Showing 12001 words to 15000 words out of 28842 words
Sojojin sun yi jinkiri, amma daga bisani sun buga ƙofar, sai mai maganin ta fito bayan ta tambayi
wasu tambayoyi.
ta saba da mutane da ke kawo marasa lafiya zuwa gonarta a dare, don haka ba sabon abu ba
ne a gare ta.
"Prince Tarhim shin ka tabbata da wannan? Mahaifinka sarki yana iya rashin jin daɗi da hakan, "
mai maganin ta ce yayin da take duban Rahila
Ta taba ganinta a lokacin da Prince ya jagoranci ta cikin sarautar su cikin ƙafa, kuma ta fara
mamakin dalilin da yasa Prince ke ceton ta yanzu.
"Ni ne zan damu da hakan ke ceto rayuwarta kawai." Prince ya ƙi jin damuwarta.
"Zai yi Prince guba ta ratsa jikin ta gaba ɗaya." mai maganin ta ce "za ki iya ƙoƙarin, taimaka
mata." ya matsa, mai maganin ta fara maganin sarauniya Rahila nan take.
"idan Atishawa tayi bayan ta sha warin wannan maganin da zan kawo, to tabbas za ta tsira,
amma idan ba ta yi ba, to ina baƙin ciki, babu abin da zan iya yi, ya Prince" mai maganin ta ce.
"To, sai ke ci gaba." yace ya amince.
Sojojin sun fara magana cikin husɓa suna kallon wannan abin da ke faruwa.
Prince ya koya musu cewa ba su da jin kai ga abokan gaba, kuma yanzu yana aikata abin da ya
ke gargadi akai mai maganin ta tafi cikin ƙaramin gida na ta sannan ta dawo da wani haɗin
ganyayyaki a cikin ƙaramin kwararan kwano.
da ta kawo warin kusa da hanci sarauniya Rahila, ta atisaye sau da dama amma idanuwanta
sun kasance rufe.
"Yarinyar tana da ƙarfin zuciya." mai maganin tsohuwa ta ce, tana girgiza kai kamar tana gano
wani sabon abu.
Gaskiya ta gano wani abu sabo saboda babu wanda ya taɓa samun damar atisaya bayan sun
sha wannan maganin a irin wannan yanayi.
Ba kawai mai maganin ba ce, amma tana da baiwar ganin gaba, kuma ta iya gano cewa matar
da take gaban ta ba ta cikin kowane irin yanayi na al'ada ba.
"Ya Prince za ka iya komawa gida yanzu, zan kula da ita. zai yi kyau." mai maganin ta tabbatar
maii
Ya yi tunanin dalilin da yasa har yanzu tana cikin wannan yanayi duk da atisayar, amma mai
maganin ta tabbatar masa cewa komai zai tafi daidai kuma ya yarda da ita.
Matar tsohuwa ta kasance mai taimako sosai ga mutanen Zuma, har ta kasance daya daga
cikin masu maganin da suka kula da mahaifinsa, don haka me zai hana?
"Ba za ki taɓa faɗa wa kowa ba, har ma mahaifina, abin da ya faru a daren nan. sanan inason
ke ɓoye ta zuwa lokacin da zan dawo bayan tafiya tafiya ta ," ya gargadi sojojin sa yayin da
suka tafi gida sojojin sun amince da cewa ba za su ce komai ba ga kowa, amma ba abu mai
ɗorewa ne ɓoyewa ba. da Prince Tarhim ya dawo gida, wasu tambayoyi sun ci gaba da gudu a
cikin zuciyarsa.
me yasa ya ceci sarauniya Rahila kuma me zai faɗa wa mahaifinsa? Wane tabbaci yana da
cewa sarauniya ba za ta kashe shi ba idan ta warke?......
BAYAN WANI LOKACI
Rana na shirin faɗuwa lokacin da Prince Tarhim ya dawo fadar fuskar sa cike da shakku da
ɓoyayyen tausayi yana sane da cewa idan aka gano cewa ya ceci Rahila, matsayinsa na ɗa ga
sarki Mujse zai shiga haɗari, amma zuciyarsa ta yi shiru a kan komai – ya fi yarda da abin da
yake ji fiye da hukunci ko hukuma.
