Showing 27001 words to 30000 words out of 49670 words
Chapter 10 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf
naga sun yi shiru,
nakuma basu abincin su nan ma sai da naga sun koshi,
kana na ɗago Naseem wannan karo shi na goya shi narike Nasmah a hannu.
A sannu narika waige-waigen gefe na nashiga kallon kungurmin dajin da muke ciki ciki kaɗuwa
da tsoron ganin guri yagama rufe wa yayi duhu ga daji bakajin motsin komai sai na tsuntsaye da
wani irin muryoyi da numfarfashin abubuwan da ban taɓa jin irin suba,
da sauri na juya hanyar da nafi tunanin tanan nabiyo nashigo cikin dajin nabi da sauri narika
tafiya sai dai abun mamaki nayi tafiya mai tswon gaske ban ga alamar titi ba,
firgici da tashin hankali yaku baibaye ni ganin kamar daɗa kusuwa cikin dajin nake ga wasu
abubuwa masu firgitarwa da razanar wa da nake ta gamuwa da su a hanya.
da sauri na ja na tsaya ganin wani abu saman sa haske kasan sa duhu mai tsoratar wa,
cikin firgici da kiɗi ma najuya da sauri mai haɗe da gudu na koma da baya jikina na cirawa,
sai da natafi da nisa sannan na tsaya,
gefe da gefe na na kalla ina tunanin ta wace hanya ce nabiyo nashigo cikin nan,
a kiɗime na kama wata hanyar ta daban wan da nake ganin ko ita zata fidda ni bakin titi,
nayita tafiya har na godewa Allah amma ita ma babu alamar titi a gaban ta.
nakuma canza wata hanyar haka nayi yawo har guri yagama rufawa gaba ɗaya..
Zuwa yanzu kam kuka na fashe da shi ina ambaton sunan Allah duk inda na juya gabar da
yamma kudu da arewa daji ne.
Wani kututture da ke gefe da in da nake tsaye ina iya hango shi sabo da hasken farin wata na
isa na zauna a kai tare da kuma sakin kuka cikin muryar kuka mai haɗe da tsantsar tashin
hankali da kaɗuwa nake faɗin
"Ya Allah kakashe ni na huta Allah ka tsiratar da waɗan nan yaran Allah ka gani basu ai kata
laifin komai ba,
ya ALLAH ni ka ɗauki raina su ka tsiratar da su kasan basu ai kata komai ba".
kukana ne ya tsananta lokacin da na ɗaga kai nakuma bin dajin da kallo,
najima sosai a zaune naci kuka har na godewa Allah...........!★
Mommyn Twins ce
Ina zaune a kan icen shiru ina ta girgiza su Nasmah dan bana so su rika kuka dan idan suna yi
sai na rika jin motsin abu kamar yana tahowa in da muke,
ina nan zaune babu alamun bacci ko gyangyaɗi a idona sai tarin ɗinbin tsoro da tashin
hankali.......
ganin guri ya ɗan yi haske ba kuma hasken farin wata ba,
hakan ya tabbatar min da gari ne ya waye
wato dai mun kwana a zaune kenan.
a hankali na mike tsaye ina bin kungurmin dajin da kallo,
duba na nakai karkashin kututturen da muka kwana a kai jin motsi da huci,
a kiɗime cikin kaɗuwa nayi baya da sauri yayin da hantar ciki na yayi wani irin kaɗawa ganin
ƙatuwar maciji tana fitowa daga karkashin iccen,
juyawa nayi da gudu narika gudu cikin matsanancin tashin hankali sai da nayi gudu mai nisan
gaske kana na tsaya, ina maida numfashi da gyara rukon Nasmah da tuni suka saki kuka dukan
su,
najuya ina wai gen baya na.
kukan nima na sake nakasa rarrashin su sai kukan dukan mu muke.
a galabaice na zube kasa na zaunar da Nasmah a kasa kana na kunce Naseem shima na ajiye
shi gefe har lokacin duk kanin mu kuka muke ina binsu da kallon tausayawa,
sai na rungume su duka nakuma fashewa da kuka.
