Showing 18001 words to 21000 words out of 28842 words
“To wallahi... haka birni yake ko dai na mutu ne an kawo ne gidan aljanna ?” kwalliyar da aka yi
mata da kayan Fulani na auren ƙauye—maye da zobe da mayafi na fulawa—ya sa ta ƙara
haske , amma a fuska akwai shakku, akwai salo na “ba sani ba sabo.” sai dai akwai mutunci a
tafiyarta, wanda ba’a koya shi a birni. “Nafisa itta ce amaryata na biya sadakinta tun can ƙauye kamar yadda na gaya miki. Allah
yasa alkhairi.”
Hajiyah Nafisa ta tabe baki cikin murmushi mai nauyin fahimta daga kallon ta ɗaya ka gane ko
da tana ƙoƙarin karɓarta, zuciyarta ba ta cikin hakan gaba ɗaya.
Sai da aka kai ta ɗakinta da aka tanadar mata cikin gida ɗaki mai faɗi sosai, bangon sa mai
launin cream da zinariya an shimfiɗa masa carpet mai laushi, akwai gado babba da labule mai
juyawa kamar na sarauta taga biyu na dakin suna kallon lambun cikin gida, inda tsuntsaye ke ta
shawagi, cike da kyan gani. dakin na da fanka da AC, amma Halima bata san amfani da komai
ba. Sai kallon su take kamar kayan sihiri.
Ta zauna a gefen gado daidai lokacin wata mai aiki – Hasiya – ta shigo da murmushi a fuskarta.
Hasiya daga Sokoto ce, mai ƙanƙantar jiki da zubin kawaici atake suka fara haɗuwa Hasiya ta
ce da ita:
“Wallahi Aunty Halima kin yi kyau, da gaske ne ke daga ƙauye?”
“Eh... daga Gembo,” ta ce da dariya mai daɗin ji. “kin taɓa jin sunan kauyen?”
“A'a, amma yanzu na ji ki. sai dai ki gyara nan Abuja fa ne Idan baki yi wayo ba, sai a cuce ki.”
Nan suka fara zama ƙawayen gaske. Halima ta fara ɗan sabawa cikin gidan, musamman da
yaran Alhaji Saminu goma da ke gidan. akwai Muneerah da Ruqayyah – ‘yan mata manya
masu haɗe da kwalliya da rashin kunya, masu jin turanci da yi wa Halima kallon kamar uwar
kauye suna kiran ta “that girl from bush” a bayan ta.
Sannan akwai Aminu Junior da Zaid, samari matasa da suka fi ɗaukar lokaci a wajen gidan
basu damu da sabuwar mace, sun fi shagaltuwa da motocinsu da rayuwar club da Instagram.
Yara uku ƙanana—Sulaiman, Abbas, da Fadilasun fi sabawa da Halima suna zuwa ɗakinta
suna wasa da ita ta dinga yi musu wasan shanu da dabbobi da kida da rawa irin na ƙauye,
suna dariya kamar an saka musu annashuwa a zuciya tana ɓoye wannan zumunci da su domin
kada uwayensu su ji.
Matar biyu kuwa, Hajiyah Mariyah da Hajiyah Sabeerah, su ne abokan huldar Nafisa amma
Hajiyah Mariyah ce shaidaniya, mai haƙurin fitina da halin mugunta tana kallon Halima da
kyankyami, tana cewa:
“Wato wannan ƙaramar ‘yar Fulani ce ta zo mana da daddare? Allah ya sa ba za ta ja mana
Alhaji ba.”
Tun daga rana ta fara tsara yadda zata nunawa Halima cewa gidan ba da sauki ba ne. tana tura
mata ayyuka kamar ba matar aure ba: “ki share wancan, ki gyara kicin, ki tafi can ki goge
banɗaki.”