A ɓangaren mahaifinsa, Sarki Mujse ana ta cigiyar ɗansa. hana mamakin dalilin da yasa bai
dawo da wuri ba, amma yana zargin akwai wani abu da ɗan nasa ke ɓoye masa.
A cikin wani ƙaramin ɗaki a ƙasan ƙaton gida mai dakuna ashirin da huɗu, tsohuwar mai magani
ta shimfiɗa Rahila akan shimfiɗa mai ƙyalli da ɗan kamshi na turare, tana jin jikin nata yana
murmurewa, amma zuciyarta ba ta fahimtar inda take ba.
“Ki kwanta, ki huta. rayuwa tana juyawa,” in ji mai magani cikin murya mai laushi kamar ta uwa.
Prince Tarhim, ɗan sarki Mujse , ya dawo daga tafiyarsa ta tsawon wata uku a ƙasar Habasha
inda ya je neman dabarun mulki da ilimin soji. Kyakkyawan saurayi ne, mai hikima da nutsuwa,
amma ba ya shiga cikin al'amuran soyayya ko fadace-fadace na fada.
Da isowarsa, ya tarar da wata ƙatuwar shiru a fada an ɓoye masa komai, amma ba don haka
ba sai da hankalinsa ya kai ga jin cewa akwai wani abu mai ɓoye a gidan sarki.
A daren da ya dawo, ya shaida ganin wani bawa yana shiga ɗakin sirri da kwanon abinci. yayi
mamaki, domin wannan ɗakin ba a yawan amfani da shi sai da wani sirri mai girma.
"Waye a ɗakin?" ya tambayi bawansa.
“mai martaba ne ya hana kowa magana akai, ranka ya daɗe,” bawan ya ce da kansa yana rawa
Tarhim ya gyara tsayuwarsa, ya ce cikin natsuwa: “Na isa in sani. gobe da asuba, zan je kaina.”
Washegari da safe, Prince Tarhim ya leƙa ɗakin sirri. kafin ya buɗe, ya tsaya yana sauraron
wani motsi.
daga ciki, ya ji murya mai rauni tana karanta addu’a cikin sanyin murya.
ya bude ƙofar da hankali... idanuwansa suka sauka a kan Rahila, wacce ta zauna cikin tabarma,
tana daure da farin zani, gashinta ya bazu kan kafadarta.
Lokaci ya tsaya.
Rahila ta dago ido lkacin da ta kalli Tarhim, zuciyarta ta ɗan tsinke – ba domin tsoro ba, amma
domin tunanin irrin halarci da ya mata na ceto rayuwar ta duk taye sanyi tasha tambaya kanta
cewa me yasa har yanzu bai dawo garita ba har sarki Mujse ya gano inda take ya rufe ta yana
azabtar da ita bisa laifin mahaifinnta duk gaba da faɗa da take tunkaho dashi tun da Prince
Tarhim ya ceto ranta ta rasa dalilin faɗan da zataye akansa tabbas tana da. burin kashe su
dukkan su to amma akan wani dalili tabbas mahaifin ta mugun sarki ne akan bayin sa ya aikata
zunubi daban daban amman hakan ba wai ya na nufin a ɗauke fansa akan ta ba ita ma bawai
tayi ta faɗa har tsawon rayuwar ta ba Amman rashin ganin Prince Tarhim ya tabbatar mata da
tazama losser !..
Bai ce mata komai ba ya juya zuwa fada kai tsaye domin ganawar sa. da mahaifinsa Sarki
Mujse ya tsaya gaban sa da ƙarfi da girmamawa " Ya kai baba na nasan rashin ɗa akwai
cutarwa musamman idan ya kasance maƙiyanka ne sukaye galaba akanka" yakai Baba na
Sarki Numan mutum ne azzalumi da duniyar mu ta sanshi akan mulkin sa baya barin kowa cikin
sallama a haka muka samu nasarar shiga har fadar sa mukaye galaba akan sa shin Baba
kasan dalili !?
