Showing 33001 words to 34797 words out of 34797 words
Chapter 12 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf
Haj sa'adatu kanwar uwar Alh
tana
nan tana zuba mana tijara iri iri da kashe
kashede
saboda yunkurin kashe aurenki da kike don ki
koma gidan dansu,wai har da yunkurin zubar da
ciki... Fatima wacce irin busa duniyar na ke yi
miki? Da kin mutu wajen wannan yunkurin naki
me za ki fada wa Ubangijiki...? Fatima ta dade
kirji cikin tsoro da tashin hankali ba na batun ta
zubar da ciki ba, na ta inda maganar ta fita har
ta isa kunnen dangin Alh. A rikice ta ce. "Momi
inji wane gwanin sharrin? Ni ina ma na ga cikin
da har zan zubar?" Momi ta yi mata wani
mugun
kallo ta ce. "Ko? To wa kike da shi wanda ya
wuce kawarki laila? Idan sharrin ne ma ita ta yi
miki don ta tabbatar da ita kuka je asibitin....
To
ko sharri ne dai ni da kawunki mun gaskata don
mun san za ki aikata,ke fa tuni mun fahimci
yunkurin kashe auren da kike daga inda
Abdullahi
ya hana ki waya ya hana ki mota,ya hana ki
kula
da sauran kasuwanci ki muka san akwai wata
akas. To karkade kunnenke da kyau,daga cikin
kalaman cin mutunci da sa'a ta yi mana ta
furta
cewa,idan ma zafin talauci ya fara ratsa ki kike
son komawa gidan dansu,to ki yi magana za su
dinga yankar miki wasu kudade masu kauri duk
wata, su dai ba sa kaunar zamakin cikin a
halinsu
don ke ba alkhairi ba ce a rayuwar dansu. Sai
kuma sakon prof.ya tabbatar miki in sanar miki
daga inda kika kaso aurenki shi kuma wallahi ya
sallame ki,sai dai ki nemi wani uban ba shi ba. Ni
ma kuma na goya masa baya fatima,ki nemi
wata
uwar ba ni ba, Allah ya gani mun yi iyakar namu
kokari har fitinarki ta gajiyar da mu.... To bai
kamata a yi mutuwar kasko ba, ke kin sarayar da
naki mutuncin da kimar,mu kuma mu yarda mu
sarayar da namu ta dalilinki ba... Ina amfanin
wulakancin da sa'a ta zo ta yi mana jiya?"
Kawai
sai momi ta fara hawaye. "Innalillahi wa inna
ilaihi raju'un" kawai fatima ke maimaitawa a
cikin
ranta lokacin da ta ji. Zuciyarta ta yi nbala'in
kuntato,tsoro,b acin rai da bakin cikin sun cika
ta
tafi ita ma sai hawaye ta ke ta kasa tankawa.
Sai da ta ga momi ta mike zata bar mata falon
sannan ta yi saurin ruko ta ta fara fitar da
sautin
kuka mai tsuma rai. "Momi ku yarda da ni akwai
sharri cikin maganar nan...." Momi ta tare ta a
kufule. "Ai daga maganarki ta farko kika
kankare
sharrin don me? Ko daya babu Abdullahi cikin
maganar nan, amma ina fara magana kika
kokar
kare,babu dalili zai kore ta? Ko kiransa zan yu
na
ji daha gare shi?" Da sauri ta girgizxa kai cikin
kuka,momi ta yi tsaki ta dora. "Sannan kin ce
ina
ma kika ga cikin da za ki zubar, wannan na
jikinki
me ye? Ko don kin tanadar masa zubewar kike
nufin za ki iya nunke mu bai bai? To me kike
shakka ne bayan ke kika haifi kanki? Ai kawai ki
yi dukkan abin da ranki ya. Kawata miki, mu
mun
zama 'yan gani da ido a cikin rayuwarki" Ba ta
jira cewarta ba ta yi tafiyarta ta barta tana
cikin
matsananciyar damuwa don haka ya kyale ta
tayi
tunani a nutse har zuwa gabar da zai sami abin
ce mata. Duk da dare ne hasken fililun titi da
na
motoci suka sanya shi gane motar da ke
gabansa, wato ta Alhaji ce direba na jan Alh da
kuma wata mace. Ya juya ya dubi fatima,sai ya
lura hankalinta ba ya jikinta,ta rafka taguni
kawai
fuskarta da alamun hawaye. Ya ciji lebe cikin
murmushi keta,ya ce. "Fadima kin gane motar
nan da ke gabanmu?" A sanyaye ta dago ta
kalli
gabanta, kallo daya ta gane abin da ke
faruwa,sai
kawai ta kawar da kai da sauri,Abdullahi ya
sauke numfashi yana kallonta a kaikaice,ya ce.
