Showing 30001 words to 33000 words out of 34797 words
Chapter 11 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf
miki da
Allahj fatima idan wani abu ya samu cikina sai
na
wulakanta ki, kuma si na hada danginki na
sanar
da su abin da kika yi min..." Ta tare shi cikin
masifa. "Malam wai a ruwa zan sha cikin ne? Na
fada maka ba ni da shi...." Shi ma ya taso mata
da fada. "Ta ya ya zan gaskata bakinki da ya
saba karya? Zan gamsu kawai idan na dauke ki
na kai asibiti aka tabbar min.... Kar ki dauke ni
wani soko kin ji! Ina sa wa abin da nake so ido
fiye da yadda kike tsammanin,duk wani
motsinki
a idona yake fatima.... Saboda haka ki shiga
hankalinki". Ya mike ya kwashe kayan gabanta
ransa a bace ya fice yana ji tana rusar kuka.
Ina
mafita? Sai ta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
kawai, hakika tana cikin tashin hankali,Allah
ya
jarrabe ta,haka ta yi kukanta ya ishe ta,har ta
share hawayenta ta goge fuska lokacin da ta
jiyo
sallamar hindatu.ta gyara fuskar ta mike ta
fito
falon. Da walwala a fuskarta ta yi mata tayin
zama suka gaisa ta yi mata sannu da jiki,suka
dan taba hira game da ciwon fatima,ta yi mata
godiyar dawiniya har suka shihga wasu hirarakin.
Karfe sha daya dai dai sai ga laila ta same su
tare da hindatu,suka gaisa sannan ta yi musu
sallam ta fice. "Wannan 'yar makota ce?"
Fatima
ta yi dariya ta ce, "Matar mai gidan nan ce".
Laila ta zabgawa kofa harara,sannan ta karasa
ragowar akan fatima cikin kaushin murya ta ce.
"Kin bayar da mata wallahi. "Da mugun sauki
tunda ba maza na bayar ba ... Fiye mayar da
allura garmawallahi ba .. Gane wata matsalar
danne wata ta ke..." Laila ta gyara zama ta ce.
"Wani abu ya faru ne? Nan fatuma ta kwashe
mata dukkan labari tun daga ranar da suka
dawo
har zuwa jiya da yau cikin bayyana takaici da
damuwa tare da nuna kaka ni kayi,amma tana
saka aya sai laila ta saki tsaki ta dora da cewa.
"Ni fada miki tuni akwai sakacin wajen cin
kashin
da mutumin nan ke miki.... Shi din banza da
zaki
bar shi ya nemi gadar miki da hawan jini..... Don
tsabar wulakantar da kai har da wani fada
masa
ba wajen Alh kika je ba.... Ba kya barinsa ya
tafi
a haka in ya ji haushi ba sai ya sake ki ba, idan
ni ce ma ba sai na ce masa cikin ma na Alh ba
ne tunda dama shi bakarare ne.
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
36
A sanyaye fatima ta dakatar da ita da hannu
amma ta kasa cewa kopmai laila tabude jakarta
ta fito mata da wayarta black berry bold 2
sabuwa tana cewa. "Sai ki tashi ki shirya mu
komawa likitan ga waya inji Alh,akwai layin Glo
a
ciki " Abdullahi ya alkwartawa kansa duk
runtsin
aiki sai ya rinka saurara masa ya waiwayi
gidansa,don dora ido akan fatima.kuma daga
yau
ya fara laila ba ta jima da shigowa ba ya shigo
gidan.da hindatu ta nemi ba'asi sai ya ce mata
takardu ya manta,cikin dabara ya ce mata.
"Fatima ta fito ne?" Ba tare da ba wa
maganarsa
muhimmanci ba ta ce. "A'a Ya kuma dubanta a
nutse ya ce. "Amma dai baki ta yi ko?" Ta
gyada
masa kai,ta ce. "Eh,ta yi bakuwa kam na ganta
lokacin da na je dubo ta". Cikin bugun zuciya ya
ce. "Ko laila ce? Ta kada kai,ta ce. "Ita ce". Ya
tilasatawa kansa jarumtar hadiye rikitarsa
gaban
hindatu ya wuce yana cewa. "Ah bari na ganta".
