Showing 18001 words to 21000 words out of 49670 words

Chapter 7 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf

07 Apr 2025

2336

da ta ajiye asusun da take tara ɗan ribar awara da kuɗin da
tabawa Alhaji Mamman yaki karɓa tasaka ciki gudun kada ta kashe,
ta fasa asusun hannunta na rawa tashiga kirga kuɗin data ciro cikin asusun,
naira dubu shida da ɗari biyar ne kacal.
cikin matukar damuwa da tashin hankali tarika juya kuɗin a hannunta wan da bai kai ko rabin
kuɗin da ake bukata a asibiti ba.
da sauri ta fita tashiga gidan makotan su bayan sun gai sa da
Kulu mai masa Kulu tace
"Gagurin zama Mama mai awara".
Mama tace
"A'a Kulu banga ta zama ba HAMDAH na asibiti za'a yi mata aiki da ma aron kuɗi nazo ki bani
ko na masa ne dan Allah,
wlh yanzu haka ni ake jira bazata iya haihuwa da kan taba dole sai amma ta aiki kuma sunce
cikin gaggawa in ba haka ba za'a iya rasa aɗaya a cikin su ko ɗan ko ita,in sha Allahu zan biya
ki bayan suna".
"Capɗi jan".
Kulu ta faɗa tana rike haɓa kana ta cigaba da faɗin
"Ikon Allah haihuwar dai tazo da gardama kenan,
wlh kin gan ni da mayafi a ka gidan mai shinkafa zani wlh tun shekaran jiya take tamin sintiri
yau kuwa da sassafe ita ta tashe ni tun ban ɗaura kaskon suya ba yanzu haka kuɗin ta zan kai
mata."
cikin matukar damuwa Mama tace
"Dan Allah in kina da wani kuɗin ki taimaka ki ara min

kokuma ki siyi wake na kici gaba da yin awarar kafin a sallame mu".
tace "Wlh sisi bani da shi in ba wannan dubun ba".
taciro gudan dubu daga bakin zanin ta ta nuna mata.
sannan ta cigaba da faɗin
"To kikira mijin ta mana ko a dajin sambisa yake ai zai iya turo kuɗin da za'ayiwa matar sa ai ki,
abu na waya yanzu kai yawaye duk duniyar da yake idan ya tura zai iso, yaushe zaki zauna
baiwa kanki wuya kune irin iyayen da kuke baiwa mazajen ƴaƴan ku kofar kin yiwa matansu
jinya, har yaushe zaki zauna baiwa kanki wuya bayan yana nan da ransa". da sauri Mama ta juya bata kuma cewa komai ba saboda sabar tashin hankali bata ma fahimtar
me take faɗa,
tana fita gidan wata dillaliya tatafi,tace tazo
tasiyi katifar ta.
dillaliyar tace taje zatazo gobe da safe,
Mama
tace
"Dan Allah ki tai maka kizo muje yanzu wlh ƴata ce ke asibiti".

Tare suka taho gida da dillaliyar,
dillaliya ta kalli katifar da ke cikin ɗakin Mama tace
"Nawa kika masa kuɗi".
Mama tace
"To dai kin ga katifar sabuwa ce bataji jiki ba ban jima da siyan sa ba wlh naira dubu 27 na siya
amma yanzu nawa zaki siya?".
dillaliya ta kuma dudduba katifar da kyau kana tace
"Na siye shi dubu 8".
Da sauri Mama tace
"Haba ke kuwa dubu 8 gaskiya bazan sai da shi haka ba ki kara dai".
fuska matar ta yaguna sannan tace
"Shi yasa bana son zuwa gidan mutum yin ciniki sabo da bana son dogon ciniki karshe kuma na
ɓata kafata a iska,
to ni gaskiyar in da zan iya siyan katifar nan dubu 10 in yayi miki to duk sabon tar sa ai yazama
na hanu,
sannan kuma zaki bada kuɗin wan da zan nima ya kai min gida".
Mama tace
"Gaskiya katifar nan yafi haka kodun halin da nake ciki yaci kiduba lamarin kigani".
tafiya dillaliya tasoma tana faɗin
"To shi kenan kya iya nemo wata ta siya nidai daga kan dubu goma babu kari yo ribar nawa
zanci ajikin sa".
shiru Mama tayi tana juya lamarin cikin matukar damuwa da tashin hankali.
taduba gabas ta duba yamma batada wata mafita,da yarage ta sai da mata haka bata da in da
zata sami kuɗaɗen da ake nima a asibiti bata dasu bata da dalilin su,
ganin tana kokarin fita a ɗakin da sauri tace
"To ki bada hakan".

