Showing 18001 words to 21000 words out of 34797 words

Chapter 7 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf

ba babu
abin da zai hadata fita da shi, sai ta yarda, sai
dai ba cikin walwalar fuska ba. "Ina maganar
zuwa duba mata talabijin?" Ya dinga nazarinta
yana son gane abin da ke zuciyarta,darare ya
ce.
Ta kara tamke gira,ta ce. "Don me? Idan kuma
kewa ce ta dame ta fa? Ka san dole akwai
ciwo,mace da mijinta mata har biyu su aure
matshi,ban da ta uku me haramar zuwa
maimakon layin kwanaki hudu da ta ke hawa ta
koma na shida.... Ka je ka rage mata kewa
kawai,duk da zan dan yi muku cikas a gabana
za
a yi gyaran, amma na san ko da kallon fuskarka
da sauraron muryarka kawai zata iya rage wasu
kewar". Da zolaya ya ce da ita. "Idan aka fasa
maganganun nan naki fa tarin ma'anini ne da
su". Ta kada kafada tare da dauke kai. "Na

sani,amma na san duk yadda za a fassara maka
wasu ba lallai ka fahimta ba, saboda bambancin
dabi'u da ke tsakaninmu ta dalilin jinsi". Ya
tari
inda ta mayar da kanta yana cewa. "Ni kuma
sai
na ke ji a raina na fahimce ki fiye da yadda na
fahimci tafin hannuna,duk da kawu a
fuskokinki
kin fi nacin nuna min daya". Cikin rashin
fahimta
ta ce. "Waccec?" Da sauri ya amsa mata.
"Bayyana abin da ke cikin zuciyarki, ko da
bayyanawar zata ci karo da burinki". Ta yi
kasake,sannan ta ce. "Me kake nufi?" Ya
ce,"ki
tambaye kanki yadda kike jina a ranki game da
sadiya. Ni dai irin wannan na daga cikin abin da
ke kara min karfin gwiwa a cikin soyayarki.ina ji
a
raina duk ranar da sauran fuskokinki suka
zama
'yan gida a tawa fuskar da wuya a sami namijin
da zai kai ni farin ciki". Ta jima tana
nazari,amma

ta kasa cankar inda ya dosa,kawai sai ta yi
masa
shiru,ya jima yana kallonta sannan ya ce. "Ki
tashi ki shirya kafin sannan na dawo daga duba
mata talabijin" Ta mike a kasalce tana cewa.
Jirani zaka yi na shirya,k duba mata mu wuce".
Ba ta dami kanta da wata kwalliya ba, ta baza
hijab suka fice,tiryan tiryan har dakin sadiya.
Ta
sami kujera ta harde tana kallonsu,sadiya na
satar watsa mata harara tana yiwa abdullahi
bayani cikin yanga. "Wani film nake kallo na
tashi
sallah,wai ina dawowa na kunna sai ta ki
samuwa". Ya kunna talabijin din yana cewa.
"To
ke ce ba ki da aiki sai na kallo ba dole talabijin
ta
buga ba?" Ta kara karya murya,ta ce. "To Abu
Turab ba sai da kallon mutum zai kara gane inda
duniyar ta sanya gaba ba, kai ka ga film din da
nake kallo yanzu? Labarin wata tsohuwar mace
ce ta gama cin nata zamanin kawai ta sami yaro
ta aura,kuma don zalunci ta raba shi da
matarsa

da 'ya'yansa.ta karade danginsa da kinibibi
kowa
ta mallake,shi kansa sai yadda ta so ta ke juya
shi, ga ta yarinya sabon jini a gefe,kai! Ai
zawarawa ba su yi ba wallahi". Da yake Abdullahi
ne bai gane inda tuggun yake ba a maganar
sadiya,sai ya amsa mata da gaskiayar ransa.
"To
ina ruwan so da tsufa? Sai nawa za ki ga
tsohuwa ta yi abin da yarinya ta kas,su
'yanmata
me suak sani ban da tsabar girman kai da son
iyawa,amma kwakwalwarsu girman kai da son
iyawa,amma kwakwalwarsu empty. Sadiya tana
juya idanu ta ce. "Koma dai yaya suke sun fi
daraja tun da manzon Allah(S.A.W) ya yi
umarni
a aure su. Ya kuma amsa mata. "Sai kuma kika
manta shi da bazawarar ya fara,wadda ta yi
abin
arzikin da ba a sami budurwar da ta yi abin
arzikin da ba a sami budurwar da ta yi kamarsa
ba. Gudunmowarta a tarihin muslunci gagaruma
ce. "Ai ba zaka taba hadata da matan yau ba,
masu auren mai kudi su tatse shi tas! Daga

