Showing 15001 words to 18000 words out of 63397 words

Chapter 6 - ANGON MATA BIYU COMPLETE Book by Maryam M Hashim.txt

15 Aug 2025

4752

ya je ya dakko tukunyar shishansa ya zo falo ya zauna, ya hada yana sha cikin takaici, Haseena ce ta fito ta sameshi, ta karasa wurinsa ta zauna gefenshi

"Mijina ka yi hakuri da abin daya faru dazu, ba laifina bane, laifin zuciyata ce, wallahi tsananin soyayyarka yake haifar min da kishinka"

Ya kalleta "wato nine munafikinki"

"Ka yi hakuri, hakan ba zai kara faruwa ba"

"Ki je kawai"

Tashi ta yi daga kan kujerar ta tsugunna a gabanshi "Don Allah ka yafe ni, wallahi na gane kuskure na" hawaye ya shiga fitowa daga idanunta, tsura mata ido ya yi na wani lokaci sannan ya ce shikenan saiki kiyaye gaba

Tai murmushi "nagode mijina" ta tashi ta rungume shi tai kissing dinsa a kumatu, ya zuba mata jajayen idanunsa

"Baby I need sucking"

Jikinta na rawa ta shiga tube masa wando

Aisha ji ta yi ba dadi, tashi ta yi ta mayar da kayanta, da niyyar ta fita ta je ta sami Don ta bashi hakuri sannan ta yi masa abinda yake bukata, da zuwanta falo ta tarar da Don zaune kan kujera ya ware cinyoyi, Haseena tsugunne tsakanin cinyoyinsa tana sucking dinsa.

Kirjin Aisha ya bada wani rasss, wani abu ya tokareta a zuciya, lokaci daya ta nemi farin cikinta ta rasa, da sauri ta koma dakinta, rufe kanta ta yi, ta zauna bakin gado tana ajiyar zuciya dakyar

"Ashe haka Aunty Haseena take ji a duk lokacin da nake tare dashi, lallai abin akwai zafi sosai"

Ta kwanta ta rungume filo ta zama kamar abin tausayi


Da Azahar ya yi Don janye jikinsa ya yi "lokacin sallah ya yi, zan je masallaci"

Haseena ta tsaya tana kallanshi cikin mamaki, abinda bata taba gani ba

Dakinta ya wuce ya shiga bayi ya yi wankan tsarki sannan ya fito yasa wasu kayan ya wuce masallaci

Haseena ta ce sabon salo, ta tashi ta wuce dakinta ta yi wanka ta canza kaya

Aisha tashi ta yi ta je ta yi alwala sannan ta yi sallah ta wuce kitchen ta fara aikin abinci, tana cikin yi Haseena ta shugo fuskarta ba yabo ba fallasa, Aisha ta kalleta

"Sannu Aunty"

"Yauwa Aisha, ki yi hakuri fa da abin daya faru dazu, sharrin shaidanne"

"Babu komai Aunty"

"To bari na tayaki aikin ko"

"Aunty ai da kin barshi"

"Habadai ai ni dake daya ne"

Nan Haseena tasa hannu suka gama aikin tare bayan sun gama suka kai komai Dining,

Daga masallaci Don wajen Wizzy ya biya suka dan yi hira, sannan Wizzy ya biyo Don akan yau yana son ya ga amaran su

Aisha da Haseena zaune a falo suna dan hira sama sama Don da Wizzy suka shugo, duk suka tashi suna yi musu sannu da zuwa, Don ya nuna Wizzy

"Babban abokina kenan Wizzy"

Suka kara gaisawa, sai ya kalli Wizzy ya nuna Haseena "ga Haseena, sai wachcan Aisha"

Wizzy ya ce gaskiya abokina ka yi sa'an mata, duk sun hadu

Aisha ta kasa hada ido da Don saboda wani kwarjini da yake mata, kuma tasan yana fushi da ita

Haseena ta ce muna farin cikin zuwanka, yanzu sai mu je Dining domin cin hadaddan abincin da yer uwata Aisha ta kammala

Babu musu, duk suka wuce Dinning, amma banda Aisha ita dakinta ta wuce

Haseena ta shiga serving dinsu bayan ta kammala ta zuba nata

Wizzy ya ce ya Aisha ba ta zo ba?

