Showing 21001 words to 24000 words out of 34797 words

Chapter 8 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf

makanta
Abdullahi yanzu ta hana shi wannan kallon
maitar da yake wa fatima, har ma ya kasa
magana sai kallon kawai,ita kuwa gimniyar ta yi
kamar ba ta san yana yi ba. "Ina ka saka min
kayan da ka wanke rannan?" Ta tambaye shi

cikin tsura masa ido fuskarta da walwala.
Bakinsa
na rawa ya ce. "Ba ki gansu ba?.... Ta tare shi
da mikewa ta nufi daki. "Ban gan su ba". Kai
tsaye ya tashi ya bita yana cewa. "Bari mu
gani."
Ya bar sadiya da gyaran murya dan ta tunatar
da
shi ya san da ita, yana shiga ya turo kofa. Har
da
murda key dan yana zaton sadiya zata biyo shi.
Sai fatima ta juyo suka fuskanci juna fuskarta
na
baYyana alamar tuhumarsa da rufe mata kofa.
Ya
kama hannayenta a rikice ya ce. "Fatima,me
yasa
kike saka irin wadannan kayan baccin ni a tare
da
ki?" Ta yi masa kallon rashin fahimta,sannan
fara
bin rigae jikinta da kallo. Ya fara yi mata
shishigi,yana cewa. "Ki dinga sanya kaya masu
kauri idan kina ke kadai dan yiwa shaidanu riga
kafi... Ko ba ki san kina da kirar da za a kalla a

kasa kawar da kai ba..? Ni kima ina da kishi
musamman a kanki,kin ji fatima. Kamar dama
bai
fada don ta amsa masa ba, ya fara sumbatarta
cikin gigita da shauki,kamar a majigi sai ta biye
masa suka bata hankalin dare matuka! Fiye da
mintuna goma sha biyar,ita kanta da ta dana
tarkon ta manta tarko ne,ta manta da sadiya
bare shi da ya fi ta zakewa. Suka samar da wasu
guraba masu muhimmanci a zukatan
juna,Abdullahi ya ba ta assigment mai zafi na
neman dalilin da ta ke kasa mallakar
kanta,idan
sun shaki numfashi juna.... Ta kasda sanin
dalilin
tana ji kuma a ranta ko rabuwa da shi zata sha
wannan kewar.... Abdul ya iya da mace ya iya
bayyana mata kauna
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
27) A yau ta samar wa zuciyarsa nutsuwar da
ya jima cikin damuwa da tantamar matsayinsa
a
zuciyarta, ya yarda ya sake ne shi yasa fatansa

ke nisa farin cikinsa na binsa a baya. Tabbas duk
lokacin da fatima ta karbi soyayyarsa sai ya
shiga sakun mazan da suka yi sa'ar auren
kyawawan mata wadanda suka karanci so. Ya
dago ta da riko kafardarta jiki a sanyaye.
"Fatima,kin tuna cewa cikin wata nan bakwai
mu
ke da aure?..... Dadewa tare na nufin sabo da
komai ma idan ta kama har da gajiya..... Amma
ni har yau ban saba d sonki ba don kullum In
wayar gari da wasu sababbin sonki wanda ban
taba dandanar irinsu ba, saboda ganinki ba ya
hana in ganin kyan fuskarki kullum,yau fiye da
jiya, yadda kike mu'amalanta ta ba ta sa ni
yanke
kaunar za ki shugabantar da ni cikin duniyar
wata
rana ba kuma ga shi ina zama wani sabon shiga
duk san da na shaki numfashinki...... Amma na
san ba komai ba ne sai tsananin kaunarki da ta
cakude da jinina,fadima ban taba jingina
kaunarki
da wani dalili ba.... Kin amince min? Ki yarda
da
ni..." Ya ci gaba da kura mata idanunwansa da

