Showing 24001 words to 27000 words out of 28842 words

Chapter 9 - BAYAN WATA BOOK ONE BY NARNAH KANWAR SOJA .pdf

20 May 2025

2517

ɓoye cikin almara ,tana rubuta mafarkinta, ƙiyayyar Hajiya Mariya, da muradinta na
ganin wata rana zata fita daga gidan nan cikin daraja.
“Ina mafarkin wata rana zan fita daga nan ba da hawaye ba, sai da murmushi kuma duk wanda
ya raina ni, zai ga matsayi na kuma wanda ya tsare zuciyarsa a gareni, zai gane cewa ba wai
'yar kauye bace, sai dai baiwar Allah da daraja ta ɓoye.”




******************"""""


Abdullahi Khalil Usman wanda da dama ke kira Mr. Abdullahi, shine shugaban babban
kamfanin gado na mahaifinsa wanda aka sani da Usman Holdings International, wanda
hedikwatarsa ke cikin Abuja, amma reshe-reshen sa sun watsu a duk fadin Najeriya da
kasashen waje duk da wannan girman arziki, Abdullahi mutum ne mai natsuwa, mai son zaman
shiru, kuma yana da ɗabi’ar kin yarda da auren dole.
“Ni bana son aure yanzu. Ina jiran yarinyar da zuciyata zata karɓa ba tare da tilas ba,” inji shi
kullum idan mahaifiyarsa Hajiya Binta ta taso masa da lamarin aure.

Tun yana ɗan shekara ashirin da shida, Abdullahi ke yin wani irin mafarki na wata budurwa mai
kamun kai, mai kyan hali, cike da nutsuwa , kullum fuskar yarinyar bata bayyana gaba ɗaya, sai
murmushin ta da kuma yadda take tafiya cikin kwanciyar hankali kamar ba ta san duniya ba.


Yanzu yana da shekara talatin da ɗaya, amma har yanzu bai manta wannan mafarkin ba har ya
kasa yarda da kowacce mace – saboda zuciyarsa tana jiran wannan mafarkiyar da bata
bayyana ba.




Ranar da ya hau jirgin daga Yola zuwa Abuja, yana tsaye yana shan iska da kallon mutane, sai
idonsa ya sauka akan wata yarinya da ke tafiya da Alhaji Saminu – cikin riga da zani, fuskar ta
cike da tsantsar kauyanci da kamun kai. Fuskar yarinyar kamar dai fuskar yarinyar mafarkinsa
ce! amma sai ya girgiza kansa: “A’a, ba zata iya zama ita ba… ai ita kauyaniya ce ko turanci ma bata iya ba.” ya fad’a a ransa,
yana danne mamakin zuciyarsa amma tun daga lokacin, idonsa na bibiyar Halima, duk da cewa
bai san sunanta ba, kuma bai ce da ita uffan ba. Sai dai a zuciyarsa… ya kamu da wata
ƙayatarwa mai cike da ban mamaki.



Yanzu da suka sauka Abuja, Abdullahi ya koma rayuwarsa, amma zuciyarsa bata daina tunanin
Halima ba duk wata yarinya da ya gani, sai ya kwatanta ta da ita, amma babu mai dacewa shi
kuwa Alhaji Saminu, yana cikin shirye-shiryen cin gajiyar auren Halima – yana kula da ita da
nisa, amma bata san yaushe zai dawo ba Halima kuwa, tana fama da azabar rayuwa a gidan
kishiyoyi, tana ta mafarkin sauyi da ƙauna, amma bata san cewar zuciyar wani saurayi mai
daraja tana neman nata ba


Abuja cibiyar kasuwanci da masarauta ta zamani wannan karon, babban taro ne da ya haɗa
manyan kamfanoni, 'yan kasuwa, da shugabannin kasashen duniya Alhaji Saminu, wanda ya
kafa taron kasuwanci, yana cikin wani kwararren d'akin taro a babban otel na Abuja, wanda ke
dauke da kyan gani da yanayi mai cike da alfarma duk duniya na kallon wannan taro da alamar
samun ci gaba ga kasuwancin Najeriya manya da ƙananan kamfanoni sun hada kai domin
samun nasara da bunkasa tattalin arzikin kasar.

