Showing 18001 words to 21000 words out of 25590 words

Chapter 7 - WASA DA SO BY AISHA MUHAMMED SANI .pdf

25 Jul 2025

2921

amma hakan bai sa sun
fada musu ko su nuna cewa sun fahimci hakan ba,kawai sun zuba musu idone suna ganin ikon
Allah.


Adam na gama waya da hameeda Mubarak ya ce, "Nikam dai yau ba zanyi shiru ba,Adam wai
mai yasa ka ke *WASA DA SO* ne?,ka son Hameeda Amman ka kasa fahimtar hakan.


Adam ya ce, ............

Urs xayyesherth
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


��������
����
*WASA DA SO*
��������
����


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

whenever U feel Blue,
i will be there for U,
Whenever u are sad'
i will stay by ur side,
whenever U need sumone to love,
i will always be there for u......

*PAGE*-22

____________________________________________________________________________


"Ba ka yi karya ba Ina son hameeda kuma ina son mace mai irin haleyar ta da ma ya na yin ta
gaba daya,Amman abinda ba Ku gane ba shine son da nake ma ta ba irin Wanda Ku ke tunani
ba ne,Hameeda jinjikinace dole na so ta kuma nai kishinta Amman ba wai so na soyayyar Aure
ba,bana tsammanin zan iya rayuwar da Hamee nah." Ya karasa fadan hakan ya na murmushi

tare da kallon hoton Hameeda da ke screem din wayar sa.


Mubarak ya ce, "Hmm Adam kennan ina ganin ni na San ka fiye yadda kasan kan ka,Amman A
kullum Ina ma fatan alkairy, domin farincikin Aminina shine na wa."

"Godiya na ke Abokina naji dadin jin hakan daga bakin ka."


Washe gari

Hameeda na zaune ta na chating A wayarta sai ga text din Muhsin ya shigo ma ta kamar haka:
_"Assalamu alkaimu ya ke masoyiya ta,hasken raina,fatan kin tashi lafiya?Allah yasa haka
Ameen,ina so in sanar da ke cewa yau zanbar cikin garin nan zan koma kauyen kano *gaya*
asarin garin mahaifina,Ku ma bazan dawo ba sai har na mallaki Abinda zan aureki dama
Wanda zan ciyar da ke da ikon Allah,Amman ina so kimin alkawari daya,bazaki taba bawa wani
damar shiga zuciyarki ba,ki killacemin kanki kamar yadda kika saba,daga yau bazan kara kiran
ki ba kuma bazan kara miki text ba har sai na dawo gareki,karki manta ina son ki ,kuma zan
cigaba da sonki har bayan raina,na baki Amanar zuciyata,ZANYI KEWARKI ,daga
masoyinki,kuma mijinki in Allah ya yarda MUHSIN."_

wassalamu alaikum


Hameeda ta na karanta text din ta na kuka ta rasa me ke ma ta dadi Aduniyar nannan.


Haka ta gama kukan ta har tai barci agun.


_________________________________________________________

A kwana atashi har Muhsin ya yi sati biyu da tafiya,Adam kuwa ya gama jarabawar sa zasu
dawo gida .


Adam da Mubarak sun shirya tsaf,hakama Nusaiba wadda ita dai da ka ganta kasan ba ta son
tafiyarnan.


Adam da Mubarak sun rakata har wajen motarta suna Allah ya kiyaye,Nusaiba ko ta kasa
magana banda hawaye ba a binda ke zuba a idonta.

Har suka shige motar da a kazo dauka Kansu tana kallon su sai da motarsu ta tashi kan itama
fara tafiya.


Hameeda tun safe ta tafi gidan Su Adam domin tarar yayanta Adam.


Ita da Aunty ne suka shiga kichin sai girke-girke su ke kala-kala,Mama in tazo hucewa sai dai ta
CE aiki bai isheku ba ne,sai ka ce Abban Autane zai dawo kun wani zakye sai girki Ku ke kun
cika ma na gida da kamshi."

Aunty ce tai murmushi ta na fadin, "Haba ke kuwa Mama D'a na ne fa daya tillo ke hanya ai dole
na dage Dan wallahi ni na zaku ma ya yi ya dawo da,da yarda zanyi yadawo karatu agarinnan
ai da na yi wallahi,gidan ba shi ba dadi."