Saboda karshen zalunci sa a hannun mu yake kuma karshen mulkin sa ya ƙare a dalilin mu
mun raunata sa mun kashe sa har abada bazai dawo ba mun ɗauke fansar kashe mana namu
da yayi ,to shine me laifin me yasa muma yanzu muka dawo azzalumai irinsa ka tuna mulkin da
kakiye cikin aminci da adalci ya za'a yi mu azabtar da Rahila bisa laifin uban ta ?, shin ta kashe mu ko ta dauke fansa ko ta cutar damu a'a Baba to me yasa ka rufe ta kake
azabtar da ita tsawon wanan lokacin "?.
Rungumar juna sukaye nan Sarki ya share hawayen sa da cewa " tabbas na aika ta kuskure
mai girma na azabtar da wanda bashi da laifi kuma nasan cewa soyayya mai girma ce a
zuciya ka daga lokacin da kaganta shiyasa na fara gaba da ita don inason ka kasance da Afra
matsayin mijin ta Amman nayi laife ka gafarta min yaro na ka zaɓi muradin ka a rayuwar nan
sanan sanyi murabus zaka kuma kan sarauta nan da wata ukku za'a yi wanan bukin ...
BAYAN WATA UKKU
Jama’a suka ɗaga kai cikin mamaki.
Dukka yankunan sun taro an tabbatar da Prince Tarhim a matsayin sarautar sa
“Ban tursasa masa ba, ya aikata haka bisa adalci da tausayi kuma yanzu na yarda da zaɓinsa.
Idan zuciyarsa ta karɓi Rahila, to hakan na nufin akwai wani ƙuduri na sama.”
Sanan Princeces Rahilat ta dawo daga muƙamin ta na asali yankunan mu na ƙarƙashin ta
sarauta ɗaya ne kuma itace asalin jinin yankin Buga Afrika
Rahila ta ci gaba da zama ginshiƙi a masarauta, yayin da ake yawan kawo mata mata da yara
don karɓar yaƙi da shawara ta zama cikakkiyar Princess nata a inda ta rungume jarumin ta
Tarhim domin a duniya idan akwai wanda take muradun to mijin ta ne shine asalin jarumin da
take buƙatar kasance wa dashi tsawon rayuwar ta......
---
BACK TO STORY
BAYAN WATA
AJIYAR ZUCIYA
Ajiyar zuciya mai nauyi Ihsan ta sauke, yayin da ta buɗe idonta a hankali, idon ta kai ga duk
sansanin da suka taru a kusa da wutar da suke zaune, idanun mutane sun cika da kewa, da
kuma ƙaunar jin ci gaban labarin da ta kawo musu suna kallonta da nutsuwa, kamar sun manta
da gajiyar hanya, yunwa da ɓacin rai tayi shiru na ɗan lokaci, sannan ta sake numfasa.
“Wannan shi ne labarin Princess Rahilat,” ta faɗa cikin natsuwa. “Ina fatan ya ɗan ɗauke muku
kewa a cikin wannan mawuyacin yanayi.”
duk suka jinjina kai sai Maryam ta ɗaga hannu cikin annashuwa.
“A gaskiya labarin ya kayatar, Ihsan. Amma ina da tambaya,” ta ce tana kallon ta kai tsaye.
“Meyasa kike mana labari da Hausa da Turanci a haɗe?”
Ihsan ta murmusa, ta gyara zama kafin ta amsa.
“Hakika tambayar ki ta da muhimmanci Maryam domin shekaru fiye da dubu biyu da suka wuce,
kafin turawa su shigo nahiyarmu, sukan ɗauki baƙaƙen fata tamkar bayi ne sun raina mu, sun
mulke mu , amma akwai wani sarki mai suna Numan, wanda ya ƙwato yanki biyar daga hannun
turawa, ya mayar da su 'yan ƙasa masu cikakken 'yanci.”
