Showing 48001 words to 49670 words out of 49670 words

Chapter 17 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf

07 Apr 2025

2333

wanke-wanken yamma daf magriba ta takoma gida,
kafin ta tafi kuwa sai da sukayi mata jawabin gobe da sassafe zatazo,
ko da ta koma gida da tasha ruwa tuwon da matar Æ´aÆ´an ta ta É—an sakura mata na tun da rana
wan da ya wuni abuÉ—e ma shi tayi buÉ—a baki da shi.
washegari da sassafen tazo ta gidan masu kuÉ—in bayan tayi wanke-wanken da shara aka kuma
jibge mata wanki har da na jiya da ta wanke aciki tayishi......
tun daga ranar kullum Mama mai awara na kan hanyar zuwa yin wannan aikin,
cikin kaskanci da wulakanci da rashin daraja É—an adam, wannan gida basa da daraja babba duk
da ta girme musu duka amma basa daraja ta ko dun girman ta, suna yi mata kallon
kaskantacciya kullum cikin wulakancin su take a haka dai har tayi wata É—aya a karkashin su,
ranar da tacika wata guda tana yi musu aiki suka É—auki naira dubu biyu suka bata suka ce shine
albashin ta,
Mama mai awara ta karɓa har hanunta na ɓari tanata zuba musu godiya.
tana komawa gida tahaÉ—a Æ´an kayakin ta tafita sai tasha,
tashiga mota zuwa garin Jos tana isa direct Narkuta ta wuce,
ko da suka iso a bakin titi aka sauke ta kasan cewar É—an kuÉ—in da ke hannunta duk yakare a
kuÉ—in mota da kafa tashiga layin unguwar su direct ta É—au hanyar gidan Malam Musa.
a sakar gida ta iske Zainabu zaune ta yi sallama tashigo, da sauri Zainabu ta mike tana faÉ—in
"Oyoyo Mama mai awara maraba lale barka da zuwa".
Mama mai awara ta yelwata murmushin fuskarta tace
"Yauwa Zainabu".
Zainabu ta kara buÉ—e taburman da take zaune a kai tare da faÉ—in
"Sannu da hanya ga gurin zama".
tazauna gefen taburman nan suka shiga gaisawa kana Zainabu ta mike ta É—ibo mata ruwa mai
sanyi cikin randar kasa ta kaso mata.
tasha tana cigaba da mata sannu da hanya.
bayan É—an gaishe-gaishe da tanbayar bayan rabuwa,
Mama mai awara takuma bin gidan da kallo akaro na ba adadi jin babu wani alamar motsin
wani acikin gidan,
ganin yan da Mama mai awara take ta raba ido cikin gidan, Zainabu taÉ—an muskuta tadube ta
tare da yin murmushi tace
"Um sai kawai kiga É—iyar ki tabiyo ki, fir taki zama fa wai
ita bazata iya zama ba kawai zata biki, HAMDAH kenan Æ´ar Mama".
Ido Mama mai awara ta waro tare da faÉ—in
"Wa É—in wai HAMDAH to ai ni ita nazo É—auka".
Zainabu tace "A'a ita kuma kika zo É—auka Mama mai a wara?, to ai HAMDAH kamma tun ran da
kika bar nan da kwana biyar tabiki in ban mance ba".

