Showing 21001 words to 24000 words out of 28842 words

Chapter 8 - BAYAN WATA BOOK ONE BY NARNAH KANWAR SOJA .pdf

20 May 2025

2332








Shi kuwa, yana da murmushin da ba'a san a zuciya akwai tsoro da jin nauyin amanar da ya
ɗauka ba bayansa, abokansa biyu da shaidu—Alhaji Babangida da Alhaji Laushi—duk sun fito
cikin kayan zamani ƙauyen ya sha ado kamar an shirya masa sallah gari ya ɗau shela da
kade-kade na kalangu da waka:

“Alhaji Saminu yazo!
angon Halima yazo!”




Tun daga makon da ya wuce, iyayen Halima sun ɗora shagalin al'ada, mata na unguwa sun taru
kullum ana sallake, ana gasa binkami, koskoso, da kilishi. Halima tana zaune cikin ɗakin
mahaifiyarta marigayiya, cikin duhun tunani da zumudin rayuwar da ba ta san me take cike da
ita ba ,aka yi mata lalle, aka sa mata ƙwarya ta ruwan turaren wuta a gefenta, aka shafa mata
manshanu a fata, aka ɗinke mata zani da riga mai alamar Fulani na gargajiya—jar zani mai
adon ratsi da santali na tsaf.


An saka ta cikin wani ɗaki mai ƙyalli da kilishi, ana yayyafa mata ƙamshi da bakhour, ana duba
fatarta da gashinta, yarinyar ce kyakkyawa da kyau na halitta, ba ado ke ƙawata ta ba—rashin
yawan maganganu da nutsuwar ta ce abin kallo.


A gaban limamin ƙauye da shaidu, aka daura auren Halima da Alhaji Saminu da sadaki naira
dubu ɗari biyar, da sarkar zinari da kayan gida., adaidai lokacin da aka furta "na ɗaura", Halima
ta fashe da kuka mai ƙarfi. Sai dai ba kuka na soyayya ko jin daɗin aure ba ne—kuka ne na
rabuwa da matar mahaifinta, wacce ta raineta tun rasuwar mahaifiyarta, wani kuzarin tunani ya
cika ta, kamar tana jin kamar yanzu rayuwarta ta sauya daga yarinya zuwa amarya, daga ƙauye
zuwa birni.

Moddibbo ya share hawayen sa da alwala, yana murmushi mai cike da damuwa, yana fatan
Halima zata dace da sabon rayuwar da zata tafi ciki, a zuciyarsa yana fatan Alhaji Saminu zai
rike ta fiye da yadda aka rike ’yar sarki.






Alhaji Saminu ya bar ƙauyen ba da hannu ba. Ya bar da ɗimbin kyaututtuka: kudi ga matan
unguwa, jakunkunan shinkafa, kayan abinci, sabbin riguna da ɗinkin zamani ga matasa, har da
jakunkuna ga yara da aka ce "na makaranta".


Wajen fitarsu, aka shigo da sabuwar amarya cikin sabuwar rigar aso-ebi da kwalliyar santali,
aka ɗaura mata gyale mai nauyin zinariya, aka raka ta da kalangu da wake-wake, aka saka ta
cikin motar farin Lexus, sai ga kafila ta nufi birnin Abuja.


Amarya ta fito daga ƙauye—amma fuskarta na cike da tambayoyi. Shin me birnin ke ɓoye
mata? Me Alhaji Saminu zai kasance gareta? shin wannan aure zai fassara soyayya ne, ko
wata kyauta ta biyayya ce da ba zata taɓa jin daɗin ta ba?




*********************************




Juyawa tayi da ƙarfi kamar wadda aka hangi zuciyarta ta nitse cikin ruwan kogin ɓacin rai. tana
mai huci da numfashi mai nauyi, ta faɗa jikin Moddibbo kamar jaririya, ta rungume shi da ƙarfi,
tana kuka mai girgiza zuciya dukkan gangar jikinta na rawar jiki, murya na rawa kamar ana
buɗe gidan hawaye a zuciya.

