Showing 27001 words to 30000 words out of 34797 words
Chapter 10 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf
shigo
gidan ba sai da rana ta fito bakwai da
rabi,wanda
wannan lokacin ma ya gama shirin fita ofis.
Yana
shiga dakinsa Hindatu ta cimmasa ta durkusa
har
kasa ta gaishe sji,sannan ta mike a ladabce ta
ce, "Abu Turab wai duk fusjin ne? Don Allah ka
yi
hakuri". Ya girgiza kai da sauri da son ya yi
murmushi,ya ce. "Ya wuce wallahi" Ta ce,"ban
ga
alamar hakan ba,jiya fa baka yi baccin kirki ba,
ka fice sallar asuba ba ka shigo gidan ba sai
yanzu. Ina ganinka ka shigo babu walwala,sai na
ga me ya yi zafi?" Ya share fuska yana kawar
da
kai,ya ce. "Ba wannan matsalar ba ce,akwai
abin
da ke damuna... Ku saka ni cikin addu'a". Cikin
tausayawa ta ce. "To Allah ya warware". Ya
ce,"amin, yi min afuwa na ga fatima ba ta da
lafiya" Ta yi saurin gyada kai tunda tana son
ya
huce,ta ce. "Babu komai". Ya yi mata godiya ya
juya ya fita. Ya same ta kudundune a gado
tana
ta faman kuka da makyarkyata,ya kara daure
fuska don ya yi tsammanin kukan rikicin da ya
yi
mata jiya ta ke, don haka ya yi mata banza ya
fara abin da ya kai shi, wato gyaran dakin,
amma
makyarkayartar da ta ke ya sanya dole ya
sanya
mata ido,murya a cushe ya ce. "Wai wannan
kukan na jin dadi ne ko na me? Ni ya kamata
na
koka don ni kika cutar,me yasa kike son nuna ke
aka cuta?" Ta girgiza kai cikin wahalalliyar
murya,ta ce. "Abdul ba ni da lafiya,zan mutu
wallahi! Da sauri ya yar da sallayar da ke
hannunsa ya isa gabanta,ya ture bargon ya
dago
ta a rikice ya ce. "Me yake damunki?" Ta cije
lebe
cikin sartun hawaye tare da rike hannunsa da
kyau ta ce. "Cikina Abdul zazzabi kaina.." Ya yi
saurin tattarota jikinsa yana rungumewa,cikin
nuna damuwa ya ce. "Ciki kuma fatima...
Wanne
irin ciwon ciki? Sannu.... Ko mu je asibiti?" Da
sauri ta girgiza kai tana kara jankane shi. "Ka
yi
min addu'a kawai... Idan ya yi min sauki ina da
magani zan sha..." Ya ce,"to... To shi ke nan....
Dai dai ina ke miki ciwo a cikin?" A rude ta ce
masa "Ko ina abdul" Ya dagota ya yaye cikin
yana kallo,hankalinsa ya rabu biyu da addu'ar
da
kuma kallon yadda cikin nata ke ta faman
motsi
alamar dai an kuntata shi. Suka kwashe lokaci
mai tsawo a haka,cikin ikon Allah sai ga sauki ya
samu har ta yi bacci a cinyarsa. Ya kara damke
hannunta cikin nasa yana bin fuskarta da
kallo,kwalla ta fara cika masa ido, lokaci daya
ta
rame kamar wadda ta shekara a kwance. A haka
ya share mintuna ashirin ko kwakkwaran motsi
ba ya so ya yi don kar ya katse mata bacci,har
sai da Hindatu ta fado masa a rai, sannan ya
lalubo wayarsa a hankali ya kirata. "Ki yi hakuri
Hindatu,mun ciki wata matsala ne,kar ki ji ni
shiru". Duk da zuciyarta a jagule ta ke,sai ta
daure ta ce. "Babu komai,ina fatan ba jikin ba
ne?" Ya ce,"shi ne wallahi". Cikin bayyana
damuwa ta ce. "Ayya! Allah ya kawo sauki,ko ni
zo akwai abin da zan iya taimakawa? Da sauri
ya
ce da ita. "Yauwa da na gode miki kuwa". Ta
sauke waya da sauri ta zura takalmi ta nufi
dakin
fatima. Ita kanta hindatu kallo daya ta yiwa
fatima ta san lallai tana jin jiki,cikin bayyana
damuwa ta ce.