Mama ta ce, "Oh wannan inaga to in kuma yayi AURE agidannan za ki ce ya tare."


Aunty tana dariya tana fadin , "Ai kin San ma wannan dole ne."


Duk da cewa Aunty ba ita ta haifi Adam ba Amman ta dauki soyayyar duniyar nan ta daura a
kan sa,tun ya na karami ta ke wahalarsa har yau kuwa ba ta taba nuna gazawarta ba,ko yarta
da ta Haifa ba ta nuna ma ta so kamar yadda ta nunawa Adam ba.

Hakan yasa kullum suke kara samun zaman lafiya da farinciki a cikn gidan su.


Auta kuwa ranar tak'i zuwa skul wai ita A dole sai yayanta ya dawo shi zai kaita,da kyar Mama
ta lallabata sannan ta yarda aka kai ta tana dawowa kuma ta fara murna bai dawo ba ita zata
fara ganinsa tuni ita da Hameeda suka je kwofar gida su ka tsaya.


Misalin karfe 3 na rana su Adam su ka iso.

Da gudu Auta ta karasa wajensa tare da rungume yayan na ta, ita kuwa Hameeda ta na
ganinsa taji wani sabon lamari jikinta duk ya mutu,kawai kunyarsa ta ke ji,da Dane da tuni ta
karasa ta na ma sa oyoyo Amman yau ta kasa.

Shi ko yadau Auta Amman hankalinsa na kan Hameeda kawai ita ya zubawa ido,ya ga ta kasa
karasowa garesa.

Ba ta rai ya yi tare da fadin, "Ke ba za ki karaso ba ne?"


Urs XAYYEESHERTH

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

��������
����
*WASA DA SO*
��������
����


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOVE MESSAGE*

My love for you knows no bounds, it’s timeless and endless. You can enrich my life in more
ways then I could ever express in words. I felt strongly connected to you the moment I looked
into your eyes. I was drawn to your soul in a way I have never experienced before. You are the
only one can see the door to my soul.
*PAGE*-23

____________________________________________________________________________

A shagwabe Hameeda ta ce, "To bayan Auta ce ta rigani." Zuwa ta ke ta na fadin hakan.


Adam ya yi murmushi ya na, "Ai na zata zaki nunamin kin girma ne an dai na min Oyoyo."

Dariya kawai Hameeda ta yi tare da karban jakar hannun sa su ka shige gida.


Su na shiga Aunty ta tawo ta rungeme D'an ta tare da fadin, "Barka da dawowa my son."

Murmushi Adam ya yi tare da durkusawa kasa yana, "Nagode Aunty na na same Ku lafiya."

Dago dashi Aunty tayi tare da fadin, "Smile lafiyan mu lau,ma za jekayi wanka ka yi sallah
sannan ka zo ga abincin ka nan komai ya na shirye."

Adam ya ce , "Ok Aunty ina Mama tsohuwa ne wa to ita ko murnar dawowa ta ma bata yi."

Mama ta fito tana, "Yoo ni ina ruwana da dawowarka ka dawo ka ishemu dai."

Aunty ta ce, "Eh munji son bar tsohuwar nan je kayi abinda ke gaban ka."


Adam kawai murmushi ya yi yatafi yana murnar kasancewa D'a ga Mama da Aunty DOMIN
akullum kara birgesa su ke yadda suka hada Kansu su ke zaman lafiya tsakanin su.


Hameeda ce ta bi bayansa da jakarsa,su na shiga Adam ya kulle kwofar tare da fadin, "Hamee
nah da alama kina cikin damuwa Dan ban sa ba ganinki cikin ya nayi haka ba."

Murmushi Hameeda ta yi tare da fadin, "Smile yayana ka yi wanka kai sallah in kaci abinci za
muyi magana."

Adam ya ce , "Oh shikenan sai na fito."

Hameeda ta fita tana, "Adai yi wanka mai kyau kar ai jika-jika."


Adam kawai dariya yayi yana, "za ki sa ni zan fito ai."

