Showing 63001 words to 63397 words out of 63397 words
Chapter 22 - ANGON MATA BIYU COMPLETE Book by Maryam M Hashim.txt
ta ce kullum sai Ammi ta biya mana karatu
Hameeda ta ce Daddy Humaira mu'allimat dinsu ta bata kyauta saboda tana da kwazo wurin hadda
Don yai smile sannan ya ce Masha Allah, ta biyo me sunanta
Aisha ta rungumesu gabadaya "Allah ya yi muku albarka gabadayanku"
Suka amsa da ameen
Hankalin Haseena ya kai kan hotunan dake cikin falon, ta kalli babban ciki, Don ne, da Aisha da Haseena, Don a tsakiyansu, ranar sunan Leemat suka dauke shi, sai ta kalli na Don da yake shi kadai, sai ta kalli na Aisha, sai hankalinta ya dawo kan na Haseena, ta dawo da kallanta ga Aisha
"Mummy waccan ita ce me sunana?"
Aisha ta kalli hoton Haseena tai smile "ita ce me sunanki, mummy Leemat kenan"
Leemat ta kalli hoton Haseena sannan ta ce mummy dama bake bace mummyna
Don ya yi sauri ya nuna Aisha "ita ce mummynki" sai ya nuna hoton Haseena "waccan kuma second mummynku ce, ta rasu, ku yi mata addu'ar Allah ya jikanta, Allah ya kai haske kabarinta"
Suka amsa da ameen
Leemat ta ce amma Dad wai kai angon mata biyu ne?
Don ya kalleta cikin mamaki "a ina kika ji?"
"Nima haka na ji ana fada"
Yai smile "eh dagaske ne"
"Amma meyasa ka zama angon mata biyu bayan kai angon mum dinmu ce kadai"
Aisha ta ce kai Leemat maganarki ya fara yawa fa
Don ya ce bari na warware mata komai, kawai ana ce min angon mata biyu ne saboda Abba ya aura min mata biyu a rana daya, da Mummynku da kuma second mummynku
Leemat ta nuna hoton Haseena sannan ta ce na jikin hoton nan da mummynmu sune matayenka ko?
"Eh hakane"
Haseena ta ce na ji ina son me sunana, dama bata mutu ba, data jira na ganta
Don yai smile yana kallan Haseena
Leemat ta je ta dauki Junior, shi kuwa sai kokuwa yake da ita, don tun daya samu kafa baya son ana daukanshi
Su Leemat sun jima a gidan, sai da suka kai yamma sannan Nannynsu ta mayar dasu wurin Ammi
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, tana sauyawa kamar abubuwa basu faru ba
*LAIFIN DADI KAREWA*
Anan na kawo karshen Angon mata biyu, sai mu hadu daku a sabon littafina da zai mayar gurbin angon mata biyu wato *HALEEMATUS SA'ADIYYA* *ALKAWARIN FANSA* kuma zai maye gurbin Dijangala
Zaku iya fara turo katin waya kamar yadda aka saba idan zan fara posting sabbin littattafai na, katin waya na naira dari kacal, sai na jiku
Taku har kullum *M JARUMA CE*