Showing 24001 words to 25590 words out of 25590 words

Chapter 9 - WASA DA SO BY AISHA MUHAMMED SANI .pdf

25 Jul 2025

2922

ayanzu,Hameeda
dan Allah kar ki gujeni akan ki zan iya rasa rayuwata,Hameeda ina son ki wallahi da gaske na
ke ina sonki, sonki ne ya kai ni cikin wannan halin,ki aminta da ni mu rayu dan Allah."

Tunda ya fara maganar nan Hameeda kawai kallon mamaki ta ke masa sai da ta ga yayi shiru
ta ce, "A'a A'a Yaya Adam ba na son wannan wasan ka bari karka kara bana so ni Muhsin zan
Aure,ka dai na min haka wasan ka ya yi yawa,ka bari dan Allah."karasa maganar tai tana kuka
tare da fincike hannun ta, ta fita daga dakin.
Adam kuwa banda hawaye ba abinda ke kwarara a idanunsa azuciyarsa ko sai fadi ya ke, "Ni
na cuci kai na daman nasan Hameeda ba za ta taba yarda da ni ba wallahi nayi dana sanin
*Wasa da so* sai ayau nasan me nene so."

_Ni xayyeesher na ce ko ya abun zai kasance? ku biyo ni domin ganin Ya zata kaya......._

Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

��������
����
*WASA DA SO*
��������
����


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

*PAGE*-28

____________________________________________________________________________


Hameeda na fita kuwa ta ci karo da Aunty, tuni ta goge hawayenta kan ta karasa, Aunty ta ce,
"Fatan dai ba jikin Yayan na ki ba nE?"


kawai girgiza ma ta kai Hameeda ta yi alamar Aa, ita ko Aunty ba ta tsaya ba ta amsa ba ta
shige ciki.

Ta na shiga ta tarar da Adam ban da hawaye ba abin da kwarara daga idanun sa, da sauri
Aunty ta kasara tare da fadin, "Menene kuma son ko dai jikin ne a kira likata."

Rikwo ma ta hannu ya yi tare da fadin, "Aa Aunty ki zauna ba komai."

Aunty ta ce, "Indai zan zauna sai ka min alkawarin za ka fadamin abun da ke damun ka."

kawai zub da kwalla Adam ya cigaba da yi domin kuwa in bai manta ba Aunty ma ta ta ba fada
ma sa cewa ya na *wasa da so* da kyar kuwa ta shawo kan sa, sannan ya fada ma ta komai
abin da ke faruwa tun ya na makaranta kawo yanzu.

Ba karamin tausayin Adam ya ba wa Auntyn sa ba domin tun tuni ta ke guje ma sa wannan
ranar.


A karshe ya kara da cewa , "Aunty Dan Allah kimin Alkawarin cewa wannan maganar ta zama
sirri, ni zan iya jure komai indai Hameeda za tai farinciki a gidan Auren ta."

Aunty ta ce, "To kai kuma lafiyar ka fa son, kennan farincikinta ya fi lafiyar ka da farincikin ka."

Murmushi kawai Adam Yayi sannan ya ce, "Bakomai Auntyna ai kanwatace."

Duk da haka dai Aunty ta kasa walwala a asibitin nan sai ya kasance Adam ya zama kaman shi
je jinyar ta sai ma ta wasa da dariya ya ke duk dan abun ya bar ran ta,duk da cewa kuwa shi ya
san mai ke damunsa azuci.

Daga karshe dai likita ya zo ya Domin sallamar su tare da ba wa Aunty shawara akan cewa,
"Duk abin da Adam ya ke so amasa indai ana son rayuwarsa."

To fa anan hankalin Aunty ya kara tashi, Adam kuwa ya nuna ma ta cewa ko ajikinsa, Gashi ba
ta da damar fada domin tq dau masa alkawari.


Tunda suka koma gida Hameeda ke gudun Adam , shiyasa da ya fahimci hakan ya ma dai na
fitowa kullum ya na daki.


Muhsin kuwa Mubarak ya sanar dashi komai akan yq taimaka ya barwa Adam Hameeda Amma
ya yi burus tare da da fadin ai shima son tq ya ke kuma ma yq fi Adam son ta.


Akwana atashi yau saura kwana daya bikin Muhsin da Hameeda.

Sun shirya tsaf domin tafiya kamu.

Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

��������
����
*WASA DA SO*
��������
����


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

*PAGE*-29/30

️_________________________________________________
___________________________

_SADAUKARWA GAREKU YAYUNA HASSAN ATK$HUSSAINI ATK ALLAH YAKARA
RAYUWA MAI ABARKA_

*Godiya ta mussaman gareka YAYA Mubarak Allah ya kara basira da daukakaALLAH YA
BAKA ABIDILLE*


*FEjin yau dai ba editing kuyi hkr da typing erorrs*


Fitowar da Adam zai yi domin tafiya ganin Muhsin da Hameeda ne ya rikita ma sa zuciya tuni ya
fadi akasa,Hameeda ko na hango hakan tuni ta tawo da gudu tare da zuwa wajen yayan na
ta,kan ta karasa har numfashin sa yadauke.

