Showing 15001 words to 18000 words out of 49670 words

Chapter 6 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf

07 Apr 2025

2328

fargaba,dajin kira kai tsaye
daga sama.
A ɓangaren Na'ima kuwa duk da itama tarazana da jin kiran,sai dai tasan bokan ta bazai barta a
rana ba.
batare da ɓata lokaci ba suka nufi gidan su Abbu,
in da Na'ima da baba mai gadi Sani direba Habu mai shara,suka taho a mota guda,sauran ma
ai katan kuma suma a mota guda...
Acikin parlour'n Mamie suka tadda kaf ƴan gidan anyi jugum-jugum,suna shigowa Aunty
Rafee'at tashiga ai kawa Na'ima harara cikin tsananin tsanar matar,a gefe kusa da Ya SALEEM
Na'ima ta zauna,in da sauran ma ai katan suka zazzauna a kasa tare da soma gai da su Abbu,
Ummi da goggo Hauwa da Aunty Halima ne kaɗai suka amsa musu.
gyaran murya Abbu yayi ya dubesu da ɗaɗɗaya da kyau kana yaso ma magana
"A cikin ku su wane ne suka ce sun ga HAMDAH da wani acikin ɗakin kwanan ta har kuma suka
bada tabbacin sun gansu a makwanci ɗaya??".
kallon-kallo Na'ima da baba mai gadi Sani Habu suka shiga yi.
yayin da hankalin mutanen cikin parlour'n yadawo kansu tun da kowa yasan cewa sune suka
bada tabbacin sun gansu da idanunsu.
Ummi kam kanta ta sunkuyar jiki a sanyaye tana jin kunnuwan ta suna yi mata nauyi da sake jin
abun da ɗiyar ta ta ai kata...


Baba mai gadi ya rusanar da kai kasa kana yace
"Gamunan Alhaji, ni da Habu da Sani sai kuma Hajiya Na'ima".
yafaɗa yana nuna ko wannensu da hannu kana yaci gaba

"Ranar da oga SALEEM yayi tafiyar da yaje yayi wata guda a ranar mutumin yafara zuwa".
nan ya zaiyana bayani kamar yan da yafaɗa wa Ya SALEEM a wancan lokacin.
Ido Abbu yazuba masa da kyau yana sauraren sa yayin da jikin sa yaɗan yi sanyi dajin
maganar daga bakin baba mai gadi,
baba mai gadi dattijo ne dan ya girmewa su Abbu'n nesa ba kusa ba.
Habu da Sani suma sukayi bayani da bada tabbacin ganin su kamar yadda suka faɗa wa
SALEEM,
kana daga bisani Na'ima ta ɗaura,
tun da Na'ima ta fara magana Aunty Rafee'at ji take kamar taje ta shaketa ta mutu dan bakin
ciki,cikin tsana da jin haushin ta tace
"Wlh karya ne cikin Ya SALEEM ne".
ganin yan da take maganar tana nuna Na'ima da yatsa kamar zata mike,
Aunty Halima ta riko hannunta cikin kasa da murya tace
"A'a Rafee'at zau na kawai".
huci take tana ai kawa Na'ima harara.

Shiru parlour'n ya ɗauko kowa da abun da yake sakawa cikin zuciyar sa,
Ummi kam wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata da sake jin abun da ƴar ta ta aikata,cikin
wani sabon tashin hankalin da ta sinci kanta ciki tashiga nanata kalmar
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
Ya SALEEM na zaune har lokacin bai yi magana ba sai dai bugun zuciyar sa da yakaru tamkar
zai fasa kirjinsa yafito,
Abbu ya sauke numfashi sannan yace
"Ina da bukatar bincike akan lamarin duk da kasan cewar ku shaidu har huɗu akan lamarin, zan
sako hukuma ciki tayi bincike sosai domin daɗa tabbatar da hakan,
kutashi kuje gobe idan Allah ya kai mu za'a fara bincike domin zuciyoyi su dai-dai ta kan abu
guda".
wani irin Rasss gaban kirjin N'ima ya buga da sauri ta mike yayin da sauran suma suka mike
sukayi musu sai da safe suka tafi.
Abbu ya mai da hankalin sa kan Abba da Ya SALEEM sannan yace
"Gobe nakeson ganin HAMDAH cikin gidan nan".
yana kai wa nan yamike yayi cikin bedroom ɗin sa....