sai da nayi kuka mai isata kana na ɗago su na basu abincin su,
sai dai na san basu koshi ba dan har lokacin basu dai na kananun koke-koke ba tabbbas dole
bazasu koshi ba banciba bare su su samu abinci a jikina, ni kai na yunwar nake ji mara
misaltuwa.
wasu zafafan hawaye na share kana na mike tsaye,
ina ɗan kalle-kallen in da muke zaune, gindin bishiyar mangoro ne ga mangorori sunata rito
kasa-kasa,
na ɗau wani kara da ke gefe na a kasa na mika hannu nayi tsalle na buga mangorori guda uku
suka zubo kasa,
ɗaya ja biyun kuma duk basu yi ba haka na ɗauka nayi ta shan su kaf sai da na shanye su.
kana nayi taimama,
waige-waige nashiga yi dan bansan inane gabar ba,ina zan fuskanta nagabatar da sallar ba, sai
kawai na nafiskanci gabana na gabatar da sallar asuba.
ina idarwa na kuma goya Naseem da tun jiya da ya faɗi jikin sa yayi zafi rau har kuma yanzu
jikin nasa da zafi sosai,
sannan na ɗauki Nasmah muka cigaba da tafiya...
Munyi tafiya mai nisa jin na gaji nakuma tsayuwa na huta, kana na kuma ci gaba da tafiyar,
wunin ranar haka na wuni ina tafiya idan nagaji da tafiyar duk inda na samu sai na zauna sai dai
ban kuma yar da na zauna kan itace ko sunkuru sosai ba guri mai ɗan fili nake samu sai na
zauna,
a duk inda nayada zango na kwatanta lokaci kawai nake sai na gabatar da sallah.
ko yanzu ma a wani guri mai ɗan fili na zauna bayan na idar da sallar isha ganin guri yayi duhu
sosai sai hasken farin wata,
ina rungume da Naseem da Nasmah,
cikin tsananin tsoro da kaɗuwa na daɗa rungume su jin matsi da kukan wasu abubuwa cikin
wasu irin muryoyi daban-daban.
idanuna na rumtse ina ambaton sunan Allah,
zuwa can da daɗewa sai na rage jin sautin muryoyin,
a haka dai har gyangyaɗi yarika ɗan fizgata nayi ta ɗan gyangyaɗin har gari yawaye...
Washegari ma haka na tashi nayita tafiya in na gaji na huta,
yunwa kishin ruwa zafin rana, zuwa yanzu kam jan kafata kawai nake Nasmah da Naseem sai
kuka suke nakuma san suma yunwar ce ke ɗawai niya da su.
yunwa da ta addabe ni tafiyar ma da kyar nake iya yin ta
zuwa yanzu kam duk wani
bishiyar da na haɗu dashi idan naga yayi min kama da na ci sai na sinka naci.
nayi tafiya har na gaji kafata duk sunyi bororo kaya sun kwakkwar janeni bani kaɗai ba hatta su
Naseem da kwarjanin kaya a jikin su dan idan muna tafiyar naga wani abun tsoro zan sa gudu
ta sana niyyar hakan zasu faɗi ko kuma mu faɗi tare haka zan tashi naɗa ga su na rarrashe su
sai in sunyi shiru muka cigaba da tafiyar...
Tafiyar da bansan ina muka dosa ba tafiyar da har yanzu bata ɓulle dani titi da nake sammanin
tana gabana ba,
tafiyar kunci da wahala..