A cikin wannan dakin, Abdullahi ya tsaya cikin cikakken kwalliya jikin sa yana ɗauke da rigar
alfarma mai kyau, wanda ta haɗa da jallabiyah mai launin zinariya da farar rawani fuskar sa
tana cike da kyan gani da kwarjini. Duk wanda ya kalli shi zai fahimci cewa yana ɗan kasuwa ne
mai daraja, wanda ke dakin taro ba domin wasa ba a cikin zuciyar sa akwai fata na samun
nasara mai girma, amma akwai wata yarinya da ta mamaye zuciyar sa – Halima.


Abdullahi, wanda iyayensa ke son shi ya auri wata mai matsayi daga cikin iyalai masu arziki,
yana neman neman soyayya ta gaskiya. bai taɓa ganin wannan soyayya ba a cikin kowanne
daga cikin yarinyoyin da iyayensa suka so masa amma a cikin zuciyar sa yana ɗokin haduwa
da Halima, wanda ya ga a cikin mafarkinsa a jirgin sama lokacin da suka haɗu tabbas yanzu
zuciyarsa yafi karkata ga cewa ya haɗu da mafarkin sa a rashin lura irin tasa .






A yayin da aka gudanar da taron, Halima tana cikin wani dakin hotel ɗin da Alhaji Saminu ya
shirya mata wannan d'akin yana ɗauke da kayan alfarma da kyakkyawar kwalliya – gado mai
kyau da tsayayyen fata na zinariya. Halima ta zauna cikin dakin, tana kallon kayan da aka
tanadar mata, amma zuciyar ta cike take da tunani wataƙila, wani abu ya faru da ta rasa kwarin
gwiwarta, ko kuwa har yanzu tana jin cewa wannan ba shi ne rayuwar da ta yi mafarki da ita ba.






Alhaji Saminu ba ya kula da wannan sha'awar da ta ke nunawa a saboda haka, yana son ta
zama abokiyar rayuwarsa, amma yana ɗaukar ta a matsayin daya daga cikin matan da zai kula
da ita daga ɓangaren kyakkyawar tarbiyya da kuma halayen aure.






A cikin taron kasuwancin, Abdullahi na cikin dakin taro, yana kallon yadda ake gudanar da
al'amuran. A zuciyar sa, yana jin cewa ba zai taɓa samun zaman lafiya ba sai ya sadu da
Halima. ya tuna da fuskarta a cikin jirgin sama, da yadda zuciyarsa ta shiga cikin hayaniya
saboda soyayyar da ta shige masa cikin zuciya ,yana ganin ta a cikin wannan dakin, amma ba

zai iya neman ta yanzu ba. wannan tsari na al’amura yana nuna masa cewa soyayya ba ta da
sauki, kuma yana bukatar lokaci don samun damar yin matakin da ya dace.
Tsawon kwanaki biyu ana wanan gagarumin meeting nin inda ake shirye shirye rufe taron a
kwana na ukku Alhaji saminu dalilin ɗauko Halima daga gida bayan kumawae sa gida cikin
gaggawar kirar taron da suke gabatar wa yanzu cikin bazata ya iso gidan ganin halin da Halimar
ke ciki ne ya bashi mamaki kwarai da gaske wannan dalilin yasa ya ɗauko ta a tare dashi ....





RANAR TARON ƘARSHE






Ɗakin taron babban hotel ɗin na Abuja ya cika da hasken chandelier mai sheƙi kamar taurari
fata-fatan zinariya da tabarmar da ta shimfiɗu kasan tiles ɗin falo suna haskakawa da salo irin
na manyan duniya.


An shimfiɗa dogon babban tebur na gilashi, aka jera kujeru masu launin royal blue da zinariya
agefen teburin akwai lambun furanni masu ƙamshi, da sauran kayan kyauta na kamfanoni.
mutane masu siriri da sirarrun suits sun cika gurin: 'yan kasuwa, manyan ‘yan banki, masu
hannun jari, da CEOs daga kamfanoni daban-daban.