Ya yi sallama falon,amma a ciki tsoro da razana
suka bayyana karara a fuskar fatima me rike
da
waya a hannu,wayar da gaba daya hankali da
idanuwan Abdullahi ke kanta.... Sai laila ta saki
baki tana kallon fatima wadda kamar a ce kyat!
Ta zura a guke, sannan ta juya ta kalli
Abdullahi
wanda ya dogare a bayan kujera fuskarsa babu
annuri sam! Cikin sakanin ta yi
nazarinda,kamka
ntar jikinsa bai kamata ace yana da kwarjini
ba,
amma ita kanta ya cika mata ido sai ta ji gaba
daya ya rude.ta fara gaishe shi a rikice shi
kuma
ya amsa idonsa akan fatima,ta yi saurin kawar
da
kai tana hadiye rikitarta. Ya yi kokarin
kyautata
muryarsa,cikin tsare gira ya ce. "Fatima
wannan
wayar fa? Ta dubi wayar ta dube shi, bakin ta
ya
hau rawa,ta kasa kuma fitar da sauti. Ya kara
murtuke fuska.lokacin da ya karasa gabanta ya
mika mata hannu. "Bani". Bakinrta ya hau
rawa
ta mike ta boye wayar a baya tana cewa... "Ya
ya za a yi na baka... Ni ba tawa ba ce..... Ka ga
mai ita". Ya gyara murya,ya ce. "Ai na sani ko
laifi ne don kin bani na gani....? Ta yi katfin
halin
amswa. "Ni ma ba laifi ba ne don na hana ka..."
Ya tari numfshinta cikin bacin rai. "Ban fadi
haka
don ina gudun na yi miki laifi ba, musamman da
yake zan iya murde hannunki na kwata...
Saboda
haka tun ina mutuntaki ki ba ni...." Bai ma jira
cewar tata ba ya kamo ta ya murde ya kwace
wayar ya zaro ta daga kwali. Ya tarwatsata a
bango ya kuma binta ya karasa sannan ya juyo
gare su da ko wacce ta shiga taitayinta, ya dubi
fatima da kyau.ya ce. "Wace ce wannan,me ya
matsayinta a rayuwarki?" Ta yi fuska ta kawar
da
kai babu alamar zata tanka, sai ya rabu da ita
ya
fuskanci laila ya ce mata. "Bisa wace hujjar
kika
kawo mata wannan wayar? Duk firsarar laila sai
ta kasa motsi,shi kuma ya ci gaba da yi mata
kallonm uku ahu,sannan ya ce. "Ke ce wakilyar
babban shaidan da karami ko? Ga shi kuma tuni
na yiwa gida nan katangar karfe da shaidanu.
Saboda haka duk makircin da kika kullo da
abinki
za ki koma,kin ga..." Ya nuna mata kofa. "Fita
ki
bar min gida,kar na kara ganin muguwar
kafarki a
cikinsa,idan ba haka ba sai na yaga miki dam
mutumcin mutuntakar da ya dam fare miki...
Annamimiya kawai. Fatima ta sha gabansa cikin
yanayin tashin hankali ta ce. "Abdul wane irin
cin
fuska ne wanmnan...." Ya zabga mata harara
yana nuna laila ya ce. "Wannan har tana da
fuskar da zan ci? Kin san Allah ba don
wulakanta
wulakantacce wani nau'I ne na wulakanta kai
ba
yau sai na wulakanta wannan matar.ban taba
gaini wani tsanannen mutum sama da ita ba,
sabnoda haka inda tana da fuskar da zan ci sai
na cinye tas na hutar da 'yan baya. Don haka ke
na ki saurare ni da kyau! Duk ranar da na kuma
ganinta a gidan nan taki fusakar zan ci tunda
ita
ba ta da wadda zan ci... Malama tashi ki bar min
gida na ce?" Ya kare da tsawr da ta cika gidan.