bisani su fita su sami yaro karami su aure,su ma
yaran da rashin sanin ciwon kai sai kwadayi ya
rude su su afka,sai ka ga sun dawo a
hannu,babu
wan babu kanin, babu kuma kudin kuma babu
KWANJIN su kuma an sha da kuruciyarsu".
Abdullahi ya sunkuya yana duba yadda ta hada
wayoyin ya ke amsa mata cikin dariya. "Ai gaba
daya sun yi min dai dai,da tsohuwar da yaron.
Ai
ba a hana mace ta auri sa'an dan cikinta ba ma,
shi ma kuma an ba shi damar aure saboda
kudi,idan kwadayin ya kai shi auren tsohuwa
mai
kudi ai ba kauce hanya ya yi ba, sai ki ga ma ta
fiye masa fakiriyar budurwar da babu
kudin,babu
kuma kyan hali.yana fama da talauci yana
fama
da rashin tarbiyarta.ita kuwa tsohuwa ta san
darajarsa,ya san tata, shi ke nan ungulu ta
biya
bukata sai balbela ta tafi da farinta. Sadiya ta
yi
iyakar kulewa,dan ta yi zargin da gayya ya yaba

mata wadannan maganganun, musamman da ta
ga hankalin fatima kwance tana murmushi. A
kuntace ta ce. "Amma dai ba haka aka so ba".
Ya
ce,"wa ya fada miki? Aure fa wuce duk yadda
kike
tsammaninsa.duk tsufan mace da wahala ta
rasa
abin da zata burge wani namiji da shi,bare a yi
kirarin ya zauna da ita bisa tilas,kin jahilci
labarin
ne sadiya,amma a mata babu babba babu
yarinya,mai hikima ce kawai zata iya samun
kan
mijinta". Sadiya ta yi dif! Ranta duk ya baci.
Ganin ta yi shiru ya sanya fatima sako baki cikin
hirar tasu. "Kayya abdul! Ai duk wanda ya
rigaka
bacci dole ya riga ka tashi,kuma da kokari ake
samun daukaka ba da kake ko uba ba, amma fa
ga wanda ya gane cewa shi zaman bariki ba
gayya ba ne, kowa da kafarsa ya zo, kuma
halinsa ke janyo masa jama'a". Sai yanzu
abdul
ya fara caftar karatun,ya saki wayoyin da suka

harde yake gyarawa da fuskar damuwa,ya ce.
"Haka ne. To mu bar maganar". Sadiya ta
fashe.
"Don me za a barta,dan kar in fadi gaskiya rai
ya
yi daci? Ai duk wanda bai ji kunyar hawa jaki
ba,
to kuwa jaki ba zai ji kunyar nana shi da kasa
ba". Nan da nan abdullahi ya bata rai. Ya tsuke
ido,ya ce. "Bana son rashin mutunci fa sadiya,
dama don haka kafa da kafa kika je kika rakito
mu?" Cikin tabe fuska ta ce.
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
INA HANYA GOIN BACK TO KADUNA FROM ABUJA....
Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
.Zuciya d kwanji 2
25) "A kaddara ma haka ne, idan ba ta yi
kasadar biyo ka ba zata ji abin da ba zai wa
ranta dadi ba ne? Ko tana ganin kafata a
dakinta
da zata ganni da kai ta ce zata shiga tsakani,
kuma da zata yi min maganar zaman bariki ba
gayya ba ne,da fa ma ba a san asalin ungulu ba