"Dama ya yi aure ne?" Ta yi dif har ya gaji da
kallonta ya mayar da kai zuwa titi, har lokacin
da
motar alh ta saka siginal zata shiga wani gida
kayan sanyi,kawai sai abdullahi shi ma ya sanya
siginal ya take masa baya. Da sauri fatima ta
dube shi bakinta na rawa amma ta kasa
magana.
Ba tare da ya dube ta ba,ya ce. "Waccan matar
ce ta yi min kama da laila, Shi ne nake so in
tabbatar". Ambaton sunan laila kawai wani
katon
rauni ne a zuciyar fatima bare batun wai ga ta
tare da Alh,da kuma wannan daren, sai ta ji
numfashinta ya fara sasarfa tana bin motar da
kallo har ta yi fakin,su na ma suka yi fakik nesa
da su. Direba ya fito ya bude wa Alh,sannan
laila
suka fito suka shiga ciki tare. Abdullahi ya
dauke
kai yana kada kai hade da rera wakar cin
amanar
kauna,fatima ta yi dif saboda zuciyarta ta kara
wani zafi,ji ta ke ina ma yanzu ta hadiye
zuciyar
ta bar duniyar gaba daya, wanne irin tashin
hankali ta ke tsintar kanta a ciki yau? Sai da
abdullahi ya koshi da yarfeb da yake
mata,sannan
ya yaficeta ya balle murfin motar yana cewa
"Zo
mu shiga mu ga abin da suke yo don kar mu
yanke musu hukunci da zato". Kawai sai ta sami
kanta da zuciyar balle murfin motar ta fito ta
bi
shi suka jera. Alh da laila an kama kujera ana
ta
kurbar fresh milk cikin annashuwa, Abdullahi ya
zarce karbo musu na su kason,amma fatima
idonta rufe ta nufi wajen su kai tsaye. Alh na
dora
ido a kanta zumbur sai ga shi a tsaye cikin
tsnannin rikita,da ambaton. "Fatima! Ya ya
aka yi
kika san ina nan? Cikin tsananin fushi ta ce.
"Ba
kai na biyu ba, wannan muna fukar na shigo in
gani da idona.." A dan kunyace laila ta ce. "Da
na
yi miki me? Don kin ganmu a nan tare? Ai
matsalarki muka zo tattaunawa a sirri". A
tunzure
fatima ta ce. " Ai ni ba ni da matsla wallahi,ke
da
shi ku. Ne masu matsala don ba ku ganni ina
ketare gwadabe na ba..." Alh ya yi dira dira
cikin
rudewa,ya yi kamar zai ruko hannunta, ta yi
saurin ja da baya. Dai dai lokacin Abdullahi ya
iso
da ice cream a hannunsa na dama yana
sha,yana
kuma rike da wani a hannunsa na hagu,da
alamin
ko a jikinsa hayaninyar da ya tarar.ya mikawa
fatima daya ice cream din yana cewa. "Ashe
abokin arziki kika hango kik barni ni kadai? Ta
runtse ido alamun tsanarsa bacin rai ta bude
idop
tana duban ice cream din da yake nuna
mata,ta
ce. "Abdul ba zan sha ba. Sai kawai ya ja
kujerar
ya zauna yana lasar ice cream dinsa,ya ce. "To
ku gama gaisawa mu tafi" Nan fa alh ya zo
wuya,cikin shakewar numfashi ya ce. "Abdullahi
har ka kai tsawon da zaka yi min wannan cin
mutuncin,ka san kuwa ba ka isa ba? Me ya hado
ka fita da fatima....? Karaf cikin masifa
fatima ta
tari numfashinsa. "Kai da girmanka me ya
hadoka
fita da wannan tsinanniyar?" A rikice Alh ya
zaro
ido,ya ce. "Fatima goyon bayansa za ki yi, kina
nufin abdullahi ya fi ni matsayin a wajenki...?