Laila ta mike cike da mugun takaici,dakin na
juyawa da ita saboda bakin ciki,fatima ta
rakota
cikin kuka tana kallon Abdullahi. "Ba zata fita
ba,sai dai in ka kore mu tare..." Ya saki wani
uban tsaki,ya ce. "Ita na kora,kuma in zaki bita
ai
ba daure ki na yi ba, iyakaci in kin bita ki ga
nawa KWANJIN.... Ba a haifi shashashar matar
da zata kawo min wauta ba..." Laila ta fizge
hannunta ta yi gaba tana numfashi ita kuma
fatima ta kara kuka,ta ce. "Ni ce shashasha
abdul?" Ya share ta ya ci gaba da bin laila da
maganganu. "Idan kin je sai ki fadawa
shaidanin
naki yadda na yi da ke,ki kuma tabbatar masa
zai
iya nasarar raba fatima da gidan nan matukar
ya
taba ganin wanda ya mutu ya farko,ki fada
masa
kuma kurarin da ya yi min jiya sun bi rariya
tunda
ni ba rago ne kamarsa ba..." Laila dai ko juyowa
ba ta yi ba ta fice a salube,inda shi kuma ya
sauke ganinsa ga fatima,ya yi tsaki ya ce. "To
wace ce ke din in ba shashah ba? Ko yawan
shekarunki suna miki amfani? A shashashancin
ma ke ba ki shiga layin wadanda suka tara suna
ba,idan kuma kina da abin yi sai ki yi.... Mts...!
Aikin wofi kawai.." Yana huci ya sa kai ya fice
daga falon,ai sai kawai fatima ta yi mutuwar
tsaye a wajen,kuka ma ya gagara.
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
37Wuni ta
yi tana tanadin tashin hankalin da zata yi da
shi,
wanda zai sa shi sakinta ko da ya fi gyatumarsa
kokari,amma ina! Sai tanadinta ya tashi a
banza,
don har ta kwanta bacci bai leko inda ta ke ba
duk kuwa da cewa girkinta ne. Da safe ma tana
jinsa ya fice ya bar gidan har rana ta take,
yamma ta yi ba ta sanya shi a idonta ba,ya dawo
amma kamar yiya bai leko ta ba. Daga nan ne fa
hankalinta ya bar kan tanadin bala'inta ta
koma
na takaicin da neman mafitar yadda zata
kukuta
daga wannan tozarcin me matukar taba rai da
ya
kwaso mata a lokacin da ta ke cikin tsaka mai
wuya na bukatarsa kusa da ita,ko kuma
sallamarta ta bar masa gida tunda ya tare
tubalin
da ya rike ta a gidansa,wato kirkinsa. Ta yi kuka
ta yi abin da ya fi,amma ba ta da mai
rarrashi,ita
kuma zuciyarta ba a nutse ta ke ba bare ta nemo
mata mafita sai ma kirkiro mata wasu sababbin
koma bayan ta ke, wato kamar na janyo mata
gorin sadiya. Har ta saka kayan bacci ta kwanta
karfe goma da rabi,ta mike cikin fushi da zafin
rai
da zura hujabi ta saka takalmi ta fita zuwa
dakinsa, ko kwankwaswa ba ta yi ba murda
handle ta shiga. Yana kishingide kan sofa yana
karanta kur'ani,yana ganinta ya diga aya yayi
addu'a,sannan ya mike zaune sosai ya saka
mata ido fuskarsa babu yabo babu fallasa,ita
kuma ta yi kicin kicin da ita kamar mai shirin
sheke shi da mari. Ya mike a hankali ya isa book
case dinsa ya ajiye kur'ani sannan ya juyo cikin
dakewa ya ce mata. "Lafiya kuwa?" Ta silale a
hankali ta zauna akan hannun kujera saboda
fushi
ya sanyayar mata gabobi,kirjinta sai harbawa
ya
ke. Da ya gama fahimtarta sai shi ya saukar da
nasa fushi ya mika mata filon kujera da sauri
yana cewa. "A'a zauna sosai mana" Sai kwalla
ta
cika mata ido, ta yi saurin girgiza kai,ta ce.
"Malam ni ba zama ya kawo ni ba...." Ya sa
mata ido kawai. "Zuwa na yi na fada maka
wallahi na gaji da aurenka..... Ni dai na gaji
wallahi,kuma dole yanzu ka sake in". A sanyaye
ya ce da ita. "Me na yi kika gaji da aurena
fadima?" A kufule ta amsa masa. "Dama can a
gajiye nake,hakurina ne kawai ya kare da na
fahimci sam ba ka da tausayi.ina zaune a
gidanka bisa tilas kai kuma kana son rataye
ni...