A nutse Adam ya yi wanka ya gabatar da farilarsa sannan ya shirya cikin Kananun kaya,bluen
Riga da farin wando,tare da Glass din sa Wanda ya saba sawa,da ka gansa kai kace wani
babban taro za shi.


Aunty da Mama ne Afalo su na zaune.



Ya na fitowa Mama ta ce, " Ai mun za ta sai an shigo an janyo ka za ka fito ne."


Aunty ta ce, "Umm su Tsohuwa dai an cika sa ido,son rabu da ita ka je ga abincin ka chan
Hameeda ta shirya."

Adam ya ce, "Aunty na rabu da Mama nasan damuwarta bai huce goro ta ke bukata ba."


Mama ta ce, "Dukkan su zaku sani ne Bari Abban Auta yadawo."

Dariya dukansu suke sannan Adam ya nufi wajen Hameeda.

Ya na zuwa ta ce, "Wooo yaya Messi na gaskiya turaran kan nan kamshinsa dadi dole in sace."

Adam ya tabu ne fuska, "Tab yasin ba ki isa ba budurwa ta ce fa ta siyamin ."


Hameeda ta ce, "Oh ka ce yan karya ne su ka siyama ba ma wannan ba ga food din ka nan
bismillah."


"Woooo Amman dai Auntyce ta yi girkin nan daga jin kamshin,Dan nasan ita kadai za ta iya."

Cewar Adam

Hameeda ta ce, "Ohooo dai ni kaci abinci."

Adam ko ya yi shiru sai afa abinci ya ke abin sa, Hameeda ko ta zuba masa ido ta na ta kallon
sa.


Sai da Adam ya ji cikin sa yadauka dam sannan ya ce, "HAMEEDA ki nutsu muyi magana ba na
son ki boyemin komai ki fadamin komai,me ke damunki? Miye damuwarki? Kar kiji tsoro ko
shakkar fada min duk abin da ke faruwa."


Hawaye ne ya fara zubowa a idanun Hameeda ta rasa me ma zata CE da yayan na ta.

Adam ne ya fara goge ma ta hawayen da ke kwarara afuskarta ya ce , "Hamee na please ki
nutsu mu yi magana."

Hameeda ta ce, "Yaya ......


Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


��������
����
*WASA DA SO*
��������
����


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

You're Always On My Mind, Day And Night
When I Think Of You, All Feels So Right
Need To Have You, Need To Hold You
And Tell You That I Love You.
My Dear, I Don't Want To See Us Apart
This Separation Just Tears Away My Heart
I Miss You, Oh, I Really Miss You
Will Need You More And More Each Day
I Know I Cannot Live Without You
I Miss You, More Than Words Can Say.

*PAGE*-24

____________________________________________________________________________

*WANNAN SHAFIN NA KU NE YAN GRP DIN BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION
mussaman ku Aisha humaira da AG ina yin ku irin sosai dinnan comments din ku na bani
nishadi*

Sai tai shiru, Adam ya ce, "Ina jin ki Hamee."
A nan Hameeda ta kwashe duk abin da ya faru tsakanin ta da Muhsin da ma na Abban Muhsin
da Dadynta ta fada ma sa.

Gaba daya jikin Adam ya yi sanyi domin ga dukkan Alamu Hameeda ta Amince da Muhsin, duk
da cewa ya na jin kishin kanwar ta sa, to Amma fa wannan karon ya zama dole ya taimaka ma
ta wajen cimma burin ta, domin farin cikin ta.


Murmushi Adam ya yi tare da riko hannun kanwar ta sa ya ce, "Haba Hamee na, A kan wannan
karamin abun ki ka shiga damuwa?,indai wannnan ne na mi ki alkawarin duk ranar da Muhsin
ya dawo, ni zan jagoranci maganar Auren."

Hameeda ta kasa d'ago kai ta kalli Yayan nata.

Adam ya d'ago ma ta da fuska ya k'ara da cewa, "Haba Amaryar Dan Shila Abokina Smile
mana kinsan fa bana son ganin ki cikin damuwa."

Tuni Hameeda ta fara dariya ta na dukan yayan na ta wai a dole ya ce wa mijin ta d'an shila.


