Showing 9001 words to 12000 words out of 34797 words
Chapter 4 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf
gurin,sannan ya hakura
ya
ninke sallaya ya shiga bandaki ya wanke baki,ya
jefa minti a baki ya tunkari dakin da karfin
gwiwa
yana ambaton Allah. Akwai alamun idonta
biyu,saboda yadda ta takure a can karshen
gadon.ta lulluba da wani bargon ta tattare masa
na kan gadon gefe guda,ya tura kofa sannan
ya
kashe gulob,kamar mai tafiya akan ruwa saboda
tsabar shauki. Ya tattare bargon da ta ware mai
ya ajiye gefe sannan ya janyo wanda ta
takura.
Sai ta motsa a firgice, ya hana zuciyarta kai
matakin karshe a firgitar bare ta dau mataki.a
rikice ya ce. 'Au fadima ba ki yi barci ba? Gajiya
ko? Bari kawai na yi miki tausa". Bai jira
amsarta
ba,ya shisshige mata ya nuna mata abin da yake
nufi.ta yi iyakar kokarinta na son ta
bijire,amma
da yake ba a sassakata da karfe ba,ga abdullahi
ya kware wajen rikita,sai ta bayar da kai bori ya
hau,musamman idan aka kirga watannin da ta
kwashe cikin kewa dan ma an halicci mace da
kawaici. Dukkansu babu wanda bai taka rawar
azo a gani ba suma da minti talatin,amma a
karshe sai ga su kace kace cikin kuka. Babu
wanda lamarin bai zo masa a bazato ba.
Abdullahi na saka ran akwai wannan
ranar,amma
bai tsammance ta cikin sauki haka ba.... Bai
kawo ta nan kusa ba.... Bai taba zaton hadin kai
gare ta kamar haka ba..... Ga kuma tsarin
likita..... Ga shi cikin yawaita ambaton Allah da
kuma neman tsarinsa daga abin ki..... Ga kuma
fadima a cikin mata sa'ida...... Kuka ma ya
zame
masa tilas dan shi yake nuna tukewar farin ciki.
Dalilin kukan fatima sun zarce nasa a yawa, sai
dai sun fi nasa nauyi sun kuma fi su tauri a rai,
dan nata ba su rabi farin ciki ba, na bakin ciki
ne
da kaico iri iri,ya ya aka yi ta sake haka ta
faru?
Ta ci amanar Alh ta dandanawa Abdullahi
zumarta,kuma matakin ne da zai hana shi
sakinta. To da wacce fuskar ma zata ci gaba da
kallonsa kuma sa wacce zata yi masa burga?
Idan ya ki sakinta ya ya shirin zuwa nan da
wata
daya da rabi? Kukanta ya tsananta sai shi ya
hakura da sheshekar nasa,ya himmatu
rarrashinta, da kalaman ban hakuri da na nuna
kauna har da wadanda bai taba tsammanin
kwakwalwarsa zata iya kirkira ba, bai samu ta
tsagaita ba sai da ya tuna mata. "Fatima kin
san
fa ba mu kadai ba ne a. Gidan nan, wani fa zai
iya jiyo wannan kukan naki," Ta yi dif! Illa
hawayenta da ya kara gudu saboda fargabar
kila
sadiya ta jiyota, kuma gobe zata iya ba ta
tabbas. Ya rungume ta dan kokarinsa na tsayar
da hawayenta,yana ci gaba da karanta mata
kalamai masu sanyi wadanda ko kadan ba su yi
tasiri akanta badan hankalinta ba ya tare da
shi,sai dai da yake Abdullahi jarumi ne mai
hakuri
neman so da juriya sai da ya jawo hankalinta ta
ba shi nutsuwarta har ta dinga jin ranta bai
rasa
komai da zai iya mallakar soyayyar mace ba,
idan
aka dauke ta tunda ta riga ta sadakar da nata
son ga soyayyar Alh. Sai ta yi masa bacci karya
tsawon lokaci yana shafa kanta zuwa
bayanta,har
ta kata alamar jan numfashin dogon bacci,
sannan ya rabu da ita ya tashi zaune
musamman
yana kallon fuskarta cikin kauna iri iri. Daga
karshe ya daga hannun yana rokon Allah. "Ya
ubangiji ka saukakawa wannan baiwa taka
al'amuranta,ka yi mata gafara,ka bude
zuciyarya
ta karbi gaskiya ni ma ka bani juriya a
lamuranta... Ka gafarta min tsawon kwanakin
da
zata juyo ta yi min kallon masoyinta... Ubangiji
ka albarkace nu da zuri'a ta gari....." Wannan
addu'o'I nasa suka dawo mata da hawayenta ba
tare da ta yarda ta motsa ba dan kar ya san
idonta biyu. tana kallon ya sauka gadon ya
shige
bandaki,ya fito da wankansa,karfe uku da rabi
ya
shimfida sallaya ya dubi gabas. Da ta damu da
son ta yi kuka,kawai sai ta mike ita ma ta shighe
bandakin tana wanka tana kuka har da
karamar
shesheka.