Yau kwanan mu biyar a cikin dajin nan,
nagama galabai ta na susucewa nafita hayyaci na,
yunwa kishin ruwa zafin rana,
baci ba sha ba wanka haka mukayi ta rayuwa acikin dajin nan har na kimanin kwanaki biyar.
a hankali nake jan kafata da ta kumbura ganin dare yayi ina ta ɗan sauri dan mufita a cikin sun
kurun da muke mu isa ɗan sararin da nake hangowa a can a gabana,
da kyar na karaso gun na sauke su Nasmah muka yada zangon mu agun,
rukon su na kyara kan kafata cikin sansanin tausayin su, na zuba musu ido,
sun rame sun dishe sun dawo abun tausayi.
ina nan zaune yunwa ya hanani sakat,
suma sai kananun kuka suke wan da nasan kuma na yunwa ce,
daƙyar na rarrashe su sukayi bacci,
niko kasa yin ɗan gyangyaɗin da nake yi ɗin ma nayi saboda tsabar yunwa,
haka na raba dare ina zaune..
koda gari ya waye kuwa nacigaba da aiki na wato tafiya....
Nayi taganin abubuwa masu razanar wa da firgitarwa idan naga wani abun ma kasa ihu ko
niman gudu nake sai dai na rufe idanuna da karfi ina ambaton sunan Allah, nakuma sadakar da
cewa rayuwa ta dana ƴaƴana yazo karshe...
Allah sarki rayuwa dani da ƴaƴana mun sauya kamanni mun rame mun fita hayyacin mu mun
dawo wasu irin abu da kama,
mun dawo tamkar mahaukata,
Zuwa yanzu karfina yagama kare wa ɗaukan su yana so yafi karfi na,
idan na ɗauke su mukaɗan yi tafiya kaɗan sai naji numfashi na nayin sama-sama idan na ɗan
tafi kaɗan sai na ajiye su na huta sosai kana mukuma yin gaba.
Yau kimanin sati biyu kenan muke rayuwa acikin dajin da nake mana fatan mutuwa dan na
tabbata ita zatafi zame mana hutu da wannan rayuwar.
cikin jan kafa da ɗan sauri na nufi bishiyar mangoro danake hangosa can sakanin mu daɗan
rata dashi,
da sauri narika jan kafata dan rabon da na haɗu da bishiyar mangoro ko wani abu mai zaki na
kai kwana biyar, sai dai naci ƴaƴan itace mai ɗaci ko tsami ko burti.
daƙyar na isa gin din bishiyar ina sauke numfashi da sauri na sauke yaran kasa naɗau san da
narika kaɓe mangoron sai da na zubo da su da yawa kana na zauna na tattaro su gaba
na,nasunku ya sha ba ko kakkautawa har jikina na ɓari,
ina kallon su Naseem suka ɗauka waɗan da ke kusa da su, suna ta gwaguya ban ko hanasu ba
dan suma nasan kalar yunwar da nake ji shi suke ji.
ina gama sha naji cikina yawani irin murɗa wa na kwanta a kasa, na da fe cikin nayita
murkususu har da hawaye.
najima zube a kasa ina juyi can naji yaɗan sassauta min na mike na ɗau kesu muka cigaba da
tafiya.....
Kamar mahaukata duk kayan jikin mu yayi matukar datti bazaka iya shaida wani irin kalar kaya
bane a jikin mu,sabo da tsabar datti,
nawa kamma duk ya yayyage daga kasa.
tun wannan mangoron da muka sha bamu kuma samun wani abun ciba a hanya ba sai da
muka kuma tafiyar kwana biyu,
daga can da nisa sosai na hangi wani katon dutsai mai girma sosai gefe da dutsai ɗin wasu
bishiyoyi ne ajere,
daga in da nake tsaye ina jiyo wani irin sauti mai kara da kugi mai karfi sosai duk da kuwa ina
juyo sa daga can da nesa,
cikin sauri da fatan Allah yasa bishiyar abun cine nakara sauri duk da azaba da zugin da
kafafuna keyi,
nanufi gurin dutsai da bishiyoyin nan suke.
duk da dai zuciya ta ciki da zullumi da tsoron jin ina daɗa matso in da kara da ƙugi wato irin
sautin gudun ruwa yake,
amma ban fasa nufar in da bishiyoyi da katuwar dutsai ɗin nan suke ba,
kuma nan nake jiyo kugi irin kugi mai amon sauti irin na ruwa mai karfi sosai ɗin nan.