To wallahi ba zai yiwu ba, idan ma yajin ne na
shirya in yi kuma babu mai matsa min in dawo
gidanka". Ya tuntsure da dariya ya na
dubanta,ya
ce. "Amma dai da kin ji kunya.da shekarun
talatin
da biyu ne za ki kwashi yaji gida? Yanzu laifi ne
dan na zagi zagagge? Haba fadima duk yawo da
ke da nake yi watannin kusan takwas ban gajiya
ba sai ratayar kwana biyun da na yi miki ce zata
kosar da ke? To yi hakuri na tuba ba zan kara
ba".$ ta dauke kai tana ci gaba da zubar da
hawaye. Ke nan! Su ishe ka da laifi amma ba ka
isa daukar mataki a kansu ba sai su ki da rauni
da neman a basu hakuri,duk goma da ashirin!
Ya
tari gabanta ya ruko ta cikin murya mai bayyaya
tarin kauna,ya ce. "Ki yi hakuri fadima,horo ba
zai
taba zama kiyayya ba, musamman a zuxiyar da
ba ta da tamkar.... Matsala ta daya ce wadda
sai
ki min uzuri a kanta, ita ce,KAIFIN SO ba ya
hana
ni tsawatarwa idan an kauce hanya da zaki guji
laifuka da kin tabbatar ba a cika samun masoyi
kamata ba". Da muryar da ke nuna son fashewa
da kuka ta ce. "Idan shashancina ya hana ni
fahimtar ka fa.Ni ka karasa fice min a rai,ba ni
da
sauran wani abin yi a gidanka... Ni kawai
tafiya..." Ya shishige mata sosai da kokarin
shigar da idonsa cikin nata,ya girgiza mata kai.
"A fatar bakinki wadannan kalaman suka
tsaya,kafin na furta miki shashanci fadima sau
nawa na furta miki kalaman yabo? Kin taba
gode
min ko kin mayar min da rabbi? Ki yi min uzurin
waccan kalmar na janye ta tunda ta bata miki
rai
kin ji? Na san ba zan taba fita ranki ba mun
riga
mun zama jiji da tsoka... Gidana gidanki ne ba
zaki taba barinsa ba..." Ya hanata ci gaba da
kallon tuhumar da ta ke masa ta hanyar
rungume
ta yana karadeta da sumba kawai sai ta sa masa
kuka don ta san kawai ya gama da ita. Tabbas
ta yarda ta fada taekonso wanda ko ta sami
dama zata gaza fita da kashin kanta... Wato
tarkon sonsa wanda ba ta gaskata ba sai da
rikice rikicen nan nasu suka bullo,idan ya yi
fushi
sai jininta ya nemi hawa.da ya kaurace mata
jiya
da yau sai zuciyarta ta nemi bugawa,yanzu ta zo
ta tuhume shi ya cika mata ido har dadin bakin
da yake mata sun samun muhalli a zuciyarta.da
ya rungume ta sai zuciyarta ta warware kullaci
ta
sami aminci ta ji kamar dukkan matsalarta ta
duniya ta warware. Ta fara kokarin kwacewa
daga gare shi,sai ya yi dabarar zare makullai
din
hannunta ya tura aljihu, sannan ya ja ta
kujera ya
zauanar yana cewa. "Ki yi hakuri fadima!'Yan
kwanakin nan sai bata miki rai nake ko? Ki yi
hakuri aski ne idan ya zo gaban goshi ya fi
zafi...
