Showing 6001 words to 9000 words out of 34797 words

Chapter 3 - ZUCIYA DA KWANJI 2 Writing MAIMUNA IDRIS SANI BELI.pdf

na damuwar
Abdul. Sai da ya yi edabarar goge hawayensa

tsab bayan ya dan sami sassauci a ransa,sannan
ya juyo mata da murmushin karfin hali,sai ya
ganta da hawaye.ya bude ido cikin murmushi na
neman ba'asi sai ta kawar da kai tana goge
fuskarta. "Ki yi hakuri kin ji, ba a son raina
nake
bata ranki ba" Ya fada a can kasan
makogwaronsa sai ta kasa hada ido da shi,ya ce.
"Gyara fuskarki mu shiga". Bata musa ba ta
bude
jakarta ta fara gyara fuskar.ta dawo fes kamar
ba
ta yi hawaye ba,sai da ta mayar da kayan
jakarta
ta rufe sannan ta ta dago ta dube shi suka
hada
ido ya sakar mata murmushi,sai ta sami kanta
da
ba shi rabbi,abin da kuma ya so birkita shi ke
nan, tare da tabbatar masa ya ciyo wani birni a
cikin zuciyarta.bai taba ganin murmushi a
kuncinta tsakaninta da shi ba.... Ya shiga
damuwar neman sanin abin da ya yi ya samo
masa ita haka,wannan ya sa soyayyarta ta kara
cika masa kirji,har sai da ta bayyana a

harshensa
ya furta mata. "Ina sonki fadima". Ta kawar
da
kai sannan ta balle murfin motar,ya yi saurin
ruko hannunta,a tausashe ya ce. "Bari na kira
maryam ta shiga da ke" Yana rike da hannunta
ya yi kiran kanwaesa maryan ta wayarsa,sannan
ya sauke ido a kanta,ya ce, "Karfe nawa zan zo
na dauke ki?" Muryarta na rawa ta ce. "Duk
santa ka shirya". Tana kokarin janye
hannunrta,
ya ki sakin hanun nata,ya ce. "Idan na bari sai
dare ban takura ki ba?" Ta gyara kai fuskarta
na
nuna damuwar son ya sakar mata hannu saboda
ta hango fitowa maryam,ya ce. "Rufo kofar
nan in
fito in bude miki kin ji?" Ba ta musa ba ta rufe
kofar har maryam ta karaso,sannan ya fito ya
bude mata,suna gaisawa da maryam dinmai cike
da murnar ganin fatima sai fara'a suke wa
juna.ya dauko kayan barkar ya ba wa maryam
cikin barkanci ya ce. "Ki kular min da mata kar
ki
sake ki barta da kadaici.yau in son filin

zuciyarta
fetal" Maryam na dariya,fatima na kawar da
kai
har suka wuce irin nishadin nasara a cikin
zuciyarsa. Ashe fatima na jin wakazi? Bai samo
lagonta ba kuwa? Ya shige mota da sauri ta
tashe ta ya bar wajen. Duk da fatima na
kasaita
da shan kamshi da yake tana da fara'a kuma
ga
ta da kyau,sai ta yi farin jini a dangin Abu
Turab,aka dinga nunata a matsayin amaryarsa
a
dangi.ita kuma ta ki nuna kosawa duk wanda
aka
nuna mata sai ta gaishe ahi dai dai matsayinsa
da shekarunsa. Maryam da sauran kannen Abu
turab din suka dinga hidima da ita,komai sai
sun
yi mata na musamman tare da jin ta fi karfin
wannan,ita kuma tana ta binsu da godiya. Ba ta
hadu da su hindatu ba sai daba da magariba da
su maryam suka yi mata rakiya dakin
maijegon,suka kara gaisawa da muwadda wato
mai jegon,tunda sun hadu da ta shiga bangaren