Haseena ta ce kasan yer uwar tawa da kunya

"Ok Allah sarki"

Wizzy ya kai cokalin abinci bakinshi, tsayawa ya yi cak yana kallan Don, Don ya kula akwai damuwa

"Lafiya"

Wizzy bai iya hadiyewa ba, ya dawo dashi

A tsorace Don ya ce akwai wani matsala ne a abincin

"Zallan gishiri aka girka ba abinci ba"

Murmushi Haseena ta yi tana fadi a zuciyarta "ai gidannan daga yanzu babu zaman lafiya sai tashin hankali"

Don ya gwada dandana abincin, ya rikirkice saboda tilin gishirin dake ciki, kallan Haseena ya yi

"Ke kika girka abincin nan?"

Ta zaro ido "ni Haseena? Rufa min asiri, babu ruwana, Aisha ta girka"

Cikin fushi Don ya tashi yabar wurin, Haseena ta ji wani dadi a ranta, dakin Aisha ya wuce

Aisha zaune kan kujera Don ya, shugo yadda ta ganshi ransa a bace yasa ta mike da sauri

"Waya girka abincin dake dining?"

"Nine, akwai wani abu ne?"

Idanunsa sunyi jawur tsananin fushi

"Ni zaki wulakanta, ni zaki nema ki ci wa mutunci, to kije ki tattara abincin ki cinye, nagode"

Ya juya ya fita ta bishi da ido don ta kasa fahimtar me yake nufi, a falo ya samu Haseena da Wizzy

"Don Allah Wizzy ka yi hakuri"

Wizzy ya ce ni zan tafi

"Mu tafi nima ba zama zanyi ba"

Haseena ta ce ni dai kar laifin wata ya shafe ni don Allah

Don bai bi ta kan maganar ta ba suka futa shi da Wizzy ta bisu da kallo cikin mamaki "karfa laifin ya shafe ni"

Aisha ta fito daga daki ta je Dining ta shiga duba abincin tana son gane meya faru da abincin, can ta dandana, ta shiga yamutse fuska saboda gishirin dake ciki

"Na shiga uku, taya haka ya kasance"

Haseena ce ta fado mata a rai "kar dai Haseena ce ta yi min haka"

Ta shiga tuno maganganun Don da yake nuna mata Haseena kishiyarta ce, kisan zamanki da ita zata iya cutar dake, maganganunsa suka rika yi mata yawo a kai, hankalinta ya tashi, daki ta koma ta fada kan gado ta hau yin kuka kamar ranta zai vita

Don da Wizzy a mota suna tafiya, Wizzy shi yake tukawa

Wizzy ya ce da alamu Aisha ta mugun raina maka wayau

Don ya ce ba Aisha kadai ba hatta Haseena, duk matan haka suke yen rainin wayau ne, ba daman kadan fara soyayya dasu sai su fara raina maka wayau, su mai da kai kamar baka san me kake yi ba

"Ai kaine Don ka saki hannu, mata basu da tabbas, tsakaninka dasu rashin mutunci, karka taba sake musu fuska, ga mata birjid a gari sai wanda ka zaba, in kaso duk matan garin nan zaka take su, kuma babu abinda zai faru"

Don ya ce wallahi yanzu zasu fara ganin rashin mutunci, zan dinga kuntata musu, kasan ma me zai faru?"

"A'a sai ka fada"

"Tafiya zamu yi zuwa lagos, zan kyale yen banza su ci ksnsu"

"Ka yi dai dai nawan, amma kwana nawa zamu yi"

"Kila mu yi wata daya"

"Amma kadaka samu matsala da Alhaji"

"Karka damu, zan masa karya akan zan je yin wani business ne"

"Ok, hakanma ya yi"

Suka cigaba da tafiya suna hira


Don zuwa ya yi ya samu Abba akan zai tafi lagos yin wata harka na kasuwanci, farin ciki Abba ya yi don tunda yake Don bai taba tunkararsa da irin wannan maganar ba, Don ya yi karatunsa daga degree zuwa masters dakyar amma baya yin aikin komai, a tunaninsa taya mahaifinsa yana da kudin da zai iya ciyar da gari guda kuma ya yi aiki, ai aiki sai yayen talakwa ko wa'inda arzikimsu bai kai ba, Abba ya goya masa baya dari bisa dari hakama Ammi, tasa masa albarka


Ranar Aisha kulla kanta ta yi a daki, tana tunanin irin zaman da zata yi da Haseena, kuma gashi tana son bawa Don hakuri amma bata da numbansa