Halima kuwa, da jin kunyar Fulani da biyayya, sai ta dinga yi tana mika hannu da zuciya, ba tare
da kuka ko korafi ba inda Hasiya ta fi shiga tsakiya, tana mata nasiha da rarrashi:
“Ki yi haƙuri Halima, nan ne birni idan kika nuna rashin juriya, sai su hana ki kwanciyar hankali
amma Allah yana tare da mai gaskiya.”
A haka Hajiyah Nafisa ta dinga kallon yadda Halima ke yi wa yara wasa, tana girki da kyau,
tana wanke-wanke da murmushi da farko tana kyamar ta, amma wata rana ta shigo dakin
Halima sai ta ganta tana dinki wa Fadila riga da hannu wani abu ya motsa a zuciyarta. Ta ce da
kanta: “Wannan yarinyar... ba ta da mugunta kuma girmanta yana shigowa hankali.”
Halima kuwa har yanzu bata san haka ba. zuciyarta na yawo ne da tambayoyi: “shin wannan
rayuwar ita ce rabona? ina mahaifina da mahaifiyata? W
wannan Alhaji Saminu fa, me yasa yake sona?
wani dalili ne yasa ya kawo ne gidan sa ya ajiye tsawon lokaci bai dawo garine ba?
Ohhhhhhhh ga Halima ga Abuja
a sannu a hankali zamu shiga labarin Halima
continued ƙanwar soja in Sha Allah
✍️
BAYAN WATA
AFTER THE MOON
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star
15 / 16
07/ 5/ 2025
Iskar hamada ta na kada yashi cikin karfi, tana fasa fuskokin su da ƙaƙƙarfar zafi gaban su babu
komai sai fure-furen duhu da tsayayyun ciyayi waɗanda rana ta ƙone su har sun bushe. kusan
ko motsi ba ya sake yi sai idan iskar ta kaɗa su kamar wasu fatalwun da ke kaɗa hannunsu don
ƙiran mutuwa.
Jiki duk jini, ruwan jiki ya bushe. Fuskarsa ta kumbura, leɓɓansa sun fashe saboda ƙishi da
rana dukansu suna daure cikin zafi da juna, Yazid ya ɗaga kai da wahala, yana wani tunani
kamar wani ɗan ruhi mai kaifin fahimta, ya fara rerawa da wata murya mai kauri wadda ke
ɗauke da ƙyamar wahala:
"Bayan wata...
bayan wata akwai haske
Bayan dare akwai rana
a duhun daji babu alheri,
a zuciya babu tsira..."
Waƙar ta ja kunnensu gaba ɗaya. Ihsan ta ɗan kai hannu ta shafi kafadarsa, Maryam ta
rungume ƙirjinta, tana kokarin hana kuka.
"ku shirya..." Maryam tace a hankali, murya kamar tana fitowa daga wani daki mai ƙyama. "Zan
baku labarin soyayya "
suka gyara zama, sun sha wahala, " amma labari na da ƙarfi fiye da na ihsan domin wanan
labarin soyayya da butulci cin amana da nishadi yana da matukar muhimmanci a yanayin da
muka tsinci kanmu "
Maryam ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tana kallon abubuwan da suka gabata a cikin
zuciyarta a yau, ta yanke shawarar cewa lokaci ya yi da za ta bayar da labarin soyayya. Labari
wanda ba kawai soyayya ba ne, har ma yana da cike da butulci, tausayi da ƙalubale, wannan
labarin yana da ban sha'awa, cike da nishadi, kuma yana dauke da darussa masu nauyi ga
wanda zai saurara “amma soyayya ba ta tsaya a nan ba,” Maryam ta ce, tana dariya. “duk da
haka, akwai abubuwan nishadi, da tausayi.
( Lokaci yayi da zamu shiga labari cikin labari Maryam zata bamu labari a cikin tafiyar su na
Bayan wata a inda aka mafarauta suka kama su ,suna tafiya dasu cikin wahala da zafin rana da
yunwa )..