iyayen abu Turab. Sannan ta umarci maryam ta
ba ta kayan wanda ita kanta ba tasan me ye a
ciki ba,ashe kaya masu kayu da tsada har sati
biyar,wannan ya sa muwadda ba ta iya hadiye
mamakin ita kawai ba,sai da ta nuna wa wata
yayar abdullahi haj Asma'u. "Anty kinga kayan
da
amaryar Abu Turab ta kawo wa baby". Haj
asma'u ta yaba ta yi godiya,abinka kuma da
dangin miji,karaf sai wata kauwa a wajen
abdullahi ta fara yiwa su sadiya da ke zaune
yarfe. "Ke dai komai kin hada,ga kyau ga
fara'a
,kyauta.wanda ya iya ya huta,kuma babu
ruwanki
da cika mutane da surutu,gara ma mai abin
kanshi tana bade mana". An ce kowa ya yi zagi
a
kasuwa yasanm da wanda ya ke, hindatu ce ta
fara amsawa da cewa. "Ban da abinki ai mikar
mutum ba ta wuce tsawon hannunsa". Sadiya
kuma na sako baki sai ta huce akan fatima.
"Idan
ana cin baure ai ba a ton cikin sa,ni ban ga
burgewa a cikin sayar da rai dan nemo suna ba.

Idan na adana wanda ya zame min wajibi na
gama aikina,ko ina tsiya ina matashin kai da
bargon da mutum zai rufa ma sai yana wujila
wujila da shi? A nan dai an zama kyandir". $
ban
da hindatu babu wanda ya san daga inda
maganar ta faro bare inda ta samar da ma'ana.
Dan haka maganar ta wuce sururuf bayan Haj
Asma'u ta tsawata,sai dai ta yi katon rauni a
zuciyar fatima.11) Ta tabbatar babu abin da ya fi kishi
ciwo,tunda komai bai wuce a canja maka fassara
a goranta maka shi ba, zuciyarta ta baci matuka
har ta dinga jin hawaye na son zubo mata a ido.
Dole ta sna neman tsari da wadannan kananan
maganganun sa sadiya wadda ko yaushe kiris ta
ke jira ta goranta mata akansa. Cikin dabara ta
mike ta bi Haj Asma'u tana cewa. "Anti bari na
zo na ga turarukan na akwai irin wadanda nake
amfanin da su,marayam ku zo mu je". Suaka
fice
ta bar wa su hindatu dakin,tana jin wata s'ida
a
ranta.ita yanzu ko ganin sadiyar bata mata rai
yake. A wajen haj Asma'u ta zabi turaruka
masu

kyau na kimanin dubu talatin,antin ta cire
mata
wani abu inda ta ce ba ta fito da kudi ba a tura
mata wani ta bayar. Tsab ta shiga cikin 'yan
uwan abu Turab ta baro su hindatu da ire iren
matan yaye da na dangi,don haka yayyen
Abdullahi da iyayensa suka dinga yabonta suna
jin dadin yadda ta ke daukarsu'yan uwanta, ba
kamar yadda sauran surukan sukan yi ba. Bayan
sallar magriba aka ce ga ke kadai kika zo". $ ta
kare da zolayarta,sai fatima ta yi dariya
kawai,ita
kuma anti da kanta ta je ta ce,ya fara kai su
sadiya,fatima na cin abinci, duk kuwa da ba
abincin ta ke ci ba. Shi da ya san dawan garin
bai wani musa ba ya hada kan su sadiya ya kai
su gida,ko kashe motar bai yi ba ya koma. Farin
cikin sa ya kura da ya ga wajen mutum goma su
rako masa fatima,har ma da yayyensa biyu,
suna
ta yiwa juna godiya tana sa su alkawarin kawo
mata ziyara. Da haka suka yi sallama ya ja
mota,maimakon ya yi baya su hau B.U K. Road
sai ya mike amin kano,dole fatima ta kau da
shirun da ya ratsa motar. "Ta ina zamu bi ne?"

Ba tare da ya dube ta ba, ya ce. "Zan ga
likitana
ne,kin san ina karbar magani." Ta tara gira,ta
ce.
"Na me?" Ya juyo ya dube ta,sannan ya mayar
da
kai ga titi "Na neman tsatso ko zan huta gorin
..... "Ga mamakin kanta sai ta ji kishi ya karci
zucitarta,tare da tunano uwar gori sadiya,sai ta
kawar da kai tana jin wancan kishin na dan
gushewa,yayin da kwanyarta ke karanta mata,
ai
sadiya damuwa ce, gori kamar a jininta yake.
Da
suka karaso asibitin ya yi mata tayin ra raka
shi,
sai ta yi fuska ta ce. "Ka manta ba ka sako min
hijab ba?" Dariya kawai ya yi ya fice ya rabu da
ita, inda ta bishi da kallo, kirjinta na bugawa
wannan asibitin ne na zuwanta,domin likintan
ya
san aikinsa, shi ya ba ta gwaggwabar
gudubmowar hana mahaifarta karbar ciki
lokacin
da ta ke gidan Alh,ba tare da sanin Alh ba. A