a sannu narika tafiya ina yi ina huta wa har na iso kusa da dutsai da bishiyoyin nan,
wani irin juyawa da tsara wa kaina yayi hango wani katon kogi mai girman gaske,
cikin ɗan ɗar-ɗar na karaso jikin dutsai ɗinan wan da can gaban sa kuma katon ruwa ne yana
gudu da sautin kugi mai karfin gaske.
koton kogi ne mai girman gaske ko karshen gaɓar sa bana gani, ruwane mai girman gaske ko
a TV ban taɓa ganin irin wannan ruwa mai girman gaske haka ba.
gefe da dutsai ɗin kuwa wasu bishiyoyi ne lif-lif-lif masu kyau sai dai da yawan bishiyoyin ban
san ko bishyar menene bane gasunan da tarin ƴaƴa a jikin su wasu jajaye wasu koraye,
daga cikin bishiyoyin kuwa akwai na mangoro gwaiba dabino kwara kwakwa da kuma tupa,
gasunan kasa-kasa. gindin bishiyoyin kuwa yashine fari soll amalale agurin kamar an share
gurin babu ko datti har zuwa bakin gaɓar ruwan.
daga gurin bishiyoyin zuwa bakin gaɓar ruwan da ɗan tazara kaɗan,
kafin ai nihin babban ruwan akwai wani ruwa a ɗan gaban bishiyoyin sai dai shi ɗan kaɗan ne
da alama dai ruwan idan yayi yawa yana haurowa har gurin idan ya koma kuma sai ragowar ya
tsaya a ɗan wannan ramin.
ruwan fari soll kamar babban ruwan kogin nan da yake gudu....
A hankali natako zuwa gun yashin nan wato karkashin bishiyoyin nan,
na sauke su Naseem na zaunar da su,
da sauri cikin jin matsananciyar kishin ruwa na nufi in da wannan ruwa ɗan kaɗan ɗin yake na
sun kuya na saka hannuna narika ɗiba ina sha,
sai da nasha na koshi,kana narika ɗibawa da hannuna ina zuwa in da su Nasmah suke na basu
suka rika sha,
haka narika kai wa da komowa ina ɗiba ruwan a hannuna ina kai musu suna sha,
haka narika yi har sai da na tabbatar da sun koshi,kafin na kyale su.
na koma gurin ruwan nayi al'wala na dawo in da suke nayi sallar azahar da nake tunani yanzu
lokacin sa yayi.
ina idarwa na mike lokacin rana yafito sosai na ɗago Naseem na tuɓe masa kayan jikin sa da
yayi wani irin datti dattin har ya wuci misali,
na ɗauko shi muka taho bakin wannan ruwan da muka sha nakuma yi al'wala da shi, na saka
hannu cikin ruwan kasan cewar rana yafito hakan yasa ruwan yaɗan yi ɗumi sai narika ɗiba ina
wanke masa jikin sa na wanke shi sosai kana na ɗago shi na goyashi,
na ɗauko Nasmah ma itama na tuɓe mata kayan ta itama da yayi matukar datti kamar bana ɗan
adam ba,
na wanke mata jikin ta sosai kana na rungume ta muka koma gindin bishiyoyin,
nan da nan kuwa sukayi bacci ina zaune rungume da su,tabbas datti wani sashi ne mai hana
ɗan adam sakewa da jin daɗi ɗan rage musu dattin jikin su nayi sai gashi sunyi bacci cikin
kankanin lokaci.
ɗankwalin kai na, na cire na shin fiɗa a kasa kana na kwantar da Nasmah dake hannuna,
sannan na kunce Naseem na shinfiɗa zanin goyon su na kwantar dashi sannan na ɗago
Nasmah a kan ɗankwali na na mai data kan zanin goyon kusa da shi,
hijabina na cire na rufe su da shi kana na ɗauki ɗan kwali na na ɗaura.
gurin ruwan na koma na wanke musu kayan da na tuɓe musu na shanya kan yashin gurin, kana
na tuɓe kaya na na wanke jikina duk da ba soso ba sabulu amma naji da ɗin saka ruwan a
jikina.
na wanke kayan su da na tuɓe musu na shan ya kan yashi.