Hankali tashe Na'ima takoma gida hankalin ta bai kuma mummunar tashi ba sai da ta sami
labarin cewa Abbu yace anemo HAMDAH,
washegari ana idar da sallar asuba Na'ima ta fita tanufi gidan bokan ta,
hankali tashe tafito daga motar ta tatube takalmin ta tanufi bukkan malam na kan tudu,
yana zaune gaban kayan tsafin sa ta zube gaban sa tana sauke numfashi kamar wacce tayi
tsare,
cikin sauke numfarfashi tace
"Boka akwai matsala".
Dariya ya sheke da shi,
itako cikin tashin hankali da rawar jiki ta cigaba da faɗin

"Boka komai ya kwaɓe iyayen sa sun dawo mahaifinsa yace yau zai faɗaɗa bincike akan
lamarin kuma yace hukuma zai sa suyi bincike akai,
sannan yace aje a nemo ta a duk inda take,
boka ka taimake Ni kamar yadda kasaba tai makona".
kai ya jinjina kana yaɗauki wani ɗan karamin tandu da zare mai kauri yace
"Za'a rufa musu baki bazasu kara yin ma maganar ba daga yau,zasu mance da batun kuma
koda sun tuno ta, baza su iya yin komai akai ba".
dariya yakuma ke cewa da shi yace
"Haka ya miki?"
da sauri tashiga gyaɗa kai tare da faɗin
"Yayi sosai ma Nagode kwarai malam ai Ni kagama min komai a rayuwa"...


Wani bakin ruwa ya zuba cikin ɗan karamin tandun nan sannan ya shiga zagaye bakin tandun
da zare mai kaurin nan, har sai da ya mamaye bakin tandun da zaren yarufe shi ruf,
kana ya jefa shi cikin tukunyar tsafin sa,yadube ta yace
"An gama".
godiya tashiga zuba masa kana tabuɗe jakar ta taɗibo kuɗin da batasan adadin su ba ta zubesu
a gaban sa ta hayo motar ta takoma gida...

Tayi ta suba idon ganin hukuma masu bincike shiru har yamma,
har dare tana baza kunne kuma jin wata magana nan ma shiru,
wasa-wasa aka shari kwana uku babu wani labari,
dariya tashe ke dashi tare da buga cinya tana hakimce a bakin gadon ta,
"Ɗa ɗan ku haka gida ma nasa, kuma na haramta wa ƴarku do min ni kaɗai kuka haifa min shi".
tayi maganar cikin nuna isa tamkar da wani cikin ɗakin..

A ɓangaren Abbu kuwa a cikin zuciyar sa yanajin son yayi bincike kamar yadda yafaɗa haka
kawai kuma sai yaji yakasa ai watar da hakan,a ɓangaren Mamie ma haka abun yake tanajin
abun a ranta sai dai bata iya furtashi a baki .......!★





Mommyn twins ce



Haka rayuwa yaci gaba da tafiya,
kamar yadda kuka sani yanzu rayuwar tafiya kawai take,dare babu wuyan yayi haka gari
bawuyan ya waye,koda gudun da kwana da yini suke ya'ishi ɗan adam yayi wa kansa hisabi,
domin kuwa rayuwar mu tafiya kawai take yanzu...★

haka naka narika rainon cikin Mama tana iya bakin kokarin ta wajen kula da Ni da abun da ke
cikina,
lokacin da cikin yakai wata bakwai da watan yakai karshe, tun daga lokacin nazamo abun
tausayi bana iya yin bacci dazarar dare yayi to bacci yakaura ce min ina so nayi amma babu
hali,dazaran na kwanta sai naji kamar na kwanta kan kaya duk inda na juya babu daɗi,
ban isa na kwanta ba sai dai na jingina da jikin garu kokuma na zauna sakankanin buhuhuna
natokare gefe da gefe na,a haka zan samu naɗanyi gyangyaɗi,
cikin ga masifar nauyi da girma ni kaina yanzu ina ganin girman cikin da Mama take faɗa.
a haka har watan yakare,ina cikin wannan halin...