lokacin duk bayan wata uku ta ke karbar allura,
amma tun bayan mutuwar aurenta ta dauke
kafa,don haka ta san yanzu idan ta shiga babu
mamaki ya ishe ta da tambayoyi a gaban
Abdullahi. Sai dai wasa! Tun tana jiran fitowar
Abdullahi da kauna,har ta yi mugun
gundura,da
ta duba agogon hannunta sai ta tarar goma ta
wuce,ke nan ta yi zaman sama da awa daya a
cikin motar. Ranta ya yi mugun baci, kawai sai
ta balle murfin motar ta fito,kai tsaye ta wuce
reception ta dinga bin mutane da ido,amma
babu
abdullahi sai wasu ma'aikatan da ta sani ne
suka
dinga kawo mata gaisuwa."Madam kwana biyu".
Inji wata nos wai ita sister Rabi,fatima ta yi
murmushi kawai domin babu amsar ba ta.ta
kuma cewa. "Kuna da appointment ne?" Fatima
ta yi saurin girgiza kai. "A'a wani yaro na
rako,amma kinga ya shanya ni kawai fiye da
awa
daya,ina jiransa" Sister Rabi ta bi jama'ar da
kallo,ta ce. "Kuma babu shi a nan?" Fatima ta
gyara kai, sister Rabi ta kuma cewa. "To ko

abdullahi ne? Shi ne ya jima tare da doctor"
Fatima ta hadiye takaicinta. A takaice ta ce.
"Shi
ne" Sister Rabi ta tafi tana cewa. "Bari na miki
magana da shi. Ba ta jima ba ta fito ta ce. "Ya
ce ki shiga". Dan babu yadda ta iya ne kawai ta
tura kofar ta shiga,ta tarar ana yiwa abdullahi
allura. Ta hau nazarin ofishin kafin su
gama,sannan ta nemi guri da zauna tana
harara
abdullahi.
4 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
12) Dr ya koma mazauninsa cike da mamakin
ganin Fatima,kuma wai matar abdullahi ce, da
me
Abdullahi ya rako wannan sarauniyar matan?
Tu'ajjinbin ya tuke a nan. Suka gaisa tana
wani
basarwa ita a dole ba ta san shi ba, shi kuma ya
ki yarda da hakan,ya ce mata. "Ki yi hakuri ya
karbi wata allura ne, ya zauna zaman jiran
rabin
awa ya sha magani sannan ya karbi wata" Ba ta

tanka ba, kuma fuskarta ba ta bayyana
matakin
da zuciyarta ta dauka ba, ya kuma tambayarta.
"Madam kwana biyu?" Ta yi murmushi kawai
nan
ma ba ta tanka ba, idanunwanta na kan
Abdullahi,tana masa duban tuhu$a. Shi kuma
ya
ki yarda su hada ido.sai ya mayar da hankalinsa
ga likitan wanda ya fara yi masa bayani. "Za
mu
dinga haka duk bayan wata daya kai kuma
Allah
ya sa akwai madam a kusa sai a hana ido
bacci... Ina mana fatan dawainiyarmu ta zo
karshe Abdullahi". Abdullahi ya mike, ya mika
masa hannun yana cewa. "Insha'Allahu dr,na
gode fa". Sannan ya juya ya dube ta, ya yi
fuska
ya ce. "Ke kuma mene ne tunda kika shigo kike
ta
faman harara ta, yi hakuri yarintar tawa ce ta
motsa in ba ki hakura ba kuma idan mun koma
gida sai ki daki abinki." Ganin likita ya sa ta
maida abin wasa. "Abin da ka yi ai ya fice

