Showing 3001 words to 6000 words out of 25590 words

Chapter 2 - WASA DA SO BY AISHA MUHAMMED SANI .pdf

25 Jul 2025

2916

su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE
YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA
SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_Let me write my love for you in the sand, so the water can wash it away and I can write it again
and again and again. I love you like crazy._



Ya Mata wata tsawa ,wadda afirgice ta tashi,jikina rawa tayi guda ta na kuka sai mota.

Ya na shigowa ko kallonta bai ba ya figi motar sukabar gidan.

Ba inda suka nufa sai gida Hamida ko ba ri ya ga ma paking ba tai ba ta fita da gudu.

Bai kulata ba sai da ya ga ma paking dinsa sannnan ya shiga gidan,aiko ba kowa afalo hakan
yasa ya hu ce dakinta direct domin yasan ta na chan,da sallamar sa ya shiga .

Hamida ta kwantar da kanta akan gado sautin kuka kawai ke tashi adakin.

Adam ya karasa gareta jiki asanyaye ya zauna agefen gadon,ya yi shiru na yan mintuna sannan
ya ce, "Hamida ki sa ni banda niyar kunta ta miki ga ba daya arayuwata indai ba faranta miki ba
ke kanki kinsan hakan,da ace zakisan zafin da nakeji azuciyata aduk sanda naganki kina zubar
da hawaye da ko wani ya ce ki yi ba za ki yi ba,wallahi bazan iya juran ganin wani na kallonki ba
kuma irin kallon da bai kamata ba,subhanallah bazan jure ba ko ma wa ye wallahi ki gafarceni."

Hamida ta da go tare da kara kurawa yayan nata ido ta ce, "yaya nasan da hakan amman
kasan da ce wa ba abinda ya fi tadamin hankali irin ace Naga bacin ranka,ko da wanine ma
yabatam banji dadi,ba re ace ni! HMM."


Adam ya yi murmushi ta re da fadin, "Haba Hamee tah ni rai na bai baci ba zafin zuciyane
kawai,Oyaa smile kanwar yayanta Amaryar kanina da ban sansa ba."

Hamida ta ce, "Ummm kai kasan wani kani ni muje muyi sallah ka ga har an fito amasallaci."

, "Toh Ta sallah muje."

Dukansu suna dariya kaman basu ba sukaje sukayi sallah tare kuma su ka yi karatun al'qur'ani
sannan sukayi sallar isha tukun aka hadu domin cin abincin dare.

Abba ne ya ce, "Ohh nikam daga gobe gidannan zai dai na dadi fa tun yanzu har nafara missing
ya'ya nah."

Aunty, "Oh wa to mu ka manta damu ta yaranka ka ke ma."

Abba ya yi murmushi Sannan ya ce , "Ke ko kishin ma da ya'yanku za ku yi?"

Mama ta yi karaf ta ce , "Yoo tunda ana nuna mana banbanci ai dole muyi."

Adam ko da Hamida banda dariya ba abinda su ke domin suna son kallon dramar su Abba da
su Mama kaman A Film.

Autace ta fara kuka ta na, "Nikam yaya zan bika please,wallahi bazan iya zama agidannan
ba."ta kara maganar tana bubbuga kafa.

Adam ne ya durkusa gaban kanwar ta sa tare da rikwo hannunta yana, "Haba Yar beautyna
nima fa banson rabuwa dake ko dan surutunki da hanani barcin da kike,toh amman yanzu
kinaso na fasa siya miki irin motar Auntyne?"

Da Sauri Auta ta ce, "Tab Yaya ai wallahi sai ka siyamin tunda dai Abba ya ce wai shi sai na
girma."

Adam ya ce, "Yauwa to kinga sai naje nayi karatun da zan sami aikin da zan siya miki."

Tuni auta ta goge hawayen fuskarta ta re da tashi tana, "Yaya gudnyt gobe ka tashe na rakaka
domin inka siyamin motar nan inba su Abba barasu hau ba sai da su kalla."


Kowa afalon dariya kawai ya ke Abba ko azuciyarsa yana jin dadin sabon da ya'yansa su ka yi.


Alokacin ko wa ya watse aka nufi dakin barci.


Washe gari
Da sassafe Duk yan gidan su ka tashi kasan cewar yau Adam zai tafi birnin kebbi,Hamida kuma
zata koma gida .


Dukansu sun shirya tsaf Har sunyi break sannan suka hadu amota daya domin raka adam
tasha.

Kawai dauriya Adam ya ke amman zuciyarsa zafi ta ke wani sa'in yakanji kaman zata fashe.

Suna zuwa kuwa akasami motar birnin kebi da shirin tashi yanzu.

Urs xayyeesherth

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


����������
*WASA DA SO* ����������

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara
sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah
ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga
al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE
YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA

SHI A TSARI*.