Haseena kuma hankalinta ya tashi da ta ga Don bai dawo ba, gashi dare ya yi, yanzu karfe goma, kiransa ta shiga yi yana danna mata user busy daga karshe ya saka numbobinta blacklist, hankalinta ya kara tashi, ta ga har sha biyu yana neman yi

"Na shiga uku, miye nawa a ciki da zai hada dani yana hukintawa"

Ta shiga safa da marwa

Don da Wizzy wurin karfe daya na dare suka tafi Club, kamar kullum matan wurin daga su sai pant da breziya suke rawa, suna ganin Don, suka yo wurinshi, wasu suna shafa shi, wasu suna rawa a gabanshi, sai watsa musu kudi yake yi yana shafa bayansu

Washegari Aisha ta fito ta shiga kitchen domin yau ta tashi tana jin yunwa, tana cikin hada breakfast Haseena ta shugo cikin fushi

"Ina kwana Aunty?"

Ta galla mata harara "ba zan amsa ba, da ban kwana ba zaki ganni, shashasha kawai, kinje kin dafawa mijina abinci kin cika uban gishiri kina son kashe mu, kinsa mijina yaki dawowa gida, to wallahi idan bai dawo ba yau sai kin gane kuranki dani"

Tunda Haseena tazo ta fara magana Aisha ta dukar da kai hawaye na fita daga idanunta, Haseena ta ja tsaki ta fita, dakyar Aisha ta karasa girki ta wuce dakinta ta fada kan gado tana kuka, ta kasa cin komai

Don da Wizzy kuwa sun dade a lagos don jirgin farko suka biyo, Naira marley mawakin kudu da ya yi suna a duniya da kanshi yazo ya dauke su daga Airport ya kawo su gidanshi dake Victoria island, ya yi farin cikin ganinsu, musamman Don da childhood freind dinshi ne kuma abokin cin mushensa ne, yasa aka kawo musu haddan Wiwi da aka nade su da dala, da kuma nau'o'in abinci da tarin wine da drinks

Bayan sun gama shan Wiwi ya rarike musu ciki suka fara cin abinci, sun ci sun koshi sosai sannan Naira Marley ya dauke su ya kaisu wani sabon wurin hutawa da aka bude, kamar ba a Nigeria ba ga tarin yen mata da suke kaiwa da dawowa

Aisha wuni ta yi a daki sai wurin la'asar da ta ji yunwa na neman ya yi mata illa, ta tashi ta je kitchen ta debo breakfast din data yi da safe ta ci ta koshi sannan ta yi sallah ta kai wa Allah kukan damuwarta

Da daddare Aisha ta fito wanka kenan Haseena ta shugo cikin fushi ta shiga masifa

"Ba zai yuhu ba ki yi laifi ya shafe ni, dole ki je ki nemo min mijina, maza fita kije ki nemo shi"

Aisha ta shiga yin kuka "ni bansan inda yake ba"

"Babu ruwana da baki san inda yake ba fita zaki yi kuma karki dawo sai da mijina"

Hankalin Haseena ya kai kan sallamar da ake yi a falo, "karki fito bari naje na duba wake sallama na dawo"

Haseena da fitanta ta ga Prof Attahir da Mum, bata gane Iyayen Aisha bane

"Sannunku"

"Yauwa sannunki"

Duk suka zauna a kujeran falo tana musu kallan rashin sani

Mum ta ce kai ke kadai ce, ina yer uwar taki?

"Babu kowa a gidan, ni kadai ce"

Prof Attahir ya ce to ina suka je?

Da gudu Aisha ta shugo falon saboda jin muryar iyayenta, sai fadawa ta yi jikin Mum tana kuka, Haseena ta zaro ido, Mum ta dago Aisha tana kallanta

"Yata meya faru?"

Hankalin Prof Attahir yana kan Aisha "mamana meke damunki'

Aisha ta kalli Haseena dake tsaye tasha jinin jikinta, Haseena ta yi saurin karbar bakinta

"Tunda me gidanmu ya yi tafiya jiya take ta kuka, tun dazu nake dakinta ina rarrashinta, zuwanku ne ma yasa na fito"

Mum ta tsurawa Haseena ido "amma ai kin ce babu kowa a gidan"

Haseena ta ce na fada muku babu kowa ne saboda bana son ku ga halin da take ciki ku daga hankalinku

Prof Attahir ya ce taya kika yi kikasan mu iyayenta ne?