kuruciya,dan na ce maka yaro is good ya ya za a
yi ka shanya ni fiye da awa daya? Idan akwai
abin da ya fice duka ma ba sai na yi maka ba,
ya
kamata duk gajiyar da na yi ka kwo ni nan ka
dire,a kalla yanzu na yi nisa da bacci. Ya hadiye
dariyar ketar da ke tattare da maganar da zata
fito bakinsa. "Watakila wata gajiyar ke
kiranki".
Ta yi masa duban rashin fahimta,amma sai ta
share saboda idon likita,suka yi masa sallama
suka fice, amma suna shiga mota ya biyo
abdullahi da kira ta waya. Sai ya dube ta,ya ce.
Don Allah zahara'u minti biyu na manto
maganin
aofishin Dr". A kufule ta mika masa hannu,ta
ce.
"Gulma dai kawai na dawainiya da ku. Ba ni key
din idan ka fice minti biyu na rantse sai dai ka
tarar da filin wajen". Yana dariya ya mika
mata,sannan ya falla da gudu. Dr ya rike
hannunsa fuska a rikice,ya ce. "Da gaske
fatima
matarka ce?" Fuskar abdullahi da alamun
mamaki

ya kada kai,likita ya sauke numfashi ya ce,
"A'a
tsaya kar muyi haka da warwara.ta amince zata
haihu da kai?" Da karsashi Abdullahi ya ce. "Ba
ta da zabi" Dr ya dururuce hannu alamar
jinjinawa ya ce. "To kar ka yi wasa, ina zaton
kukanmu ya zo karshe,don mahaifarta na
saurin
karbar ciki,sai dai ba ta da juriyar rike shi idan
ya
yi kwari,idan hakan ta kansace yana da wata
uku
za mu yi mata wani aiki,sannan mu bi lamarin
da
addu'a. Abdullahi barkatai suka taru a
kwanyan
Abdullahi lpkaci guda,albishir din likita da
fargabar yadda za su kwashe da yar rikicin ban
da minti biyun da ta ba shi. A gaggauce ya yiwa
likitan godiya ya fice. Ya dinga jan motar a
sannu
kamar ba dare ba, ne ma sai da ta yi magana.
"Yanzu don Allah a titin nan zamu kwana?" Ya
dan yi mata wani duba,ya ce. "Ai na ga kin gaji
ne bai kamata na fige motar ba ko? Ta yi shiru

ta
kawar da kai". "Kin san maganin gajiyar nan
taki?
Muna zuwa gida ki yi wanka da ruwan mai dumi
sannan ki dan ci kayan marmari ki sha zuma
kofi
daya,tsab za ki ji kin wartsake. Nan ma ba ta
tanka ba, har suka je gida yana nemanta da
magana tana sharewa, shi kuma bai hakura ya
bari ba. Suka shiga dakinta ya ajiye mata kayan
da suka shigo da shi zai fice zuwa dakinsa,ita
kuma zata shiga wanka. Ta kira shi ranta a dan
bace.ya juyo ta ce. "Kar ka kuma shigo min da
wanin bargo da filo dakin nan". Ya yi nazarinta
da
kyau,amma yanayin bacin fuskarta ya sanya shi
hadiye tambayarsa,ya yi mata. "Zumar zan
kawo
miki?" Ba ta tanka ba ta wuce bandaki,shi kuma
ya fice ya dan jima sannan ya dawo mata da
zumar a kofi,ba tare da shakka ba ya ishe ta
har
dakin bacci tana zaune gaban madubi daure da
towel. Fuskarta ta nuna rashin jin dadin
shigowarsa,sai dai bakinta bai furta ba. Ta karba

tana dan binsa da kallonm nazari,shi kuma ya
birkida tunaninta da siyasa,dan ya nuna bai
damu
da yadda ya same ta ba. Ya cire riga ya shiga
wanka a toilet din cikin dakin. Da sauri ta shirya
ta zira kayan bacci masu kauri ta dauki zumar
ta
fice falo cikin damuwa irin irin ta Alh da ta
shishigin da abdullahi ke mata yau
2 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Amun hakuri rashin sa page 5
Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
13) Da kuma na gorin sadiya,babu wanda
zata iya magani ba tare da ya gagare ta ko in ta
yi maganinsa ta cutu ba, wato ba ta da damar
magancewa Alh matsalarsa,shishigin Abdullahi
kuma makale da gorin sadiya,wanda maganin
gorin shi ne ta karbi tayin shi da shishiginshi, a
nan ne kuma ita zata cutu. Duk zakin zuma sai
dinga shanta kamar magani, har dai ta dire
kofin
ta dan kishigida a kasalce.ya fito shi ma sanye