sai ta yi burgar daga masar ta zo. Na ga kina
amaryaki ma shar kofar danki ma bai ishe shi
kallo ba, sai da aka shiga aka fita aka wasko
kansa shi ne yanzu za ki yi min maganar hali?
To jiya ma me ta yi bare yau, kin san auren fari
shi ne auren so,ke kuwa kin watsar da naki
ladan
sai dai ki ga ana yi.... Kin fara ganin shaida
dazu
da kuncinki ya kusa diban yatsu biyar....!"
Abdullahi ya zuba mata ido cikin bacin rai har
sai
da ta dire sannan ya kada kai, ya ce. "Shi ke
nan
sadiya,kin kyauta sai dai ki sani ba fatima kika
wulakanta ba, ni kika ci wa fuska... Fatima zo
mu
tafi." Ya yi gaba fatima ta mike tana
murmushin
yake,ta ce. "A'a ka tsaya ka gyara mata
talabijin
mana kar dukan ya yi mata yawa. Na kwace
mata miji kuma babu abin dauke kewa, sorinki
yarinya tunda kika rasa abin da zai hana yaron
mijinki daga kai ya auro tsohuwa sa'arsa,ke dai

kurunciyarki ba ta amfane ki ba wallahi,dole ki
dau hakurin rungumar filo idan kina kan
layi,dan
ma kin ci sa'a na kulle kofar bare ki fada layin
kwana shidda..... Wata kila da wata rana karfe
biyun dare za ki burmo mana kofa..." Sai da
abdullahi ya hada da jan fatima suka fice daga
dakin suka bar sadiya da hayaninya har da
ashar.
Cikin mutuwar jikin bacin rai yake,don haka
babu
wanda ya tanka wani har suka isa gidan
abincin,suka yi odar tuwon biski da miyar taushe
da farfesu tare da kayan marmari,suna ci kowa
bakinsa a dinke,kafin ya ci rabin nasa har ta
share nata sai fili,ta fara shan kayan
marmarin
cikin yanga,ya tsura mata ido cikin tunanuwa
barkartai. A nutse ya ce. "Kin koshi kuwa?" Ba
tare da ta dube shi ba,ta ce. "Idan ban koshi ba
cewa zan yi a karo min?" Ya yi saurin girgiza
kai,
ya tura mata nasa. "Ki ci wannan,bari na ji da
farfesun tunda ba kya ta tasa". Babu musu ta
ja

farantin da kwanon miyar ta ci gaba da ci. Bai
gaji da kallonta ba, ya hada da kallon nata da
shan farfesun,ya zuba mata ruwa ya tura mata.
"Yau ba ki ci abincin rana ba ko?" Ta yi shiru ta
ci gaba da sha'aninta, shi ma farantin ta
ture,a
sannan ne kuma ya jefa mata tambayar da ta
makale masa makoshi,tun kwanaki da suka
gabata. "Fatima me kika yi da pt-strip?" Ya
ce,"wanda na gav maryam ta siyo miki
kwanaki,kuma me ake yi da pt-strip?" Ta yi
fuska,ta ce. "Ina tsammanin gwajin ciki ake da
shi,ni kuma a ina zan sami ciki?" Ya yi
dariya,ya
ce. "To fadima mace da mijinta sai a tuhumeta
inda za ta sami ciki? Fadima wannan hausar ai
ba ta hadu ba". Ta fara goge hannu sannanta
matsi santizer tana cewa. "Masu auren shiri ke
nan, ni yanzu aka ganni da pt -strip ma ba sai
a
gudu ba, mu shafe wannan maganar,wajen yara
zaka ga pt-strip ka nemi ba'asi sai ka bari idan
mun koma gida ka saka damba,ka kai mata
kwanan dan nasan ta fi ni bukatarsa". Ya cije
lebe yana dariya ya kada ido,ya ce. "Da alama

kama kin fi ta himma,tunda ga shi ba a ga pt
strip a wajenta ba aka ganshi a wajenki,ko ma
mene ne ke yake shirin yi wa lamba,kuma idan
ba
ki tabbatar min an ga pt- strip wajenki ba to in
tabbatar miki yau zan saka dambar da za a
ganshi a wajenki wani makon". Ta ji batun a
jikinta,amma sai ta hadiye ta tabe baki,ta ce.
"Kamar kana da wannan himmar ka ajiye
yaran
mata shekaru rututu babu labari..." Ya tare ta
da
cewa. "To himma biyu ai ta fi daya,yanzu ba ga
shi da himmar tawa ta sami karfin gwiwar taki
ba
suna shirin bayar da mamaki har duniya ta
gani....ai ko cikin miliyan na mata dole in na
kira
ki jaruma". Ta ja kujerar saboda rasa amsar ba
shi. Ta ce "Kan ka ake ji, ni zan tafi gida". Dole
shi ma ya mike yana dariya,ya ce. "Wato ke dai
ba za a taba jan hirar arziki da ke ba ko? To za
ki yi guzurin biskin ne,ko kuma gobe kin dawo?"
Ta yi tafiyarta ta kyale shi, sai da ya sallame su
ya tarar da ita jikin mota suka yi gida yana