Haseena ta yi murmushi "Habadai ya ba zan sanku ba kuna Iyayen mijina, Mijina ya nuna min hotunan danginsa gabadaya"

Prof Attahir ya kalli Aisha da idanunta suka yi ja "mamana hakane duk abinda ta fada?"

Aisha ta kalli Haseena sannan ta kalli prof Attahir ta gyada kai alamun Eh

"To mamana ai hakuri ake yi, baki ga yer uwarki ta yi hakuri ba, kuma ai zai dawo, uncle dinki yau yake fada min ya tafi lagos kulla wani kasuwanci, ki yi masa addu'ar kin ji"

Aisha bata ce komai ba, Haseena ta shiga kitchen ta kawo musu kayan marmari da drinks da sauransu sannan ta zauna ta sake jiki suna hira sosai, sun kai wurin karfe goma sannan suka yi shirin tafiya, Aisha ta hau yin kuka sai dai su tafi da ita, suka yi ta rarrashin ta sannan suka kara damkawa Haseena amanarta, dakyar dai ta barsu suka wuce

Haseena wani rankwashi ta yi wa Aisha a kai, sannan ta ja kunnanta daya da karfi, Aisha sai ihu take yi

"Idan har kika kuskura kika fadawa wani wani abu dake faruwa sai na miki tsinannan duka, shashasha kawai"

Haseena ta ja tsaki ta wuce dakinta, Aisha rusune a falo tasa kanta a tsakankanin gwiwowinta tana ta faman kuka

Haseena ta tsaya a tsakiyar dakinta tana tunani "au ashe tafiya ya yi, kuma ya je kulla wani kasuwanci, to yaushe zai dawo kenan" sai ta shiga gwada numbobinsa amma basa shiga, ta shiga safa da marwa

Aisha daga karshe ta tashi ta koma dakinta, ta kwanta tana tunanin iyayenta

Don da Wizzy, Naira Marley ya kaisu wani club da mata tsirara suke rawa, eh lallai iskancin Lagos ya fi na Abuja, Don ya zabi lafiyayyun yen mata da zasu tayashi kwana

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya har tsawan kwana goma, Aisha ta rame, ta yi wani fari, zazzabi ya tasa ta a gaba, Haseena kuwa kullum saita kira Don amma har yanzu bai cire ta a blacklist ba, ga tsinannan azaban da take bawa Aisha, Aisha tsoron Haseena take kamar ita ce zata zare mata rai

Don da Wizzy suna ta rayuwarsu a Lagos, Wizzy ya yi mamakin ganin Sallahn jam'i baya wuce Don, kullum sallahnsa sau biyar a masallaci yake yi, hakan yasa jefi jefi yana binshi masallac, kusan kullum sai ya yi tunanin Aisha, amma yana mantawa da Haseena Matarsa ce, Sannan iskancin Don ya karu, shan Wiwi da zuwa club, wasa da yen mata duk sun karu, kuma akidarsa na rashin son haihuwa ya karu, a ganinshi duniya yanzu aka fara, yana da sauran lokaci, gwara ya ci karanshi ba babbaka bayan wasu shekaru sai ya haihu

Haseena tasa Aisha ta yi mata sinasir da miyan gyada, Aisha na cikin yin aikin, zuciyarta ya rika tashi, ta kasa control din kanta, sai ta barke da amai, tun daga falo Haseena take juyo karan aman, da sauri ta tashi ta shiga kitchen din ta tsaya tana kallan Aisha cikin mamaki dake amai kamar zata fito da kayan cikinta

"Ke kada dai ace ciki kika yi?"

Haseena ta karasa wurin Aisha bayan aman ya yi sauki, ta shiga kallan kwayar idonta tana kallan tafin hannunta, Haseena fita ta yi tabar kitchen, Aisha ta cigaba da aikinta jikinta na rawa, can sai ga Haseena ta dawo da abin gwajin fitsari na ciki, ta mikawa Aisha wani karamin roba

"amsa roban nan ki tsugunna ki yi fitsari a ciki"

"Aunty bana jin fitsari"

"Don uwarki ina wasa dake ne, amsa ki yi, kwakulowa zaki yi"

Hannun Aisha na rawa ta amshi roban

Aisha ta tsugunna ta rufe jikinta da zanin jikinta, ta yi fitsari a roban, bayan ta gama ta tashi

"Aunty na gama" Haseena ta galla mata harara ta je wurin fitsarin ta duka sannan ta tsoma abin gwajin cikin a cikin fitsarin sannan ta fito dashi ta tsaya tana kallo, ta dade tana kallo amma shuru babu amsa, fita ta yi ta dawo falo ta je wurin AC ta tsaya saboda result ya fito amma shuru, gabadaya babu wani layi daya fito, wurin na nan yadda yake, hankalinta ya kasa kwanciya