da yalwatattun kayan bacci, kallo daya ta yi
masa ta kawar da kai,shi ne ya dora mata
ido,har
ya kada kai zuwa kicin ya yanko
lemo,abarba,kan
kana da gwanda ya dawofalon ya zauna kujera
kusa da ita ya sanya kayan marmarin tsakiyarsu
kan hannun kujerar,ya ce mata Bismillah". Ko
motsi ba ta yi ba, babu kuma alamar zata tanka
masa bare ta sa hannun.ya share ta ya ci gaba
da shan kayansa yana kallonta ta janyo
mayafin
ta dora aka, sannan ta kara kishingidawa can
gefe,ta juya masakeya. Ya dinga nazarinta
yana
tunanin inda zai kamo zarenta ta kula shi. Ya yi
gyaran murya tukunna ya ce. "Wai fadima me
ke
faruwa ne nake ganin ranki a bace?" Ta girgiza
kai kawai ba ta ce komai ba. Ya dan ja fasali
sannan ya ce. "Me yasa kika hana ni shigowa da
filo alhalin kina rufe dakunanki?" Ta juyo a
sanyaye ta dube shi, idanuwanta sun dan kada
alamar ranta a bace yake.ta ce. Sai ka dinga
shiga nan dakin ni ina shiga can, kafin Allah ya

yi
ikonsa akan mu... Mts! Ba na son kananan
magana ne, wai babu abin da ya wuce a ci maka
fuska a kansa,ai kishi bai yi ba wallahi." (Allah
ya
yiwa sadiya albarka) abin da ya yi ta
maimaitawa
ke nan a ransa,amma ya hana fuskarsa nuna
farin cikin da zuciyarsa ke yi,sai ya tara
jimamin
duniyar nan afuskarsa, sannan ya shiga
lallabata.
"Kofofin da nake ta fatan ki toshe ke nan tun
tuni,idan ba ki bayar da kofa ba mutum ma
shakkarki zai yi.yanzu me ye ma na sai mun
raba
dakin? Ko babu komai ai zamu dinga debewa
juna
kewa..." Ta yi saurin dubarsa,amma saboda
fuskarsa na bayyana jimami sai ta kawar da
kai,ta ce. "Ban iya yaudara ba" Ya amsa a
tausashe. "Dama babi ita a tsakaninmu,na
sanki
farin sani, kina furta min gaskiyar zuciyarki
saboda haka na san matsayina a wajenki, ni ma

bana boye miki dukkan abin da ke raina,ya sa ki
farin ciki ko akasin haka,ba na damuwa dan in
sin
tabbatar miki da gaskiyata,ke ma tun kina
ganin
bekena har ranki ya yarda babu cuta a
tsakanina
da ke..... Babu soyayya ya isa rike wani gidan
auren". Ta yi shiru ba ta tanka ba, kanta na
kallon kasa,kwalla duk ta cika mata ido. Ya
jima
yana kallonta. Harshensa bai bar addu'a ba,
tsawon wasu mintuna sannan ya ce. "Don Allah
ki rage sanyawa kanki damuwa fadima,duk abin
da muke. Cin karo da shi a rayuwarmu
rubutaccen al'amari ne daga ubangiji,damuwa
da
bacin ranki ko cida zuci na. Ba zai canja komai
ba. Nan ma ta yi shiru,ya kara jimawa yana
ambaton ismullahil azam cikin ransa, sannan ya
ce. "Ki je ki kwanta ki huta,sai ki dan bar min
dan
guri kadana ma da zan sanya hakarkarina. Duka
duniyar ma nawa ta ke,duk burikan mutum
wata

rana kabari zai sami kansa". Ta mike ba tare da
ta tanka masa ba, ta wuce daki. Ya bita da kallo
cikin dukan zuciya har mintuna goma bai ji ta
murzawa kofar key ba,ya sauke ajiyar zuciya
yana hamdala ga ubangiji,shi ya san hakuri da
na
ci da addu'a sun fara rana. Biyayya ke nan mai
kai akuya dakin kura har ta yi mata tausa
1 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.14) A nutse cikin tsarkin zuciya ya dauro
alwala ya gabatar da nafila raka'a shida tare
da
neman daukin ubangiji a dukkan bukatunsa na
daren yau,ya mallaka masa fatima,ya takaita
masa wahalar neman soyayyarta,sannan ya ba
shi dan kansa. Da hawayensa ya dinga yiwa
ubangiji kirari yana jaddada kokensa.bayan ya
sallame ya jima zaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login