Abdullahi, sanye da suit mai launin baki da farin riga da blue tie, ya zauna a tsakiyar babban
kujerarsa girman sa da kamewar sa ya ja hankalin kowa — da kallo daya zaka san ba na yau
aka haife shi ba fuskar sa ba dariya, ba kuma fushi tsaka-tsakin kamewa da matsayi
Hausawa sukace yaro da kuɗi abokin tafiyar manya


Har lokacin da Alhaji Saminu ya shigo cikin taron, aka mika masa gaisuwa irin ta manyan masu
kuɗi ya zauna da kamun kai, yana ta gyaran hula da hancinsa lokaci-lokaci, alamar rashin jin
daɗin zama saboda tunanin a maryar sa , lolz


A takaice an yi taron a cike da muhimman magana: aka rattaba hannu akan sabon kwangilar
gine-gine da haɗin gwiwa bayan an gama taron, mutane suka shiga gefe suna ta yin hotuna,

musabaha da exchange card.




A gefe kuma, Halima wacce aka bar a dakin hotel na VIP floor, tana kwance tana ƙoƙarin danne
kukan kewar gida da tsoron birni.
tana sanye da kayan gida masu kyau amma ƙauyanci ke bayyana sosai a fuskarta Fuskarta
bata da kwalliya, sai ruwan hawayen da ta share, tana kallon window tana ganin duhun dare
yana sauka kan manyan titunan Abuja.


bayan taron, Alhaji Saminu cikin gaggawa ya amsa kira daga gida an kira shi da sauri, wani
ɗan matsala ce ta dangi da gaggawa ya fice daga hotel ɗin... amma sai ya manta da Halima a
cikin ɗakin hotel ɗin!


Halima tana jiran shigowar sa, tana jin tsoron shiru da tunanin abubuwa daban daban
Halima ta jawo ƙofar ɗakin a hankali, tana hango hanyoyi masu haske da furen bango. tana
sanye da doguwar riga mai launin shudi mai launin ruwan sama, wanda ke fita da kyau akan
fara fatarta, tana tafe da ɗan ƙaramar gyale mai launin milk da ya ɗaura mata fuskarta kamar an
kare ‘yar Sarki.

Tsoron da ya mamaye ta ya hana ta saka takalma — tana tafiya a siraran ƙafarta, tana kallon
dukkan gefuna da tausasan idonta.
tana jin kowane sauti kamar wani abu zai fito daga cikin duhun corridors ɗin hotel ɗin.
ta isa ga wani ɓangare na babban hotel ɗin gaban lift — lokacin da abinda ta gani ya firgita ta.


Da gudu ta nufi cikin tsoro tana neman mafaka — gaban ta a bude — tayi karo da mutum mai
tsayi, sanye da baƙin suit mai sheƙi, riga fara ta ciki, wanda ba kowa bane illa Abdullahi.


Shi kuma yana tsaye yana danna wayarsa, iska mai sanyin ƙanshi na air conditioner yana
kadawa a gashinsa mai santsi.zuciyarsa tana bugawa da sauri kamar ana gaggauta dokin
sarauta, Halima cikin firgici ta fado jikin Abdullahi — hannuwanta suka kama rigarsa, tana fitar
da ƙaramar ajiyar zuciya, idanun su suka haɗu ,wani zafi mai daɗi ya ratsa tsakanin su, wani
sirrin shiru mai nauyi ya cika sararin tsakanin su.
wayar sa ta tsaya hannu, zuciyarsa ta kasa ci gaba da bugawa daidai Idonta ya cika da tsoro,
nashi kuma da wani irin salo na jin "na gan ki amma ban gane ki ba".

A hankali Abdullahi ya daidaita kansa, yana ƙoƙarin saukewa Halima daga jikinsa.
Ya sauke ta a hankali kamar kar ya tsoratata, sai ya ɗauke numfashi ya runtse ido tsakanin su
shiru ne mai nauyi, kamar ana iya jin karar fitar numfashin juna.
Abdullahi ya tsaya wuri guda, idanuwansa suna zurfafa cikin kyawawan idon Halima waɗanda
ke cike da tsoro da rashin tabbas cikin kin sauti mai kaɗan amma cike da girma da tsari, anji
muryar Receptionist “Please, Hajiya Halima...! Reception is calling you, Hajiya Halima!”