1 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.15) Ta rasa da ludayin da zata kamfato
wannan rayuwar da ke neman zame mata
dole,wato zama da abduk,zuciyarta ce ke son ta
yarda tsakani da Allah abdul ke sonta, sannan
ya
cika mizanin soyayyar wadda ta isa abin
kallo,bayab wannan me ya hadata da
shakkarsa?
Me ya hadata da shiga wani garari idan ya rabe
ta? Ai ba a kansa ta fara auren ki ba, amma Alh
bai taba dadata da kasa ba Bayan wadannan
tambayoyin da zaciyarta ta kasa amsawa,akwai
illolin da za su hana ta zaman auren Abdul ko
da
kuwa ta hadiye soyayyar Alh. Shekarunta
talatin
da biyu ke nan a duniya,tsawon wannan lokacin
ba ta taba dandanar zakin so ba sai watannin
da
suka wuce wanda ta ke zargin tana kaunar
Alh,duk da ranta na raya. Mata son nasa kawai
zata tsira da shi a aurensa, tunda bai dace da
muradan ta na mijin aure ba kamar yadda ta
shekara goma da auren nasa,amma dai dai
rana
guda ba ta taba farin ciki da auren ba. To yau
tsautsayi ya gamo ta da auren Abdullahi wanda
ya girme mata da shekara daya kacal, sai dai
ya
iyawa dabi'arta kwarai! Ya mallaki kirki da
kyautatawa wadda su ne makamashin samun
soyayyar mace.kirkin aljihu na fatar baki na
bautawa da gangar jiki na hakuri,na sadaukar
da
lokaci,na nuna damuwa a cikin damuwarta,Duk
abdullahi ta yarda ya mallaka wadannan duk
da
bai mallaki makudai kudade ba,amma duk da
wadannan ..... Shekarin nasa babba ne matukar
a
zuci,tunda gashi ya ajiye mata uku yana shirin
kawo ta 4. Wannan shi ne matsalar tata, wadda
abin mamaki sa ta fi kona ranta fiye da na
katangar da yake shirin ginawa tsakaninta da
Alh,da kuma yake shirin ginawa tsakaninta da
Alh,da kuma na alfarmarta da ya keta a yau
da
kuma shakkat ita ce kuwa ta biye masa hankali
kwance da hadin kan da sai ta rantse ba ta taba
ba wa alh rabinsa ba? Tun tana kuka kamar ta
hadiye zuciyarta har ta hadiye din ta koma
hawaye,kuma ta bar tunane tunane da hasashe
hasshen da suka cika zuciyarta. Ta yi wanka ta
fito daure da towel tana ta faman ajiyar
zuciya.Ta
bude wardrobe ta dauki wasu kayan baccin ta
zagaye Abdullahi yana sallah ta fice fala.ta
saka
kayan sannan ta nemi kujera ta zauna kawai ta
zabga tagumi duk da ta yafewa tunani,amma
hawaye fa na aikinsa har toshe baki ta ke kar
kuka ya kubuce sadiya ta jiyo. Yana sallame
raka'o'in da ta fita ta bar shi yana yi ya biyo
bayanta,saboda ciwon da kukanta ke masa,me
kama da saukar narkakkiyar dalma a gyambo.