Nan dillaliya ta caske dubu goma ta bata da fari tace zata cire naira ɗari uku acikin kuɗin ta bai
wa ɗan dakon da zai kai mata katifar gida,
Mama tace dan Allah tai maka kada ta cire ko sisi cikin kuɗin ta bita bashi zata bata...

Kuɗin mama ta haɗa da wan da ta ciro a asusu yazamo dubu shashida da ɗari biyar,
ɗakin ta bi da kallo babu wani abun da zata kuma ɗagawa ta siyar wan da zai bata ko da dubu 2
ne bare yacikita ragowar kuɗin,dama katifar ce kaɗai a cikin ɗakin sai ɗan tarkacen ta da ayan
zu take ganin basu da amfani tun da bazata sai dasu su kawo mata kuɗi ba.
numfashi ta sauke gaba ɗaya hankalin ta na asibiti da halin da HAMDAH take ciki, tasan tana
can tana kan shan azaba.
da sauri ta fita ta nufi gidan Malam Musa mai maganin maciji dan suna mutun ci dasu sosai a
tsakar gida da sami Zainabu matar malam musa tana al'walan sarllar isha,
bayan sun gaisa
Zainabu ta ɗan yi dari tace
"Mama mai awara kin biyo bashin awar ki na shekaran jiya ko? kin ga Wlh kwata-kwata na
mance da naci bashin awara sai da na ganki na tuno".
Mama tace
"Wlh Ni ba abun da ya kawo ni ba kenan ai nima na mance da ma kin siyi awara,
rancen kuɗi nazo kibani HAMDAH na asibiti za'a yi mata ai ki,kuɗin hanuna basu kai wan da
ake nima a asibiti ba dan Allah ki ranta min bayan suna in sha Allahu zan biya ki".
salati Zainabu ta saka tamike tsaye tana faɗin
"Subhalallahi ayya HAMDAH yan da haihuwar yazo mata kenan Allah sarki yanzu an yi ai
kinne?".
Mama tace
"A'a ni ake jira nakai kuɗin yanzu sai a mata".
da sauri Zainabu ta shige ɗaki tana faɗin
"Ikon Allah Allah yabamu da sauki".
tafito rike da kuɗi ta mikawa mama tace
"Wlh iyakacin arzikina kenan ɗaka da waje wannan dubu huɗun gashi malam yafita bare musa
ran samun wani abu a gurin shi duk da dai shima naji yau yana kokawa".
Mama ta amshi kuɗin tare da faɗin
"Wlh hakan ma na gode zan haɗa dana hanuna na kai musu suyi mata ai kin kafin gobe na
nemo musu cikon".
tajuya da sauri tanufi kofa, Zainabu tabita da addu'a da fatan Allah yasa a yi ai kin a sa'a...

Gida ta koma ta ɗauki laidar kayan jariri da take siya da ɗai-ɗai tana ajiye wa idan HAMDAH ta
haihu za'asawa abun da ta haifa har na kwana bakwai,wato kala bakwai kenan kayane irin wan
da mace da na miji zasu iya sawa,da ɗan sauran kayakin bukatu na jariri a talakance.
tafito ta tari abun hawa tanufi asibitin.
ko da ta isa
ta kai musu kuɗin ta rokesu da Allah kan suyi mata ai kin idan Allah yakai rai gobe zata kawo
musu ciko.