Muryar ya sake maimaitawa daga speaker din da ke jikin bango, kamar an daga karar.
Halima ta ji sunanta a sarari, kamar daga sama, kamar ruwa an zuba mata ,wani sabon firgici
ne ya sake ratsa ta kamar numfashin ta zai tsaya a firgice, ta sake matse jikinta da ƙarfi a cikin
ƙirjin Abdullahi, tana neman mafaka daga kowa da komai ,Abdullahi kuwa ya saki wayarsa ta
faɗi ƙasa ya kasa motsi. Numfashin sa ya tsaya cak
gaba ɗaya jikinsa ya birkice kamar karamin yaro da aka tsorata masa da aljani.


A hankali yana jin kamshin furen Halima — kamshin shinkafar ɗanye da ƙamshin turaren wuta
idonsa ya lumshe, zuciyarsa na harbawa da irin bugun da bai taɓa ji ba a rayuwarsa.
ya buɗe idonsa, ya kura mata ido, yana kallo cikin fuskarta mai tsantsar kyau da rashin fenti
fatar ta laushi tamkar auduga, launin idonta kamar kalar ruwa mai tsafta


Bakin Halima ya motsa kaɗan, tamkar zata ce wani abu, amma ta kasa.
Abdullahi ya bi bakin nata da kallon da ya kashe masa nutsuwa — laɓɓanta sun yi ja kamar
sabuwar ɗan itacen ɗinya, santsi da kauri irin na 'yar asali.


Abdullahi ya shige duhu da hasken idonta.
wani abu mai daɗi da tsoro na haɗuwa ya cika shi abu da bai taɓa jin sa ba tun daga
haihuwarsa " tabbas ittace mafarki na ".
Abdullahi ya kasa inda zai sa kansa.
Zuciyarsa tmkar an kunna ganguna.
wani yanki na zuciyarsa na ba shi shawarar ta hanyar hankali: "ka sauke ta, ka da ka zalunce
ta!"
Amma wani sashe kuma, na tunani mai zurfi da sha'awar kasancewa tare da ita a dau dai
wannan lokacin yana fisgarsa tamkar walkiya:

Wani numfashi mai nauyi ya saki — yana jin tamkar zuciyarsa zata fashe da nauyin soyayya da
radadin rashin tabbas.
idanunsa suka kai ga fuskarta.


Daidai lokacin da yake shirin sauke wata ƙaramar ajiyar zuciya, sai suka ji motsi da sautin
takalmi mai nauyi,
Alhaji Saminu ne ya shiga jikin sa akwai alamar gajiya da fushi, yana janye zuciyarsa da sauri
daga tunanin da take shirin narke shi.


Alhaji Saminu ya tsaya cak, yana kallon yadda Halima ke manne da wani saurayi, shi kuma
saurayin kamar an soka masa gashin zuma a ƙirji fuskarsa ya cika da shakku da mamaki.
Yayi wani takun ɗan girma da iko, ya nufo su.


Abdullahi ya gano hakan cikin kwana na biyu na idon sa ,ya ja hannun Halima da sauri, cikin
ladabi da nutsuwa, suka tafi daga wurin.


Halima kuwa, tana kallon Abdullahi tana kuka mai sanyi, hawaye na bin fuskarta tamkar silin
ƙwai da ya fashe a hankali.
bata so a raba su bata so a bar wannan ɗan lokaci ya wuce ba.


Har lokacin da suka rabu, Halima na ta juyawa tana kallonsa cikin raɗaɗin zuciya — kamar tana
jin cewa ba za su ƙara saduwa ba, tana maimaita sunan sa a zuciyar ta da jaddada cewa
tabbas shine a mafarkin ta ,
shi kuma Abdullahi, da yatsun sa guda huɗu ya shafi labbansa a hankali yana jin ɗumin
halittarta har yanzu a jikin sa, yana binta da kallo tamkar yana so ya hango sirrin da bai
bayyana ba.