Fatima kin san kuwa muhimmancin ki a
rayuwata...? Na rantse miki zan iya komai don
na
tsira da ke, ciki kuwa har da kisan kai idan ta
kama... Saboda haka kai ka shiga taitayinka".
Yasa kai ya fice a fusace. Fatima ta janyo wani
dogon tsaki ta dauke kai kai daga kallonsa ta
sauke akan laila wadda ta yunkuro ta ke son ta
wanke kanta. "Fatima ni kike kira
tsannainya...?
"To me ce ce ke? Mijin aurenki ne ya kwaso ki a
bayan mota kuka nufo nan don ku sha minti, da
wannan daren ko? Kawance da ke ai bai yi ba
laila..." Ita ma laila ta zo wuya don haka ita ma
ta yunkuro cike da bacin rai. "Ai babu bambanci
tsakanina da ke, shi wannan matsiyacin da kika
dauko kuka taho nan me ye a tsakaninki da
shi...?
Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
39
Fatima ta tare ta. "Akwai abin da tsinancewar
ki
ta hana ki taka matsayinsa,wato aure,kin san
kuwa ko banza masa ta fi kashin shanu,don ko
me wankin takalminsa kika samu ya adana ki a
dakinsa ya fi wannan gantalin da kike... Ko da
yake ina tsammanin kin yi zaton gulama da
sharrinki ya ishe ki taka matakan da na taka,
kika
kwashi kafa dangin Alh tsugudidi..." Jin fatima
ta
debo fasa mata ciki ya sanya ta tarewa da nufin
tona mata asirin gaban mijin da ta ke shakka.
"Auren naki na gaibu,mara ma'ana da
manufa...
Ai in dai bariki ne, to tare muka kwaso shi da
ke,ko kin taba ni zuba da ciki? Ni kuwa satin da
ya wuce ma na raka ki zubar da ciki,a uare kika
sami cikin kika zubar?" Sai a lokacin fatima ta
tuno akwai Abdullahi a wajen.ta yi saurin
dubarsa
cikin tsoro da firgici amam sai ya dauke
kai,fuskarsa kuma ba ta fassara mata komai
ba,ya koma bin laila da kallo wadda ta ke ficewa
daga wajen. Fatima ta yi tsaye kawai a wajen
cikin yanayi na kila wa kalan yadda rayuwa zata
cinmata. Abdullahi ya dake ya karasa shan ice
cream dinsa ba tare da ya dubeta ba,ya ce. "Zo
mu tafi" Inna lillahi wa innan ilaihi raju'un,ta
ambata a ranta ta sa kafa ta biyo shi cike da
fargabar ruwan bala'in da zai sheka mata idan
sun koma gida,ko kuma kalar fushin da zai
mata
wanda ta tabbatar wanna dole ne daga yadda
ta
fahimci takunsa a yanzu. Bai ko jira ta sun jera
ba ya wuce mota,ita kuma ta bi shi kamar kazar
da kwai ya fashewa a ciki, ya shige mota abinsa
ba tare da ya bude mata kamar yadda ya saba
ba. Jikinta na bari ta bude ta shiga ya tashi
motar ya fice a fusace. Suna fitowa daga
harabar
wajen suka wuce laila tsaye tana ta faman tare
adai daita sahu,suna wucewa saboda daren da
ya
fara yi. Har sun dan gota ta kadan sai Abdullahi
ya sauka titi a hankali,ya yi fakin bai tankawa
fatima ba ya fice daga motar.ta bi shi da kallo
cikin dukan zuciya,sai ta ganshi kai tsaye laila
ya
nufa. Nan numfashinta ya fara yin sama
sakamakon hargitsawa da cikinta ya yi,ciwon
cikinta ya dawo mata sabo. Duk da haka ba ta
kasa dauriyar tattara hankalinta ka su ba.
Kafin
ya karasa laila ta fara tafiya,don haka yana
tarar
da ita suka jera. A nan zan dakata sai mun
hadu
a littafi na uku taku..... Amierah S man meh copy n paste. ....
Compelled by hauwee jidderh abdulkadir AKA mss jidderh