RUGAR FULANI
Rugar tana cikin zurfin dajin Arewa maso gabas, cike da ciyayi kore-kore da ke motsawa cikin
sanyi na safe gidajen su cike da tsari na gargajiya, daga bukkoki masu rufi da itatuwa da kwari
na fulawoyi masu ƙanshi. a gefe akwai madugu mai fitowa daga tsauni, yana gangarowa zuwa
tabkin da shanun su ke zuwa kowane safe a cikin rugan ana jin karajin shanu, da waƙar kiwo da
yara ke rerawa, kowane gida na da kangon dabbobi, da inda matan gida ke nono da jujjuya
fura.
Sunanta Halima, kyakkyawa ce tamkar wata a tsakiyar dare idanunta farare ne masu zurfi, suna
ɗaukar hankali da kyalli mai launin kwayar gwal fuskarta farin fata ce kamar nonon shanu, tana
da dogon hanci da siraran leɓɓa gashinta baƙi ne da sheƙi, an nade shi cikin ɗamara ta Fulani
mai launin ja da zinariya tana sanye da zanne mai ɗinki na gargajiya, da ƙyarar kunne na
azurfa, da zobba masu sarkar ƙaho tana da shekaru goma sha biyar, amma hankalinta da
nutsuwarta sun fi na shekaru.
Halima tana da ƙwarewa wajen kiwon shanu, ta san kowanne suna, kuma tana iya busa algaita
da wake-waken daji da suka gada. Tana da natsuwa da ladabi, amma cikin zuciyarta akwai
mafarkin soyayya da birni, duk da tana jin kunyar faɗa ,a kullum tana kallo daga gefen ruga
tana mafarkin rayuwa mai zurfi, tana ɗora fatarta kan murya da waƙar wani saurayi da ya taɓa
tsayawa bakin tabki yana kallo duk da cewa bataye ilimin zamani ba amman tabass tana da
ilimin addini da ilimin sanin halayyar ɗan Adam
Kamar yadda kowacce shekara take kasancewa, haka wannan shekara ma ta zo da nata
alkawura ,daga nesa, ƙura ta fara tashi. Yara suka fara ƙwala ihu suna fadin:
"ga motar Alhaji! ga motar Alhaji!!"
Motoci biyu Honda guda fari da ɗaya baki suka bayyana cikin natsuwa, suna karasowa cikin
ƙauyen Gembo Saƙa-saƙan ƙura ke biye da su, kamar girgijen albarka. dun tsaya kai tsaye a
gaban bukkar Moddibbo, wanda shi ne babba kuma mai daraja a wannan yanki wata irin
lumana da nutsuwa ke lullube daƙalin gidan nasa, kamar yana jiran zuwan ɗan sarki.
Alhaji Saminu ya fito daga motar fari cikin dogon riga shadda mai launin zinariya, da rawanin da
ke sa hasken rana ya bayyana a goshinsa. Murmushin sa na cike da annuri, yana ɗaukar
zuciyar kowa da kallo kallonsa kaɗai na saka mutum jin kwanciyar hankali.
Moddibbo kuwa, ya fito da kansa daga cikin ɗakinsa, cikin natsuwa irin ta dattijo mai hangen
nesa. Suka runguma kamar ’yan
Moddibbo kuwa, ya fito da kansa daga cikin ɗakinsa, cikin natsuwa irin ta dattijo mai hangen
nesa. Suka runguma kamar ’yan uwa da suka jima ba su hadu ba. baiwa da mutunci sun
kasance tsakanin su tun shekaru goma da suka wuce — alaƙar da ba kuɗi ko matsayi ba ne ya
ɗaure, illa kirki, imani da gaskiya.
“Barka da zuwa, Alhaji,” Moddibbo ya furta cikin murya mai nauyin daraja.
“Lafiya lau, Moddibbo. Allah ya tabbatar da alheri kamar kullum,” Alhaji Saminu ya amsa da
ladabi.