Aunty ta nunawa Mama tana, "Ni ko Mama Anya ba soyayya tsakanin Son da Hameeda kuwa?"
Murmushi Mama ta yi tana, "Ai indai Adam da Hameeda ne ni na ka sa gane mu su kawai mu
zubawa sarautar Allah ido."

Aunty ta ce, "Haka ne Amman dai zan yi farinciki in son ya sami Hameeda A matsayin Mata,
barin yadda ta san halin sa shi ma ya san na ta."

Mama ta ce, "Haka ne kam."


Ranar kuwa Hameeda ta k'i tafiya gida Anan ta kwana ban da labaran makaranta ba a bin
ya ke ba wa kanwar ta sa har ma da labarin Nusaiba da dramar da su kai A wajen cin abinci,
ban da dariya ba abin da Hameeda ta ke mussaman in ta tuna gun cin abincin nan.

Karfe 11:00 Hameeda ta ce, "Umm good night yaya Adamu gwanda kai, ku ma kar ka man ta
gobe da sassafe za ka ta shi mu fara karatu."

Adam ya ce, "Ok night sweetie saura ku ma ki zo ki isheni tun A suba."
Dariya kawai Hameeda ta yi ta tafi dakin ta.

Ta na zuwa tai alwala ta yi sallah sai da ta yi karatun QUR'ANI sannan ta yi Addu'ah ta kwanta.

Haka ma Adam domin sun saba haka iyayen su su ka nu na mu su tun su na k'anana.

Washe-gari

Bayan sun yi sallar Asuba duk sun koma barci, Hameeda har ta kwanta ta tashi tuni taje ta tashi
Auta da ya ke yau weekend ne su ka nufi d'akin Adam da ruwan sanyi su aboye.

Su na shiga Auta ta fara mintsinin Adam ta na, " yaya ka tashi safiya ta yi."

Ita ku ma Hameeda na ta watsa ma sa ruwan .

Adam ya na, "Haba Auta ku barni na yi barci na mana dan Allah na gaji fa."

Ya gyara kwanciyar sa kawai ya cigaba da barcin sa.

Hameeda ta fadawa Auta abu a kunne .

Ai ko tuni Auta ta gantsarawa yayan na su cizo a kumatu.


Da ihu Adam ya tashi ya na, "Auta wallahi yau sai na zane ki A gidan nan."

Kan ya ta so Hameeda ta dau Auta sun bar d'akin da gudu.


Adam ma gudu ya ke ya na bin su a baya.

Su na zuwa falo su ka zaune ku sa da Abba.

Abba ya na , "An fara ko?"

Auta ta ce, "Umm ba Yaya ba ne ya ki tashi mun tashe sa, shi ne wai sai ya da ke mu."


Abba ya ce, "Ah to ba abin da zai mu ku, ku zauna anan abin ku."

Ai ko sai ga Adam ya shigo ya na, "Allah yau Auta da Hameeda sai na zane ku a gidan nan."

Abba ya ce, "A'a fa ni na ce su ta so min kai."

"Allah fa Abba wallahi yaran nan sun raina ni ka bari in zane su."

Abba ya ce, "To ku bashi hakuri dan bakuda gaskiya."

Kunnuwansu su ka kama su na "sorry Yaya bazamu sake ba."

Abba ya yi murmushi ya na, "Yauwa yaran kirki."

Adam ya ce, "Umm za ku sa ni ne."

Hameeda ta kalle sa ta ma sa gwalo

"Abba ka ga yarinyar nan har gwalo ta ke min fa?"


Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

��������
����
*WASA DA SO*
��������
����


_{ Ganganci }_


*TRUE LIFE,LOVE STORY.*
_(Labarin Soyayyar Gaske)_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.*
_________________________



*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani*
_(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*



*LOVE MESSAGE*

when you wait for someone for few mintues-its need
for few hours-its trust
for few weeks-its friendship but when you know the person will not come and still wait-its love.

*PAGE*-25

*Sorry for d late wishes br amman duk da haka vazan yi kasa agwiwa ba domin kuwa wannan
shifin na ka ne kai kadai*

Wishing you all the fun and excitement that only birthdays can bring. Happy birthday yaya hayat
admin of Admins,Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login