Showing 1 words to 3000 words out of 28842 words

Chapter 1 - BAYAN WATA BOOK ONE BY NARNAH KANWAR SOJA .pdf

20 May 2025

2324

BAYAN WATA
AFTER THE MOON


BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA




SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star








GABATARWA

Wanan Labarin zai fara zuwa muku Ranar Litinin da yardar Allah shafin shine asalin gundarin
labarin matafiya ne wanda suka bar kasar su zuwa wata ƙasa domin muradun su, a sannan
labarin ne cikin labari domin dukkanin su zasu bamu labari mabanbanta daga cikin tafiyar su
sanin haƙiƙanin labarin lallai sun mun shiga ciki domin karatu tare....

Masu laɓe a cikin group wanan sabon littafi ku fitoo kafin ayi waje daku fatan zaku na sharhi da
share Nagode..






Chapter 1 & 2
Tafiya Mabuɗin ilimi






مسب الله نمحرلا ميحرلا
مهللا لص ىلع دمحم ملسو




Ƙara duba email nasa yayi nan John ya dafa kafaɗar sa " Common man muna late fa " ajiyar
zuciya ya sauke mai nauyin gaske cikin tunani tsarin ɓarauniyar hanyar da zasu bi daga Kano
zuwa Dubai cikin kwana 150
Addu'a suka fara bayan kammala wa motar tasu ta zubin taxi ya tashe da matuƙar gudu
Duk wani abun buƙatar su na abinci kuɗi sutura tare da abun bukatar su na yau da gobe yana
cikin wannan motar
Hannu tasa tana lissafi cikin buguwar zuciya




" Kano (Nigeria) Yobe → Chad → Libya → Egypt → Israel → Jordan → Saudi Arabia → United
Arab Emirates (Dubai)
Yanzu wanan ƙasasshen dukka sai mun tsallake su Innallilahi wai'na illaihin rajiuon " take
hawaye ya fara zubuwa a idon ta, harara Maryam ta buga mata " Haba Ihsan meyasa kina da
saurin kuka ne tafiya ce kawai duk da munsan akwai wahala a hanyar mu amman ai muna tare
ke tuna buri da muke dashi a rayuwar mu idan bamubar Nigeria ba ina zake samu bukatar aikin

da muke so " ..


Tunda suke magana Yazid na latsa wayar sa wanda yake buga game nasa cikin nishadi sosai


Yazid ,
Yaro ne mai shekaru 25 a rayuwar sa ya gama makarantar secondary school sai dai yana da
Babban buri a rayuwar sa ma buɗe katafaren Company gine gine hakan yasa ya yanke
shawarar zuwa ƙasar Dubai inda suka samu labarin ana zuwa neman kuɗi sosai kuma ana
dace domin kuɗaɗen su mai matukar girgiza ruhin mai neman kuɗi da wanan niyyar ya baro
gida


Ihsan
Yarinya ce wacce take da shekaru ashirin a rayuwar ta sai dai ta tasu daga gidan marayu na
nan Kano tabbas Ihsan yarinya ce mai basira sosai ga kuma kyau da ilimi sai dai Ihsan yarinya
ce mai neman na kanta duk inda taga zata samu kuɗi tana zuwa neman aiki lungu da sako
Ihsan yanzu babban burin ta shine ta samu jari sosai wanda zata fara kasuwanci gari zuwa gari
har ma da ƙasasshen waje Amman yanzu dole sai ta tafe Dubai domin samun aiki ko na aikatau
ne domin cikkar muradun ta.....




John
Idan ana neman yaro mai karfe da fikira to John ya samu wanan shaidar babban abokin Yazid
kinan wanda suka ye makarantar tare sai dai shi ya samu aikin soja wanda aka Kore sa daga
aiki dalilin mugun ƙazafin da abokan sa suka masa shi kuwa ya yanke hukuncin baren ƙasar
domin ya tafe nemo kuɗi kodon huci takaice abinda aka masa .....