suke fitar da kwalla suke son su yi tasiri a
zuciyarta su sanya ta yin abin da babu niyyarsa
a
burikanta, sai ta yi kasa da ido,ya dago kanta
yana nuna mata agogo,a sanyaye ya ce. "Kin ga
kin sani na makara fadima,duba agogo me zaki
ci? To taya ni mu gyara dakin ko" Ba ta tanka.
Shi ba, kuma ba ta taya shi ba, sai ma ta nufi
ward robe ta dauko after dress ta maka ta yi
zamanta kan sofa tana kallonsa har ya gama da
dakin ya fice falo,sai can jimawa ya shigo mata.
"Zan tafi fatima". Ta dago ta bi shi da kallo,
ya
daga gira ya ce. "Ki yi hakuri,zan turo miki
break
fast kamar jiya,na makara...ki yi min wannan
uzurin". Sai ta sami kanta da daga masa hannu
da sarkarkiyar murya,ta ce. "Babu komai ka
je,ba
sai ka ka turo ba zan nemi abin da zan ci". Ya yi
kaske yana kallonta, murna duk ta cika masa
zuciya.... Da ya rasa abin da zai ce mata sai ya
debo mata sambatu. "Dama ace ke za ki karbi
girki,da da wuri zan dawo na yi miki tuwo da
kaina". Ta ci gaba da sa masa ido kawai har ya

gama sambatunsa ya fice. Ta mayar da kai a
hankali,tare da son fadawa cikin tunani,sai a
sannan sadiya ta fado mata,da sauri ta fito
falon
sai ta ganshi wayam! Sai Abdullahi da ke ficewa.
Ta zube a kujera cikin tsananin dariya tare da
furta. "Yarinya kin kuma kiran me alewa ba ki
da
kobo". Shi kansa Abdullahi sai a lokacin ya tuna
wai fa tare da sadiya ya shigo.dan haka a
tsorace
ya silale ya bar gidan.
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
.28) A
gaggauce fatima ta yi wanka zuciyarta cike da
fargabar yadda zata fita ta dawo ba tare da
Abdul
ya san da fitarta ba,ita kanta sai ta dinga
mamakin tsoron da ta ke masa, wadda ta ke jin
ba tsoron ne kawai ba har da rashin son bacin
ransa, da kuma hangen matakin da zai iya
dauka
wanda ta ke canke canke akai.da fadawa kawu

sirrinta zai fanshe ko kuma da yi mata dukan
shan gishiri? Bayan wannan komai nasa ya
karade zuciyarta, tana tuna shi a muhimman
lokutansu,da jarumtarsa wajen bayyana mata
kauna yadda ya kware wajen gigita fuskokin
shaukinta, sannan ga bautar da yake mata jiki
da
jini. Wadannan dalilan suka sanya ta jin kamar
tana son ta ci amanarsa a yunkurin ta na zubar
masa da ciki musamman a matsayinsa na me
neman haihuwa ido rufe. Wannan alhini bai
hana
ta shiryawa tana duban agogo ba,wanda ya
nuna
sha daya da 'yan mintuna. Tana tsaye a
falonta
ta jaka da mayafi a hannu,sai ga kawarta laila
kuma tafinta tsakaninta da Alh a lokacin da ta
ke
zaman gida. Ta yi farin ciki da ganinta
sosai,suka
gaisa sannan suka zauna suna bincikar labarin
juna. "Sai yau nake ganinki a gidan nan laila
kin
watsar da ni kin barni ni kadai da azancina.

Abdullahi na ta samun nasarori a kaina,ina
Alh?
Laila ta dinga bin dakin da kallo cikin tabe baki,
sannan ta ce. "To in zo in yi me a wannan bakin
gidan? Ai da alkwarin na yi har ki bar shi ba zan
tsomo kafata mai daraja a cikinsa ba. To da
alama ke ba kya ganin duhunsa da
kuncinsa,tunda na ga har wata 'yar kwarya
kwaryar kiba kika yi.... Kin bar Alh na can yana
fama da jinya,to jiya ya sauka kasar nan kuma
shi ya buga sammako da kansa ya same ni har
gida ya ce lallai na zo na ji inda naki lissafin
yake,ya ya aka yi kika bace haka... Fatima ina
wayoyinki?" Fatima ta dan yi walai da ido
alamar
bayyana jimami,sannan ta nuna kofa tana
cewa
"Ya karbe". Laila ta ji batun gingirin,ta tsule
gira
ta dubi kofar sannan ta dubi fatima ta ce. "Ya
karbe?"Wanne sale dan kwadago ya samu haka
har ya sami wannan zakewar,ke kuma wuka ya
dora miki a wuya ya kwaci wayoyin ko kuma
barazana ya yi miki da bindiga cewa,in kika
kuma