kwasarta da maganganu,ita kuma hankalinta
na
ga lissafin yadda zata kubuta daga tarkonsa na
sa wa cikinta ido. Sai fita cin abinci tare ya
zame
musu dabi'a,duk ranar girinta tunda ta fi son
dukkan abincin da ya danganci tuwo,shi kuma
ba
shi da sukunin girka mata, sai ya dinga jifan
tsuntsu biyu da dutse daya,wato ya samar mata
farin ciki ta hanyar ba ta abincin da ranta ke
so,
da kuma samin damar hira da ita ko zai samu ta
fasa masa cikinta dangane da abin da yake
zargi.
Shi yasa yake dokin ta karbi girki,yayin da yake
shiga damuwar abincin da zata ci duk ranar da
ba
ta da girki,dan ma ya samo dabarar siyo mata
ya
kai mata. Sai wanan ma ya zama wani kaso a
cikin abin da ke dagawa su sadiya hankali,shi
yasa wata safiyar da zata fita girki yana ta
hanzarin ya fita saboda siyowa fatima karin
kumallo,ita kuma sadiya ta kankare shi dan

tsabar neman rigima wai sai ta raka shi,ya ce.
"Sadiya wacce tsirfa za ki tsiro idan zan je
gaishe
su sai na tafi da ke?" Ta ce,"ina jin ai ba a
kaina
aka fara ba, ranar da ka kwaso fatima ka kawo
min ita wai ta rako ka duba min talabijin ita ba
ta yi tsirfa ba?" Dole ya hadiye ya ce. "Shi ke
nan
mu je". Suka fara ta dakin Hindatu,ita kanta
Hindatu sai ta ga wani sabon abu, ranta ya yi
mata babu dadi, musamman da yake tana da
bukatu na tambayar fita da ana tambayar kudi.
To ga sadiya ta tsaye mata kerere kamar wani
badogariya,sai shi Abdullahin ne ya zauna har
ya
sanya mata albarka a abincin da ta ke ci ba tare
da ta yi masa tayi ba. Hindatu ta yiwa sadiya
kallo tara ahu da murya kasa kasa ta ce.
"Sauda
ke nan" Sannan ta mayar da kai ga
abdullahi,ta
ce. "Ina ta neman wayarka tun jiya ban same
ka
ba, sam na manta da maganar dubo Anti

siyama...." Ya yi fuska ya ce. "Tunawar yanzu
ma
ba zata amfane ki ba, tunda kin karya ka'ida".
Ta
yi dariya ta ce". "Haba Abu Turab,uwa daya
uba
daya ai ya fice wasa, hakuri zaka yi a kawar wa
da ka'idar nan kai.... Ba zan kuma ba". Ya
ce,"haka dai kullum maganarki ke nan,ni dama
tun jiya da na ga uban turaren da kika yi na
san
yau sai kin tambaye ni fita. Wai har yaushe zan
dinga maimaita a daina tambaya ta fita ranar
da
za ayi ta?" Ta kara dagewa. "Hakuri zaka yi
Abu
Turab,antu ba zata ga kyautawar mu ba, ace sai
an kwashi kwanaki zan je dubo ta...". Ya tare
ta.
"Kar ki hada ni da ita,a dawo lafiya. Ya zaro
dari
biyar ya mika mata. "Ga kudin mota". Ta shiga
juya dari biyar din tana bin aljihunsa da kallo.
"Abu Turab... To kudin da na yi maka magana
jiya fa.... Ka ce yau zaka ba ni..." "Ni da

