Showing 27001 words to 28842 words out of 28842 words

Chapter 10 - BAYAN WATA BOOK ONE BY NARNAH KANWAR SOJA .pdf

20 May 2025

2334

farko na
ci gaba da wulakanta ta, musamman Hajiya Mariya, wacce kullum take ƙoƙarin ganin ta gaza
Halima kuwa, tana rayuwa ne tsakanin kuka da shiru, tsakanin mafarkin soyayya da gaskiyar
rayuwa kullum cikin tunanin cewa ƙaddara ce ta raba ta da masoyinta, kuma soyayyar da take
jin daɗinta tun ƙarama ba zata cika ba har abada.


"Idan soyayya kaddara ce, to ni na riga na mallake ta, ko da da hawaye zan sha..." Halima na
faɗa cikin zuciyarta a duk dare, yayin da take kwana tana duban sararin sama daga taga mai
ɗimbin ƙawatawa, amma mara 'yanci.


Rayuwa ta ci gaba da tafiya...
sai dai zuciyoyin masoya biyu suna ci gaba da harbar juna da addu'a cikin nisa, cikin rashin sani
ko Allah zai kawo wata rana su haɗu ko kuwa soyayyar su zata kasance soyayyar da bata da
makoma?
duk da wulakanci da mugun hali da Halima ke fuskanta a gidan Alhaji Saminu, zuciyarta ta ki
rabuwa da sunan Abdullahi.
Abdullahi — wanda tun ranar da suka haɗu a hotel din, zuciyarta ta tabbatar da cewa shine
mafitar rayuwarta.
duk daren da ta kwanta cikin kuka da zubar da hawaye, da ƙaunar da take shirin fashe mata
ƙirji, sai ta runtse ido tana kiran sunansa da shiru.
"Abdullahi... kai ne mafita ta... amma ka riga ka zama mafarki..."
ko da cikin jikinta yana girma, bata daina jin ƙaunar Abdullahi ba. Sai ma ƙara shigewa da ƙara
jin saukin duk wani raɗaɗi idan ta ambaci sunansa a ranta.


Amma fa duniya bata tsaya jira ba,rayuwa ta cigaba da danne ta a karkashin ƙafa, har ta kai ga
lokacin haihuwa ya kure.
ranakun karshe da suka rage mata a duniya, wahala ta fi karfin bakinta cikin da ta ɗauka cikin
ciwo da azaba ya girma har ta cika da tsoro da fargaba ba wanda ke kula da ita
ba wanda ke tambayarta lafiya ko da take ciwo dare da rana, sai Alhaji Saminu ya ce da ita "ke
kanki kika ja wa kanki, na gaji da wannan kuka da ciwo ."
ba komai ya jawo hakan ba sai sanin cewa tsantsan soyayyar da takewa wani alhali tana da
nata auren
A karshe, ranar da komai ya ƙare

ranar da zatai haihuwa Halima ta shiga wani ciwo da ba a iya kwatantawa, Alhaji na chan
hotel yana meeting bai ma san cewa Qatar haihuwar ta ya kama ba.
A kwance a ɗakin da aka ajiye ta cikin wulakanci, ba likita, ba uwargida, ba taimako sai kuka da
ciwon da ke yawo daga ƙasan jikinta zuwa ƙirjinta yana neman karya ta.


Kuka take kamar zata fashe.
Tana kiran Baffa, tana kiran Abdullahi, tana neman taimako amma shiru!


Abdullahi a lokacin yana cikin wani babban business meeting, yana fuskantar matsin rayuwa
sakamakon tarin matsaloli da ya dinga samu tun da ya yarda da zaɓin da iyayensa suka masa.
soyayya da Halima ta fara girma masa a zuciyarsa ba ta gushe ba, kullum yana mafarkin fuskar
ta, murmushinta, da halayenta.
amma bai san halin da take ciki ba.
bai san tana shirin barin duniya ba.


A cikin tsananin raɗaɗin haihuwa, Halima ta ƙara ruɗewa, ta kurma ihu, ta kifa kanta a shimfiɗa
tana ihu kamar rai na fita:


"Ya Allah... Abdullahi... Abdullahi... na yarda da ƙaddara..."inda yayi dai dai da shigowar Alhaji
sakamakon korar Hajiya nafisa sai dai, kafin a kawo taimako, kafin a kawo likita halin ya lalace
,numfashinta ya fara yanke-yanke.
zuciyarta ta yi shiru.
Idonta ya tsaya a sama yana kallon wani abu da kowa baya gani, ahankali Halima ta kwantar da
kanta gefe, ta saki numfashinta na ƙarshe da kalmar:
shahada , ta mutu.
ta mutu cikin radadin soyayya.
ta mutu cikin ciwon zubar da hawaye.
ta mutu ba tare da samun saukin zuciya ba.