sannan
na dawo in da suke na kwanta a gefen su wani nannauyar bacci yaɗau keni.
bacci ne mai nauyin gaske yaɗauke mu dukan mu ban farka ba sai can dadaɗe wa koda na
tashi na fahimci cewa yamma tayi sosai dan guri yayi duhu,
al'wala nayi nazo na gabatar da sallar la'asar,
ko da na idar tagumi nayi a gaban su na zuba musu ido,
sun rame sun dishe wagasu kananun kuraje da suka fito musu duk jiki,
ido na rumtse yayin da tausayin su ke daɗa rasa ni har sai da wasu zafafan ƙwalla suka zubo
min batare da nasan da fitar suba.
nakai hannu nashare ina cigaba da kallon su a raina nake faɗin
"Ya Allah ka tseratar da su ka fidda su a cikin wannan kungurmin daji"...
A hankali na mike tsaye jin cikina na murɗan yunwa na sinko ƴaƴan itatuwa da yawa wanda na
sani har da wan da bansan su ba duk wan da na sinko na gusura najisa da zaki sai na kama ci,
nan su Nasmah suka farka da kuka na ɗago su na basu abincin su suka sha wanda sai dai
susha ne kawai bawai kodun ya koshar da su ba.
suna rungume a jikina a haka guri yarufa sosai lokacin tuni sun koma bacci sai nayi musu
addu'a na kwantar da su naje nayi al'wala bayan na idar da sallar magriba da isha sai na
kwanta gefen su.
Washegari naji daɗin bacci a gurin sosai bakamar na sauran kwanakin da mukayi a cikin dajin
ba,tabbas nan gurin da muke zaune wata rahama ce dan kuwa anan muna samun ruwan sha
da ƴaƴan itatuwan da zance,da ruwan da zanyiwa ƴaƴana wanka da kuma ni kaina duk da bada
soso da sabulu muke yin wankan ba. da waɗan nan abubuwan mukayi ta rayuwa a gefen ruwa har na tsawon wata guda.
gurin ya zame mana tamkar gida kuma ɗaki,
a gurin na kan iya ajiye su na ɗan zaga ta bayan bishiyoyin nan na sinko mana wasu kalar
kayan itatuwan nakawo mana dan yanzu har su Naseem ma ci suke mu samman abu mai ɗan
laushi....★
Zaune muke bayan na musu wanka suna kan kafata ina ta yi musu wasa sai ɓarkewa da dariya
suke,
cikin dabara na sauke su namike naje nayi wanka kayan su dana wanke musu ɗazu da nayi
musu wanka nashan ya kan yashi yabushe na ɗauko nazo na sa musu.
ina zaune a gefen su Naseem ya lankwasa kafar sa ya rarrafo yazo in da nake,
cikin tsananin farin cikin ganin yau yaron ya fara rarrafe nashafa kansa ina dariya da faɗin
"Iye lallai Naseem wato kayi wa Nasmah wayo ko kai ka fara iya zama shine kuma zaka riga ta
iya rarrafe ko,
amma dai zaka barta ta iya da wuri itama ko?".
baki yawashe kamar yasan abun da nake faɗa,
na kama kuma tun Nasmah ina faɗin
"Kema ki dake kinji kada yarika yi miki wayo da yawa".
nayi maganar cikin shauki,
itama dariya ta saka min duk na rungume su ina dariya,
a take kuma naji wani kuka yazo min sai kuma na fashe da kukan.....
cikin ƴar dar Allah bayan sati ɗaya kuwa Nasmah itama ta fara rarrafe.
tun da naga rarrafen su yafara yin kwari, sai bana yin nesa da su dan gudun kada su rarrafa
suje su shiga cikin ruwan nan idan zan je tsinko mana abun da zamuci sai na ɗauke su mu tafi
tare,
ko bacci nake ji har idan idon su biyu bana yar da natafi na barsu su idan su biyu,
dan duk lokacin da naje na musu wanka Naseem yarika zillewa yana son shiga ruwan yarika
bori da