3 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
34
"Subhanallahi,me yake damunta haka?" Ya
dan
muskuta a hankali yana gyara mata kwanciyar
don ya ji dadin zama,ya ce. "Daga zazzabi ya
koma ciwon ciki,da kin ganta a dazu sai kin
mata
hawaye..." Hindatu ta ce masa. "Gaskiya dubi
yadda lokaci daya ta rame, wannan ai sai ku
tafi
asibiti,da me zan taimaka maka? Ya ce,"da
ruwan
zafi a fulas,wanda zata sha tea sai ki dan gyara
mata kicin ki wanke mata kwanuka.idan har kin
gama ba ta farka ba,sai ki zo ki dan hada mata
ruwan wanka sai na tashe ta". Hindatu har
zuciyarta ta ce. "To,babu laifi". Da sauri kuma
ta
fice kicin din tan aikin da aka sa ta, har ta
gama
ta je ta hada mata ruwan wanka, sannan ta
sanar masa tare da cewa. "Yanzu haka ba ta yi
baccin dare ba shi yasa yanzu ta ke fanshewa".
Ya ce,"ni ma na yi tunanin haka". Ta
ce,"yanzu
haka zaka tashe ta? Ya amsa mata da cewa. "Ai
ya zama dole, gara ta tashi ta sha magani". Ya
sunkuya ya fara hura mata kunne,ta motsa a
hankali tare da salati tana dafe ciki,ya dago ta
a
hankali suna yi mata sannu shi da
hindatu,muryar
hindatu ta sa ta bude ido da sauri tana binta
da
kallo,ta sauke ido akansa da tambayoyi a ido iri
iri,da ya kasa amsa mata sai ta ja jiki a hankali
ta janyo filo ta kwanta.ya suke kafafunsa yana
cewa. "Ki tashi ki yi wanka,ki samu ki karya ki
sha magani". Ta girgiza kai a sanyaye ta ce.
"Ba
zan iya ba..."$ "sai na taya ki". Ta tari
numfashinta da fatar hakan,amma sai ta yi
mursisi ta kara jan bargo tana cewa. "Abdul bar
wankan nan don Allah". Cikin tausayawa ya ce.
"An bar shi, sai ki wanke baki ki dan kurba tea
don ki samu ki sha magani". Ba ta tsinka ba, ya
tashi ya kawo mata tasa da brush ya taimake ta
ta tashi,hindatu ta dago tasan ta zuba mata
ruwa
a brush din ta mika mata, tana mata sannu shi
kuma ya tsaya hada mata tes din. Da kansa ya
dinga ba ta da cokali tana sha tana faman rike
ciki,saboda karta da yake mata har ma shan ya
gagare ta, dole ta koma ta kwanta tana juyi.
Babu shiri Abdullahi ya fice waje ya kira likita a
wayarsa cikin tashin hankali ya ce. "Dr akwai
matsala fa, ciwon ciki ya matsa mata matuka...
Yakamata ka zo ka taimaka ko kuma mu zo." Dr
ya tausaya,sannan ya ce. "Hakan zata iya
faruwa,a cikin magungunan da na ba ta har da
na
wannan matsalar me yiwuwa ba ta yi amfani da
su ba ne, ka bincike su,amma idan ya ki tsayawa
nan da yamma sai ku zo". Ya yiwa dr godiya
sannan ya koma dakin da sauri. Ya ce mata.
"Ina
magungunan?" Da kyar ta amsa masa. "Suna
falo" Ya fita da sauri,hindatu kuma ta bude
karamin firij din da ke kusa da ita ta dauko
ruwa,tun ma kafin ya karsaso ta zuba a
tambulan
tana jiransa,suka bata ta sha ta yi mata
sannu,can ciwo ya dawo sabo,hankalinsu gaba
daya sai da ya tashi. Haka suka yi ta
fama,abdullahi na faman yi mata add'a a
cikin,hindatu ma na tata a cikin zuma har Allah
ya kawo sauki bacci mai nauyi ya dauke ta.
