gatanta don bata rasa komai.
Dawowar Dahiru kasar ke da wuya ya sami aiki a kamfanin Etisalat. Abu ne da ba zato ba tsammani wani abokin karatunsa ya takura masa suka cike form online. Ashe kawunsa wani babba ne a kamfanin sai gasu suna isowa ba jimawa aka basu offer shi yana Kano abokin nasa yana Lagos.
Haka Allah Yake abinSa Ya baka a lokacin da baka zato bare tsammani. Yanzu haka wani aiki aka tura shi Qatar na wata biyu shine ya dawo jiya ya wuto Kano yau.
Da tunani kala kala ya kwana washegari lahadi da yamma yace zai koma saboda baije ofishinsu ya yi reporting ba. Inna dai tunin aure tayi masa da barazanar idan baiyi wasa ba watarana zai dawo ya tarar da mace an auro masa.
Jikinsa duk ba kwari tun jiya ya kasa samun sukuni da tunanin ko zai kuma ganin Mawadda. Shatara ta arziki yayi musu kamar yadda ya saba ya fita.
Da isarsa Kano gidan Baba Prof ya wuce. Dattijon arziki yayi matukar farincikin ganin Dahiru. Shima murnar yake har ya dauke hankalinsa daga damuwa da tunani.
Yana cin abinci suna hira Haj Mama matar Prof ta shigo.
"Tuzuru na daya...kodayake Attahir ya yiwa kansa fada magana tayi nisa yanzu kai kadai ka rage mana"
Prof yayi dariya don zancen da suke kenan ta damu da rashin aurensa. Ta zauna sun taba hira ya bata tata tsarabar tayi ta sa masa albarka. Da ta fita Prof yake masa fadan yaushe rabonsa da gidan Dr Auwal.
Mukulli yasa yana sosa kai hade da murmushi.
Prof yace "irin haka ko ban fada ba kasan ba dadi ko kazo ka wuce gidansu ka shigo nan. Shekaru sun ja ko kuwa riko ka fara ban sani ba" ya kare yana dariyar rigimar da ta hado Dahiru da uwar dakinsa Dr Tani.
Zaman gidan dena yiwa Dahiru dadi yayi tun bayan da Haj Mara ta samu ta yanke alakar dake tsakaninsu ta hanyar tura BB Dubai wai ya karo karatu. Ba kunya ta sharawa Dr Tani karyar babansa ne ya tura shi wai sai kura ta lafa akan case din Mawadda. A take Dr Tani ta nuna su a wurinsu babu komai ana iya auren ma a tura Qareeban. Son 'ya tayi aure yasa bata tunani yadda ya dace.
Qareeba bata da aiki sai koke-koke yayin da iyayen suka biye mata. Abu yayi gaba BB yafi shekara bai dawo ba. Tun suna bibiya har suka hakura. Albashin Dahiru tsabar kyashi yasa ta rage shi ya koma dubu biyar.
Haka yayi ta karatunsa har Prof ya gama cukucukun nema masa scholarship da admission. Sai da komai ya kankama yaje sanar da ita. Yana fada mata zaiyi tafiya bata tsaya taji me zaice ba ta tabe baki.
"An gaji da karyar bokon za'a koma gida kenan! Dama ido na zuba maka wai nan karatu kake kana mai shara da wanki ni ban taba jin ko alfarmar kudin registration ka roka ba. Ga kwadayi yana dawainiya da kai ka shigewa iyalin Prof Abdulhadi tun da suka dawo unguwar nan"
Takaici ya hana Dahiru magana suna haka Attahir ya shigo dama a bakin mota ya sameta. Hannu tasa ta yafito Attahir yazo ya gaisheta.
"Dama sanin hali na mutanenmu na kauye yasa nace kada yaron nan ya cuceku ya fake da mu wallahi iyakarsa shara da kuma wanki da guga. Idan ma wani abin yayi a gidanku kazo nemansa don yanzu haka ma zancen tafiya yake min to ka shaidawa iyayenka tun wuri maiaikinmu ne kawai"
Daga Dahirun har Attahir aka rasa me baki magana. Dama copy din admission letter dinsa Prof ya bayar yace ya bashi ya nuna musu.
Tun daga wannan ranar Dahiru bai sake shiga gidansu ba kuma duk zuwansa ko a hanya bai taba cin karo da wani dan gidan ba. Maigadin da ya sani ya dade da aka canza shi.
Alkawarin zuwa gidan yayi cikin sati a gaisa albarkan shekarun baya. Ya sami labarin duka mazan sunyi aure sai Hajiya Qareeba kadai ta rage. Duk abinda Dr Tani tayi dominta bukata bata biya ba.
Canja hirar yayi yace Prof yazo su ga sabuwar motarsa. Maimakon murna Haj Mama dai fadan aure ta sake dasawa wai bata ga amfanin kwalisa babu matar da za'a burge ba.