*LOvE MEssEGE*

_Sometimes I think we’ll never see each other, with oceans between us and the skies above us.
But the more I stay in fear of losing you, the more my heart yearns for you. I miss you!_

*PAGE* 6

Adam ya shiga mota ya kasa waiwayo ya kalli Hamida ita ko sai dariya ta ke ta na, "Toh su Yaya
Adam agaida yan matan makaranta banda wasa."

Alokacin motarsu ta tashi sannan su Abba su ka kai Hamida ma gida.


MISSALIN KARFE HUDU

Dai dai Adam ya isa Makarantarsu Dake Birnin Kebbi Tare da Abokinsa Mubarak wanda daman
shi tun jiya ya dawo.

A kofar, Adam na shiga ya hadu da wata tsalleliyar budurwa wadda tunda ga saukarsa amota ta
ke kallonsa ga duk alamu itama yanzu ta sauka.

Da sauri ta karaso garesa tare da fadin, "Am Nusaiba And You?"

Ya yi murmushi tare da fadin, "Ni fa banajin turancin nan ki yimin hausa."

Abun ya matukar ba ta dariya domin tasan ga dukkan alamu wasa ya ke mata ta ce, "Toh ai
nima ban iya ba Amman dai sunana Nusai ba kai fa?"

Oh, "Ni kuma sunana Adam amman inkinso zaki iya kirana da Messi."

Nusaiba ta ce, "Ok sorry fa daga zuwanka na isheka da surutu, bari in barka kaje hostel nima
na tafi anjima ma hadu." Da ganinta kasan irin yan matan nan masu yan gar tsiya.

Adam ya ce, "Ok."

Mubarak ya hango Adam daga nesa ai tuni ya tawo da sauri ya na, "Oyoyo abokina tun tuni kai
na ke jira wallahi,kazo mu tafi dakin mu."


Adam ya ce, "Yess muje na yi wanka dan kasan ni ba irinka bane bazan iya doguwar tafiya

banyi wanka ba."

Mubarak, "To uban yan tsurfa a school din ma ba'arage ba ,toh nidai muje."

Su ka shiga ciki sunata dariya .
Bayan Adam ya yi wanka tare sallah suka ci abinci sannan fa ya fara zuba.

, "Abokina ina fada maka ina shigowa school dinnan na hadu da wata yar baby, gaskiya dole na
dage dan kasan banson raini, dan haka kar mu fita kana wani kulasu fa su raina mu."

Mubarak ya ce, "Toh uban yan karya da gidan talakawa ka fito da wallahi bansan ya zaka yi ba
kai kam komai kafison sa karya aciki, "hhhh ayi dai mu gani kasan ni dan kallo ne, yauwa na
manta fa akwai taro da aka hadawa sababbin dalibai nasanin juna dan haka ka shirya muje."

Tuni Adam ya miki woooo abunnan fa yamin dadi za mu hadu da yarinyar nan kenan.



Adam ya ci kananan kaya da yake daman shi ba gwanin manyan kaya bane .

Sun shirya tsa, aiko su na fita da Mubarak sai ga nusaiba nan.

Adam da saurin sa ya ce, "Ah friend sannunki,kema gun zaki?"

"Eh wallahi." cewar Nusaiba.

suka jera tare su na tafiya abinsu gwanin sha'aawa Mubarak ko ya na kallon ikon Allah, domin
haka su ke tafiya su na fira kamar can dama sun san juna.

Bayan sun isa wajen aka fara hidima kowa sai fitowa ya ke ya na baje kolin basirarsa daga
karshe aka bukaci Nusaiba da ta fito domin ta fadi albarkacin bakinta. Sai ta fito kuwa ta na
tafiya ta na rangwada kamar wacce za ta kare, tun anan aka rufe ta da tafi. Sauran matan da ke
wurin sai kyashi su ke, amma kam ba yadda yan adawa za su yi domin duk gayun da ke wurin
ta tafi da su. Akan step ta hau ta karbi Michael phone, kan ta ce wani abu aka kara rangada ma
ta tafi. Sai ta dan gyara murya ta ce.....

*Oh Pls amsorry mu hadu a shafi na gaba.*


_It's Ur's Xayyeshert_……✍

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

����������
*WASA DA SO* ����������

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara
sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah
ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga
al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE
YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA
SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_I feel very confident that we will make it through. Though we fight a lot I know that we will be
together. -Vernon Straights i love you_

*PAGE* 7

_WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA YAN GRP DINA WASA DA SO FANS TARE DA
YAN GRP DIN KHALESAT HAIDAR INA JIN DADIN CMMTS DINKU_

°°°°°°°°°
"Da farko dai sunana Nusaiba A Muktar an haifeni a Sokoto state, kuma magatana suma yan
Sokoto ne karatu ne ya kawo anan kamar yadda ya kawo ku anan.

Da wannan dama na ke so na bada wayan su shawarwari domin ci gaban karatunmu." A
lokacin da ta kawo nan da zantukanta sai duk 'yan matan da ke wurin su ka dai ihu wai ala dole
sai ta yi turanci. Su kuma gayun da ke wurin su na goya ma ta baya akan ta ci gaba da
maganganunta. Adam kuwa ya na gefe ya na kallon ikon Allah ta yadda ta dawo da yarenta na
Hausa a maimakon nuna kwarewarta na harshen turanci.