kaina?"
Ya fada ba tare da ya jira ta ba, ya ce.
3 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
26) "Sadiya mu je". Hindatu ta biyo shi har da
gayyar ture sadiya tana yi masa magiya,sai da
ya
ce. "Idan kin yi cinikin turaren ki ara min."
Dole
ta hakura ta kyale shi cike da haushin sadiya
wadda ta tabbatar idonta ne ya hana ya bata.
Cikin magagi fatima ta bude musu kofar ta
koma
ta zauna da bacin rai,dan tana ganin kamar
gayya ce ta sa ya kwaso mata sadiya dakinta.
Ta yi kicin kicin shi kansa ko kallonsa ba ta yi
ba. Tunda ya ga haka sai ya shafa mata lafiya,
kai tsaye ya wuce kicin yana cewa. "Me za ki ci
yau?". Ta yi masa banza,sai da ya shiga kicin
din
ya fito ya kuma tambayarta,kamar dole ta
amsa.
"Ba ni da zabi". Ya dube ta da kyau,sannan ya
dubi sadiya da ta tsaye musu,ya san kuma

ganinta ne ya tunzura fatima,duk sai ya ji
haushinta ya turnuke shi,dole ya hadiye ya
kuma
wucewa kicin ya jima tsaye ya ma rasa abin da
zai yi fiye da mintuna biyar,kawai sai ya fito
yana
cewa. "Ko za ki koma baccin,bari idan na je
office
zan turo a kawo miki abinci,yanzu in na tsaya
zan makara".. Sai ta kasa tanka masa,bare
sallamar da yake mata, suka fice sadiya biye da
shi tana jin kamar ta yi fifike don farin ciki.ta
ga
ma ashe ita ta sake tun tuni ta ba su damar
shigar mata hakki. Fatima ta dauke kai daga
kallon kofar da suka fice tana cije lebe,tare da
gyada kai, cikin tunanin mafita tare da
alkawarta
wa kanta daukar mataki. Haka kuwa washegari
sadiya ta ga hanyar ya gama shirinsa yana ta
faman kunci dan kar ta sami kafar cewa zata yi
masa rakiya kamar jiya,ita kuwa ta share shi
yana mata sallama ta makale jakarsa a kirji ta
biyo shi,babu yadda zai yi da ita suka tafi
tare,don haushi Hindatu daga bakin kofa ta

sallame su, don tana bude kofa ta ganshi sadiya
ko gaishe shi ba ta yi ba ta ce masa". "A dawo
lafiya,Allah tsare. Ba ta ko jira cewarsa ba ta
rufe
kofarta. Ya yi murmushi kawai ya kada kai,
suka
doshi dakin fatima. Ya sa key din hannunsa ya
bude,amma sai ya ji alamar sakata cike da
mamaki ya fara kwankwasawa dan bai taba
riskarta karkama masa sakata ba. Babu jimawa
ta zo ta bude bayan ta tabbatar tare yake da
sadiya. Ba Abdullahi da ta danawa tarkon ba,
hatta sadiya sai da ta yi turus da ganin fatima
a
haka, tana sanye da farar rigar bacci sol mai
zubin net,iyakar rabin cinya wadda da kadan ta
zarce babu saboda babu abin da bai bayyana ba
a jikinta har da kalar pant din da ta ke sanye
da
shi wanda shi ma yake fari. Da alamun kasala ta
jagorance su cikin falon,ta yi zamanta kan
kujerar
tana doguwar hamma. Da kyar Abdullahi ya
gama
kokawa da numfashinsa da kwakwalwasa mai

hajijiya da shi saboda ta gano masa hakikanin
fatima da ganin da bai taba mata ba.ya samu
ya
zauna a kujerar da ke fuskantarta kamar wani
mutu mutumi. Ya kokarta ya ce. "Sannu da
bacci". Ta yi masa wani duba da wutsiyar ido,
sannan ta kawar da kai ba ta tanka ba. Ya dan
yi
kasake yana lalubar ta inda zai sami ganin
dariyarta. Ta sake dan kishingida bayan ta yi
doguwar hamma,ya ci gaba da nacin
kallonta,muryarsa na rawa yana kokarin dai
daita. "Wai duk baccin ne, yanzu kike tashi
ne?"
Ta sauke numfashi cikin yauki ta ce.
"Wallahi,kin
tashi lafiya,sadiya ya ya dawainiya?" Ta sauke
ganinta ga sadiya ke nan wadda ta yi mugun
muzanta sai kikkifta ido ta ke tana kallon
Abdullahi wanda ta ke jin ma zata iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login