Showing 15001 words to 18000 words out of 28842 words

Chapter 6 - BAYAN WATA BOOK ONE BY NARNAH KANWAR SOJA .pdf

20 May 2025

2330

da ragowar fitsari. ta sha kadan
gaban Allah, ya fi komai wannan ba lokacin kunya bane, ko tsoron mutuwa. wannan yanayi ne
da rayuwa take ƙi barin jikinsu , Maryam na jingine da dutse, tana kallon jikin ta kamar ba nata
bane. “I’ve become sand,” ta ce. “Even my voice sounds like wind.”

Daga nesa...


Ado, wanda ya fi ƙarfinsu kaɗan saboda tsawon jikinsa da kwazon zuciyarsa, ya fara bin
duwatsu da sandar da ya kakkarya bayan lokaci – sai ya hango wani abu wani rami mai zurfi da
ke wani rami kamar tukunyar wuta. Yayi tsalle, ya kalla – ƙananan ragowar ruwa!
Yayi ihu kamar kura mai murna: “Ruwa! Wallahi, ruwa!” ya dawo da gudu yana faɗuwa, yana
hura numfashi kamar za a sa wuta a jikinsa. “gashi chan ! gashi chan!”


Suna ta matsowa da karfin halin da ba su san inda ya fito ba. kowa da dabara, suka tsinke leda,
suka tattara ƙwanƙwaso daga jikin su, suka kai bakin su... dan kadan, amma ceto. sannu a
hankali zuciyarsu ta dawo ba da kyau ba, amma da rayuwa suka kwanta, suka kalli sama,
tsibirin da suke kai tsaye ne a tsakiyar Sahara, ba ruwa sosai, amma nan ne Allah ya basu
mafaka.


Yazid ya ce da karamin dariya, “Idan muka tsira daga nan sai na ce duniya ba baƙi bane. duniya
rana ce da yashi, amma ina da mafarki.”
Ihsan ta ce, “Na fi son mutuwa da mafarki fiye da rayuwa babu buri.”
Maryam ta rufe idanunta " ya Allah mun gode maka da kyautar ruwa lallai ruwa zai rayu inda ba
halitta amman mutum bazai rayu ba ruwa ba "..

Ruwan da suka tsinci ya zama tamkar aljanna. kowa ya samu ɗan kaɗan ya ji cikinsa ya huta.
bayan kwanaki biyu a cikin wannan tsibirin – inda babu ciyawa, babu dabbobi, amma akwai
inuwa da ƙaramin ramin ruwa – sai zuciyarsu ta ɗan dawo.


Ihsan ta janye rigarta mai sheƙi, ta taka da ƙafarta mai jini zuwa ga sauran su, ta ce cikin sanyin
murya:
“Ku ji ni mana...”


“Mu ne matafiya,
Wanda ba su da gida,
amma zuciyarmu da rai,
suna cikin mafita...”
Maryam ta kama hannunta, suka fara juya da kasala, suna dariya da hawaye. Yazid da Ado
suka buga ƙafa a yashi, John ya murɗa murya kamar yana wake, sai suka kama da karfi.


“Ruwan nan, ka ceci mu,
yashi da rana sun cinye mu,
amma muna raye,
muna tafe – cikin fata!”


Sai suka rungume juna – gaba ɗaya biyar – suna sharar hawaye, suna murza fatar jikinsu da
suka rasa. Wannan rana ce da suka yi murmushi cikin azaba.


" Bayan wata akwai haske
Bayan wuya akwai daɗi "...




Bayan sati biyu a wannan wuri, ruwa ya kusa ƙarewa sai suka yanke shawarar ci gaba da
tafiya, domin sun san idan sun zauna za su mutu da yunwa da ƙishirwa. sun ɗaura jakarsu da
fata, suka fito daga tsibirin suna zamewa a yashi.


Kwana biyu sun yi suna tafiya cikin rana da yamma. rana na dafa ƙafarsu, yashi na kai musu
zafi daga ƙasa. idanuwansu sun fara ganin abu biyu, zuciyarsu ta fara shakku da juna. Maryam
ta fara rikicewa, ta yi ihu tana zagin Yazid tana cewa:

“Ka ce zaka kawo mu Dubai! ka ce za mu ci kuɗi! Ashe ba haka bane?!”