Wunin ranar nan kusan a haka ta yi,don haka
ko
aiki abdullahi bai leka ba, hasalima masallaci
kawai kan fitar da shi. Hindatu kuma tsurku
biyu
ya hade mata,ga na tabatar kallon fatima da
ciki,ga na lissafin kwatancin matowar da
Abdullahi ya yi akan fatima wadda sam ba ta
damu da shi ba.tunda hindatu ta ke da
Abdullahi
ba ta taba ganin hawayensa ba, amma a yau
inda
tana da bukatar tarar hawayen ko gwanhwanin
madara ne sai ta samu, wannan abu yana
matukar daure mata kai, sai dai wannan bai
hana
ta hadiye kishinta ba,suka dinga hidimar
fatima
tare har dare,bayan iska lokacin da ciwon ya
jima
bai motsa ba. Wannan kokarin nata da
kyautatawar ne ya sanya Abdullahi jarumtar
barin
fatima hannun Allah,lokacin da dare ya yi, don
dai
kar ya cika shiga hakkin ita Hindatu,ya yiwa
fatima bankwana tare da bar mata daya
wayarsa
da zummar ko wani abu zai faru sai ta kira shi.
Yana dab da ficewa daga dakin ya ce mata.
Biyewa shaidan idan ya zuga ki kiran Alh da
wayar don wannan laifin yana daga cikin wanda
ba zan iya yafe miki ba,zan ma dinga kaiwa
ubangiji na kararki". Ta dago cikin matukar
kasalar jiki da ta zuciya tana ture wayar
gefe,ciki
murya mara dadi ta ce. "Zo ka dauki wayarka".
Ya bata rai, ya ce. "Ai ba don halinki na baki ba,
in don halinki ne ma fadima kallonki na yi? Ko
da
yake ban sani ba ko a haduwar da kuka yi jiya
ya
ba ki wata wayar". Kai tsaye ya fice ba tare da
ya
jira cewarta ba sai ya barta da kwalla da son
fadawa cikin tunanin barkatai,mafi ciwo a
wajena,
shi ne uzurin da ya yi zuwa ga hindatu alhalin
tana bukatar kulawa.ga shi ma'abocin iya jinya
wanda ba ta taba riskar irinsa a rayuwar ta ba,
sai ta ke ji a ranta kamar idan yana tare da ita
ciwon zai fi saukaka mata.ta rasa daga inda
wannan kishi nata ke bullowa. Yana shiga ya
sami hindatu ta fito wanka da walwalarta,ta
tambaye shi. "Ta yi bacci?" Ya girgiza kai, ya
ce.
Har yanzu idonta biyu". Ta ce,"ina fatan ciwon
bai kuma tashi ba? Ya amsa,"haka ne". Ta dan
ja
fasali kafin ta dora wata tambayar, zuciyarya
cike
da fargaba. "Abu Turaba anya ba ciki ne da
fatima ba?" Dabararsa ta fara kokawar tsaida
lugunden kirjinsa, ya yi matukar juriya kafin
ya yi
fuska ya amsa. "Wallahi ba ta taba yi min
wannan maganar ba, me yasa kika fadi haka?
Cike da mamaki ta kada kai. "Ba hasashe nake
na Abu Turab,ina shakkar in fatima ba ta da
ciki
wata kila salon alakar da ke tsakaninku ne ya
hanata sanar maka kunna na yi mamakin da kai
ba ka ganshi da idonka ba,ga shi nan ya fito?"