Maza da yara sun fara taruwa a kofar gida, ana kallon motoci da murmushi, yayin da matasa ke
harhada shannaye daga gindin kuka da ke kusa da gona, domin Alhaji ya saba fita da kansa
yana zaɓar dabbobin da zai yanka domin hidimar Sallah ga iyalansa da maƙwabta.
Bayan doguwar gaisuwa ta mutunci da girmamawa tsakanin dattijan biyu, sai ga Halima yarinya
mai kyaun da ke bayyana a hankali kamar safiya mai sanyi ta fito da kwanon madara a
hannunta, fuskarta daɗaɗɗiya, idonta mai cike da nutsuwa, ta isa gaban baƙi cikin kamewa da
girmamawa.
"Assalamu alaikum," ta faɗa da siririyar murya
"Wa alaikumus salam," Alhaji Saminu da Moddibbo suka amsa a tare, suna kallonta.
Alhaji Saminu ya karɓi madarar hannunta, yana dubanta cikin ido da murmushi da ke ɓoye wani
sirri mai zurfi. Halima ta sunkuyar da kanta, tana juyawa cikin girmamawa kamar yadda aka
koya mata.
Bayan ta shige ciki, Alhaji Saminu ya ɗan juyar da kallonsa zuwa ga abokin zamansa.
"Moddibbo... shekarun Halima sun cika goma sha biyar yanzu, ko ba haka ba?"
Moddibbo ya gyara zamansa, ya ɗan sosa gemunsa yana murmushi mara kyar.
"Eh, haka ne. shekaru goma sha biyar rabon da ka min wannan alkawarin."
Alhaji ya lumshe ido. "Na tuna sosai ka ce Halima zata zamo matata, kuma kai da kanka zaka
miƙa min ita ranar da ta kai munzalin aure."
Moddibbo ya ɗan sauke ajiyar zuciya, yana kallon ƙasa.
"Ka sani Alhaji... ban taɓa mantawa da alkawarin nan ba. kuma na tsaya akan shi har yau
saboda girmanka da darajarka a idona. Amma fa mutane sun fara tambaya, sun fara zargi...
wasu na cewa wai ni na hana Halima aure saboda son zuciya wasu ma na ganin kamar ina
fuskantar matsin lamba daga wani ɓangare."
Alhaji Saminu ya ɗan sunkuyar da kai, muryarsa na nuna laushi da tausayawa.
"Moddibbo... ka sani Halima tana da muhimmanci a gareni fiye da yadda za a iya fassarawa da
baki amma idan hakan zai cutar da mutuncinka ko na yarinyar... sai mu sake duba hanyar da za
a bi cikin adalci da amana."
Moddibbo ya ɗan kalli tsohon abokinsa, yana girgiza kai da murmushi mai ɗan nauyi.
"Alhaji, ni dai ba zan karya alkawari ba kuma Halima ma ta san da cewa tana da wani babban
makoma da muke jiran lokaci ina so a kyautata komai cikin tsari da girmamawa... da zarar ka ce
lokaci yayi—ni a shirye nake."
Alhaji Saminu ya ɗaga kai, idonsa na ɗauke da abu fiye da kalmomi.
"To lokaci yayi, Moddibbo kuma Halima zata dawo gareni—amma ba kawai a matsayin amarya
ba, a matsayin amanar da zan ci gaba da kulawa da ita kamar zinariya mai tsarki."
Get ready fans ga Halima ga Alhaji Saminu menene abinda wannan gajeren labarin Maryam ya
ƙunsa , let's go..........
https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y
BAYAN WATA
AFTER THE MOON
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star
15 / 16
08 / 5/ 2025
Kamar yadda aka saba duk shekara, Alhaji Saminu bai taɓa yin ƙasa a guiwa ba wajen nuna
ɗimbin darajarsa a idon mutanen ƙauyen Gembò amma wannan karon daban ne. wannan karon
ba kawai don shanaye ya zo ba ya zo ɗaukar amana.