John ya zube a ƙasa yana dariya da kukan hauka. “We’re already in Dubai – in hell's part!”
Ihsan da Ado suka kama su, suka kwantar da su kamar yara.






Bayan wata guda cikin tafiya da yunwa, sai suka hango wani gari daga nesa – amma ana
shigarsu kusa da shi sai suka ji hayaniya. mutane masu bindiga da dabbobi ke yawo a kusa –
mafarauta ne amma ba na noma ba – ‘yan fasa-ƙwauri ne da ke farautar masu tsallaka haddi
don su sayar da su ga masu aikatau ko masu fatauci.

Sun kamasu a dare sun ɗaure su da igiya, suka ajiye su a cikin wani daki tamkar kurkuku da
yashi a ƙasa. Maryam ta fara kuka, John ya yi shiru yana kallon su kamar wanda ya hakura da
rayuwa. Yazid ya yi ƙoƙarin fita, aka yi masa dukan tsiya, aka zubar da jininsa.


Ihsan da Ado sun tsaya suna kallon juna da hawaye. Ado ya ce:
“Na rantse, idan muka tsira daga nan, ko ruwa ne, ko wuta, zan kawo ki gida da hannuna.”
Ihsan ta runtse ido. “Zan riƙe ka da zuciya har ƙarshe.”






Continued .............
by narnah ƙanwar soja ✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y






BAYAN WATA
AFTER THE MOON


BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA




SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star




15 / 16
08 / 5/ 2025

Kamar yadda aka saba duk shekara, Alhaji Saminu bai taɓa yin ƙasa a guiwa ba wajen nuna
ɗimbin darajarsa a idon mutanen ƙauyen Gembò amma wannan karon daban ne. wannan karon
ba kawai don shanaye ya zo ba ya zo ɗaukar amana.






A gaban Moddibbo da wasu dattawan gari guda biyu, Alhaji Saminu ya fito da sadakin Halima.
kudi ne masu yawan da fulani ba su fiye gani ba a lokaci guda baya ga hakan, ya kawo 'yan
dabbobi da kayan gyaran amarya, tare da alkawarin dawowa bayan Sallah da sati biyu—kai
tsaye daga birnin Tarayya Abuja inda matarsa ke zaune.

Moddibbo ya karɓi sadakin cikin nutsuwa da girma ya san me hakan ke nufi: yanzu Halima zata
koma karkashin Alhaji Saminu amma ko da yake zuciyarsa na cike da nauyin amana, bai nuna
ba, saboda a rayuwa irin tasu, alƙawari tamkar doka ne da ba za a karya ba.


Halima kuwa... ta zauna a gefen mahaifinta da cike da kunya, fuska a kasa kamar yadda aka
koya mata, duk da cewa an ba ta labarin cewa rayuwar birni ce zata zame mata gaba, kuma
Alhaji Saminu mutum ne mai arziki da daraja—amma a zuciyarta babu motsin soyayya ko ɗokin
aure.

Zuciyarta tamkar fili ne, babu shuka, babu furanni kawai akwai wata siririyar lafazi da take
maimaitawa a ranta:


"Na yarda da mahaifina na amince da kaddara. kuma zan bi Alhaji Saminu, ko da zuciyata ba ta
motsa ba."


Irin wannan biyayya ce da ta sa ta karɓi sadakin da lafazi guda biyu:
“Na yarda.”


Moddibbo kuwa kamar kowa yana ganin yana murna amma shi da zuciyarsa sun san gaskiya ,
ya san Halima ba ta kai matsayin aure ba tukuna ta girma da sauri, amma zuciyarta har yanzu
karama ce, tamkar macen da bata fara sanin al'amuran soyayya ba.

Sai dai kuma, Moddibbo mutum ne mai daraja da mutunci ya rike amanar Alhaji Saminu fiye da
yadda wasu ke rike 'ya'yansu. Yana fatan Alhaji Saminu zai kare martaba da tsaron Halima
kamar yadda ya rike alkawari na shekaru goma sha biyar.