Ta dan yi shiru, tana kallon yadda idanu suka cika da sha'awa.
“Shi ya sa ya zama sarki na musamman a zamaninsa duk da kuwa mahaifin Rahilat azzalumi
ne, amma saboda bajintarsa da yaki da turawa, aka ba diyarsa Rahilat sarauta – don ta ci gaba
da kare mutuncin mutane kamar ku da ni. Wannan ne dalilin da ya sa nake haɗa Turanci da
Hausa – domin har yanzu muna da ragowar tasirin turawan, amma da karatun irin wannan ne
za mu dawo da mutuncinmu da fahimtar tarihinmu.”
Hannu suka sa, suka rungume ta duka daga gefe kuma Yazid ya ce da dariya:
“Wallahi, Ihsan, wannan tafiya tazo da darussa labarin Rahilat ya ɗaga min zuciya!”
John ya ɗora: “It’s like traveling into history and coming back with strength.”
Ado ya jinjina kai yana murmushi, “toh yanzu fa dai na tabbata, Ihsan ke ce jigo a cikin wannan
tafiya, bari mu ci gaba da tafiya gobe, amma yau... yau dare ne na tunani.”
Suka kalli juna da murmushi, suka miƙe suna shirin kwana.
Daga can gefen zuciyar Ihsan, sai ta ɗan lumshe ido tana tunani:
"Bayan wata... akwai haske kuma wannan shi ne farkon komai."
continued by narnah ƙanwar soja ✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT
BAYAN WATA
AFTER THE MOON
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star
Page 13/ 14
04 / 05 / 2025
مسب الله نمحرلا ميحرلا
مهللا لص ىلع دمحم ملسو
Maryam ta shafa gumi a goshinta, hannunta na rawa sai yanzu zafin jikin da ya ɗauke ta tun
safe ya fara raguwa duk da haka, Idanunta sun ƙi buɗewa sosai, sai ihun zuciya da tafasar
hawayen da take riƙe.
"Ihsan..." ta kira da rauni, "zan iya tafiya."
Ihsan ta rungume ta, hawaye na gangarowa daga idanunta. “kin ƙarfafa zuciyata fiye da yadda
na zata,” ta ce cikin sanyi
Su Yazid, John da Ado sun zuba ido, zuciyoyinsu cike da yanke shawara basu da ƙarfi sosai,
amma lokaci yana guje musu.
“Yanzu ko ba yanzu ba ne idan yanzu muka tsaya nan wata rana, za a cafke mu.” Yazid ya ce
da ƙarfi, yana gyara jakar sa a bayansa.
sukai shiru har sai da aka ji murya kamar ƙarar iska daga can nesa sai suka lumshe ido, suka
lumshe zuciya.
Su biyar suka tattara kayan su da ƙarancin haske suka ratsa cikin duhu, gaban su cike da
fargaba, amma babu wanda ya waigo baya,
Gabar boda na ƙasar Libiya ba kasafai ake iya shige ta da sauƙi ba. Rana ba ta faɗuwa sosai a
hamada. Gashi da ke fesowa daga ƙasa kamar harshen wuta, yana fitar da zafi da ƙamshi irin
na ƙasa mai mutuwa babu bishiya, babu ruwa, sai yashi mai girma kamar kogon wuta.
Tsakanin dare da kwana biyu, sun ratsa titin ƙasa da ƙafa, su na bin jagorar wani tsoho wanda
suka biya sauka-ka-tafi tsohon yana da hannu biyu kawai, amma gwaninta da sanin hanya sun
fi soja da komfuta.
“Yanzu nan,” ya ce da ƙasƙantar murya yayin da suka isa ƙaramin rami da aka lulluɓe da
dausayi. “Nan ne na ƙarshe kafin ku tsallaka Libiya. bayan nan, ba ruwa, babu tsaro kawai da
zuciyar ku kuke tafiya.”
“Shikenan,” Yazid ya ce, yana gyara rigarsa. “za mu fuskanta.”
