Showing 36001 words to 39000 words out of 49670 words

Chapter 13 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf

07 Apr 2025

2331

wandon sa sai na haɗo da ɗankwalina dana ɗaura
musu duwatsun nan aciki,
ina ɗago ɗankwalin sai guda ɗaya yafita ya faɗi, na ɗauka na sa masa a hannunsa ina faɗin
"Ungo abun wasan ka kaje gurin Bappa sai kun dawo Mero kai shi".
nafaɗa ina mika mata shi bayan na sa masa wandon,
ta karɓe shi tafita ta kaiwa Bappa shi,
ya karɓe shi yana faɗin
"Mutumin zamuje gurin shanu ko".
yayi dariya tare da yin gwalaɓen shi yana tsalle a hannun Bappa.
har sunkai bakin kofa zasu fita dutse ɗin da ke rike a hannun Naseem yafaɗi kasa, ai ko
yashiga zillewa yana kokarin zamowa kasa,
Bappa yagyara rukon sa tare da kallon kasa jin abun yaɗan bigi kafar sa yana faɗin
"Tsaya na ɗauko maka abun naka kar.."
cak ya haɗiye maganar nasa cikin matukar ɗinbin mamaki yake kallon abun kamar a mafarki,
hannunsa na rawa ya mika yaɗauko dutse ɗin,
shiko Naseem hannu ya mika yana kokarin karɓar abun wasan sa yana washe baki.
cikin tsananin mamaki da kaɗuwa Bappa ke kallon dutse ɗin, kana murya na rawa hatta
hannunsa rawa yake yace
"Waya baka wannan abun a ina ka samu!".
yafaɗa yana kallon yaron da mamaki yake juya dutse'n a hannunsa wan da hakan yake
tabbatar masa da ba mafarki yake ba.
kwaɗawa Inna wuro kira yashiga yi yana faɗin
"Sumaye Sumaye Sumaye".
da sauri Inna wuro ta fito tana faɗin

"Na'am Malam".
dutse ɗin ya ɗago yana faɗin
"Wannan abun a'ina yafito daga ina yafito a hannun wannan yaron nagani!".
naganar yake cikin kaɗuwa.
Inna wuro ta matso gurun Bappa tana faɗin
"Wani abun kuma?". tafaɗa tana leko hannunsa yace "Wannan abun daga ina yafito".
tace "Bansan ta in da yafito ba a'ina ka ganshi?".
tayi maganar ita ma cikin girgiza da ganin dutse'n da yake nuna mata.
Bappa yace "A hannun wannan yaron nagani".
Inna wuro ta saki kabbara da karfi tana faɗin
"Malam ta ya akayi abun nan yashigo cikin gidan nan".
Bappa har jikin sa na cirawa yafara kwaɗa min kira yana faɗin
"HAMDAH HAMDAH HAMDAH".
da sauri na karasa fitowa daga ɗaki dan dama fitar zanyi da naji Inna wuro ta saki kabbara da
karfi a tare muka fito da Mero har muna rige-rige.
dutse ɗin yaɗago yana nuna min yace
"Ta ina yaron nan yasa mo wannan abun a hannun sa nagani".
kasan cewar rana yafito dutse ɗin yafafa walkiya har yana kashe ido.
murmushi nayi ina faɗin
"La wannan ai abun wasan su ne".
Ido Bappa ya waro cikin ɗin bin tarin mamaki da shiga shok yace
"Abun wasan su!!??" yafaɗa cikin kakkausar murya.
kai na gyaɗa ina faɗin
"Eh abun wasan su ne na bashi yayi wasa da shi".
baya Bappa yayi cikin tarin mamaki yace
"Abun wasa? wannan abun shine abun wasa kinsan meye wannan kuwa!?".
kafaɗa na ɗaga nace
"Oho ni ban san shi ba kawai dai na ɗiba musu ne acan in da muka zauna na ɗiba musu
sunayin wasa da shi, to da zamu tafi shine na ɗibo musu naga suna son wasa da shi."
baki da hanci Bappa da Inna wuro suka buɗe suna kallona,cike da ɗinbin mamaki kana Bappa
yace
"Wannan suke wasa da shi? da ahi sukeyin wasa!".
yayi maganar yana juya dutse ɗin a a hannunsa.
"Bappa to ai akwai wasu ma da yawa na ɗibo musu bari ma kagani".
nafada tare da juyawa da sauri nasgige ɗaki,
na kunce ɗankwalin na ɗibo guda 9 a hannuna na kulle ɗan kwalin da sauran biyu a ciki na fito
da sauri.
ina faɗin
"Kagan su Bappa". baya Bappa yaja da sauri tare da jinginuwa da jikin garu yana bina da wani
irin kallo mai cike da al'ajab tsorone a'a mamaki ne.
ni kai na sai da naɗan razana tare da kallon duwatsun hannuna ko ganin yaga wani abun ne ni
dai ban ga komai ba sune dai duwatsun a hannuna.
Inna wuro ma kirji ta dafe tare da waro ido tace