Wani iska ya buso daga arewa, ya kada ganyen kuka da ke bakin ruga Halima ta lumshe ido,
tana jin iskar kamar wata alama ce daga sama ko soyayya zata zo daga baya? ko kuwa hakan
nan ne rayuwa ta rubuce mata?




Bayan sati biyu da cikar alkawari, ƙauyen Gembò ya sake fuskantar wata rana da ba za a taɓa
mantawa da ita ba rana ce da komai ya sauya—rana da tarihi ya ƙara rubutun zinariya cikin
ƙwarya mai ƙyalli.


A safiyar ranar asabar, tun ƙarfe tara da mintuna goma, sai ga jere-jeren motoci guda shida
masu sheƙi da ƙyalli irin wanda bai saba zuwa ƙauyen ba, motoci ne kirar Lexus LX 570 guda
biyu, guda bakar fata, guda kuma fari ɗan haske mai cike da adon zinariya. Sauran kuwa
motoci ne kirar Hilux da Toyota Highlander, dukkansu cike da kaya, kujerun zamani, manyan
jakunkuna da akwatuna masu lulluɓe da furen ado da yajin rawaya.


A wata ƙaramar Prado, wanda aka ɗora babban laifan jajjayen furanni da tutar Kaunar aure,
Alhaji Saminu ne ya fito sanye da babban ɗan-baban Shadda mai launin zinariya da ruwan
hoda , babbar hula ce ta fulani bisa kansa, mai ɗinki na musamman da adon sarka fitarsa daga
mota ta sa yara suka yi tsalle, mata suka fara cewa:

“Ga angonmu ya iso! Allah ya sa a dace!”






Shi kuwa, yana da murmushin da ba'a san a zuciya akwai tsoro da jin nauyin amanar da ya
ɗauka ba bayansa, abokansa biyu da shaidu—Alhaji Babangida da Alhaji Laushi—duk sun fito
cikin kayan zamani ƙauyen ya sha ado kamar an shirya masa sallah gari ya ɗau shela da
kade-kade na kalangu da waka:

“Alhaji Saminu yazo!
angon Halima yazo!”




Tun daga makon da ya wuce, iyayen Halima sun ɗora shagalin al'ada, mata na unguwa sun taru
kullum ana sallake, ana gasa binkami, koskoso, da kilishi. Halima tana zaune cikin ɗakin
mahaifiyarta marigayiya, cikin duhun tunani da zumudin rayuwar da ba ta san me take cike da
ita ba ,aka yi mata lalle, aka sa mata ƙwarya ta ruwan turaren wuta a gefenta, aka shafa mata
manshanu a fata, aka ɗinke mata zani da riga mai alamar Fulani na gargajiya—jar zani mai
adon ratsi da santali na tsaf.


An saka ta cikin wani ɗaki mai ƙyalli da kilishi, ana yayyafa mata ƙamshi da bakhour, ana duba
fatarta da gashinta, yarinyar ce kyakkyawa da kyau na halitta, ba ado ke ƙawata ta ba—rashin
yawan maganganu da nutsuwar ta ce abin kallo.


A gaban limamin ƙauye da shaidu, aka daura auren Halima da Alhaji Saminu da sadaki naira
dubu ɗari biyar, da sarkar zinari da kayan gida., adaidai lokacin da aka furta "na ɗaura", Halima
ta fashe da kuka mai ƙarfi. Sai dai ba kuka na soyayya ko jin daɗin aure ba ne—kuka ne na
rabuwa da matar mahaifinta, wacce ta raineta tun rasuwar mahaifiyarta, wani kuzarin tunani ya
cika ta, kamar tana jin kamar yanzu rayuwarta ta sauya daga yarinya zuwa amarya, daga ƙauye
zuwa birni.


Moddibbo ya share hawayen sa da alwala, yana murmushi mai cike da damuwa, yana fatan
Halima zata dace da sabon rayuwar da zata tafi ciki, a zuciyarsa yana fatan Alhaji Saminu zai
rike ta fiye da yadda aka rike ’yar sarki.