Nan suke sanar mata ai ammayi mata CS ɗin sabo da ganin rayuwar ta da abun da ke cikin ta
suna cikin haɗari.
wasu nurse's ne guda biyu suka iso in da su Mama suke tsaye da ɗaya daga cikin Dr ɗin da
sukayi wa HAMDAH CS,
ɗaya daga cikin nurse ɗin tadubi mama tace
"Tun ɗazu muketa nemanki Ina kayan babys da sauri mama tamika musu ledan dake hannunta
su shige labour room domin su kimtsa babyn.
Mama ta dubi Dr tace
"Likita ya ita mai jegon dai?".
Dr ta juya tashige room ɗin dake gefe da labour room tana faɗin
"Babu komai in sha Allah har an fito da ita ma tana wannan room ɗin".
wuf Mama tayi zatabi bayan ta tayi saurin cewa
"A'a tsaya tukun akwai likitoci a kanta suna ai kin su bari su gama tukun".
tafaɗa tana shigewa cikin room ɗin.
ajiyar zuciya Mama ta sauke tanayiwa Allah godiya,
taja gefe ta tsaya idanunta akan kofar da akace HAMDAH na ciki.


Bayan wasu ƴan mintuna likitoci'n suka fito Mama na ganin da sauri ta matso in da suke tana
tambayar su ya jikin nata,
sukace zata iya shiga yanzu.
cikin hanzari ta juyo zata shiga cikin room ɗin tajiyo Muryar nurse's ɗin da suka karɓi kayan
jariri suna faɗin
"Yauwa mun gama ga baby's ɗin".
da sauri ta juyo da mamaki take kallon nurse's ɗin dukan su rike da baby,
sai tasa hannu takarbi guda daya na hannun wacce take kusa da ita tajuya zata wuce,
sai ɗayan nurse din tace
"Baki da me taimaka miki ne ga ɗayan fa,
ko kin bar min ne".
tafaɗa tana murmushi ɗayar tace
"Ai kuwa nima yaran sun tafi da ni Wlh ni ban taɓa gyara kyawawan baby twin's irin waɗan nan
ba kallesu fa wlh ko ƴaƴan turawa bazasu nuna musu komai ba kai ni sai nagama sunfi min
ƴaƴan turawan".
da maki Mama ke kallon su da jin abun da suke faɗa
tace
"Kuna nufin yanbiyu ne ta haifa duka waɗan nan ƴaƴan ta ne?".
tayi maganar cikin matukar mamaki.
dariya sukayi mata ganin yanda take maganar bilhakki,
Nurse ɗin ta mika mata ɗaya babyn tana faɗin
"Duk natane,yauwa na mijin shi aka fara cirowa kafin macen".
rungumar yaran mama tayi a kowani hannunta guda tajuya cikin tsananin farin ciki har da kwalla
tanafadin "Alhamdullilahi Allah mun gode maka".
cikin hanzari tashige dakin da aka kai HAMDAH.

dasauri takarasa inda take kwance da yaran a hannunta tana fadin
"HAMDAH bude idon ki kiga abin da kika haifa".
jin Muryar mama yasani buɗe idanuna a hankali,
asannu nashiga juya kai na saiji nayi kamar an ɗaɗɗaure ni,
dasauri mama tamatso kusada ni ta ajiye yaran dake rike a hannunta a gefe na,tana cigaba da
faɗin
"Allah mai iko kai sannu HAMDAH sannu kinji".
asannu najuyo kaina da kyar kallon yaran da mama ta ajiye a gefe na nayi kana daƙyar nabude
baki murya can kasa nace
"Mama waƴannan yaranfa?".
sai da ta maso sosai kafin ta iya jin abun da nake faɗa,
fuska ɗauke da yelwataccen murmushi tace
"Dukkansu nakine".
cikin tsananin farin ciki da murna Mama ta ɗago ɗaya daga cikin yaran ta karkato shi saitin
fuskanta
tana faɗin
"Kalli kyakkyawar mai gidan nan nawa
da sukayi ta baki wuya,ga kawata ma nan".
ido na kurawa jaririn yayin da naji wani irin mummunar faɗuwan gaba ya ziyarci zuciyata,
fuskar Ya SALEEM kaɗai nake hangowa kan fuskar jaririn,
idanuna na rumtse da karfi tare da kuma buɗe shi kan fuskar jaririn,
mai mugun kama da Ya SALEEM tamkar an tsaga kara.