"A ina kika sami wannan abun!?".
Bappa kam kasa magana yayi yana cigaba da bina da kallon mamaki.
nace
"Wlh acan in da muka zauna kusa da ruwan nan na samu acikin wani ruwan da muke yin wan
ka shine na ɗiba musu shine suke yin wasa da shi".
sai yanzu Bappa ya buɗe baki da kabbara
"Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar!". yayi ta nanata kalmar har sau uku kana ya mika
hannu yakarɓi sauran na hannuna yana juyasu a cikin hannun shi.
ya dubeni da kyau kana yace
"kinsan meye wannan?".
kai na girgiza nace "A'a".
"Allah mai girma da ɗaukaka".
Bappa ya faɗa tare da kuma cigaba da faɗin
"A wani ruwa kika same su tayaya a kayi kika same su idan mukaje zaki gane ruwan??".
yajero min tambayar.
na gyaɗa kai na nace
"Eh zan gane ai a bakin ruwan mukafi daɗe wa ma".
nan nabasu labarin lokacin da ruwan yacika kogin ya mamaye ko ina bayan wucewar sa muka
dawo gurin zaman mu da yan da akayi har nasa mi duwatsun.
cikin matukar mamaki suka haɗa baki wajen faɗar
"Ikon Allah Allah buwayi gagara misali".
Bappa yace
"Wannan dutse da kike gani kuma kike masa kallon abun wasa dukiya ne arziki ne, kwalli ɗayan
sa ma kaɗai ya ishe ki rayuwar duniya ingantacciya mai tsafta,
hakika Allah yayi miki ni'imar da bakowa yake masa ba sai wan da yaso".
kallonsu kawai nake taya za'ayi ace dutse shine kuɗi nace
"Bappa baka gansu da kyau bane fararen duwatsu ne fa".
dun kule su yayi a hannunsa gamgam yace
"Da ma tun zamanin iyaye da kakanni sunsha faɗan cewa acikin yankin nan akwai arziki muna
da arziki sai dai arzikin sai mai rabo yake iya ganin sa har ya same sa,tabbas kun tabbata ke da
ƴaƴan ki ku masu rabo ne,
wannan duwatsun da kike gane sune *LU'ULU'U*.......!!!!!!!!!★







Mommyn Twins ce

HAMDAH

t NA
*RASHEEDA S DIRECTOR*


_BOOK TWO_




*Sakon ta'aziyya gareki Aysha Aliyu Garkuwa*
*Tabbas babu abun da yakai rashin hamaifiya zafi da kunci Allah yajikan Mahaifiyar ki yayi
mata rahama ya gafarta mata yasa Aljanna ce makomar ta da sauran namu iyayen baki ɗaya
ku da tabari ya baku hakurin rashi ya sanya albarka a rayuwar ku da zakuyi shi bayan rashin
UWA!!*. *Sannu Aunty Aysha rashin mahaifiya akwai zafi Allah yabaku ikon cin jarabawar da yayi
muku*