MARYAM
Kuna neman matsoraciyya yarinya ga tsoro ga rashin jin magana ga kuma taurin kai sai
Maryam wacce take da shekaru ashirin da ɗaya chifff Maryam ta tasu gaban muguwar kishiyar
uwa wacce sai abinda tace baban ta zaiyu hakan yasa take azabtar da Maryam ta kowani
yanayi kyakkyawan yarinya ce ga ilimi boko da na arabiyya sanan tayi karatun health care
ƙaramar nurse ce dalilin barin ta gida kuwa kishiyar uwarta ne ta yanke mata hukuncin auren
wani tsoho a unguwar sa wanda baban ta ya amince hakan yasa ta gudu tabar gidan sai gashi
ta haɗu da ƙawa a titti wato Ihsan wanan yasa ta yanke shawarar binsu chan ko ita ma zata
tsira da gujje gujje da take ye akan hanya ..

ADO
Engineer kinan saurayi mai shekaru ashirin da tara mai hazaƙa da basira baiye makarantar ba
sabo da tsananin talauci wa da bai san uwar sa ko uban sa ba a kan titti ya gansa yana tafiya
bashi da kowa ko komai Amman ko wacce mota ce ya iya gyara ta sanan ya iya duk wani
abinda ya shafe igiyar wuta, sanan ya taɓa shiga ƙasar Chad neman kuɗi a takaice dai Ado
yana cikin wanan sahun tafiyar domin yana da buri mai yawa a rayuwar sa ...












A haka suka kama hanyar Yobe state domin fara tafiya zuwa Chad, muna fatan tafiya yayi kyau
a dawo da cikakkiyar nasara...








Please don't forget to comment and share
Continued........
Narnah ƙanwar soja ✍️✍️


BAYAN WATA
AFTER THE MOON


BY
NARNAH KANWAR SOJA














Royal Star Association,
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na
marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister
Zahrah Royal Star

Page 1 & 2


Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba ,
mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya
show me some love guy's


مسب الله نمحرلا ميحرلا
مهللا لص ىلع دمحم ملسو




Zaman motar ya fara yi musu nauyi tun kafin su iso Yobe daga nan sai suka shiga ƙasar Chad
da yamma, rana ta fara dusashewa cikin baƙin gajimare da iska mai ɗauke da ƙura gaba ɗaya
zuciyar su ta fara karaya koda kuwa basu furta ba.


John ne ya fara gyara zaman sa yana duba agogon hannunsa.
"Wannan hanya wallahi kamar babu wanda ke bi ta yanzu," ya faɗa cikin ƙaramin murya
Maryam ta kama hannun Ihsan tana danne tsoro da karfin hali, "Mun riga mun fito, ai sai gaba."


Motar ta dinga kutsawa cikin kura da kankara, har aka kusa tsallaka wata ƙaramar kwazazzaba
da aka samu a tsakiyar duwatsu. wani ƙara mai firgita ya tashi daga motar.
"Grrrrkkk—krrr!"


Kafin su fahimta, tayar gaba ta tsinke da wani ƙarfi motar ta faɗi gefe kamar zata tintsire Yazid
ya damƙe sitiyari yana ƙoƙarin tsayar da ita amma komai ya gagara Ado ya rike bangon motar
yana fadin:
"ALLAHU AKBAR!"


Sai kawai suka ji "dduuummm!", motar ta buge da wata babbar dutse, ta tsaya cak anan ne
shiru ya biyo baya, babu motsi, sai sheshshekar Ihsan da Maryam suna kuka.


Yazid ya fito daga motar yana duba tayoyi, idanuwansa sun cika da 'kura. "tayar gaba da gefe

duk sun ƙone clutch ɗin ma ya tarwatse. muna cikin matsala mun rasa motar mu."


John ya farka daga karyewar da ya sha, ya dubi hanya yana shan iska mai zafi, sannan yace:
"Wannan ba hanya ba ce, wannan tabo ne. mu kwashe kayanmu mu shiga cikin dajin nan idan
muka tsaya nan dare zai riske mu, barayi ko dabbobi za su iya far wa."