Moddibbo ya kama kanta yana bubbuga bayanta da hannunsa mai sanyi da tausayawa.
"Allah ya sa ki dace Halimatu," ya faɗa da wani murya da yafi shiru nauyi. "ki rike mutunci, ki
tsaya da imani kiye koyar da mahaifiyar ke a fagen haƙuri zaki ci ribar zaman duniya ... rayuwa
ce bata da tabbas."

Shi kansa idonsa cike da ruwa, kodayake zuciyarsa ta taɓu sosai—ya jima yana kallon Halima
tamkar zinariyar sa wanda yanzu ya mika hannunsa ya mika ta ga duniya. ya mika al’amuranta
ga wani mutum da ya fi shi daraja da kima, amma ba shi da tabbacin soyayya.


Bayan kuka da ban kwana mai cin rai, sai Halima ta shige cikin motar Alhaji Saminu da zuciyar
da ba a iya fassara. Alhaji yana ƙoƙarin rarrashi da annuri, yana ƙyalƙyala dariya mai taushi
yana faɗin:


"Amaryata kada ki damu, Abuja ba abin tsoro ba ne ke zauna lafiya, za ki ga alheri."
Halima bata ce komai ba ta fuskanci gilashin motar tana kallon ƙauyen su da ke raguwa a
bayanta kamar mafarkin da ya ɓace. hannunta na cikin haɗaɗɗiyar rigarta, amma zuciyarta na
cikin tsohon zanin ƙauyenta.






Motoci suka fice daga Gembò, suka fasa hanyoyi masu kura, suka dosa garin Yola inda jirgi zai
tashi zuwa Abuja. Halima na zaune cikin mota, amma kamar a mafarki ta kasa kallon sabbin
gine-gine da suka wuce su, kamar ba su da ma'ana gareta.


A lokacin da suka isa filin jirgi, an ce mata "Halimatu! Ki sauka ",ta sauka cikin rigima, tana
kallon ƙasa kamar tana tsoron ƙasa ce zata buɗe ta haɗiye ta ba ta san me ake nufi da “ticket”
ba ba ta san yadda ake biya ba yanzu ne Halima ke fara jin bambancin rayuwa, ta kasa cire
takalmanta a wajen sakan na’ura, sai da ma'aikaciyar ta fara dariya ta ce: “Yarinya! ba salla za ki ba wannan tsafta ne da dokar jirgi.”
taji kunyarta sosai Idonta ya cika da ƙyama da tozarta a zuciyarta:
“kai! ashe akwai duniya kamar haka?”






Bayan an kaita cikin jirgin, aka ɗaure mata seat belt, ta riƙe kujerar kamar wacce ke cikin ruwa

mai zurfi. Da jirgi ya tashi, ta saki ƙara mai firgitarwa:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wayyo Moddibbo…! na mutu!”
Alhaji Saminu ya rike hannunta da dariya “babu komai Halimatu, jirgi ne ke tashi kawai.”






Kamar sabuwar tsuntsuwa aka ɗauke daga ciyawa, aka ajiye cikin gini mai fanfo. As zuciyarta,
birni kamar wata. Amma tambaya ɗaya ke ci mata rai: Shin wannan sabon garin da take ciki zai
taimake ta ta samu sabuwar rayuwa, ko zai ɓata mata tunanin da take tsaye da shi tun
ƙuruciya?



Tunda suka hau cikin jirgin sama, Halima ta kasa zaman lafiya idanunta na zagaye cikin
hadadden komai wanda ba ta taɓa mafarkin wanzuwarsa ba , tana kallon tagar gefe, tana ganin
sararin samaniya da ƙasa na raguwa kamar yadda aka rage wa tunaninta hankali. amma wani
abu ya sake ɗaukar mata hankali...

A kujerar bayan nata, wani saurayi ne zaune, ya murtuƙe fuska, idonsa kamar na damisa mai
zurfin tunani , fuskar sa doguwa ce, fara tas kamar bulo, ƙuncinsa yana da ɗan launin ja,
bakinsa siriri ne amma mai ɗan ƙasaita gashin kansa an rage shi tsaf yana sheƙi, sai karan
agogon zinare a hannunsa na hagu ya ƙara ɗaukar hankali.