Kuka ta fara tare da kiran su Mama,Momy da Aunty,ai ko tuni aka dau hanyar asibiti.



Su na zuwa aka fara Adam taimakon gaggawa , anyi sa'a wannan karan bai kai na wancen
jimawa ba amman wannan din ya fi hatsari domin kuwa ya na dab da rasa rayuwar
sa,Hameeda na dakin ta ki fita rikye ta ke da hannun Yayan na ta, ai ko ya na farkawa
murmushi ya yi tare da fadin, "Hamee na bakuje gun kamun ba ne, ku ta fi nima zan zo."
Hameeda ta ce, "Aa ai an ma fasa."

Adam zai yi magana kennan sai ga likita ya shigo.

"Barkan ka dai Adam ya karfin jiki?"

Murmushi ya yi tare fadin , "Jiki Alhamdulillah likita."

Likata ya kara da cewa, "Ka na dai daurewa ne kawai, amman dole akwai abun da ka ke so
kuma in baka samu yanzu ba ina da tabbacin ka kara faduwa irin ta yau ka yi ta karshe
kennan."


Daga idon Hameedan har Adam hawaye ne kawai ke zuba,sai ita tai dauriya tare da fadin, "Ba

zai mutu ba insha Allah likita,zai samu abun da ya ke so."

Adam na jin hakan tuni ya tashi daga kan gadon tare da fadin, "Da gaske ki ke Hameeda?.

Daga ma sa kai kawai ta yi tare da rufe fuskarta.

Adam bai san lokacin da ya rungume Hameeda ba tsabar murna.

Likata kuwa fita yayi kawai yana murmushi sannan ya sanar da su Abba da Momy duk abin da
ya fahimta ga me da hakan,ba karamin farinciki Aunty tayi ba da jin hakan.


Tuni aka sallami Adam.

Suna komawa ba jimawa Muhsin da kan sa ya zo yana taya Adam Murna tare da fadin ai
bakomai daman Allah ya yi Hameeda ba matar ba ce ya dauki hakan amatsayin kaddara kuma
ya sanar da iyayensa komai sun fahimta.


Ancigaba da shagalin biki kamar yadda aka fara amman fa Adam baya barin Hameeda ko ina ta
yi yana biye da ita duk wanda ya masa magana yakan ce masa, " *Ni fa ku barni nasan illan
wasa da so gwanda nai tatttalin abuna, dan da tuni an gama kayar dani*."

Shi dai Adam gani ya ke za akwace ma sa Hameedar sa.

Dariya kawai su ke domin su kan su sun dau babban darasi akan rayuwar Adam Da Hameeda.


An daura Auren Adam da Hameeda, Dady ya ba su wani karamin gidan sa achan su ka tare.

Mubarak kuwa soyayya ta kullu tsakanin sa Da Hameeda suma an fara shirin Auren su.....


Bayan shekara biyu......

Hameeda ce ta fito da wani lukekyn cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta na shagwabe fuska tare
da cewa, "Honey ni fa ice cream zan sha."

Adam da ke kallo A TV juyowa ya yi ya na, "Ah Mama Lutiya yau Yan abun sun motsa kennan
yau ba ni ba hutu daga wannan sai wancen."


Zama Hameeda tai tare da fara kuka tana, "Ni wallahi in ba zaka siyomin ba sai na baka

Babynka daman ni na gaji."

Dariya Adam ya yi, ya tashi ya na, "yoo ni nama isa?, ai tashi muje."

Rikyeta ya yi suka fita tare.


Haka Rayuwa ta cigaba da kasancewa cikin farinciki Da anashuwa tsakanin Adam da
Hameeda.


*ALHAMDULILLAH,ALHAMDULILLAH YAU DAI ALLAH YA YI NA KAMMALA WANNAN
LITTAFINA MAI SUNA WASA DA SO,ABIN NAYI KUSKURE ACIKI ALLAH KA YAFEMIN,ABIN
DA NAI DAIDAI ALLAH YASA YA AMFANAR DA AL UMMA, AMEEN YA ALLLAH*

_Nagode sosai masoyana wajen bani hadin kai acikin wannan littafin nawa inan ta fe da sabo
amman kan ya zo ga wanda na fara nan ni da kawata eyman maj suna *Yaya Imran* fatan zaku
cigaba da bibiya kamar yadda akasa ba_

Duk mai shawara,sharhi,neman karin bayani ta nemeni ta wannan number

08103080717

Urs xayyeesherth

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login