Haka dai Nusaiba ta daure ta ci gaba da maganganunta duk da ya ke ba dadin wurin ta ke ji ba.
"Zan bada shawara ne guda uku wayanda na tabbata idan har mu ka yi amfani da su to za mu
kammala karatunmu cikin nasara insha Allahu." Kasancewar bata jin dadin wurin ya sa ta
zayyano su a gurguje ta ce,"da farko dai mu girmama kanmu da kanmu sannan mu girmama
mallamanmu, abu na biyu kuma mu yi karatu sosai kamar cin abincinmu, abu na uku kuma lallai
mu nemi abokin rayuwa nagari wanda zai dora mu akan hanya idan mun sauka. Alhamdulillahi
da wannan na ke son abokaina su gane abinda ya kawo mu anan wassalam." Ta sauko daga
kan Step jikinta a sanyaye, duk da ya ke kowa ya san halin Nusaiba da masifar izzah da kuri ita
yar gidan ma su hali ce da kuma yanga, amma dai yau ba ta nuna hakan ba, hasalima duk ta
karaya jikinta a sanyaye.

Adam bai tsaya aka kirashi ba ta na saukowa daga kan Step din ya hau ya karbi mic, sannan ya
kwala ihu cikin magana tare da cewa Hello, duka jama'ar da ke wurin kowa ya yi tsit ya na
sauraren abinda zai fada. Adam yaro ne mai matukar farin jini a cikin makarantar kuma babban
yaro ne wanda ya san yakamata, haka yan matan da ke wurin su ka hau tafa ma sa shi kuma
sai ya ce,"hold off tafi ba shi ne abinda na ke bukata a wurinku ba hankalinku na ke so ku bani.



_it's Ur's xayyesherth.......✍_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

����������
*WASA DA SO* ����������

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara
sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah
ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga
al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE
YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA
SHI A TSARI*.


*LOvE MEssEGE*

_When I miss you I re-read our old conversations and smile like an idiot._

*PAGE* 8

_*WANNAN PAGE DIN KACOKAN SADAUKARWANE GA YAN GROUP DIN POWA
PATISKUM WRITERS ASSOCIATION INA YINKI IRIN OVERN NAN*_ ❤❤❤


ina son ku gane shi harshen turanci ba shi ne abin burgewa ba, domin idan har turawa ba su
damu da yarenmu ba to mu miye amfanin damuwa da na su yaren. Ina son ku gane muna

koyon turanci ne badaon komai ba sai don idan mun fita kasashen waje inda mu ke haduwa da
wayan da ba sa jin namu yaren, kuma anan kasar tamu idan mun hadu da wani yare wanda
baya jin namu yaren. Babban abin da yakamata mu gane shi ne ta ya ya za mu samu ci gaba a
wannan kasar tamu. Babbar hanyar da zamu ci gaba shi ne hanyoyin da Nusaiba ta lissafo
domin lallai karatunmu shi ne alfaharinmu kuma darajarmu yarenmu, hakika babu dakiki irin
wanda ya raina kansa, idan kuma ka raina asalinka to tabbas ka raina kanka ne. Saboda haka
yaren Hausa shi ne babban yare a gare mu 'ya'yan Hausawa."


Duk jama'ar da ke wurin su ka kara rangada ma sa tafi tare da fadin tabbas Adam abinda ka ke
fada gaskiya ne kuma mun gansu sosai da sosai Allah ya kara basira. Haka dai aka yi taron
wannan yazo ya fadi nashi wannan ya fadi nashi har aka watse.

Akan hanya Adam ta komawa hostel da ya ke wurin nesa ne sai ya hadu da Nusaiba a cikin
motarta kirar Vibe itama za ta je hostel duk da ya ke ita gida ta ke komawa ba'a hostel ta ke
kwana ba.


Nusaiba ta tsaya tare da ce wa, "Adam inba damuwa ku shigo na rage muku hanya ma na."

Adam ya ce, "No kibari kawai." azuciyarsa ko ce wa ya ke kawai na hau motarki araina ni dan ni
banzo da ta wa ba.

Nusaiba ta ce, "please ina so muyi magana ne ,aboki tunda kai bansan sunan ka ba sa baki
mana ku shigo na rage mu ku hanya."


Mubarak ya yi murmushi tare da fadin, "Bakomai Abokina mu shiga mana."
Adam bai so shiga ba dan ba yadda ya iya da Mubarak ya sa ya shiga domin gani ya ke in an
gansa A motar ta raina sa za ayi.

Nusaiba ta budewa Adam kwofa ya zauna a gun mai zaman banza shiko Mubarak ya shiga
baya.

_It's Ur's xayyesherth_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation


����������
*WASA DA SO* ����������

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________


*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.

*Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.


*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara
sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah
ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga
al'umma su amfana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login