Shima yana kallon Halima, ba da sha’awa ba, amma da mamaki da tausayi kadan kamar yana
cewa da kansa, “Ina aka samo irin wannan ‘yar ƙauye mai tarin kamala?”
suna cikin tashi ne Halima ta saki ihun da ya gigita kowa
“Wayyo Allah naaa! waye ya ce jirgi zai ɗaga?! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”






Mutane sun juya suna kallonta, mata suka dinga dariya a nutse, wasu kuma suka tausaya
amma shi saurayin da ke baya—ya kalli fuskarta da jajayen idanu, yana juyar da kansa a
hankali cikin murmushin gefen baki, kamar wanda ya saba da irin haka a rayuwar zuciyarsa ,
sun sauka a filin jirgin Abuja, wanda ya bude musu sabon shafi a rayuwa.

Alhaji Saminu ya nufi Maitama da su, inda katafaren gidansa ke cike da girma da kima. gidan
na da kofa babba mai lanƙwasa kamar ƙofar masallaci a Makka. farfajiya ce a waje, da lambu
mai yalwa, sai tsuntsaye ke ta raira waka kamar sun san sabon baƙuwa ta iso.






Yayin da Halima ta kalli ƙofar katafaren gidan, zuciyarta na wani irin doki da tsoro da fargaba,
wani sashe na ruhinta na faɗin "kin fito daga ƙauye, amma an jefa ki cikin birnin masu hannu da
shuni..." da zuciya ɗaya ta shiga, sanye da kayan aure na gargajiya: mayafin fulawa, zobba a
yatsu, da dankwali mai yatsin zinariya.

A cikin gida, motoci sun sha jerin gado, masu gadin gidan biyu a ƙofar shigowa suna miƙa
gaisuwa da ban girma. Gidan kuwa – katafaren alfarma ne wanda ba a taɓa mafarkin Halima
zata taka kafarta ciki ba. Babban falon yana da manyan tagogi masu labulen fata na turkiyya,
cike da fitilu na chandelier masu hasken zinariya, cikin falon ne Hajiyah Nafisa ta karɓe ta da
murya mai cike da mamaki:


Matar Alhaji Saminu, Hajiyah Nafisa, ta fito sanye da kayan alfarma gashinta a jikin mayafi yana
sheƙi kamar rigar sarauta ta kalli Halima da murmushi na ɗan lokacin, amma idanunta na cike
da alamun tambaya:
“Itace wannan yarinyar?”
Halima ta kasa magana ganin palon gida kadai ya isheta tiles ne na zinariya da hoda mai
sheƙi, fanfo a bango da tebur na gilashi. tana takawa kamar ana binsa da ƙasa. Zuciyarta na
cewa:
“To wallahi... haka birni yake ko dai na mutu ne an kawo ne gidan aljanna ?” kwalliyar da aka yi
mata da kayan Fulani na auren ƙauye—maye da zobe da mayafi na fulawa—ya sa ta ƙara
haske , amma a fuska akwai shakku, akwai salo na “ba sani ba sabo.” sai dai akwai mutunci a
tafiyarta, wanda ba’a koya shi a birni. “Nafisa itta ce amaryata na biya sadakinta tun can ƙauye kamar yadda na gaya miki. Allah
yasa alkhairi.”
Hajiyah Nafisa ta tabe baki cikin murmushi mai nauyin fahimta daga kallon ta ɗaya ka gane ko
da tana ƙoƙarin karɓarta, zuciyarta ba ta cikin hakan gaba ɗaya.

Sai da aka kai ta ɗakinta da aka tanadar mata cikin gida ɗaki mai faɗi sosai, bangon sa mai
launin cream da zinariya an shimfiɗa masa carpet mai laushi, akwai gado babba da labule mai
juyawa kamar na sarauta taga biyu na dakin suna kallon lambun cikin gida, inda tsuntsaye ke ta
shawagi, cike da kyan gani. dakin na da fanka da AC, amma Halima bata san amfani da komai
ba. Sai kallon su take kamar kayan sihiri.