wani irin zabura Mama tayi tare da buga kirji tace
"Tun tafiya ta da kwana biyar tabar gidan nan to ina taje?".
Zainabu tace "Mama kina nufin wai baku tare da ita?".
shiru tayi cike da tsananin damuwa a ranta take faÉ—in
"To ko ta koma gurin iyayin ta ne".
sai kuma tayi saurin kuma cewa
"Ina baza ta koma ba ko dun gudun ta sana diyyar ta Ummi ta tabar gidan Abba'n ta, ina bazata
taɓa komawa gida ba".
cikin tsananin matukar tashin hankali Mama tace
"Ina Zainabu bataje in da nake ba!"
ido Zainabu ta waro tare da buga kirji tace "Bataje ba? nan fa ta shirya tace zata biki nace ta
hakura ta barki kidawo tun da kince bazaki jima ba tace a'a zata biki kawai, to ina taje?".
Zainabu tayi maganar hankali tashe.
hankali tashe Mama mai awara ta mike tana faÉ—in
"Bataje ba Zainabu bataje ba".
tanufi kofa, Zainabu ma ta mike taÉ—au mayafin ta tabi bayan ta,
duk gidajen da Mama mai awara take tunanin ko HAMDAH zata iya zuwa gidan wato gidajen da
suke mutunci da su anan cikin Narkuta.
amma duk in da taje sai suce ai su rabon su da ganin ta tun ranar sunan ta.
batun tashin hankali gun Mama ba'a magana,
tunani tafara tashiga mota taje Bauchi ta tuba ko ta koma can, sai dai bugu da kari batasan
gidan su a cikin garin Bauchi ba,ita dai tace mata ita Æ´ar Bauchi ce amma bata faÉ—a mata ko
awani unguwa take ba,to yanzu idan taje ta ina zata fara neman ta, Bauchi babban gari ne ba
karamin gari ba, idan taje ta ina zata fara neman ta....

Ranar Mama mai awara kuka da hawayen ta tayi da shar-shar, tunanin ta bai wuce ina tatafi
wani hali take ita da Æ´aÆ´an ta.
kwanan Mama uku ta fara shirin komawa dan tana ganin zaman ta anan nauyi take É—aura
musu, duk yan da taso samun kuÉ—in mota tatafi batare da sunsan bata da shi ba abun yacu
tura, karshe dai malam Musa shi ya bata kuÉ—in motar komawa.
a haka ta koma taje ta cigaba da rayuwar kunci da bakin ciki acikin gidan su wacce matar yayan
ta ta mallake ita da Æ´aÆ´an ta, kullum tana cikin tunanin HAMDAH da Æ´aÆ´an ta da halin da suke
ciki,
duk san da tatuna hakan sai ta zubda ƙwalla, sai dai batayi kasa a guiwa wajen yi mata addu'a
ba, duk san da zatayi sallah sai ta sanyata cikin addu'o'in ta.....★
wannan kenan



Acan kasar saudi kuwa bayan sati uku da canza Diamond É—in har yanzu muna cikin masarautar
Saudi mun zamo tamkar Æ´an gida,
Bappa yace bazamu koma ba sai munyi aikin hajji da yake dumfaro wa yanzu.

wata ranar juma'a bayan mun dawo daga masallaci shugaban kasar mu na Nigeria yakirawo
wayar Mahmoud yahaÉ—a su da Bappa,bayan gaisawar da ya guda na sakanin su shugaban
kasar ke magana kan cewa tun ranar da aka tura kuÉ—in Diamond baikuma jin wani magana ba,
shin akwai wanda za'a basa ATM É—in bankunan da aka zuba kuÉ—aÉ—en ciki nan kasa Nigeria
kafin su sudawo?.
Bappa yace
A'a yarike ATM É—in a gurin sa dan bayida wan da zai iya cewa abashi sai dai bari yayi wa ita
yarin yar magana,
yaji ta bakin ta ko da abun da zatace kan lamarin bari a nemeta aji ta bakin ta.