Cikin ikon Allah yau cikin yashiga wata 8 dai-dai.
kamar ko wani lokacin zuwa awo na idan yayi da sassafe Mama ke tashi na mutafi yauma
hakan take,
kasan cewar natafi da wuri da wuri nafito daga asibitin,
da kyar nake ɗaga kafata nanufi gida,
ina tafiyar ina hutawa har na isa gidan.
azaune na iske Mama kan kujera ƴar tsuguno,tana ganina tamike taɗau taburma tashin fiɗa
tana faɗin
"Zauna ki mike kafafun ki sannu kinji".
Kai na gyaɗa nazauna ina sauke numfashi,cikin tausaya wa ta dubi cikin ta cigaba da faɗin
"Kai wannan ciki naga alama shi yake janki Ni sai gani nake kamar ma cikin yafi karfin ki".
kallon cikin nayi tare da yin murmushi,
tamike ta kawo min abinci da kunun tsamiya tace
"Ci sai ki kwan ta ko zaki samu ki ɗan yi bacci".
nace To...
Ina gama ci Mama tamike tace
bari ta kawo min pillow na mike a nan dan yafi iska, nace to.
tana shiga ɗaki aka fara kwaɗa sallama da karfi-karfi murya naɗaga na'am sa sallamar da nake
jin sa kamar ihu acikin kunnena.
mirgina wa nayi da kyar na mike nanufi kofar gida,
wani katon mutum na gane
a tsaye daf da kofar gidan, kallon mutumin nayi dan na gane shi ganina da shi na biyu kenan
gaishe sa nayi ya amsa fuska a turnuke sannan yace
"Fasuma tana ciki?".
nace "Eh".
fuska yadaɗa turnike wa ya turo tunbi gaba yace "Je kice mata Alhji Mamman ne yazo".
nace to. najuya nako ma ciki
Mama na sun kuye tana gyara min pillow da ta dauko min na karaso in da take tace
"Yau wa zo ki kwanta ko Allah zai sa ki Sami bacci ko bakiyi da daddaren ba zai zo da sauki".
nace "To, Mama wai Alhaji Mamman yazo".
cak ta sai da hannunta daga abun da take,ido naɗan tsura mata ganin yanayin da ta shiga daga

faɗa mata wan da yazo ɗin, tana sunkuye kanta a kasa bata kuma aje pillow'n dake hannunta
ba.
karo na uku kenan aduk san da Alhaji Mamman yazo ina lura da ita irin wannan yanayin take
shiga,
"Ko me yasa?". nayi tambayar azuciya ta,a sanyaye ta ɗago ta nufi ɗaki can tafito da mayafi da
kuma kuɗi a hannunta,
tanufi kofar gida.

Daga in da nake zaune inajuyo sautin Muryar Alhaji Mamman sai dai bana fahimtar abun da
yake faɗa,
taɓa lokaci kafin tashigo,ido na bita da shi har takara so in da nake,
kan kujera ƴar tsuguno ta zauna jiki ba kwari,
tadube ni nima ita nake kallo kallo ɗaya zaka yi mata kasan cikin muguwar damuwa take,
"To wanene shi?".
nakuma yi tan bayar a zuciya ta, wan da bansan har ya fito ba sai da naji tace
"Hmm wan mai gida nane ubansu ɗaya".
da sauri na kuma duban ta taci gaba da faɗin
"Shi ne mai wannan gidan zaman haya dama muke aciki,
to bayan rasuwar sa sai nauyin yadawo kaina ni nake biyan kuɗin hayar to yanzu yana bina
kuɗin shekara 2 ne da ban samu na biya ba shine yake ta sintirin karɓa,
ƴan kuɗaɗen da suke hannuna na kai masa kafin na samu wasu na kara masa yaki karɓa,
wai sai na haɗa masa duka na shekara biyun,
yanzu dai na basa hakuri yatafi,
to bari mu gani mu ɗan taɓa sana'ar na ɗan kwana biyu ko Allah zai za a samu ɗan wani abu
sai a haɗa abashi".
tau sayin Mama ya kama ni kwarai nace
"Allah yasa a samu acikin satin nan ma sai a basa".
tace "Amin"...