" *LU'ULU'U?*" nafaɗa ina duban Bappa da mamaki kana nace "Bappa Diamond ƙenan fa?".
yace "Eh shine kwarai shine wannan".
kai na jinjina cike da matukar mamaki,
tabbas naji a na faɗan Lu'ulu'u amma ban taɓa ganin sa ba ko a hoto ne bansan ya kalar sa
yake ba,
kuma tun da nake tunanin abun bai taɓa zuwa min ƙwaƙwalwa ta bare har na ƙiyasta kamannin
sa acikin zuciya ta ba,
ni dai naji ana faɗar sunan sa Diamond wato Lu'ulu'u,sai dai kaman ninsa kam sam ban sani ba.
baki na washe tare da mika hannu ina faɗin
"La ashe dama wannan shine Diamond ɗin da ake faɗar nan ashe akwai a Nigeria ma? in sake
ganin su Bappa." nafaɗa ina kokarin karɓa a hannun sa.
da sauri Bappa ya daɗa dun kule su a hannunsa yana faɗin
"To ai gashi kin gani ai mu arzikin da Allah yayi mana a Nigeria ma wata kasar bata samu
kwatankwacin irin sa ba, ke zaki bada shaidar haka tun da gashi kin samo da hannun ki,
wannan ba abun wasa bane barsu a hannuna kawai".
baki na washe nace

"Ashe Diamond ɗin haka yake".
Gefe da gefen sa Bappa ya kalla tare da like kofar gida kana ya juyo ya dubi Inna wuro yace
"Da muke maganar nan Allah sa dai ba wanda yake kusa ko kin ki motsi alamar mutum a
kusa?".
ɗan shiru Inna wuro tayi alamun nazari kana tace
"A'a kam banji alamun wani a kusa ba".
Kai Bappa ya jinjina sannan ya dube ni yace
"Kikace zaki gane ruwan idan muka je?". nace
"Eh zan gane".
da sauri ya juya yashige bokkan sa yayi musu kyakkyawar ɓuya kana yafito,
ya dubi Inna wuro da muke tsaye har lokacin yace
Kada ta kuskura tafita kuma kada tabar wani ya shigo gidan.
tace To,kana ta ja hannun Naseem da Nasmah suka zauna kan taburman dake sakar
gidan,tana ta jan su da wasa har muka fita basu sani ba...

Muna fita yakira wo waɗannan matasan da suke yi masa kiwon suka taho da amalanken shanu
Bappa yace nahau.
kana ya dube Ni yace "Ta'ina zamubi?".
nan nashi kwatanta musu hanyar da muka bi ranar da na biyo shanun muka shigo cikin rugar.
ina kan amalanken su suna tafiya a kasa nan muka ɗau hanya.
mukayi ta tafiya tafiya mai nisa kafin muka iso in da na sami shanun suke kiwo,
koda muka iso gurin,
sauka nayi nan nashiga waige-waige abun mamaki hanyar ta ɓace min na tsaya shiru ina ta
kalle-kallen gurin amma kwata-kwata na kasa gane hanyar, ko wannan babban tudun da muka
faɗo a kan tama ban ganshi a gurin ba nayi ta waige-waige amma babu ko a lamar sa.
"Kodai ba nan bane".
nayi maganar a kasan raina.
Bappa da tun ɗazu yazuba min ido sai yanzu yayi magana
"Kin tabbata tanan ne hanyar?".
kai na gyaɗa alamar Eh.
yadubi matasan da muka taho da su, tare da kiran sunan ɗaya daga cikin su yace
"Isa Kunzo kiwo a nan wace rana kuma?".
suka ce masa Eh suka kuma faɗa masa ranar,
kuma ranar da nabi su muka shiga cikin rugar su, duk da kuwa basusan ina biye da su ɗin ba.
Bappa ya jinjina kai kana ya mai da duban sa gare ni yace
"Ta'ina ne gurin?".
ɗan shiru nayi tare da lumshe idanuna a hankali suffar gurin duk da bawai mance sa nayi ba
yashiga zuwa min idona, na buɗe ido da sauri.
nace "Gurin akwai dutse babba sannan a gefen dutse ɗin akwai bishiyoyi karkashin bishiyoyin
kuma yashine,
gaban su can kuma babban ruwa ne kafin wannan babban ruwan kuma akwai wani fuwa ɗan
karami ne sosai".
shiru Bappa yayi kana yace