Babu wanda ya musa kowa ya ɗauki nashi kaya cikin tsoro da damuwa. Ihsan na riƙe da
kwalbar ruwa, Maryam na lulluɓe da veil tana kare jikinta daga cizo.sun fara takawa cikin ƙaton
daji, cike da raɗaɗin ƙasa mai kaifi da ciyayi masu yankan ƙafa Ado na gaba yana amfani da
torchlight wayarsa yana duba hanyar da zasu bi tsakar dare ne lokacin da suka hango wani
tsohon baranda kamar dafa-gari. ba za a iya ce masa gida ba, amma yana da rufi da bango.


"Mu tsaya nan mu huta. Allah ya kawo safiya lafiya," Yazid ya faɗa.
Maryam ta kifa kanta a kafadar Ihsan, tana kuka cikin salo mai ciwo, "Idan na mutu a hanya ki
ba baba sanina... ki ce Maryam ba ta jure tsanani ba." John ya dan murmusa cikin firgici, "Zamu
mutu fa kafin mu isa Dubai idan muke tsoron hanya haka tun a Chad."a haka dare ya cigaba da
raguwa, zafin rana ya mayar da dare sanyi mai shigowa jiki kowa ya kwanta da kaya a jikinsa
yana jiran asuba da fata, da addu’a, da fargaba.




Dare ya yi tsayin gaske kamar zai hana wayewar gari ,sanyi ya ratsa kowane sassa na jikinsu,
kowane yana neman ɗan nutsuwa da kwanciyar hankali, amma babu shi.
sai dai ƙasa mai kaifi da raɗaɗin tunani.


Asuba na ƙaratowa, Ado ya farkar da su ɗaya bayan ɗaya.
"Ku tashi, lokaci yayi... sai mu yi sallah kafin rana ta fito."


Sun fito daga barandar ruwan zufa da ƙura na hade da jikinsu. kowa ya shimfiɗa ɗan zane a
ƙasa, suka gabatar da sallah da natsuwa da ƙasƙantar da kai. bayan sun idar, Yazid ya zaro
ɗan kwali daga cikin jakarsa.


"Ga ruwa nan da snacks ɗin biscuit da gurasa. Amma sai mu kiyaye amfani da su, ba mu san
inda zamu isa da kafafu ba."

Ihsan ta amsa kwalbar ruwa tana goge fuskarta da tissue, Maryam na gefenta, kukan jiya ya bar
wani ɗan kumburi a idonta.


"Da gaske zamu ci gaba da tafiya ne?" Ta faɗa da rauni.
"Me kike tunani?" John ya juyo yana gyara jakarta. "Za mu jira motar da ba za ta zo ba? Ko
barayi su zo su kwashe mu da kaya?"
hka suka kammala shiryawa, suka kwashe komai da suka iya dauka akwai leda mai ɗauke da
tuwo da miya wanda suka saya kafin shiga Chad, ruwan robobi guda shida, da wasu kuɗaɗen
kasar da suka musanya kafin barin Nigeria.


Ado ya latsa map ɗin da ya saukar a waya, duk da babu signal sosai, yana ƙoƙarin duba hanya
mafi kusa da wata rijiya ko gari “wannan hanyar zata kaisu cikin wata ciyawa mai tsayi—amma
akwai wata ma'boyar ruwa da nake tunawa da ita daga lokacin da na taba zuwa Chad.”sai suka
kama hanya, dajin yana cike da tsuntsaye masu shewa, ƙasasshiyar ƙasa na sa ƙafafunsu
zubar da gajiya. Ciyayi na yanka ƙafafun su, ganyaye na goce su a fuska.


Yazid ya riƙe jakar abinci yana gaba, John na gefe yana duba kowane motsi, kamar soja na
sahun fama. Maryam na tsakiyar Ihsan da Ado, amma ita ce ta fi fitar da kuka.