Ta
kwaso masa rantsuwa,yana dariya ya dakatar
da
ita. "Ki daina saurin rantsuwa,gara ki bari a
tabbatar don haka ina barar sirri,ki kulle
bakinki a
kan wannan maganar,kar ki sake na ji ta a
bakin
wani". Ta dan yi kasake,sannan ta ce. "Kana
daukaka dai wata magulmaciya ko?" Ya yi
saurin
girgaza kai yana dubanta kai tsaye ya ce. "A'a
na
san ki dai da dan banzan surutu, kin san kuma
an
ce shi zance ado ne, amma kawaici kubuta ne"
Sai da ta ja fasali sannan ta dube shi da
kyau,ta
ce, "Wannan kasheda kasheda suke tabbatar
min
fatima na da ciki,kuma kasan da shi ko in ce
kun
san da shi, ban san don me kake son ka boye
min
ba. Ya jima yana kallonta kafin ya sami abin ce
mata. "In rantse miki ba mu taba maganar cikin
da fatima ba ki kasa gaskata ni? Ni ma ban san
me yasa kike son ki fitine ni akan wannan
maganar ba". Ta dinga girgiza kai fuskarya na
canjawa,muryarta a sarke ta ce. "Ba laifi ba ne
don na nemi in san cewa dama in da sadiya ne
ba ma haihuwa ke nan? Ya dinga dubanta cike
da
mamaki,sannan cikin tara gira ya ce. "Kin saka
wannan hasashen naki a magwajin hankali da
ilimi kuwa? Ina tantamar haka ban sani ba ko
idonki ne ya rufe. To amma ba zan hana ki
hasasshenki akan batun don jin wannan
maganar
a wajen ko cikin gidan ta bakinki na tabbatar
miki,ita zata sa na warware amincin da ke
tsakanina da ke. Sai kawai ta zura masa ido.bai
jira cewarta ba, ya kada kai ya wuce bandaki ya
barta da hidimar binsa da kalloZuciya d kwanji
35
******************************
*********** Kafin ya
fita sallar asuba,sai da ya shiga dakin fatima
don
tabbatar da lafiyarta.sai ya same ta tana bacci
mai nun koshi lafiya,ya jima yana kallonta
sannan
ya farkar da ita. "Ya ya jikin?" Ya tambaye ta
bayan ta farka,ta sa masa ido kawai, mamaki
da
shakkarsa ta ke, ya bude KWANJI da kyau yana
kulawa da ita, amma fuskarta ba ta fasa nuna
yana fushi da ita ko da yake zargin da yake
mata
adalcinsa ne ma kawai ke sa shi kular da ita.wai
wajen Alh ta je, ita da kanta tana ganin abin
tir a
zargin duk kuwa da wani bangaren zuciyarta na
ganin tsabar iya mulkinsa ke son nuna mata fin
karfi wajen rabata da Alh,ba tare da yana da
wannan damar ba. Cikin sanyin muryar wanda
ya
ji jiki a cuta ta ce. "Alhamdulillah". Ya ci gaba
da
binta da kallo,fuskarsa babu walwala. "Ciwon
cikin ya kuma tashi?" Ta girgiza kai kawai.ya
kara dubanta a kaikaice cikin tare gira,ya ce.
"Amma ina ganin har yanzu akwai matsala
daga
shi nan a kumbure". Cikin dar dar ta kara jan
bargo tana rufe jikinta,sannan ta juya masa
baya,
shi ma ya fara ja da baya yana hadiye
dariyarsa,ya ce. "A'a ki tashi ki yi sallah,in dai
bai
sace ba nan da gobe dole mu je asibiti,ban san
abin da ya baki kika ci ba yake neman kashe min
ke,an gama da ciwo ga kumburi,kuma a haka
kike
masa kallon masoyi..." Ko motsi ba ta yi ba bare
alamar zata tanka, don ta dan fahimce
shi,idan
yana cikin fushi ba ya son yana magana ana
mayarwa.tana jinsa har ya gama zungure
zungure rigimarsa ya fice. Bai kara waiwayarta
ba, sai tara saura ya shigo mata da take
away,ya
fara da hada mata ruwan wanka,babu walwala
tare da shi ya yi mata umarnin ta je ta yi,
kafin
ta fito ya gyara dakunan tsab ya baza musu
kamshi. Ta fito ta same shi yana dube sube a
wayar da ya bar mata,fuskar nan tasa a
murtuke!
Ta dinga satar kallonsa har ta kai ga tankawa
cikin dar dar din kirji. "Ko tabawa ban yi ba".