Mama ta mai da yaron ta kwantar ta ɗago ɗayar tana faɗin
"Ga kawata nan tabar kallah masha Allah".
hancin babyn ta lakata tana washe baki da cigaba da faɗin
"Ikon Allah wannan girman ciki yayi yawa ashe dai kune kuka baje ciki".
kai na na rausayar gefe da kyar,
jin wasu zafafan hawaye sun zubo min kokarin danne zuciya ta daketa son fama min mikin
dake cikin ta nake,
rumtse idanuna da karfi nayi duk yan da naso danne zuciya ta sai da na tuno.
fahimtar yanayin da na shiga yasa Mama tayi ta jana da hira duk da bana ammsa mata da ido
kawai nake binta.
haka tayita kokarin gusar min da damuwar da take hangoshi cikin idona,
har sai da taga na saki raina,
har naɗan juyo da kaina ina kallon yaran,
Allah mai girma da ɗauka wai duk waɗan nan ƴaƴan a cikina a ka ciro su.


Mommyn twins ce

Ranan Azaune mama ta kwana rike kuma da yaran idan ɗaya yayi motsi sai ta aje na hannunta
taɗau ki ɗayan,
duk san da na farka sai na ganta zaune tausayin ta yakama ni,
na tabbata tun da rana dana fara labour batasa komai a bakinta ba har kuma yanzu, domin
gabakinta abushe,
haka tayi-tayi dayaran har gari yawaye.
washegari da safe
Zainabu suka zo da ita da wata makociyar Mama,sukazo mana da abun karyawa niki-niki.
suna rike da yaran a hannunsu kowa sai sanbar ka yake,
Zaunabu data kurawa ƴa macen ido tace
"Oh ikon Allah jibi waɗan nan yara wazai gansu yace tagwaye yara katin-katin dasu kamar
haihuwar ɗaya,
kai sannu HAMDAH gaskiya kinyi kokari waɗan nan kam ai sai dai CS ɗin".
murmushi matar da sukazo da ita tayi tace
"Wlh kam yara tabar kallah ga wayo ni dai tun zuwan mu idanun su abuɗe suke".
Mama tayi dariya tana faɗin
"Waɗan nan awaye kazan birni ai tun jiya idanunsu a buɗe yake suna jin motsi zasu juya ido
gun kamar masu jin magana,
kunga wannan bakyauyiyar kawar tawa idanunta a kan fanka, shi ko angon ido yakurawa kwan
wuta".
dariya duk suka saka ai kuwa sai yaran suka shiga raba ido kamar sun san me ake faɗa,
Zainabu tace
"Ai kuwa yaran akwai wayo ga yan da suke kokarin juya kai suna jin magana"...

Haka suka yi ta kallon yaran cikin ban sha'awa.
nan mukata hira dasu sai kusan azahar sukatafi.
mama ta rakasu tadawo tana dawowa daga rakiyarsu nadubeta cikin yanayin gajiya da
kwanciyar da tun jiya ban motsa daga in da aka kwantar da ni ba,
nace
"Mama dan Allah ki dagani nikam nagaji kokuma injuya gefe".
Mama tace
"Sunce bayanzu ba". dasaura nace
"To Mama kishin ruwa nakeji dan Allah kibani ruwa nasha".
dubana take cikin tausayawa da tsigar rarrashi tace
"Kiyi hakuri HAMDAH su sun fimu sanin dalilin da yasa suka ce kada a baki komai tun da ai kin
sune ki kara hakuri dan Allah kibari likitocin suzo tukun".
kai kawai najuya cikin gajiya da kwanciyar guri daya gamugun ƙishin ruwan da nakeji...
karfe
huɗu na yamma har lokacin ina nan kwance duk yadda naso Mama ta ɗagani ko taban ruwa
nasha fir taki.
kuka nasaka mata ina faɗin
"Ni dai nagaji nagaji ƙishin ruwa nake ji".
Ido Mama ta zuba min tana jijjiga baby boy ɗin dake ta zandara ihu tun ɗazu,ta bashi ruwa yafi