"Gsky, idan Dubai ne zai kashe mu haka, to wallahi zan koma gida."
"To sai a auri tsoho, ko?" Ihsan ta harare ta cikin dariya mai taɓarɓarewa.
Maryam ta kyalkyale da dariya cikin hawaye" ke Ihsan wallahi da aure Baba audu gwanda na
mutu a hanyar nan"


Sun dauki kusan awa biyu suna tafiya cikin daji kafin suka kai ga wani tabo mai ɗan sanyi,
kamar ruwan fanfo ya ƙyalƙyala sama, suka zauna a can suka sha ruwa suka ci ɗan abu.
Yazid ya duba agogon sa. "Zamu ci gaba da tafiya bayan minti talatin... don kada rana ta fara
zafi mu gaji."


Cikin wannan rana, sun fara fahimtar cewa tafiyar nan ba zango ba ce, ba yawon shaƙatawa ba
ce hanya ce ta ƙalubale da jarumta, da fahimtar juna. Kuma suna cikin ita....




Garin da suka zauna sun ɗan ji sanyi da natsuwa bai kai awa biyu ba, sai ga wani ƙara ya
karad'e sararin samaniya. wani irin hadari ne ke tasowa daga gabashin jeji, ganye na yaye

sama, ciyayi na karyewa, iska na tashi da kura mai kauri "Na shiga uku! wannan fa kamar
guguwar jeji ce!" Ado ya faɗa yana rintse ido "Ku tattara kayan nan! Ku kamo jakunkunan ku!"
Yazid ya ɗaga murya.


Cikin daƙilewar lokaci suka fara tattare kayan su, Maryam ta faɗi jakar ruwa, sai kuma aka jiyo
busa kamar karar motar iska tana fashewa wata bishiya ta karye tana gangarowa da sauri!
John ya ɗago Maryam da sauri suka fice daga wajen,kowa ya rikice.ƙasa ta ɗan girgiza, sai
ƙara da kuma wata shanya mai ɗauke da ganye da ƙasa ta tashi ta rufe hanya.


"Wayyo Allah na! kayi mana sauƙi!" Ihsan ta yi ihu.


Kowa da nashi, sai suka gudu sun rarrabu kadan, amma a ƙarshe suka taru bayan sun kusan
rasa juna. tafe suke da keɓaɓɓen numfashi, zuciya cike da tsoro da gajiya, bayan tafiya mai
nisa da hawan ƙasa da tsallake kwari, sai suka hangi wani ƙauye a can gefe da daji. wurin
tamkar ya zauna a gaban dutse ne, akwai ɗan ruwa yana kwarara daga wani ƙanƙanin dutse.

Ado ya saki numfashi. "Wannan tamkar lahira muka tsira daga ciki muka dawo duniya ne
wallahi."Yazid ya yi dariya. "Kai dai karka fara wahalar da mu da falsafa yanzu shin ka taɓa
zuwa lahira ne."
Ihsan ta tura masa kafa, "Wai yanzu ni dai idan na nitsu zan rubutta wanan hargitsen cikin
wannan littafin domin tarihi sai na rubuta wani Irin Jeji da na shiga."suka tafi da dariya, duk da
gajiya ta cika jiki.


Sun isa ƙauyen, mutanen gari suka karɓe su da jinkai, suna ba su ruwa da wuri su huta. Sun
zauna suka ci abu kaɗan, suka kwanta ƙarƙashin inuwa, Ihsan na kwance a gefe ta ce, "Wallahi
idan na isa Dubai, zan fara kasuwancin ganyen magarya na gaji da dogon buri."dariyar su
tashi, kowa ya ƙwalla dariya mai sa hawayen idanu.

Bayan hutu da shan ruwa, suka sake tashi da niyyar cigaba da tafiya gobe da safe. kamar ba
suba, suna dariya, suna kwance da juna kamar ƴan uwa, daga cikin hargitsi da wahala, nishad'i
ya fara zame musu masoyi.