*****
Sati biyu kenan da Mawadda ta karbi sakamonta na makarantar yaki da jahilci da tayi. A daya bangaren kuma yau aka fara bikin Rafi'a.
Biki suka shirya daidai karfinsu na burgewa da kamun kai. Jamila ma ta dade da Ja'e ya mayar da ita da izinin babarsa yanzu gidan zai rage Mawadda kawai da 'yan maza.
Danlami sarkin shige shige ne Allah Ya kawowa katin daurin auren har kasuwa inda yake sana'arsa. Sai da ya nanata tambayar wanda ya bashi shima dan garinsu ne ya tabbatar masa da gaske kanwar Mawadda ce. Ranar da wuri ya tashi ya tafi ofishin Dahiru.
"Kai kuma daga ina haka kamar an jeho ka? Mutum da 'ya'ya biyu ya kasa girma"
Katin ya ajiye masa kafin ya mika hannu. Alkawari na yiwa kaina zan nemo maka Mawadda to ga katin auren kanwarta. Abu daya zaka bani ladan aiki shine ka ban mukullin motarka don Allah in zaga garin nan da iyalina muma mu kashe selfie.
Dahiru bai ce komai ba bayan karanta katin sai mukullin da ya jefa masa.
"Gobe da safe kafin na gama shiryawa ka dawo min da ita"
Danlami ya dauka yana ta murna yayi waje. Tabdi yau yasan Azima zata jidadi. Matarsa akwai saukin kai shiyasa yake son burgeta.
Dahiru kuma adaidaita sahu ya nema ya kaishi har layin gidan nasu ya tabbatar ba karya bane. Haka kawai yaji gabansa na faduwa wai cikin taron jama'ar dake waje ko cikin gidan nan Mawaddansa tana ciki.
Komawa yayi gidan da yake haya tare da wasu marasa auren na wurin aikinsu. Ranar yayi bacci mai dadi amma cike da zulumin ko tayi aure.
Washegari a daddafe ya kai karfe shida a office. Gida ya koma ya shirya yayi kyau sosai kamar ba Dahiru mai ahirin ba.
Su Mawadda ana ta shirin kai amarya suyi nan suyi can. Ba ita ba ba Rafi'a ba kowacce tayi kyau sosai. Jikinsu ya saba da gyara kowa na sha'awarsu.
Dahiru na zuwa ya tarar da motocin daukar amarya sai kawai ya shiga cikinsu yayi parking a karshe. Motarsa tafi ta kowa kyau da haduwa a wurin mata suka fara kokarin shiga. Lock ya saka kawai yana ta murmushi shi kadai ko a yaya zasu hadu da Mawadda.
Wata mai tsaurin ido cikin 'yan matan amarya ce taje ta fadawa Mawadda wani abokin ango yaki bude motarsa. Mayafi ta dora kan riga da skirt din jikinta ta ce bari ta duba idan angon yace wadda za'a saka amaryar a ciki baka ce kila mutumin amarya yake jira.
Yarinyar ta fada mata ruwan goro ce mai masifar kyau.
"Bari naje na gani idan bai daukeku ba da motarsa mai masifar kyau ko iyaye ya taimaka ya diba" ta fada tana murmushi tayi waje.
[08/01 8:32 pm] : *GUMIN HALAK...*💰12
*Batul Mamman*💖
Tana fitowa wata yarinya ta kwala mata kira "Anti Mawadda mai waccan motar yace a fada muku a tasa za'a dauki amarya"
Kallon motar tayi ta ga baka ce kamar yadda angon ya fada mata. Kamar ta juya sai ta hango motar da aka kai karar mai ita ga mata da yawa da basu sami tafiya ba kuma dangin ango suna ciki kowane lokaci zasu iya fitowa a tafi. Yanke shawarar rokarsa tayi don duk tunaninta cikin tawagar angon yake.
Sannu a hankali take takawa da takalminta mai tsini tayi kyau sosai.
Tun da ta doso motar Dahiru ya nemi nutsuwarsa ya rasa. Zuciyarsa kamar ta fito saboda halin da ya shiga na ganin macen da har yau bai taba son wata kwatankwacin yadda yake sonta ba. Matar da tunaninta bai taba barinsa ba tsahon shekara takwas da basa tare. Idonsa yaji yana masa zafi alamun taruwar kwalla ya shiga mika godiya ga Allah da rayuwar Mawadda bata tagayyara ba kamar yadda yayi ta jin tsoro. Kashe motar yayi ya kifa kansa akan sitiyari yana kokarin daidaita tunani da nutsuwarsa don a yadda yake ji a lokacin cikar kwanciyar hankalinsa shine ya rungumeta.