Bayan sati biyu.

hakan yayi dai-dai da watannen cikina 8 da sati biyu, zaune nake a ɗaki bayan na idar da sallar
azahar da sauri na yunkura na mike da kyar jin fitsari ya taho min lokaci guda kamar zai fito,da
sauri na fita naje bayi nayi,nayi mamakin ɗan fitsarin da nayi bana kirkiba amma nake jin sa
kamar zai fito kafin na isa bayin. Na komo ɗaki ina zama bada jimawa ba nakuma jin irin fitsarin ɗazu, koda na koma bayin
shima ba da yawa nayi ba,sai dai nayi irin haka har sau hudu,zuwa yanzu kam abun yafara
damu na,yunkurin mikewa nake jin wani ya taho,amma nayi nayi na iya mike wan na kasa,
da kyar na tattaro ragowar karfi na na yunkura zan mike, ba shiri na koma zaune da sauri jin
wani irin sarawar da bayana yayi da mugun karfi.
a take kuma marana shima ya amsa dayi min wani irin mummunar murɗa,
sulalewa kasan ɗakin nayi nashiga murkususu.

Cikin tsananin jin azaba da karfi na furta
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un!".
da sauri mama dake ai ki tsakar gida tashigo tun kan ta karaso take faɗin
"Yaya dai lafiya HAMDAH?".
cikin hanzari takaraso in da nake kwance ina juyi cikin azaba cikin tashin hankali tace
"Subhalallhi yaya dai HAMDAH".
kai nashiga juyawa cikin jin azaba da kyar na iya furta
"Wayyo Allah bayana marana wayyo Mama zan mutu".
a kiɗime ta
ɗa goni ta tallafo ni jikin ta tana faɗin
"Ikon Allah sannu ina ganin juyi ne dai dai lokacin haihuwa kam da saura sannu kinji"..
hannunta na kankame da karfi jin marana ya kuma murɗani sai naji fitsarin nan irin naɗa zu nan
da nan jikina yakama rawa nadaɗa kankame Mama da karfi nabuɗe baki zanyi magana sai naji
wani ɗumi yana bin kafata,
da mamaki Mama ke kallon kafata tace
"Ikon Allah ga alamar haihuwa kuma tun lokaci baiyi ba".
ni dai a sama nake jinta dan azabar da nake ji yanzu yafi min kama da nafitan rai duk da
bansan zafin fitar raiba amma nasan babu abun da yakai shi zafi,
nagama sadakarwa raina ne zai fita dan azabar da nake ciki yanzu yawuci na kwatanta shi.
maganar ta nakuma ji a sama tana faɗin
"Tabbas haihuwa ce an ɓata da lissafin ne dai".
pillow ta janyo ta saka kai na a kai kana ta mike da sauri tafita,can an jima ta wado rike da kofi
da ruwan hulba wan da ta tafasa shi ta tallafo kai na tasaka min kofin a baki tace
"Sha da zafin sa in sha Allahu zai zo miki da sauki".
da kyar na buɗe baki na soma sha nan take wani sabon zufa yashiga keto min..

Akai-akai tarika bani ruwan idan yaɗau sanyi sai taje ta ɗuma takuma bani nasha,zatona zan ji
sauƙin kamar yadda tace amma me sai ji nake kamar ana daɗa hangizo ciwon ne,
kofin tamiko min tace "Karasa wannan sai na je na karo wani in Allah ya yar da yanzu zaki
warke".
kuka na fashe dashi cikin muryar kuka nace
"Wayyo Allah Mama Ni dai idan nasha ciwon karuwa yake daɗa yi".
da sauri tace
"A'a yi shiru dai na kukan ba'a yin kuka a irin wannan ciwon ai karuwa ciwon yake yi idan kace
zaka yi masa kuka,ko kina so ya karu ne?".
da sauri na girgiza kai tace
"To in kuwa haka ne kada ma kibari wani yaji kukan ki ko Ni da nake kusa dake in kuma ba
haka ba to ciwon bazai taɓa bari ba sai dai ma yakaruwa addu'a zaki rika yi da salati nima kuma
zan taya ki".
cikin jin tsoron abun da tafaɗa na haɗiye kukan sai juya kai nake cikin jin azaba...