I na zaune cikin É—aki ina sakawa su Naseem kaya da yanzu nayi musu wanka, cikin kayan da
É—azu Bappa yabani kuÉ—i nasiya musu da muke dawowa daga masallaci.
nan yake yimin bayanin yan da sukayi da shugaban kasar mu kana ya É—aura da faÉ—in
"Ko akwai wan da kike ganin za'a bashi kafin mu koman?".
nace "A'a Bappa yan da kace É—in hakan yayi".
yace "To madallh shike nan".
ya mike yafita....
da daddare duk muna hallare a katafaren parlour'n da yake masaukin mu, muna cin abin cin
dare Mahmoud ya dube ni sannan ya nisa yace
"Bappa ya faÉ—a miki yan da sukayi da shugaban kasa ko?".
nace "Eh yafa É—a min".
kai ya jinjina tare da faÉ—in "Ok to yanzu kina so a bar kuÉ—in cikin account banki surika juyawa ne
ko da wani abun da zakiyi da shi?".
Bappa yace "Tan bayar da shugaban kasa yayi min É—azu kenan da nace masa yabar ATM É—in
agurun su,
ni ma dai nayi tunanin ko za'a siyi wasu Æ´an kaddarori ne in yaso sai abar sauran banki yarika
juyawa".
baki na washe tare da faÉ—in
"Eh wlh Bapp a siyi wani abu da kuÉ—in".
Mahmoud yace "To me kike so a siyan".
hannayena biyu na dafe kumatu na, nayi sama da kwayar idanuna ina É—an jujjuya su, naÉ—an yi
shuru alamun nazari, sai nakuma washe baki nace
"Bappa kasan me nake tunani kuwa".
kai ya girgiza tare da yin murmushi ganin yan da nayi maganar, Mahmoud ma sai da ya
murmusa. cikin muryar dariya
nace
"Bappa kuÉ—in zai kai yasiya mota da gida?".
nayi maganar ina rufe fuskata da cigaba da dariyar,
Mahmoud yace "Me zai hana shi kai wan har abun da yafi gida da mota ma zai siya, gidaje da
motoci ma ba gida da mota kaÉ—ai ba har abun da yafisu ma kuÉ—in zai siya da shi har yarage".
da sauri nace "Yauwa to kawai a siya motoci irin manyan motocin nan wan da suke loda kaya
aciki ana kaiwa garurruwa masu nisa É—innan,
da gidan mai".

yace "Gidajen mai dai". nace "To shi da kuma asibiti da masallaci, umm da kuma irin abubuwan
sadakatuj'jariyan nan".
Bappa yace
"Rijiya bishiya masallaci bohul makaranta asibiti,da dai sauran su duk sadakatuj'jariya ne".
kai na gyaÉ—a da sauri nace "Yau wa Eh Bappa".
nakarashe maganar cikin muryar dariya,
yace "Gaskiya kinyi tunani mai kyau abun da yakama ta ayi kenan".
dariya kawai nayi dan ni ban É—auki maganar da wata girma ba dan ni atunani na mun dai yi sa
cikin rahane amma kuÉ—in bazai iya yin abun da na lissafan nan ba.
Mahmoud kuwa kai ya girgiza ganin yanayin yaranta cike taf cikin maganar tawa......

A daren Bappa ya sanar wa shugaban kasar mu abun da nace ina so ayi da kuÉ—in,
shugaban mu ya jinjina lamarin matuka yace nayi tunani dan hakan ma ci gaban kasa Nigeria
ne kwari da gaske.
za'ayi abun da nace in yaso sauran kuÉ—in kuma banki sai ta rika juyashi.
bayan sun gama maganar Mahmoud yace to shifa gobe idan Allah ya kai mu zai koma bakin ai
kinsa.
Bappa yace "To Allah yakai mu mukam muna nan sai munyi ai kin hajji tukun, idan kaje karika
zuwa duba mahaifiyar ka akai-akai gobe ma zaka kuma kirowo min Isa ya hadamu mukuma yin
magana da ita".
yace "To ba da muwa Allah yakai mu"....
washegari da misalin karfe 11 Mahmoud yabi jirgi zuwa Dubai in da daga can zai shiga wani
jirgin zuwa Nigeria...



★★★★
*After 1 year*
★★★★


🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻😹 *da yar dar Allah anan book 2 yakawo karshe sai mun haɗu a littafi nagaba
wato littafi na uku wan da shine zai zamo littafi na karshe da yar dar Allah*



*Zazzaɓin gida-gida yafara kyarkyara ta*




Mommyn twins ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login