Kwanaki sun shige suna lissafa wa cikin jeji da ƙasa marar alamar birni, bayan haɗari da suka
fuskanta, motar su ta hantsila a ƙasar Jamhuriyar Chad, suka kasa gyara ta, sai suka bar ta can
da ƙyallen tarihi suka fara tafe da ƙafa, kamar masu hijira daga duniya zuwa mafarki.tun daga
lokacin ne suka soma 'kulla wani ɗaurewa da ba wai jinƙai kaɗai ba, amma kamar ana zuba

wani zuma a zukatansu, suka zama kamar ƴan uwa da aka haifa daga ciki guda.


Maryam, mai natsuwa da laushin murya, ita ce jinyar jikin su duk sanda ciwon tafiya ya kama
daya, za ta tsaya ta fidda ƙananan kayan asibiti daga cikin jakar matafiyar ta—ta fiddo da tawul,
ta sha da ruwa, ta gyara bandage. Ita ce ta fi sanin yadda ake shafe jiki da ganyen da suka ci
karo da shi a hanya domin rage raɗaɗi.

Ihsan kuwa ta fara zama ƙawarta ta gaskiya. su biyu idan suka haɗu sai dariya da tsokana,
suna ƙoƙarin mantar da sauran wahala. Ihsan da bakinta mai ɗaukar dariya, ita ce ke ba su
nishadi, tare da Yazid wanda kullum da sabuwar waka a bakinsa. Yazid na iya busa leda da
furar baki har kowa ya manta da gajiyar tafiya.

John, babban mutumin da ke ɗauke da baƙin laya a wuyansa, shi ke gaba da su a koda yaushe
ƙarfin jikinsa da jajircewarsa ke kare su daga tsoron jeji da dabbobi. Idan dare ya fado, John ne
ke ɗebo itace, yana hura wuta, yana saka su su ji kamar gida suke ciki.


Ado, ƙwararren masanin hanya, shi ke tsara hanya. Duk sanda suka tsaya yana fiddo taswira
ko yana duba taurari da rana don sanin gabas da yamma,baya cika surutu, amma idan ya buɗe
baki, kalmarsa zata zama haske.


A daren da abinci ya ƙare, sukayi shiru gaba ɗaya. ba kowa da bakin magana sai ƙarar cikin da
ke ɗaukar wululu. Maryam ta rufe idonta da ƙirjinta, tana share hawayen da ba kowa ya gani ba.
zai dai Ihsan ta ɗan matsa kusa da Yazid, suka fara raira waka:


"A cikin duhu akwai fata,
A cikin yunwa akwai madara,
Rana ta fito daga bayan wata..."


John ya sa dariya, ya ce:
"Kun sani, idan muka tsira daga wannan tafiyar, zaku fi daraja fiye da zinariya a gare ni."


Ado ya duba sama, yana murmushi da ƙyamshi, sannan ya ce:
"Idan muka kai Libya lafiya, zan gaya muku sirrin da ya sa na bar gida."

John ya ɗago kansa, ya ce:
"To, mu haɗa zuciyarmu." suka kama tare da muryar da ke daɗi ga kunne, duk da gajiya da
yunwa, suka rera:


Bayan wata akwai dare,
Bayan dare akwai haske,
Bayan yunwa akwai cika,
Bayan hawaye akwai dariya.


Idan rana ta ɓuya,
Mun san wata zai leƙo,
Idan hanya ta dushe,
Mun san ƙafafunmu zasu kai.


Bamu daina ba, bamu ja baya ba,
Zamu cigaba har gobe ta zo.
Mu da juna, zuciya ɗaya,
Rana ta fito daga bayan wata"…


Yayinda suka rufe baitin ƙarshe, wutar da John ya kunna ta ƙara walƙiya, kamar yadda wata ke
ɗaukaka cikin dare.


Tun daga wannan daren, wannan waƙa ta zama taken tafiyarsu duk sanda sun gaji, ko dare ya
musu tsayi, ko cikin su ya fara kuka, sai daya daga cikinsu ya fara:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login