"Haka ruwan yake".
nace "Eh".
ya tan baye su Isa ko sun san wani gurin ruwa mai irin yanayin da na siffanta?, suka ce
Eh sun san wani ruwa mai dutse da bishiyoyi.
Nan muka juya zuwa wannan ruwan da suka ce sun sanin.
Muna zuwa gurin na tsaya na kalli gurin gashi nan shima dai babban ruwa ne amma sam bai
kai wan da muka zauna a gefen sa ba,
Kuma shima akwai dutse da bishiyoyin amma ba irin wancan ba.
nace ba shi bane.
Bappa yace muje wani guri shima ya san wani ruwa irin wan da na siffanta,
muna zuwa can ɗin ma na kalli ruwa nace bashi bane.
ranar munyi yawo mun wuni muna yawo muna zuwa gurin ruwa daban-daban duk wani ruwan
da muka je ko kaɗan bai kai girman wanda muka zauna a gefen sa ba daga wan da bai kai shi
girma ba sai wanda shi kwata-kwata ma baya tafiya a guri guda yake.
Abun mamaki nayi-nayi na tuna hanyar da nabi har mukaje wannan gurin ruwan nakasa gashi
dai ina ganin ruwan da duk wani abun da ke gurin ruwan a ido na amma sam na kasa tuno
hanyar gurin.
duk inda nayi tunanin ta nan ne idan muka je sai naga ba gurin bane,
daga karshe muka je gurin wani katon ruwa mai girman gaske girman sa yakusa kai wancan
ruwan yanayin ruwan yana kusan shigen kama da wancan amma shi babu dutse da bishiyoyi
da wani alamun gurin da muka zauna agurin babu shi.
Bappa yayi shiru yana duban katon kogin kana yace
"Anya wannan ba shi bane?".
nace "Allah Bappa ba shi bane wancan ruwan yafi wannan girma kuma wannan babu dutse da
bishiyoyi".
yace "To ai shima ga dutse tacan".
yanuna gefen mu tacan da ɗan tara saka nin mu, nace
"Shi wancan dutse ɗin ba a tagurin yake ba".
Shiru Bappa yayi kana daga bisa Ni yace muko ma gida.
Washegari ma muka kuma fita niman wannan ruwan sai dai yau tacan makotan rugan su
Bappa mukayi,
a cewar sa ko tacan ne ruwan yake kai na yakife nake ganin kamar ta in da muka je jiyane.
shima har yamma muna yawo babu alamar sa,
kwana uku muka jera muna fita, ranar na ukun da yamma muka dawo gida a galabaice muka
zube a tsakar gida bisa taburma...

Bappa yayi tagu mi lokaci zuwa lokaci sai yace
"Allahu Akbar Allah mai girma".
Inna wuro tace
"Kwarai kuwa buwayi gagara misali".
yace "Kwarai kuwa Sumaye Allah buwayi ne gagara misali, tabbas maganar tun zamanin iyaye
da kakanni ya tabbata,
tabbas maganar su na cewa a kwai arziki a yankin nan kuma sai mai rabo yake iya ganin sa

har ya same sa ya tabbata ya tabbata sai mai rabon,ita kaɗai take da rabon gani da kuma
samu".
Bappa yakuma faɗin
"Allah mai girma taya kika gani ne cikin babban ruwan kika shiga kika samu?".
nace "A'a Bappa a dai cikin wannan karamin ruwa da ke kusa da babban da na faɗa maka
muke wanka da sha da Sallah da shi ɗin, aciki na samu bayan da ruwan ya cika kogin har gurin
da muke zaman nan".
nan nakuma basu labari kamar yadda nabasu da fari da lokacin da naso tafiya na barshi a gurin
da kuma faɗuwar da mukayi naso kuncesu na zubar da su na ɗauki ɗan kwali na.
"Ikon Allah wannan abu naki ne shi yasa bai baki ikon zubar da su ba,
yayi ta sa miki da ke da ƴaƴan ki son abun a ranku duk da baki san menene shi ba,
in da baki da rabo da ko ganin suma bazakiyi ba,idan yaga dama kuma sai ya nuna miki
yakuma nufeki da barin su agirin ɗin"...