Alhaji Saminu ya bar ƙauyen ba da hannu ba. Ya bar da ɗimbin kyaututtuka: kudi ga matan
unguwa, jakunkunan shinkafa, kayan abinci, sabbin riguna da ɗinkin zamani ga matasa, har da
jakunkuna ga yara da aka ce "na makaranta".


Wajen fitarsu, aka shigo da sabuwar amarya cikin sabuwar rigar aso-ebi da kwalliyar santali,

aka ɗaura mata gyale mai nauyin zinariya, aka raka ta da kalangu da wake-wake, aka saka ta
cikin motar farin Lexus, sai ga kafila ta nufi birnin Abuja.


Amarya ta fito daga ƙauye—amma fuskarta na cike da tambayoyi. Shin me birnin ke ɓoye
mata? Me Alhaji Saminu zai kasance gareta? shin wannan aure zai fassara soyayya ne, ko
wata kyauta ta biyayya ce da ba zata taɓa jin daɗin ta ba?




*********************************




Juyawa tayi da ƙarfi kamar wadda aka hangi zuciyarta ta nitse cikin ruwan kogin ɓacin rai. tana
mai huci da numfashi mai nauyi, ta faɗa jikin Moddibbo kamar jaririya, ta rungume shi da ƙarfi,
tana kuka mai girgiza zuciya dukkan gangar jikinta na rawar jiki, murya na rawa kamar ana
buɗe gidan hawaye a zuciya.

Moddibbo ya kama kanta yana bubbuga bayanta da hannunsa mai sanyi da tausayawa.
"Allah ya sa ki dace Halimatu," ya faɗa da wani murya da yafi shiru nauyi. "ki rike mutunci, ki
tsaya da imani kiye koyar da mahaifiyar ke a fagen haƙuri zaki ci ribar zaman duniya ... rayuwa
ce bata da tabbas."






Shi kansa idonsa cike da ruwa, kodayake zuciyarsa ta taɓu sosai—ya jima yana kallon Halima
tamkar zinariyar sa wanda yanzu ya mika hannunsa ya mika ta ga duniya. ya mika al’amuranta
ga wani mutum da ya fi shi daraja da kima, amma ba shi da tabbacin soyayya.


Bayan kuka da ban kwana mai cin rai, sai Halima ta shige cikin motar Alhaji Saminu da zuciyar
da ba a iya fassara. Alhaji yana ƙoƙarin rarrashi da annuri, yana ƙyalƙyala dariya mai taushi
yana faɗin:


"Amaryata kada ki damu, Abuja ba abin tsoro ba ne ke zauna lafiya, za ki ga alheri."

Halima bata ce komai ba ta fuskanci gilashin motar tana kallon ƙauyen su da ke raguwa a
bayanta kamar mafarkin da ya ɓace. hannunta na cikin haɗaɗɗiyar rigarta, amma zuciyarta na
cikin tsohon zanin ƙauyenta.






Motoci suka fice daga Gembò, suka fasa hanyoyi masu kura, suka dosa garin Yola inda jirgi zai
tashi zuwa Abuja. Halima na zaune cikin mota, amma kamar a mafarki ta kasa kallon sabbin
gine-gine da suka wuce su, kamar ba su da ma'ana gareta.


A lokacin da suka isa filin jirgi, an ce mata "Halimatu! Ki sauka ",ta sauka cikin rigima, tana
kallon ƙasa kamar tana tsoron ƙasa ce zata buɗe ta haɗiye ta ba ta san me ake nufi da “ticket”
ba ba ta san yadda ake biya ba yanzu ne Halima ke fara jin bambancin rayuwa, ta kasa cire
takalmanta a wajen sakan na’ura, sai da ma'aikaciyar ta fara dariya ta ce: “Yarinya! ba salla za ki ba wannan tsafta ne da dokar jirgi.”
taji kunyarta sosai Idonta ya cika da ƙyama da tozarta a zuciyarta:
“kai! ashe akwai duniya kamar haka?”






Bayan an kaita cikin jirgin, aka ɗaure mata seat belt, ta riƙe kujerar kamar wacce ke cikin ruwa
mai zurfi. Da jirgi ya tashi, ta saki ƙara mai firgitarwa:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wayyo Moddibbo…! na mutu!”
Alhaji Saminu ya rike hannunta da dariya “babu komai Halimatu, jirgi ne ke tashi kawai.”