wata wayar zai harbe ki? Fatima ta yi
murmushin
yake tare da sauke ajiyar zuciya mai bayayyana
gajiyar zuciya,ta ce. "Ya faki idona ya
kwashe,sannan ya toshe hanyar da zan fita
bare
in mallaki wata wayar,tsawon watannin nan
bakwai fa da muka yi tare ban yi fita ta kai
goma
ba, kuma ga kafata ga tasa,sai sati biyun da
suka
wuce na saci hanya na je asibiti, shi ma ba ki ga
dan bikin da ya yi min ba, har fa da mari...."
Labarin ya girgiza laila kwarai,ta jinjina
"Mari?"
Fuskar taki ya mara fatima? To dan ganye
ne?"
Fatima ta yi murmushi,ta ce, Ko daya idan ma
yana sha ba zai wuce giyar sona dake bugar da
shi ba. Na rantse miki na kasa gane wanda ya fi
so na tsakanin sa da Alh....." Laila ta yi saroro
kawai tana kallonta,tara gira ta ce. "Da alama
kuma kin biye masa.... Soyayyar da yake miki ba
hujja ba ce da zaki yi zaman watanni bakwai a
gidansa.... Ke ni gani nake ma tsaurin ido ne

mutumin bai fice baranki ba ya iya furta
soyayyarki". Fatima ta jima shiru tana juya
maganganun lailan,ta yarda a ranta laila ba ta
san waye Abdullahi ba,koda yake suna da
bambancin dabi'u da alkibla ita da laila.
Ma'ana
kudi sun runtse idon laila,yayin da ita ta ke son
rayuwar'yanci da rayuwa da abin da ta ke so
wanda kuma ta. Zabar wa kanta da kanta da
dalilan da ko kusa baba kudi a cikinsu. Sai ta
sami kanta da kwalla,ta dubi laila ta ce da ita.
"Ki yi farin ciki laila da Allah bai yo ki kamar ni
ba,kyan tarnaki ne a cikin rayuwa wanda mafi
yawan lokuta yake hana mutum zabar abin da
yake so ake hada shi da zabin wasu,sakamako an
yi masa shigar sauri don a rayu da shi dole! Na
tabbatar yawancin kyawawan mata ba sa auren
mazan da suka dace da burinkansu". Cikin
fuskar
rashin fahimta laila ta ce. "Me kike nufi?"
Fatima
ta yi saurin amsawa. "Ba ki ga aya a kaina ba?
Na zauna da Alh bisa kaddara ta kara hadani
da
Abdul..... Wanda nake ganin kamar ya fo Alh

zafin so na... Kamar ya fi shi sadaukarwa..."
Laila ta tare a kufule. "Idan kin zauna da Alh
bisa
dole,wallahi ba ki fadi ba zahra'_ don ya isa ya
ajiye kamarki a gidansa,sannan ya mallaki wani
abu da zai rage miki takaicin kiyayyarsa....'Udi
ai
su ne a yanzu,don haka ban ga dalilin da za ki
zauna da mai gidan nan ba, me ya ajiye,da me
ya
cancanci mallakar mace kamar ki... Da me za ki
karasa ragowar rayuwarki..." Fatima ta yi saurin
tare ta fuska a hade. "Wannan ra'ayinki kike
fada
laila, akwai muhallai da yawa wadanda ba kudi
ke taka rawa a cikinsu ba, musamman na
dadada
zuciya ba, laila ni ban fifita darajar kudi a
cikin
raina fiye da bukatun da suke gina zuciyata ba,
idan dai zan samu in ci kuma in nema dai dai
gwargwado in samu ba zan rasa ba, wannan ya
wadatar da burina,don haka ki cire min
maganar
kudi a zamana da Alh na baya,ko hasashen na