Bari na kawo miki ruwan sanyi ki sha. Ya wuce
ba ta . Da ya ji ta bakinta ba. Ta bi shi da kallo
tana shakkar halin da ta tsinci kanta
tsakaninta
da shi. Haka ya dinga janta da maganganu na
nuna kauna da sanyaya rai, yana ba ta labaran
ban dariya, amma ta ki sakewa damtse ya kawo
musu abinci ya yaudare ta suka ci tare yana
labarta mata rabonsa da cin abincin kirki,tun
shekaran jiya. Ko a ranta ba ta karyata shi ba
don ta ga alamar rama a fuskarsa. Ta dubi
agogon da ya nuna sha biyu da kwata, sai ta
fara
neman makullanta ya yi dariya ya ce. "Na
adana
miki su,ai na yi tsammanin za ki taya ni kwanan
a nan". Sai ta kasa musa masa, shi kuma ya ci
gaba da himmar dauke damuwa daga
zuciyarta,har ya sami rage kaso mai
tsoka.musamman da ya ke ya share ta da
maganar ciki,kuma hakan ne ya sa ta nutsuwar
rai,ta yi bacci har da saleba a kirjinsa. Yaya da
ta
barshi da tunanin shaukin nasarar da ya samu a
kanta.tabbas saura kiri ya gama mallakar
zuciyarya,zuciyar da babu wani kaunarsa da ya
raba samunta. Ranar bai runtsa ba, don sai sulu
sin daren bacci ya rika fizgarsa,amma ya daure
masa ya tashi ya gurfana gaban mahalicin shi
khushu'I dauke tarin bukatunsa. Sai bayan ya
dawo masallacin suka hau rama baccin tare son
dama gaba dayansu sun ci bashinsa,kwana
biyu,Allah kuma ya yi musu gamon katar week
end na,ba su tashi ba sai sha daya ta haura.
Haka suka wani yana lallabarta tare da nuna
mata kauna,ya share maganar cikin tsab! To ita
ma duk da ba ta ba shi raddi to ba ta gwale shi
ko kuma turbune masa fuska,sai ya zamana ya
sami kansa da farin cikin da bai taba samu daga
gare ta ba, tunda ya aureta. Da yamma ya
lalaba
ta suka fita da zummar ya kai ta su gayar da
kawu da momi,kuma ya kirkiro fitar ne don ya
faranta mata,sai daiba ta yi farin cikin ba,don
ba
ta kaunar su ganta da ciki har su fara yamadidi
da ita a dangi zancen ya fito Alh ya zatar mata
cin amana.Amma babu yadda ta iya tunda abin
kunya ne ta nuna masa ba ta son zuwa
danginta,sai ta yi shahada ta bi shi suka tafi.
Me
zai faru? Karbar da suka yi mata ta kada mata
ciki kwarai,har ta fara zargin ko dai Abdullahi
ya
tona mata asirri ne? Kallon arziki ba ta samu
daga kawu ba, gasuwar tata ma ciki ya
amsa,dukkan kulawarsa da fara'arsa tana ga
Abdul,momi kuma sai wani irin kallo ta ke
mata,don haka a tsorace ta bar musu wajen ta
tafi wajen su safiyya. Babu jimawa momi ta aiko
akayi kiranta,ta same ta dakinta.ta nemi gurin
zama tana satar kallonm idon momi,wadda sam
babu annuri a ciki. "Me ne ne matsayi laila a
wajenki da kika yarda ta fi mu sonki,ta fi
mijinki
sonki,sannan ta fi mu sanin dukkan abinb da
zai
amfane ki? Tambayar da momi ta jefo mata ke
nan cikin kaushin murya wadda sai da ta janyo
cikinta ya juya.
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
38
Saboda firgita don haka ta kasa ko motsi bare ta
amsa sai da momi ta kara daure fuska ta ce.
"Ko
ba kya ji?" Ta muskuta ta kwaso in'ina da
rashin
ma'anar zance. "Wallahi... Wal... Momi
kururuta
lamari ne kawai irin na Abdul..... Ba ki ga cin
kashin da ya yi mata ba rannan.... Wai kar ta
kara zuwar masa gida.... Ni ban ga laifin da ta yi
ba....' Momi ta bude ido da kyau tana kallonta
cike da takaici,ta ce. "Kin ga kin kara bayar da
shaida a kanta da kuma abin da kanwar uwar
Alh
ta zo mana da shi gidan nan,don kwata kwata
babu Abdullahi cikin wannan maganar,tsoro na
daya Allah ya sa bai san da maganar kin kai wa
likita cikinsa ya cire ba... Haka ne? A kalolin
tashin hankali babu wanda bai birkito a zuciyar
fatima ba, yanzu ta fahimci lamarin babba
ne,sai
kawai ta yi zuru numfashinta na bugawa dai
dai.
Momi ta koro bayani cikin bacin rai. "Jiya har
kusan iyanzu