Kamar sabuwar tsuntsuwa aka ɗauke daga ciyawa, aka ajiye cikin gini mai fanfo. As zuciyarta,
birni kamar wata. Amma tambaya ɗaya ke ci mata rai: Shin wannan sabon garin da take ciki zai
taimake ta ta samu sabuwar rayuwa, ko zai ɓata mata tunanin da take tsaye da shi tun
ƙuruciya?

Tunda suka hau cikin jirgin sama, Halima ta kasa zaman lafiya idanunta na zagaye cikin
hadadden komai wanda ba ta taɓa mafarkin wanzuwarsa ba , tana kallon tagar gefe, tana ganin
sararin samaniya da ƙasa na raguwa kamar yadda aka rage wa tunaninta hankali. amma wani
abu ya sake ɗaukar mata hankali...

A kujerar bayan nata, wani saurayi ne zaune, ya murtuƙe fuska, idonsa kamar na damisa mai
zurfin tunani , fuskar sa doguwa ce, fara tas kamar bulo, ƙuncinsa yana da ɗan launin ja,
bakinsa siriri ne amma mai ɗan ƙasaita gashin kansa an rage shi tsaf yana sheƙi, sai karan
agogon zinare a hannunsa na hagu ya ƙara ɗaukar hankali.

Shima yana kallon Halima, ba da sha’awa ba, amma da mamaki da tausayi kadan kamar yana
cewa da kansa, “Ina aka samo irin wannan ‘yar ƙauye mai tarin kamala?”
suna cikin tashi ne Halima ta saki ihun da ya gigita kowa
“Wayyo Allah naaa! waye ya ce jirgi zai ɗaga?! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”






Mutane sun juya suna kallonta, mata suka dinga dariya a nutse, wasu kuma suka tausaya
amma shi saurayin da ke baya—ya kalli fuskarta da jajayen idanu, yana juyar da kansa a
hankali cikin murmushin gefen baki, kamar wanda ya saba da irin haka a rayuwar zuciyarsa ,
sun sauka a filin jirgin Abuja, wanda ya bude musu sabon shafi a rayuwa.





Alhaji Saminu ya nufi Maitama da su, inda katafaren gidansa ke cike da girma da kima. gidan
na da kofa babba mai lanƙwasa kamar ƙofar masallaci a Makka. farfajiya ce a waje, da lambu
mai yalwa, sai tsuntsaye ke ta raira waka kamar sun san sabon baƙuwa ta iso.

Yayin da Halima ta kalli ƙofar katafaren gidan, zuciyarta na wani irin doki da tsoro da fargaba,
wani sashe na ruhinta na faɗin "kin fito daga ƙauye, amma an jefa ki cikin birnin masu hannu da
shuni..." da zuciya ɗaya ta shiga, sanye da kayan aure na gargajiya: mayafin fulawa, zobba a
yatsu, da dankwali mai yatsin zinariya.

A cikin gida, motoci sun sha jerin gado, masu gadin gidan biyu a ƙofar shigowa suna miƙa
gaisuwa da ban girma. Gidan kuwa – katafaren alfarma ne wanda ba a taɓa mafarkin Halima
zata taka kafarta ciki ba. Babban falon yana da manyan tagogi masu labulen fata na turkiyya,
cike da fitilu na chandelier masu hasken zinariya, cikin falon ne Hajiyah Nafisa ta karɓe ta da
murya mai cike da mamaki:


Matar Alhaji Saminu, Hajiyah Nafisa, ta fito sanye da kayan alfarma gashinta a jikin mayafi yana
sheƙi kamar rigar sarauta ta kalli Halima da murmushi na ɗan lokacin, amma idanunta na cike
da alamun tambaya:
“Itace wannan yarinyar?”
Halima ta kasa magana ganin palon gida kadai ya isheta tiles ne na zinariya da hoda mai
sheƙi, fanfo a bango da tebur na gilashi. tana takawa kamar ana binsa da ƙasa. Zuciyarta na
cewa:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login