gaba". Laila ta yi tsuru tana kallonta cikin
bugun
zuciyar fargaba yadda fatima ke son ta fifita
mijinta na yanzu a fakaice,don haka da ci da
zuci
ta ce mat. "Wannan ce hujjarki ta share guri ki
zauna a wannan kejin gidan,kuma don tsabar
zubar da aji tare da wasu mata har biyu
wadanda
ba su wuce 'yan share sharen ki ba a matsayin
kishiyoyinki?"
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
29) Sai yanzu ne ma zuciyar fatima ta kuntata
da lamarin Abdullahi,wanda ta tabbatar ba zai
wuce na tuna su sadiya ba, ta kyale baki ta ce.
"Ko daya,ya kankane ni ne,amma kullum ina
iyakar kokarina,yanzu ma da kika ganni asibiti
zani a yunkurina na zubar masa da ciki". Laila
ta
zaro ido gami da dauke numfashi ta dafe
kirji,ta
ce. "Ciki fatima? Da wannan kazamin yaron
kika

yarda kika sami cikin?" Ga mamakin fatima sai
maganar laila ta yi mugum bata mata
rai,musamman ta kiran Abdullahi kazami. Ta
jima
tana kallon laila sannan ta kawar da kai tana
bin
talabijin da kallo cikin tunanwan abdullahi da
suka karade mata kwanya musamman a safiyar
yau. Ta juyo ta dubi laila da bindin ido,ta ce.
"Wai cewa aka yi miki gardi na aura ne?" Laila
ta
tare ta da cewa. "Kwarai da gaske! Ba na ji an
ce
wani dan malam ba ne da ya ki halin malam...
Duk tsiya kuwa na san duk inda gidandanci yake
a nan ya yi gida ya tare...." Fatima ta tareta
da
dariya. "Gaskiya to kin jahilci waye malam,ni
dai
zan iya ba ki shaidar malam ya fi ko wanne
namiji iya soyayya,watakila don shi ya karanta
ya
san wace ce mace,ke nan ko kazami ne zai iya
ribatata masu rikita lissafi kamar
Abdullahi,idan

ban rufe ki ba fa ke nan!" "Ya kamata na
ganshi".
Da kalmar da laila ta fanshe mamakinta ke
nan,fatima ta ce. "Sai ki sami yammaci ki zo,ko
kuma wani week end" Laila ta sauke gwairon
numfashi ta ce. "Shi ke nan,mu ajiye
maganarsa
gefe mu yi ta alh.bayan doguwar jinyar da ya
sha
a dalilin cin amanar da kuka yi masa,jiya ya
dawo da alama kuma ya kasa ganin laifinki,shi
har yanzu sabuwa kike cikin zuciyarsa,ya bukaci
na zo ki sanar da ni bakin zaren idan akwai
hanyar da zai fara warwara bayan nasa
matakin
da yake shirin dauka wai duk dan a samu
wannan
kallagaggen yaron ya sahale miki...." Fatima ta
yi
murmushin yake,ta ce. "Wallahi ni babu wani
mataki da zan iya dauka akan Abdul laila... Ya
fi
karfina,kawai sai. Dai mu taru a bangaren
Alh....,sai dai ina rokonki abu daya,kar ki sanar
da kowa maganar cikin nan shi kuma alh kun

hadu ki sanar masa matakin da yake shirin
dauka
in dai zai fallasar da maganar auren kinsan
wutar
da na yi,to ya canja wani dan ba karamin
hatsari
maganar nan take da shi a kunnen kawu ba....
Kuma bana son abin da kawu zai la'ance ni....
Dan bai taba wulakanta diyancina ba, na
tabbatar
idan ya tsine min sai ta bi ni". A sanyaye laila
ta
ce. "In Allah ya so haka ba zata faru ba, da
kanki
ma zaki iya sanar da Alh,zo na kai ki asibiti ba
sai mu biya gidansa ba idan mun dawo...."
Fatima ta tare cikin zare ido. "Kina da hankali
laila? Idan tsautsayi ya hado ni da abdul ya
ganni fa... Ko kuma ya dawo gidan bai tarar da
ni
ba...." Cikin rashin ko'inkula laila ta ce. "Sai ya
yi miki abin da muke so kawai..." "Tunda ba shi
kadai ne matsalaha a lanurana ba, ina son
hada
dukkan burikana a lokaci daya,sakina da kuma