Bai
ko juyo ya dube ta ba bare ya tanka,ya zura
abarsa a aljuhu kawai,sannan ya janyo mata
stool ya ajiye gaban mirrow har da bude mata
mayukan da ya fahimci ta fi mu'amula da
su,sannan ya koma gado ya zauna ya jingina da
allonsa sai ta share mirrow din ta nufi can
karshen gadon ta zauna ta juya masa baya.ya
dan bita da kallo.amma sai ya ki tankawa ya
tashi ya kwashi mayukan da karamin kurar
kayan
kwalliyarta ya ja ya kai gabanta har da kai
mata
foot stool,sannan ya koma mazauninsa ya kuma
zama. Ya dinga komai cikin kasala saboda ciwon
jiki da damuwa a rai,idanunsa a kanta tunda
ba
ta kallonsa,tausayinta na damursa a rai, yana
jin
ba don yana son nuna mata kurenta ba man ma
sai kawai ya shafa mata. Yana ta duban agogo
saboda lokacinsa da ke tafiya,amma haka ya
hakura ya share ta har ta gama lakakinta.ya
fito
mata da kayan sawa sannan ya mayar da kayan
kwalliyar,ta shirya ta kon sofa ta kishingida, ya
fita ya kawo mata abincin,ya zauna kusa da ita
da magungunanta a gabansa da ruwa da
tambulan a hannunsa. Ta fara karyawa cikin
kwalla,gaba daya rayuwar ta yi mata zafi,ta
rasa
gane wannan masifa in dai Abdullahi na mata
fushi sai ta rasa inda zata soma ranta gaba
daya
sai ta ji kuncin duniyar nan ya ishe ta. Abin
takaici ma abin da yake zarginta da shi ba ta
aikata ba, kuma abin da ta aikata din ba ta yi
nasara ba don ta hakkake likita yaudararta
kawai
ya yi bai zubar da cikin nan ba. To ina mafita ke
nan? Sai ta zabi farawa da maganin wannan
fushin nasa da ke kuntata mata Zuciya ba tare
da
yakamata ya kuntata mata din ba. Bayan ya ba
ta magungunan ta sha tana mika masa
tambulan
din bakinta na rawa,ta ce. "Abdul wallahi
shekaran jiya ba wajen Alh na je ba. Ya kwashi
sakkani masu dama kafin ya tanka a takaice.
"Ina
kika je? Ta dan yi wura wura tana neman inda
zata ce kamar ta ce kasuwa sai ta tuna
kishinsa,ta ce, gidansu ya kira ya tambaye su.
Kawu sai ta sami kanta da kada kai kawai ta ce.
"Asibiti na je". Ya bita da kallo,ya ce. "Kika yi
me?" Sai ta ji tamabayar kamar ta gayya ko ta
sanin abin da ta je yi asibiti,don haka ta kasa
amsawa. Ya kara dubanta da kyau,ya ce. "Idan
ba ki ba ni amsa ba zan dauka akwai wata 'yar
burum burum da kike min, in baki sani ba ki sani
ina zargin akwai dana ko'ya ta a cikinki, in dai
asibiti kika je to ina zargin kin sonm salwantar
min da ciki,wanda shi ne abu na karshe da zaki
yi
min ki cuce ni,shi ne kuma zai iya sa ni
jarumtar
runtse ido na yi miki rashin mutuncin da zan yi
shakkar yiwa wanda na fi ki a filin duniyar nan,
a
matsayinki na wadda na fi kauna a cikinta. Sai
dai kar ki yi zaton rashin mutummcin shi ne
saki,
har in mutu ba zan sake ki ba, sai dai ke ma ba
zaki ji dadin zama da ni ba Fatima. Ta runtse
ido
sannan ta bude su da ballowar hawaye.tana
cikin
tsaka mai wuya ke nan, in cikin ya zube ko bai
zube ba, duk babu sauki! Ashe Abdul ya rankota!
In ta zubar da cikinsa ta shiga aukubar fushinsa
tunda ya ce babu saki,in kuma ta zauna da cikin
nasa kila har abada Alh ya tsere mata. Ta fara
dauke kwallarta sannan ta dube shi, ta ce. "Ni
bani da wani ciki abdul,har yaushe na sanka da
zan yi ciki da kai... Don Allah ka saurara min ni
bana son tashin hankali,in dai fita ce ba zan
kuma fita ba har ranar mutuwar tawa kamar
yadda ka zaba min.... ,shi ke nan? Sai dai ba
zan
kasa tun mata cutar da ka yi min ta zama da ni
ba tare da so rai na ba". Ta kare da kuka,amma
sai ya hadiye tausayin nata da kaunar tata da
ke
bijiro masa ya kawar da kai,ya ce. "Ni yanzu ta
cikina da ke gare ki nake yi ba maganar fit da
zaman gida ba. Fita dai ba kin riga kin yi ba,kin
kuma ki sanar da ni inda kika je da abin da kika
je yi, kin fita cikina yana cikin koshin
lafiya,kin
dawo min da shi a wahale kina neman jaza min
mummumnar asarar da ban taba irinta ba, don
tsbar son Zuciya irin naku. Na rantse