Maryam ta kama hannun Ihsan. “In muka tsallaka, to Allah ya bamu mafita.”
John ya lumshe ido. “I’ve never seen darkness this wide... but I feel hope.”
Suka shiga cikin hamadar da babu ƙyalli, suna tafiya suna shan iska mai zafi kamar wuta tana
hura musu cikin hanci, cikin dare, rana tana walƙiya, ba saboda haske ba – sai saboda yashi
yana motsi kamar ruwan teku.
Ado ya ce da jinjina kai, “wannan garin ba na mutane bane...”
“amma mu fa mutane ne da mafarki,” Ihsan ta ce, murya kamar zuma “mu ma muna da hakkin
tsira".
Zuwa wannan lokaci, tafiyarsu daga bodar Libiya ta ɗauki kwanaki, daga na farko zuwa na biyu,
ƙarfinsu yana ragewa. Na uku sun fara kwana da cikinsu babu ruwa, babu abinci rana ta huɗu,
numfashinsu ya zama kamar na dabbobi, idanu sun ɗebe, fata ta bushe ta fara fashewa.
Hamadar Sahara ba fili bane na yashi kawai wani lokaci dutse ke cikinta, wani lokaci gami da
koguna da suka bushe shekaru da suka wuce amma duk inda suka kalli yanzu, sun haɗu da
komai: rairayi masu santsi, ƙasa mai zafi, iska mai ƙarfi da tsintsiya da ke ɗagawa daga ƙasa
har sama kamar baƙin hayaki.
Maryam ta fara jan ƙafarta a jikin yashi. takalminta ya dade da karyewa, yanzu ƙafarta bare –
jajaye sun yi, cike da toka, ƙyalli daga rana. “Ihsan... ruwa... just one sip,” ta furta kamar
mafarki.
Ihsan na bin ta da ido, kanta yana juyawa. Idanunta sun canza launi, sun zama kamar ƙwai, ba
su da ƙyalli gashinta ya manne da gumi da ƙura, har ta daina jin sauyin iska. “Ba ruwa, ba
komai amma ki tsaya Maryam... ki tsaya.”
Yazid yana gaba, yana rarrafe, yana fitar da numfashi kamar wanda aka sakar daga ƙarƙashin
ruwa. John yana masa baya, amma yazo ƙasa. “I can’t feel my tongue...” ya ce da harshen da
ya fara murɗewa.
Ado, wanda shi ke riƙe da jakar kowa, ya durƙusa. “I’m seeing mirages I saw my mother – she
was standing in water, calling me.”
Yashi ke rawa, rana ke ƙuna. Iska ta taso – iska mai nauyi, ƙamshi kamar zafi duka suka
durƙusa, suka lulluɓe kansu da tsintsiya da kaya, amma iska ta kwashe su kamar hayakin
gobara sun yi ta birgima kamar jakunkuna, har aka jefar da su zuwa wani ƙaramar rami – wani
tsibiri a cikin sahara, tamkar tafkin dutse da ya bayyana daga ƙasa, cikin haka suka faɗi su ka
suma.
Wani lokaci daga baya...
Cikin ɓangararren inuwa da aka samu daga wata harsashen dutse, suka farka jikinsu a sanyi,
amma cikin yashi babu ganye, babu ruwa, babu abinci. sai ga jikinsu ya fara nuna alamar
rushewa – la'bbansu sun fashe, hancinsu ya bushe, idanunsu ba sa kallon juna, fatar hannu da
ƙafa sun fara murɗewa, ta rikiɗe tamkar kaho
“Zan mutu,” John ya furta, yana kallon sama, “Ba ruwa na sha fitsari na jiya ba zai isheni yau
ba.”
Yazid ya kalli jikin sa, ya ji kamar naman jikinsa yana motsi. ya taɓa fatarsa – ta cire. “Wallahi
mun gama.” ya fashe da kuka, amma ba kukan da kake ji ba ƙara, sai hawaye masu zafi kamar
gawayi.
Ihsan ta lumshe ido, ta kai bakinta ga wani ƙaho da ke ƙunshe