rufin asirina,da kuma rabuwa da Abdul
salin'alin
ba tare da na tafi da kewarsa ba, na tabbatar
idan na rantse ba zan yi kaffara ba, Abdul ya fi
Alh sadaukar min da rayuwarsa,don shi mai
kadan ne, yake kuma sadaukar min da kadan
din
ya hada min da lokacinsa da KWANJINSA,
sannan
da asarar farin cikinsa ta hanyata batare da ya
nemi fansa ba. Amma Alh fa! Duk kofar kishin
bakuta da yake toshe min da kudi yake toshe
min, wadanda ya mallake su babu adadi,kuma
yana fanshea da abin da ya aure ni
dominsa,wato
kyau na da nunawa duniya da abokansa
kyakkyawar matar da ya aura". Laila ta rasa
abin
da zata ce mata,sai ta dau jaka tana cewa.
"Taso
mu tafi in yaso idan mun dawo asibiti sai mu
biya a sai waya wadda za ku dinga tattaunawa
da Alh,sai kuma ki san hanyar da za ki boye ba
tare da ya kamaki da kokawa ya karbe ba".
Fatima ta san magana ta fada mata, amma sai

ta
kyale ta ta buge fa murmushi kawai ta mike ta
yafa mayafi suka fice ba tare da ta yiwa su
Hindatu sallama ba.
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
30)
Bayan laila ta sami wurin ajiye motar,ta fito ta
rufe tana kallon yadda fatima ke waiwaye
waiwaye ta kasa fitowa cike da mamaki laila ta
ce. "Wai wa kike son gani?" Fatima ta balle
murfin motar ta fito tana cewa. "Ko dai waye
bana son gani,ina fargabar kar na ci karo da
Abdul". Laila ta yi dariya ta ce. "Ina mamakin
yadda kike shakkar wannan mutumin wanda ke
yakamata ya yi shakka musamman da yake son
zama da ke karfin hatsi....". Suka jera zuwa
cikin
asibitin fatima na cewa. "Har yau ni ma
wannan
shakkar ke damuna,mutum sai ka ce wanda ya
yi
min sihiri,gaba daya ya mayar da ni wata
kidahuma". A kufule laila ta ce. "To wa ya

sani?"
Sakon zuwan fatima na isa ga likita,kafin ya ba
ta izinin shiga sai da ya kira Abdul a waya.
"Fatinma fa ta iso". Zuciyar Abdul ta buga,ya
ji
labarin kamar wani sabo a kunnensa da
sha'aninsa da fatima A rikice ya ce. "Dr da
gaske
fatima ta ke zata zubar min da ciki?" Likita ya
yi
ajiyar zuciya ya ce. "Ya wuce wai, tunda ga ta
ta
zo...." Suka ja shiru saboda likita ya rasa abin
cewa,Abdullahi kuma yana kokawa numfashinsa
da ke son ya tsaya cak! Har sai da ya sami fitar
da kwalla,sannan ya sami bakin magana.
"Likita
ba za a iya yi mata aikin daure bakin mahaifar
a
yau ba? Tunda kwanaki suka rage ya cika
watanin hudu?" A nutse likita ya amsa. "Za a
iya". Abdullahi ya yi ajiyar zuciya ya ce.$ "to
taimakon da zaka yi min ke nan, yi mata
wannan
aikin a matsayin na zubar da ciki,ku rabu lafiya

in
ta dawo gida sai mu hadu,duk da ina son
shigowa asibitin yanzu".. Da karsashi likita ya
ce.
"Shi ke nan ka kawo shawara mai kyau,Allah
kuma ya saukaka mana al'amuran...ya inganta
abin da aka samu, ya albarkace shi".$
Abdullahi
na nade kwallarsa ya ce. "Amin na gode". Suka
sauke waya,sannan likita ya kira abokin
aikinsa,suka dan yi tattaunawar sirri,kana ya
yiwa fatima izinin shiga. Ko gaisawa ba su yi ba
ya mike yana tattara takarda ya ce mata. "Ina
fatan yau ba ki ci komai ba?" Ta gyada kai cikin
shan kamshi,ya ce. "Kin tabbatar?" Ta gyada
kai,laila ta yi karaf ta ce. "Ai na yi zaton allura
zaka yi mata". Ba tare da ya dube ta ba,ya ce.
"A'a aiki za a yi mata a fitar da shi kawai".
Fatima ta zaro ido cikin dukan zuciya a tsorace
ta ce, "Anya likita babu matsala? Ni da nake so
ka yi min komai yanzu na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login