Tun da ya fito ta sanya masa ido irin kallo na
rashin hayyaci,ya zauna kujerar da ke
fuskantarta
ya zuba mata ido shi ma, amma shi da nasa
hayyacin,sai dai zuciyarsa a dame ta ke kwarai
da tashin hankali. Ya san wannan tagumin ta yi
shi ne kawai amma zuciyarta ba ta aiki bare ace
tunani ta ke,ke nan yana bukatar dawo da ita
doka da oda tukunna idan ma rarashi zai yi ya
sami shiga. Ya koma ahannun kujerar da ta ke
zaune ya dafa kafadarta,ya ce. . "Fatima kina
son
yanke kauna da rahamar ubangiji ko,ko kuma
kina son karfi wajen cimma burikan ki?" Ta
dago
kai ta bi shi da kallo,sannan ta sauke numfashi
ta shiga goge hawayenta wanda ta ke son
tilastawa kanta tsayar da su,ko don kara su ci
gaba da tafiya a banza,lokacin amfaninsu bai
zo
ba dan tana ji a jikinta in dai zata rayu da
auren
Abdul,to an budewa rayuwarta kuntataccen
shafi.
Ganin ya sami hankalinta,sai ya dora cikin
hawaye. "Na yi nadamar abin da ya fari da mu
yau ba tare da na nemi aminciwarki hakika
ba,na
yarda abin da na yi bai kamata ba, amma ina
rokon afuwan in Allah ya so ba za ki kara
kamani
da laifi iron wannan ba..... Na miki wannan
alkawarin dan ki san ba shi kadai ne makasudin
aurena da ke ba,akwai fatan zamowarki uwar
iyalan da zan yi alfahari da su manzon Allah(S
A
W) ya yi alfahari da mu gaba daya,kin ga ke
nan
kamata na fi nema daga gare ki ba. Gara na
nemi
amanincinki da yardarki na zamowa iyalina don
ta
wannan hanyar ne wadannan zasu saukaka gare
mu.... Dan haka nake nadama,kuma ba zan
fasa
neman afuwanki ba fadina..... Idan ma ba ki
gamsu ba zan iya janye jikina daga shigowa
dakinki har sai kin yi min izin-,....
3 · Like · React · Report · May 16, 2015
Maimuna Idrees Matawalle
Tnx
1 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
16) Sai a wannan lokacin ta kara dubansa
tana hawaye ,ta ce. "Don Allah abdul ba ka ji a
ranka ka zalunce ni ba......?" Ya yi saurin tare
ta
yana gyada kai. "Na ji.... Tabbas na ji!" Ta
koma
yi masa kallon zargi da tuhuma,ta ce. "Amma
ka
san da haka kake son ci gaba da rike ni cikin
zalunci har kake kirarin mayar da ni kamar
wadda
aka rataye,kewa da gorin matanka ya kashe ni
ko. "Zan yi hakan ne da zabinki, kuma idan har
zai faranta miki rai ko da zai bakanta min". Ta
fara gyada kai cikin sartun hawaye. "Idan
haka ne
kana son farin cikin na sallama ni kawai,shi ne
kadai abin da zai faranta min rai.ina zargin
kuma
ba zaka kalubalamce ni da komai ba,ka dora min
idda ko? Yanzu ina da damar da zan yi zaman
halali da Alh?" Ya yi saratro yana kallonta,har
ta
fitar da rai zai ce wani abu,ta dora. "Abdul don
me zaka yaudare ni? Idan ka san ba zaka
yaudare ni? Idan ka san ba zaka iya aurena ka
saki ba, don me ba ka sallame Alh da tayin
aurena da ya yi maka ba? Ban taba tsarawa
kaina miji irinka ba wallahi... Ni ban iya
hayaniya
ba ban iya bakat magana ba...kusan shekarunmu
daya,kai babu haihuwa ni babu.... Da me zamu
ji?
Ta ina zamu yi tarbiyar da 'ya'yan da kake
mafarki?... Ko ta ina ba mu dace da Abdul,ka
dubi girman Allah ka sallame ni na tafi inda na
fi
wayo inda zan iya rayuwar da na saba.... Kar ka
zama me son kai Abdul,Alh ya fi ka bukatata.....
Ba shi da kowa bai san son kowa ba sai nawa".
Ya yi saurin rufe mata bakinta da tafin
hannunsa,
ya ja ta ya rungume,tsawon lokaci sannan cikin
rawar murya ya ce. "Ina da kishi fa fatima,ina
hadiye iyakar abin da zan hadiye cikin yi miki
kawaici akan Alh, saboda haka kar ki kara
ambaton sunansa a gabana,kin ji?