Ta zauna a gefen gado daidai lokacin wata mai aiki – Hasiya – ta shigo da murmushi a fuskarta.
Hasiya daga Sokoto ce, mai ƙanƙantar jiki da zubin kawaici atake suka fara haɗuwa Hasiya ta
ce da ita:
“Wallahi Aunty Halima kin yi kyau, da gaske ne ke daga ƙauye?”
“Eh... daga Gembo,” ta ce da dariya mai daɗin ji. “kin taɓa jin sunan kauyen?”
“A'a, amma yanzu na ji ki. sai dai ki gyara nan Abuja fa ne Idan baki yi wayo ba, sai a cuce ki.”






Nan suka fara zama ƙawayen gaske. Halima ta fara ɗan sabawa cikin gidan, musamman da
yaran Alhaji Saminu goma da ke gidan. akwai Muneerah da Ruqayyah – ‘yan mata manya
masu haɗe da kwalliya da rashin kunya, masu jin turanci da yi wa Halima kallon kamar uwar
kauye suna kiran ta “that girl from bush” a bayan ta.

Sannan akwai Aminu Junior da Zaid, samari matasa da suka fi ɗaukar lokaci a wajen gidan
basu damu da sabuwar mace, sun fi shagaltuwa da motocinsu da rayuwar club da Instagram.


Yara uku ƙanana—Sulaiman, Abbas, da Fadilasun fi sabawa da Halima suna zuwa ɗakinta
suna wasa da ita ta dinga yi musu wasan shanu da dabbobi da kida da rawa irin na ƙauye,
suna dariya kamar an saka musu annashuwa a zuciya tana ɓoye wannan zumunci da su domin
kada uwayensu su ji.



Matar biyu kuwa, Hajiyah Mariyah da Hajiyah Sabeerah, su ne abokan huldar Nafisa amma
Hajiyah Mariyah ce shaidaniya, mai haƙurin fitina da halin mugunta tana kallon Halima da

kyankyami, tana cewa:
“Wato wannan ƙaramar ‘yar Fulani ce ta zo mana da daddare? Allah ya sa ba za ta ja mana
Alhaji ba.”






Tun daga rana ta fara tsara yadda zata nunawa Halima cewa gidan ba da sauki ba ne. tana tura
mata ayyuka kamar ba matar aure ba: “ki share wancan, ki gyara kicin, ki tafi can ki goge
banɗaki.”


Halima kuwa, da jin kunyar Fulani da biyayya, sai ta dinga yi tana mika hannu da zuciya, ba tare
da kuka ko korafi ba inda Hasiya ta fi shiga tsakiya, tana mata nasiha da rarrashi:
“Ki yi haƙuri Halima, nan ne birni idan kika nuna rashin juriya, sai su hana ki kwanciyar hankali
amma Allah yana tare da mai gaskiya.”








A haka Hajiyah Nafisa ta dinga kallon yadda Halima ke yi wa yara wasa, tana girki da kyau,
tana wanke-wanke da murmushi da farko tana kyamar ta, amma wata rana ta shigo dakin
Halima sai ta ganta tana dinki wa Fadila riga da hannu wani abu ya motsa a zuciyarta. Ta ce da
kanta: “Wannan yarinyar... ba ta da mugunta kuma girmanta yana shigowa hankali.”






Halima kuwa har yanzu bata san haka ba. zuciyarta na yawo ne da tambayoyi: “shin wannan
rayuwar ita ce rabona? ina mahaifina da mahaifiyata? W
wannan Alhaji Saminu fa, me yasa yake sona?
wani dalili ne yasa ya kawo ne gidan sa ya ajiye tsawon lokaci bai dawo garine ba?