Adaren ranar Bappa yakira babban ɗan sa Mahmud,
Mahmoud costom ne yana da zama a Abuja, matar sa ɗaya da ƴaƴansu uku.
nan Bappa ya shige bukkar sa dan acewar maganan sirri ne.
bayan sun gama magana da Mahmoud yafito nan yake faɗa mana "Gobe idan Allah yakai mu
Mahmoud zai zo zai yi hanyar da za'ayi a canza Lu'ulu'u zuwa kuɗi,kuma yace dole sai an haɗa
da manyan shuwagabannin Nigeria, tun da har yawan su yakai guda goma,
sannan kuma barin Lu'ulu'u a cikin gida tare da mu yana da mugun haɗari,
domin kuwa har idan labarin yafita zamu iya fuskantar matsala, dan kuwa ba shakka za'a iya
kawo mana hari,
gobe da sassafe yace zai taso dan ma yanzu dare yayi ne".


washegari da rana Mahmud ya iso rugar, yayi mamaki da jinjina lamarin ta yadda nayi nasamo
Diamond masu yawa irin haka,
yayi murna da godiya wa Allah da samun wannan ɗinbin dukiyar,yakuma ji daɗin da abun ya
shigo acikin gidan su, dan kuwa ba shakka hakan abun alfahari ne.
bayan ya huta yaci abinci,zaune muke a tsakar gida Bappa da Mahmoud suna zaune kan
taburma guda yayin da ni da Inna wuro Mero Nasmah muke zaune kan taburma guda,
Naseem kam na can kan kafar Bappa ya like masa sai tsalle yake a jikin sa.
ina zaune shiru duk maganar da Mahmud da Bappa su ke da tsare-tsaren da Mahmud yake na
yan da lamarin zai tafi cikin sauki,
ban iya cewa komai jikina yayi sanyi natuno wani sashi a rayuwa ta, tun isowar Mahmud da yayi
sallama cikin gidan inadaga ɗaki sai da naji gaban kirjina ya yabuga, jikina sai ya kama ɓari
muryar sa tamkar muryar Abba har na fara tunanin ko Abba ne sai da naji Mero tana faɗin
Oyoyo Yaya Mahmoud.
ko yanzu da muke zaune ganin fuskar sa shima ya sani shiga wata yanayin, kamannin sa irin
na Abba yana matukar kama da Abba.
sai dai shi baikai Abba girma ba shekarun sa bazai wuce 38 zuwa 40 ba,
kira ce tashigo wayar sa da sauri ya ɗaga kiran kana yakara wayar a kunnen sa "Ok godiya

nake".
abun da yafaɗa kenan tare da sauke wayar.
maganar sa naji a sama yana faɗin
"Tun jiya na nimi ganawa da gwamnatin jihar nan, gashi da ikon Allah cikin sauki an bani
tabbacin ganawa da shi cikin sauki in sha Allah, wa gwamnati za'a siyar domin samun cigaban
kasa".
ya mike tsaye yana cigaba da faɗin
"Bappa mu hanzar ta."
tun kan ya rufa baki Bappa yamike yana faɗin
"masha Allah hakan yayi".
bukkar sa yashiga zuwa can yafito yana gyara babbar rigar da yasa ka kan kayan jikin sa,tuni
Mahmud yayi waje Bappa na fita ya shige mota suka ɗau hanya...
kwance nake a kan gado Nasmah da Naseem suna gefe na sai wasa suke,Mero ta shigo nace
ta ɗauke su sufita dan kaina ciwo yake min sai kuma dami na da surutun su suke, suna fita na
gyara kwanciya ta,gaba ɗaya yau tunanin gida da ya dame ni tun ganin da nayiwa Mahmoud
tunanin family na ya addabe ni,ina kwance shiru a haka har bacci ya ɗauke ni...
Bappa sun isa cikin Adamawa batare da ɓata lokaci ba suka sami ganawa da Gwamnan jihar
su, saboda muhimmin abun da ke tafe da su.
bayan sun gabatar da abin da ke tafe dasu, shi kansa Gwamnan yayi mamakin yawan Diamond
ɗin, yace gaskiya wannan Daimond ɗin kam sai dai a jingina da shugaban kasa. sabo da babu
kuɗin da zai iya canza wannan Diamond ɗin a fadar jahar.
batare da ɓata lokaci ba yayi magana da fadar shugaban kasar Nigeria, kana ya haɗa su da
wasu jagororin da zasu tafi tare, sannan yace dole sai sun tafi da wanda yasamo Diamond ɗin
sabo da za'a iya bukatar hakan acan fadar shugaban kasar.
da yamma lis

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login