Duniya ta yi wa zuciyoyinsu nauyi
wani sanyi da rashin lafiya na musamman ya mamaye Abdullahi, zuciyarsa na fuskantar wani

sabon yanayi da bai saba da shi ba.




Halima ta kasa daure hawaye tana cikin ɗa
Abdullahi ya tsaya cak yana kallonta, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, amma ya tilasta kansa ya
sake ta ta tafi da Alhaji Saminu.
aguje zuciya, yana ji tamkar an sare wani ɓangare na ruhinsa.
yana kallon bayanta har ta ɓace a cikin motar , ya runtse idanu cike da damuwa, numfashi mai
nauyi ya suɓuce daga bakinsa.








Da zarar Alhaji Saminu ya dawo, ya zube a babban kujerar falo yana huci.
wani irin kishi ne da fushi ya turnuƙa masa zuciya har yana jin idanuwan sa na sauya launi
Hajiya Nafisa da sauran matansa suka taru suna kallon sa cikin mamaki da tausayi, amma basu
isa su tambaye shi komai ba.








Ya ɗauki kofin shayi dake gabansa, ya buga da ƙarfi a ƙasa, kofin ya tarwatse.
yara suka firfito daga ɗakunan su suna kallon sa cikin tsoro
Halima kuwa, tana zaune a bayan kofa , tana kokarin hana hawaye kwarara daga idanuwan ta
tana jin tamkar wata sabuwar ƙaddara ce ke shirin saukar mata.
a wannan daren, gidan ya cika da nauyin shiru da hayaniyar zuciyoyi shiru mai ɗauke da kishi,
da ƙyalle-ƙyallen wani mugun fushi da za a sake fallasa a kan Halima…

https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y


BAYAN WATA
AFTER THE MOON


BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA




ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION

SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star






Page 21 / 22






Bayan Shekaru Biyu




Tunda ranar da suka rabu a babban ɗakin taron hotel ɗin Abuja, Halima da Abdullahi basu ƙara
ganin juna ba. kamar dai wata fata da iska ta ɗauka ta ɓoye a doron ƙasa, haka soyayyar da
suka ambato da shiru a idanuwansu ta ɓuya cikin zuciyarsu duk da lokaci ya shude, rana ta fito
ta fadi sau dubbai, a zuciyarsu har yanzu tamkar jiya aka faru.

Abdullahi, da zarar ya koma gida, ya shiga tashin hankali mai tsanani mafarkin Halima, kallo
daya da ya yi mata, da sautin murya da numfashinta, suka mamaye dukkan tunaninsa duk da
irin dattijon haiba da ƙwazo da yake da shi, ya zama tamkar yaro a duniyar soyayya. ya yi iya
ƙoƙarinsa ya guje mata, ya ɓoye a cikin aikin sa da tafiyar kasuwanci, amma zuciyarsa ta ƙi
amincewa da sabuwar rayuwa har dai iyayensa suka matsa, suka zaɓa masa matar aure daga
cikin manyan iyalan su, suka lallaɓa zuciyarsa da hujjar cewa "ba a dukan soyayya ake rayuwa
ba."


Da damuwa da karyewar zuciya, Abdullahi ya karɓi zabin iyayensa amma a zuciyarsa ya san:
soyayya ta gaskiya daya tal ce kuma Halima ce yayi aure a matsayin ɗan biyayya, ba a
matsayin ɗan farin ciki , bayan ya tabbatar da cewa Halima mata ce a gidan Alhaji Saminu.

A bangaren Halima kuwa, rayuwarta da Alhaji Saminu ta fara dusashewa da kwanciyar aure.
Alhaji Saminu bai sake kallonta da idon da ya saba da shi ba tun ranar da ya ga yadda ta
rungume wani saurayi a hotel kullum yana ganin tamkar ta kai girma da zata saki jiki da wani
ko da kuwa ba laifinta bane, ko da kuwa ransa ya tabbatar cewa tsoro da ruɗani ne suka jefa ta.

Auren Halima ya koma tamkar ɗakin sarauta mai cike da shiru da fargaba matansa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login