abu kamar wasa sai daɗa zamowa gaskiya yake,tun azahar har la'asar ina abu guda faɗar kalar
azabar da nake ciki bazai misaltu ba,
zuwa yanzu Mama ta fara shiga damuwa ganin an shari wasu ƴan awanni babu wani labari,ta
dube ni cikin tausayawa tace bari taje gun Malam Musa ta amso min magani.
tafita da sauri,
batare da ɓata lokaci ba ta dawo rike da kwarya a hannunta tana kusa kan ta cikin ɗakin tayi
wurgi da kwaryar da gudu takaraso in da nake durkushe sai kakkkarwa nake narike marata
danake jin kamar zai fashe da karfi,sai nanata kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un nake.
taruko ni tana faɗin
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, taso muje asibiti sannu ƴar nan daure ki mike".
sai kuma ta sake ni tafita da sauri tana faɗin
"Bari na taro mai abun hawa".
tana fita akaci sa'a tasamu a kofar gida yasau ke wata mata ta tsai da shi takomo ciki da tai
makon ta na iya mikewa tsaye a duke muka fito,muka shiga napep muka nufi asibitin danake
awu,
batare da ɓata lokaci ba suka karɓe ni aka shige dani ɗakin da aka tana da domin masu
haihuwa.
nan da nan nurse's suka fara ai kin su,
sai dai har yamma labari bata sauya ba, sai gashi-gashi haihuwa zai zo sai ya tsaya duk wani
iya bakin kokarin nurse's ɗin sun yi amma abun yaci tura,har aka kira sallar magriba,
sukace gaskiya yafi karfin su mutafi babban asibiti.

A cikin adai-daita mama narike da ni dan zuwa yanzu karfi na yakare gaba ɗaya,da kyar na buɗi
baki nace
"Mama ki mai dani gida kawai ni nasan mutuwa zan yi".
cikin tashin hankalin da take ciki tace
"Ki dai na faɗan haka HAMDAH in Sha Allahu zaki sauka lafiya da yar dar uban giji"....
koda muka isa asibitin aka shiga bani tai makon gaggawa, likitoci mata uku ne a kaina biyu
mata ɗaya na mini.
Inaji cikin harshen turanci suke faɗin
"Bazata iya haihuwa da kan ta ba dole sai an mata CS yanzu kuma batare da ɓata lokaci ba".
kuka na fashe da shi ina faɗin
"Wayyo Allah Inna Ummi na wayyo Allah na".
rarrashi na suka shiga yi nan suka nimi ganin miji ko uba domin sa hannu kafin suyi CS ɗin,
sannan kuma sai an ajiye 25k shima ɗin na siyan kayan ai kin da za'a yi amfani da sune kuma
cikin gaggawa.
hankalin Mama yakuma mummunar tashi,tace
"Mahai finta ya rasu Mijin ta kuma baya gari amma yaba da izinin ayi mata amma dan Allah kuyi
mata yanzu zanje nakawo kuɗin".
Mama tafita cikin tsananin tashin hankali.
Ni da kai na da naji azabar yanin ka na ɗazu nace
"Dan Allah kuyi min kuraba ni da wannan cikin.....★

★★★
2hr ago
★★★

Bayan waɗan nan awan nin
Likitoci suka sami nasarar yimin ai ki wan da duk abun da ake idanuna biyu ina kuma ji, in da
suka ciro baby'n sai dai duk yan da suka so na kalli abun da na haifa fir naki dan har lokacin ina
cikin jin azabar ciwo duk da kuwa allurar da akamin....!★


*Kukaran ta da hakuri‍♀️ ban sami damar yin editing ba*

*Saura kuce yayi kaɗan bari ma na fece‍♀️*
*Nasan ki sarai Rabin jiki maman korafi Allah yasa naji wani magana sai natafi yajin ai ki*
*To oga yace Saturday and Sunday lokacin sane to gashi na ɓantara muku lokacin sa*
*Ƴan HAMDAH FANS 2 sun fiku son na adana oga*



Hankali tashe Mama ta isa gida in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login