A gaban Moddibbo da wasu dattawan gari guda biyu, Alhaji Saminu ya fito da sadakin Halima.
kudi ne masu yawan da fulani ba su fiye gani ba a lokaci guda baya ga hakan, ya kawo 'yan
dabbobi da kayan gyaran amarya, tare da alkawarin dawowa bayan Sallah da sati biyu—kai
tsaye daga birnin Tarayya Abuja inda matarsa ke zaune.
Moddibbo ya karɓi sadakin cikin nutsuwa da girma ya san me hakan ke nufi: yanzu Halima zata
koma karkashin Alhaji Saminu amma ko da yake zuciyarsa na cike da nauyin amana, bai nuna
ba, saboda a rayuwa irin tasu, alƙawari tamkar doka ne da ba za a karya ba.
Halima kuwa... ta zauna a gefen mahaifinta da cike da kunya, fuska a kasa kamar yadda aka
koya mata, duk da cewa an ba ta labarin cewa rayuwar birni ce zata zame mata gaba, kuma
Alhaji Saminu mutum ne mai arziki da daraja—amma a zuciyarta babu motsin soyayya ko ɗokin
aure.
Zuciyarta tamkar fili ne, babu shuka, babu furanni kawai akwai wata siririyar lafazi da take
maimaitawa a ranta:
"Na yarda da mahaifina na amince da kaddara. kuma zan bi Alhaji Saminu, ko da zuciyata ba ta
motsa ba."
Irin wannan biyayya ce da ta sa ta karɓi sadakin da lafazi guda biyu:
“Na yarda.”
Moddibbo kuwa kamar kowa yana ganin yana murna amma shi da zuciyarsa sun san gaskiya ,
ya san Halima ba ta kai matsayin aure ba tukuna ta girma da sauri, amma zuciyarta har yanzu
karama ce, tamkar macen da bata fara sanin al'amuran soyayya ba.
Sai dai kuma, Moddibbo mutum ne mai daraja da mutunci ya rike amanar Alhaji Saminu fiye da
yadda wasu ke rike 'ya'yansu. Yana fatan Alhaji Saminu zai kare martaba da tsaron Halima
kamar yadda ya rike alkawari na shekaru goma sha biyar.
Wani iska ya buso daga arewa, ya kada ganyen kuka da ke bakin ruga Halima ta lumshe ido,
tana jin iskar kamar wata alama ce daga sama ko soyayya zata zo daga baya? ko kuwa hakan
nan ne rayuwa ta rubuce mata?
Bayan sati biyu da cikar alkawari, ƙauyen Gembò ya sake fuskantar wata rana da ba za a taɓa
mantawa da ita ba rana ce da komai ya sauya—rana da tarihi ya ƙara rubutun zinariya cikin
ƙwarya mai ƙyalli.
A safiyar ranar asabar, tun ƙarfe tara da mintuna goma, sai ga jere-jeren motoci guda shida
masu sheƙi da ƙyalli irin wanda bai saba zuwa ƙauyen ba, motoci ne kirar Lexus LX 570 guda
biyu, guda bakar fata, guda kuma fari ɗan haske mai cike da adon zinariya. Sauran kuwa
motoci ne kirar Hilux da Toyota Highlander, dukkansu cike da kaya, kujerun zamani, manyan
jakunkuna da akwatuna masu lulluɓe da furen ado da yajin rawaya.
A wata ƙaramar Prado, wanda aka ɗora babban laifan jajjayen furanni da tutar Kaunar aure,
Alhaji Saminu ne ya fito sanye da babban ɗan-baban Shadda mai launin zinariya da ruwan
hoda , babbar hula ce ta fulani bisa kansa, mai ɗinki na musamman da adon sarka fitarsa daga
mota ta sa yara suka yi tsalle, mata suka fara cewa:
“Ga angonmu ya iso! Allah ya sa a dace!”