a kirga da zaran ta cire fida a bakin sa sai ya sa kuka.
Ana cikin haka sai ga ɗaya daga cikin
Doctors ɗin da sukayi min CS yashigo,
yace
"Mama mai kikayi wa pationt din mu ne haka take kuka".
yafaɗa da murmushi yana karaso wa bakin gadon da nake,
Mama tace
"Wallahi tuntini wai so take a ɗaga ta tagaji kuma wai kishin ruwa take ji shine nace tayi haƙuri
sai kunzo".
murmushi Dr yakuma cikin kwarewa da iya tafiyar da mara lafiya ya dube ni yace
"Idan zaki iya tashi to tashi".
nayi yunƙurin tashi naji Nakasa sai ji nayi kamar cikina yana buɗewa in da aka min CS ɗin,
ido na matse sai ga hawaye sharr.
Ido yaɗan kura min kana yace
"Sorry bari nurse's suzo su tai maka miki".
yafita ba jimawa nurse suka shigo suka ɗagani suka goge min jiki suka kimtsa ni,
kana suka cewa mama takawo ruwan zafi kadan a kofi akabani nasha,
sannan sukace na gwada kwanciya da kai na in zan iya,nan ma na kasa,su suka mai dani
suka kwantar dani. sukace wa mama taringa haɗa min milo inasha duk bayan awa daya
domin zai taimaka
min yakawo min ƙarfi ajikina.
tace to insha'allahu nan suka fita...

Da daddare nurse's ɗin suka kuma zuwa,
yanzu kam cewa sukayi na tashi da kai na daƙyar na iya mikewa zaune, bayan sun gama
gyara min jikina sukace na kwanta da gefe in zan iya shima nakwanta,
Washegari ma da kaina na tashi nurse's suka gama ai kin su suka fita,
Mama tasa min pillow a baya na na jingina dashi,
bayan nagama shan tea mai zallar milo da Mama ta haɗa min,
tadube Ni tana faɗin
"To tun da kin koshi kibashi nono yanzu kam kin ga dai tun jiya kuka yake,
ga ƴar'uwar sa ma yau ta tashi da kukan, yunwa duk suke ji".
Baki na tura dan tun jiya take ta bina nabashi nono toma ni ta'ina ma zan fara,
miko shi tayi taɗaura shi kan cinya ta sai dai bata sake shiba tana rike dashi ta ɗan gyara shi ta
inda bazai fama min ciwo ba,
tace
"To ɗan gyara sai ki bashi"...
yana kama nonon nayi saurin fizge nonon a bakin sa tare da sakin ƴar karamar kara,
na yarfe hannu ina faɗin
"Wayyo zafi".
ai ko shima sai ya saki kuka yana cusa hannunsa cikin baki,
Mama
tace "Daure ki bashi kinji".

sai da Mama tayi ta lallaɓi na kafin na yarna na maida masa nonon bakin sa ina matse ido
harda kwalla.
bayan yasha ta kwantar da shi ta ɗauko ta ita ma tasha.
kana tayi musu wanka
nan da nan kuwa sukayi bacci....★


Kwanan mu uku a asibiti kullum sai Zainabu ta ai ko mana da abinci.
zuwa yanzu kam jikina Alhmdllh dan har ina sauka na taka da kaina,
Muna zaune Mama nata jana da hira yayin da take ta yiwa yaran wasa.
Malam musa yashigo da sallama bayan an gaisa yake
tambaya haryanzu baban yaran baisamu isowa bane?
Mama tace
"Eh. a takai ce.
ƙasa nayi da kai na ina wasa da yatsun hannuna yayin danaji wani abu yataso yatokare
zuciyata nan take naji ƙwalla yaciko min ido dasauri namai dasu,ta hanyar ambaton sunan Allah
a cikin zuciya ta,
Har yanzu mutanen da suke hulɗa da Mama basusan ko wacece niba,
har yau Mama bata sanar musu koni wacece ba abun da kaɗai suka sani takuma sanar musu
Ni ɗiyar kanin tane kuma mijina soja ne yana bakin ai ki haihuwa nazo,
rumtse idanuna nayi yayin da kwallar da naketa mai dasu suka zubo,
nakai hannuna nashare batare da nabari sun gani ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login