Ohhhhhhhh ga Halima ga Abuja
a sannu a hankali zamu shiga labarin Halima


continued ƙanwar soja in Sha Allah


✍️


















https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y


BAYAN WATA
AFTER THE MOON

BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA




ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION






SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star










Wannan page na sadaukar dashi ga mutum biyu Sister Juwairiyya M Lawan tare da Najeeb
Allah ya bar zumunci enjoy the page guys

19 / 20










Wata bakwai kenan cif da zuwan Halima gidan Alhaji Saminu wata uku na rayuwa da ke cike da
shiru, da sanyi, da kewa, da dogon kallo zuwa fitilun falon cikin dar wata bakwai bata taɓa ganin
fuskar mijinta ba sai sau biyu kacal sau na farko da ya kawo ta gida, na biyu kuwa yana
wucewa da mota, ya tsaya da taga yana kallon ta ba tare da ya sauka ba.

Tunda lokacin, Halima ta fara tantama: “shin ni matar aure ce ko kuwa ba haka bane? ko kuma
na fi zama ‘yar aikin gidan alfarma da ba ta san ko wane ne mijinta ba?”


Gidan kuwa kamar gida ne na almara: bangarori fiye da shida, kowane ɗaki kamar wani gida
daban. Halima ko bandakin da aka ce na nata ne ma sai da Hasiya ta koya mata hanyarsa da
yadda za ta kunna ruwa daga famfon lantarki ta ƙi fita daga dakin nata sai idan da gangan,
yaran gidan sun zama mafita ga zuciyarta Sulaiman da Fadila na mata wasa, suna biye mata
da dariya da kida da rawar kauye ita kuma tana jin daɗin hakan, tana samun nishadi duk da
zuciyarta na ci gaba da yin rauni da damuwa.
a wannan daren, kamar kullum, ta zauna a dakin nata cikin sanyi mai daɗi daga AC da fitilar
tagwayen da ke ba dakin ƙamshi ta jingina da kujera, tana kallon hoton kwane-kwane da aka
ɗora a bango hoton tsaunuka da furen da bata taɓa gani da ido ba, hawaye ya fara gangaro
mata ta shafa su da gefen zane, tana kiran zuciyarta da sunan gida: “Kauna, Kaka, Baraka...
ina kuke? ko na fice a nan in dawo Gembo da ƙafa ne? ko gidan da kuke tsirfa hatsi yanzu, ko
na fi wannan?”

Daga nan, bacci ya ɗauketa cikin sanyin dare mai ɓoye zuciya cikin mafarki, Halima ta tsinci
kanta a kusa da wani tafki mai ruwan shudi gabar tafkin akwai ciyayi masu launin zinariya,
tsuntsaye na waka, iska na busa kamar karamar waka, ta tsaya cikin tufafin fararen zinariya,
kanta a rufe da mayafin rawaya , can gefe kuwa, wani saurayi na kallon ta tsayuwarsa mai
ƙayatarwa ce: dogo, baƙi, yana sanye da farin riga da wando. amma fuskar sa dukk ta ɓoye a
inuwa kamar fuskarsa na ɓoye da nufin ya dawo wata rana.
“Halima...” muryarsa mai sanyi, mai kaɗa, tana ratsawa har cikin jijiyoyinta.“kai wa kake ne?” ta
tambaya da muryar yarinya. “kayi kama da wani na kusa da zuciyata...”
“Ni ne mai zuciyar da ta kira ki cikin bacci... da zuciyar da zata so ki fiye da yadda kike so
kanki.” ya miƙa mata hannu, amma kafin ta kamo ta farka tashi da sauri, numfashinta ya kadu,
zuciyarta na bugu tana kallo sama kamar zata gan shi a cikin silin.
“waye wannan? me yasa mafarkin nan ya shige ni haka? Kuma me yasa fuskar sa ta ɓoye
kamar akwai abu da ba a shirya bani ba?” karo na farko tun da ta zo birni, Halima ta fara jin
wani abu daban – kamar mafarkin soyayya da sabuwar rayuwa na faɗa mata, "akwai wani sirri
da ke tafe... kuma akwai wanda zai sauya maki rayuwa, ko da ba yanzu ba."


Kullum cikin dare, Halima na ƙoƙarin rubuta abubuwan da ke faruwa da ita a cikin wani ƙaramar
littafi da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login