Bayan rasuwar Halima...


Tunda aka sallaci Halima tare da jaririnta da bai samu damar saukar numfashi ba, gidan Alhaji
Saminu ya sauya tamkar makoki.

duk wata annashuwa da alfahari da yake alfahari da ita a da, ta shige masa ta barshi da
nadama da dimuwa.


Alhaji Saminu ya dinga zubar da hawaye cikin sirri — hawaye na butulci da rashin amana da ya
yi wa baffa Moddibbo, wanda ya amince da shi ya ba shi Halima cikin kwanciyar hankali.
yanzu kuma ya gane: ya ci amanar sa... kuma duniya ta rama masa cikin kunya da asara!
zuciyarsa ta kasa kwanciya.
Ko motsin iska da aka yi cikin gida sai ya tuno Halima ,ya zauna ya shafa kansa yana cewa:
"Ni Saminu... ni na kashe Halima da hannu na. ni na lalata amana!"


A ɓangaren Abdullahi kuwa, yana zaune cikin ofishinsa ne duka business da meetings ɗin sa
suna tafiya, amma zuciyarsa ta gaza samun natsuwa tun ranar da suka rabu a hotel.


Ana cikin haka sai ya ga sakon gaggawa daga Alhaji Saminu:
"Ina mai baka hakuri, Halima ta tafe gidan gaskiya yanzu ta tafi ta tafe da kuka rashin ka tabbas
soyayyar da take ma gaskiya ne ... ta mutu kuma ban cancanci gafararta ba."




Zuciyarsa ta buga!
Idanunsa suka cika da kwalla.
ya dinga kallon sakon kamar zai kira Halima ta amsa masa amma ya sani, babu mai amsawa.


"kin mutu Halima?..." Ya fadi da baki a raunane, numfashinsa yana fita da ƙyar.
sai wayar ta faɗi daga hannunsa.
Gaban mutane sai ya durƙusa.
kamar an fasa masa zuciya, dukkan jikinsa ya rikice, gaba ɗaya duniya ta tsaya masa cikakkar
shiru.


"Halima...
Halima...
na bar ki cikin wahala, na kashe ki da rashin ƙarfin zuciya ta..."


Cikin kukan da bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa, Abdullahi ya fito daga taron ya fice kamar
mahaukaci, yana rike kirjin sa da hannuwa biyu, yana kuka tamkar jariri, yana ambaton
sunanta.

Duniya ta kare masa a wannan rana.
ya rasa komai.
ya rasa zuciyarsa.
ya rasa Halimarsa
sai tunanin mafarkinsu na yara ya fara dawo masa.
yanda take dariya, yanda take tsoron iska mai kaɗawa...
yanda suka tsaya suna kallon juna a hotel ba tare da sun fahimci komai ba — har abada.
Abdullahi ya narke kamar karamin yaro yana kuka ,ya rasa inda zai kai zuciyarsa.
Soyayyar Halima ta zama masa mafita da karfi.
yanzu kuwa... an binne mafarkin sa da soyayyarsa a ƙasa.








ƘARSHEN LABARIN HALIMA


Bayan rasuwar Halima, kwana biyu kacal sai Abdullahi ya tashi daga gida ya nufi inda aka
binne ta , zuciyarsa cike da nauyi kamar dutse mai nauyi, idonsa kuwa har ya kumbura da kuka
da rashin bacci.


Lokacin da ya isa makabarta, an waye gari — iska tana kadawa, rana na nufar faduwa.
kabarin Halima yana can gefe, kamar ba halitta ce ciki ba wsai iska da tsuntsaye.


Abdullahi ya tsaya daga nesa yana kallon kabarin — jikinsa ya mutu, zuciyarsa tana sukar
numfashi kamar zai yanke, ya karaso a hankali, kafafunsa kamar an daure su
ya durƙusa a gaban kabarin, ya dafa ƙasa da hannayensa biyu cikin rawar murya ya fara
addu'a:
"Ya Allah, ka gafarta wa Halima... Ka sanyata cikin Aljannah tayi ƙoƙari ta zauna da kowa da
mutunci ta sha wahala ta mutu cikin rashin adalci. Allah ka mayar mata da jin daɗin da duniya ta
hana ta."
"Allah ka haɗa zuciyata da ita a lahira idan babu haduwa a duniya."