Aisha bata san me Haseena take nufi ba data sata ta yi fitsari ba, kawai ta cigaba da aikinta, sai ga Haseena ta shugo a fusace

"Bar aikin nan, zo mu je asibity"
Babu musu Aisha ta ajje aikin tabi Haseena har harabar gida, Haseena da kanta ta jasu a mota har zuwa asibity

Da isarsu asibity Haseena ta yiwa likita magana akan su bincika mata Aisha ko tana da ciki

Nan aka shigar da Aisha dakin gwaji, aka shiga bincikata

Haseena ta shugo cikin Office din Likita jikinta na rawa ta zauna tana son sanin sakamako, Likita ya mika mata result ta amsa, cikin sauri ta shiga dubawa, Haseena ta mike a rikice

"Na shiga uku na lalace, tawa ta kare, Don Allah Doctor ka taimake ni a cire cikin nan, wallahi zan biya ko nawa ake bukata"

Likita ya girgiza kai, "ki yi hakuri bana abortion"

"Doctor zan biyaka daga million daya zuwa sama ka taimaka min a zubar da cikin nan"

"Zaki iya fitar min daga office, na fada miki bana zubar da ciki"

Ta watsa masa kallon banza sannan ta ja tsaki, ta fita ta samu Aisha tsaye a harabar asibitin

"Yau sai kin ci ubanki dani, wato ciki kika yi Aisha"

Aisha ta zaro ido "Aunty ina da ciki ne?" Sai kuma ta yi mrmushi

Haseena ta ce au murmushi ma kike yi

"Aunty ina son baby sosai"

"To dan ubanki baki isa ki haifi wannan cikin ba da raina a duniya, da kaina zan zubar dashi"

Haseena ta ja hannun Aisha da karfi suka fuce, gida suka dawo, Haseena ta yi parking a harabar gida, ta fito a fusace, Aisha na fitowa Haseena ta kai mata wani wawan mari da da ya yi sanadiyar ta fadi kasa, ta fara kuka

"Aunty ki yi hakuri"

"Don ubanki waya ce ki yi ciki a gidan nan?"

Cikin muryar kuka Aisha ta ce Aunty ba laifina bane Ya Umar shiya biyoni daki ya yi min ciki

Haseena ta kara kai mata wani duka

"Wallahi sai cikin nan ya bare yau"

Aisha tasa hannu ta kare cikinta tana kuka "Aunty ki barni da cikina, ki yi min komai amma karki taba min cikina"

Haseena ta daga kafarta zata bigawa cikin sai ta dakata sanadiyar bude Gate da Security suka yi alamun mota zai shugo, Haseena ta yi sauri ta daga Aisha

"Yer uwata yi hakuri kin ji, kar ki yi fushi"

Mota kirar Land cruised prado ya shugo harabar gidan, Haseena ta rungume Aisha tana rarrashinta

"Zaki sanu lafiya, kin ji yer uwata"

Aisha ta shiga manajin munafurci irin na Haseena


Abba da Ammi ne suka fito daga motar, Aisha na ganinsu ta janye jikinta daga na Haseena ta je rungume Ammi tana kuka

Ammi da Abba suka rikice gabadaya, Haseena ta shiga gaida su, basu bi ta kan gaisuwarsu ba suka fara tambayar meke faruwa

"Bata da lafiya yanzu muka dawo daga asibity"

Ammi da Abba suka zaro ido "meke damunta" suka fada a tare

Haseena shuru ta yi wani bakin ciki na cinta a rai, ganin bata basu amsa ba yasa Ammi ta fara duba Aisha, ta duba idanunta da tafin hannunta, ta kalli Abba, gaban Haseena sai faduwa yake yi

"Kamar Aisha nada ciki"

Wani farin ciki ya baiyana a fuskar Abba, Haseena ji ta yi kamar ta kwarmatsa ihu, Aisha ta rike cikinta kam kam kamar za'a kwace mata ta kara fashewa da kuka

Ammi ta Jawota jikinta "yata yanzu cikin kikewa kuka?"

"Ammi don Allah kar a rabani da Baby na, ina son Baby na sosai"

Ammi tai murmushi "wa zai rabaki da Bebinki, wani ya fada miki za'a rabaki da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login