1 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
17) Ya yi saurin rufe bakinta da tafin
hannuwansa, ya ja ta ya rungume,tsawon lokaci
sannan cikin rawar murya ya ce. "Ina da kishi
fa
fatima,na hadiye iyakar abin da zan hadiye
cikin
yi miki kawaici akan Alh, saboda haka kar ki
kara
ambaton sunansa a gabana,kin ji?". Sai ta sami
kanta da kasa tanak masa. Suka dauki lokaci a
haka,sannan ya dagota yana kallon kwayar
idonta. "Fatima,ki rabu da zaciya da
sakokinta,sai
ta saka miki dubu babu alkhairi a cikin daya,
lura
da ita duk abin da ta raya miki idan babu Allah
a
cikinsa ki watsar kawai,ki daina barin shaidan
na
wasa da zuciyarki,shi ne ya raya miki yanzu na
dora miki idda kin halatta miki auren Alh? Kin
jahilci hukuncin da ya haramta miki auren Alh
fatima, manzon Allah (S A W) ya tsinewa mai
halattawa da wanda aka alattawa,ko kin manta
na san da wannan a tsakaninmu? Da na yi miki
shiru sai ya kuma yi miki wasu sakokin. Ba ki iya
hayaniya ba... Shekarunmu ba ki shirya auren
mutum irinan....... Ashe mutumin da ba shi da
wani garanti a rayuwarsa wadannan hujjojin
sun
ishe uzuri? Dama yadda ka tsara rayuwa kake
samunta? Ina tsammanin ke za ki fi bayar da
wannan shaidar dan tun kina budurwa kike
shiryawa kanki mijin aure. Ga shi shekarunki
sun
fara nisawa amma ba ki cimma wannan burin ba,
me ya hana?". Suka dauki shiru tana jin
nauyin
nasiharsa cikin ranta,ba ta ga laifinsa ba,
amma
ta fara tsanar kanta da kaicon yadda ta ke
samun rayuwa. Ya lura tana son komawa kuka
sai ya dora da cewa. "Ki dan buda min filin a
zuciyarki kadan yawan shekarunmu daya wani
abin kaye ne a cikin soyayyarmu har nake ji a
raina kamar hakan na kara min gardin
soyayyarki,
wadanda ke sa hasashe kala kala masu yiwuwa
da wadanda zasu yiwu ba.na ji raina da ace
mutum na da ikon da rayuwarsa,tabbas da na
jira
wannan lokacin na fi koshi taf! A cikin
soyayyarki,zan fi gamasar da ke irin son da
nake
miki, sannan ni ma zan fi gamsuwa da farin
cikin
kasancewa tare da ke ko yaushe. Duk da haka
zan yi kokari na kwatanta rokona da ke kawai ki
bire katangar debe kaunan a tsakaninmu,insh
a'Allah sai mun wadata da 'ya'yan
kanmu,sauran
korafe korafen ki kuma mu kai wa Allah kuka
sai
ya magance". Yana diga aya ta zare jikinta ta
mike ta shige daki har da murza mukulli.bai
nemi
takura mata ba sai ya bita da kallo kawai.ya
jima
yana kallon kofar dakin,sannan ya sauke kai ya
kishingida cikin jinjina taurin kan
fatima,wadda ko
kadan ba ta jin rarrashi sai dai tana da saukin
jayayya. Da asuba yana dawowa masallaci ya
shiga kwankwasa mata kofa yana kiran sunanta
a
hankali. Dole ta tashi ta bude dan kar sadiya ta
sami abun fada. Tana sanye da hijabi ta zauna
bakin gado ba tare da ta yarda sun hada ido ba,
ya janyo stool ya zauna a gabanta yana ta
faman
kallonta,sai can ya kira sunanta a hankali.ta
daure ta dago kai ta kalle shi sai ta ga kwalla a
idanunsa,sai kawai ta yi kasa da ido jiki a
sanyaye. Ya kuma tausasa murya ya ce. "Don
Allah ki yi hakuri". Ta sauke ajiyar zuciya
kawai,ya kara raunana murya,ya ce. "Na fi ki
damuwa fatima,don Allah ki yafe min..." Kawai
sai ta sami kanta da kada masa kai idonta ya
fara zubar da hawaye. Ta fara jan jiki zata
tashi
ya yi saurin ruko hannunta ya yi kokarin suka
hada ido,ya girgiza mata kai. "Na gode,saura ki