Yana cikin addu'a sai hawayensa suka fara gangarowa ba tare da ya lura ba.
Kamar yaro ƙarami ya fashe da kuka mai sauti, yana jijjiga kansa da kafadunsa.
mai karatu da kansa sai ya ji zuciyarsa na karyewa — hawaye na sauka daga idonsa.
Domin kuka ne na gaskiya, na azaba da soyayya da ba ta sami cikar burinta ba.


Abdullahi ya zauna a ƙasa har rana ta fara faduwa.
Iska mai kaɗawa tana motsa ganyen kabari.


Daga nan sai ya ɗaga kansa sama, yana kallon sararin samaniya da idon da ya riga ya
ƙumbura, yana faɗin cikin muryar da ta rame:
"Halima... zaki kasance a zuciyata har abada."
"kaddarata ta jefa ni nesa da ke, amma soyayyarki za ta kasance kamar numfashina."
"Allah ya haɗa mu a wuri mafi alheri."






Daga nan ya tashi da ƙyar, yana tafiya daga kabarin da matakin zuciya mai nauyi — ya bar
soyayya a ƙasa, ya ɗauki kewa a zuciya.


Maryam ta yi shiru na ɗan lokaci, idanuwanta na cike da hawaye waɗanda suka zuba akai-akai.
Ihsan ta dafa kafadarta cikin tausayawa—tun daga farkon labarin Halima ta kasa dafa kuka.
John, da alama ba zai iya zamewa ba, ya gyada kai da ƙiyayya:
“Maryam, me irin labari ne wannan? mai tsuma zuciya, mai ban tausayi… me yasa ta mutu? me
yasa ba su haɗu ba daga kallo na biyu suka rabu?”






Yazid kuma, wanda zuciyarsa ta yi sanyi ganin halin da ƴan masarautarsu suka tsinci kansu, sai
ya sauke ajiyar zuciya, ya ce:
“Na yi tunanin zaki ba mu labarin da zai ƙarfafa mana zuciya amma sai gashi kin ba mu labarin
da ya tabbatar mana: ba kowane buri ne a duniya zai taɓa cika yadda muke so ba.”

"Ƴan uwa na matafiya "suka kalle juna Gaskiya ce: a duniyar marubuta da ’yan wasan
kwaikwayo, za a samo labarin da ya haɗa auren jarumai har su cika buri amma a zahiri akwai
ƙaddara a soyayya—ba duk buri ne ke cika ba. anan sai Maryam ta miƙa ɗan gajeren labari na
gaba, na Ummi: “Ummi maƙobchiyar mu, tun tana yarinya take soyayya da ɗan uwanta. , sun yi rayuwar ƙauna
mai ƙarfi ƙaddara bai amince ta aure saba nan ta aure wani daban amma mijinta ya sake ta, ya
ci gaba da rayuwarsa ta chigaba da jimammen zawarci duk da haka, soyayyarsu ta ƙarfafa su
na shekaru , suka sake ƙulla amana da alkawarin aure …

Amman kash ƙaddara bata amince ba Allah bai yardar musu ba nan aka haramta mata auren
sa yanzu ta kuma yin wani aure sun zaɓi ɗaya a zuciyarsu, sun ƙebewa junansu ƙauna ta
musamman wannan labarin na gaske ne—ba don jin daɗi ba, amma domin mu gane: soyayya
na da ƙaddara, kuma ba koyaushe ake samun ƙarshe mai daɗi ba.” sn kasance cikin shiru da tunani, kowa na jin wannan sabuwar hanyar rayuwa—ta ƙauna da
raɗaɗi




BACK TO STORY
zamu chigaba da labarin matafiya guda biyar Maryam ta bamu labarin HALIMATU SADIYA
gaskiya ne kaina wannan page ya sani hawaye tabbass soyayya gaskiya ne kuma ba kowane
soyayyar bace cikakkiyar.
Ihsan ta bamu labarin Princeces Rahilat
zamu chigaba da tafiya daga Egypt har Dubai ko da ƙafa ne fans ku shirya wannan shine
karshen Bayan wata book one




sai mun haɗu a kashi na biyu
********
Alhamdullah
Narnah ƙanwar soja ✍️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login