Ita kuma tana karasowa taji motar a kashe kuma da yake glass din tint ne bata iya ganinsa. Tagar mazaunin dreba ta matso sosai ta dan duka kafin ta girgiza kai tana murmushi a ranta tace ashe ma babu kowa shiyasa ba'a bude ba. Dahiru yana zaune yana kare mata kallo shi kadai yana murmushi ganin ta sake dukawa tana kallonsa wanda a zahiri fuskarta take kallo ta gilas din.
Sassanyan murmushi tayi kamar tasan ya shagala da kallonta ta gama turo bakinta da ya sha pink din janbaki kamar wadda zata dauki hoto sannan ta mike ta barshi da dariya a hankali. Juyawarta kenan zata koma yayi saurin budewa ya fito kada ta tafi baiyi mata magana ba.
Tsayawa tayi cak tana tunanin me motar nan ya gama da ita. Yanzu da ta dauko soson powder ta sake gogawa a fuskarta kamar yadda tayi niyya ai ya cuceta. Irin haka tunda ya iya yin shiru da farko ai da ya hakura gabadaya sai ta tafi ya fito.
Shiru ya wuce na wasu 'yan dakiku ita taki juyawa saboda yadda jikinta ya bata kallon ta ake yi shi kuma tsabar farinciki ya rasa me zaiyi. Daga kafa tayi zata yi tafiyarta kamar daga sama taji an ambaci sunan da mutum daya ke kiranta da wata murya daga can kasan makoshi har sai da tsigar jikinta ta tashi.
"Mawaddatan wa Rahma"
Mutuwar tsaye tayi jikinta ya soma rawa. Dahiru ya tako a hankali ya zagayo gabanta ya tsaya.
Anya zuciyarta za ta gaskata abinda idanunta suke gani kuwa. A hankali kamar mai tsoron kada ace karya ne abinda ke gabanta tace
"Yayanmu?....Yayanmu ne?? Yayanmu Dahiru???"
Kamar shi amma wannan yafi wancan komai sai dai bata jin akwai canjin da zaisa ta kasa gane fuskarsa duk kuwa da ya boyeta cikin kyakkyawan sagensa.
"Ashe dai zaki gane ni" ta sake jin muryarsa a karo na biyu.
Mamaki da farinciki ne suka lullubeta a lokaci guda. Ta bude baki tayi masa magana amma ko harafi daya ta kasa hadawa. Dahiru kuwa ganinta ya sauke masa duk wata sauran damuwar dake ransa.
Tabata taji anyi ta baya ta juya a firgice sai ta ga 'yar yayarta Bilki.
"Anti Iya tace kizo ki fitar da Anti Rafi'a ko tayi mata duka wai suna ta kuka ita da Ade da Yaya sun hanata fitowa ga mutane na jira"
Sauran yayyen nasu duk suna gidan amarya ana karasa gyare gyaren da ba a rasa ba. Ita kadai ta rage sai su Iya da Innar Fatihu.
Yarinyar ta kama hannunta tana ja Dahiru yayi mata alama da hannu akan ta tafi.
Tamkar wadda iska zata dauka haka take jin jikinta ta soma tafiya kawai taji yace
"Kinyi aure?"
Ko da ta juyo ita yake kallo suka hada ido karo na farko bayan shekarun da suka yi basu hadu ba. Kai kawai ta iya girgizawa saboda ta kasa magana sai idanunta da ta kautar daga nasa.
"Alhamdulillah, amma kina da saurayi?"
Samari kai, ita manema aurenta yawa garesu amma tafi kowa sanin dalilin da ya hanata bawa kowa cikinsu dama. Dr Imran ne ya fado mata a rai sai ta gyada kai.
Yanayin fuskar Dahiru bai sauya ba duk da haka ya sake cewa "Iyaye sun shiga maganar?"
Wannan karon sai da ta murmusa kafin ta kuma girgiza kai.
"Wai, Allah Ya soni ina da sauran dama"
Wayarsa mai kyau da tsada ya miko mata ko bai fada ba tasan me yake nufi. Numbarta ta saka ta mika masa.
Tsayuwar wurin tayi mata wuya kuma tasan ana jiranta sai kawai ta kuma juyawa a karo na uku ya sake dakatar da ita ta hanyar cewa
"Mawaddatan wa Rahma...naji dadin sake ganinki. Sai na kira mu gaisa"
Sai lokacin ta tuna ko gaisawa basuyi ba. Tana juyawa ya shige mota ya dago mata hannu. Bata bar wurin ba sai da ya fita daga layin ta sauke ajiyar zuciya.
Har suka shiga mota a hanyarsu ta zuwa gidan amarya bata dawo daidai ba. Lokaci lokaci take sakin murmushi ko tayi ajiyar zuciya.
*****
Gidan Bilya ya wuce kana ganinsa zaka yi tunanin anyi masa albishir da kujerar Makka ne. Furaira matar Bilya ya gaisar ta dauke kai.
Yayi dariya