cirewa zuciyarki damuwa ki saukakawa kanki
al'amura,ki karantawa kanki dogon buri da saka
karfin wajen cimmasa. Duk wani abu da yake
gaibu dan adam bai isa samar da shi ta hanyar
karfi da dabara ba fatima balle ya tilasta mai
hukuntawa ya hukunta,Allah ba a yi masa dole
fatima,kuma ba a laynace masa aikin da aka
bayyanar da wanda aka boye. Saboda haka nake
shawarartarki zama cikin hankalinki,ki sami
lokaci
ki yi tunani mai kayu ki raba kanki da wannan
kuncin,ki sake ki yi abin da aka halicce ki
dominsa,wati bautar ubangiji. Sannan ki ware ki
more ni'imar da ubangiji ya samar dominki,ki
bude zuciyarki farin ciki ya shiga ki rayu cikin
farin ciki da kowanduk abin da zaki so ki so shi
dai dai misali.haka ma wanda za ki ki, domin
manzon Allah (S A W) ya hore mu da rikar
al'amura tsaka tsaki. Don haka ba zan taba
matsa miki ki so ni ba, amma zan shawarceki cire
kiyayya ta daga zuciyarki saboda har kasa ta
rufe
idona babu saki a tsakanina da ke, ki kawar da
kai ga kallon ni ban cancanci kasancewa mijinki
ba, saboda ba ni da kudi duk da na yarda
neman
dai daito a aure muhimmanci abu ne, amma
aurenmu ba na shiri ba ne. Wayar kanmu kawai
muka yi cikinsa, kuma da yake ba kutatacce ne
ni
ba sai na ga kamar zan iya kwatanta
dawainiyarki,duk da ko na gaza ubangiji bai
janye
miki yi min biyayya da kayutata min ba a
matsayin bautarsa. Dukiyar nan ta ki ba zata
zama uzurinki ba, kuma ba zata cike miki
wannan
gibin ba... Kin fahimci ni? Ki kaddarawa ranki
aure na wata jarrabar ubangiji ce irin ta rashin
samun abin da rai ke so,ki yi hakuri mai kyau
Allah sai ya ba ki tarin lada kin ji?
HafsatZuciya d kwanji
18) Ya kurawa kwayar idonta ido, wadda ke
zubar da hawaye, zuciyarsa ta kara rauni,ya ja
ta
jikinsa ya fara rarrashi. Rarrashi irin wanda
babu
macen da ke juyar da shi,ya rungume ta
sannan
ya share hawayenta da harshensa tare da
sumbatarta. Tunda kwkwalwarta ba zata iya
manyan ayyuka biyu a lokaci guda ba, sai ta saki
hawayen ta karbi wannan rarrashin mai kunce
lissafi tare da nzarin makin da ya kamata ta ba
wa wannan gwarzon lakantar mace da abubuwan
da ke dauke hankalinta. Kamar masu shirin
komawa ruwa. Sai dai sun mallaki zuciyoyinsa,
muradinsu kawai su gusar da tsatsa a zuciyar
juna. Abdullahi na son nuna masa ta gamsu da
rarrashinsa,suka bata lokaci kafin su hakura da
juna,suka hada ido Abdullahi ya sakar mata
wani
murmushi sace zuciya,sai ta shanye shi ta kawar
da kai fuskarta babu yabo babu fallasa, ta ja
jikinta gado a kasalce tana jan bargo,ya saurin
sa
hannu yana taya ta, yana cewa. "Bacci ko? To
dan runtsa sai ki yi wanka ki karya,ki kwanta ki
huta sosai". Ya fara gyara dakin,sannan ya
wuce
falo.nan ma ya mayar da komai fes ya fesa
freshner ya dure kicin,ranar har wanke wanke
sai
da ya yi,samar musu karin kumallo,kana ya
shige
wanka, bayan ya fito ya tayar da ita,ita ma ta
shiga wanka. Suka karya kumallo tare kowa shiru
idan ka. Dauke sakon murmushi kauna da yake
dawainiyar jafa mata ita kuma ta hadiye ta
maze
har ya shirya ya fice bayan ya karanta mata
kalaman kauna masu zaki. Ita kuma ta koma
rudadden baccinta mai mamaye da Abdullahi
da
komai nasa,a numfashinta mafarkinta,hars
henta,kunnuwanta da dukkan iskar da ta ke
shaka,sun tura Alh wani dan sako mai kama da
kurkuku suka zagaye shi da tausayi, wanda ke
son kokawa da sabon lamarin Abdullahi