Showing 30001 words to 33000 words out of 49670 words
Chapter 11 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf
shure kafafu wai sai dai na barshi yashiga ruwan,
shi yasa nake jin tsoro kada wata rana nayi bacci yace zai je yashiga ruwan bugu da kari ma zai
iya tunkarar babban kogin nan,
to haka zan yi ta zaman gadin su har sai sunyi bacci kafin nima nayi.....
Zaune nake na buga uban tagumi nayi shiru ina lissafa kwanakin da mukayi a cikin daji tabbas
yau idan ban mance ba kimanin watan mu biyu kenan acikin dajin,
wasu hawaye ne suka zubo min na share su.
Ikon Allah haka zamuyi ta rayuwa a cikin daji har mu mutu karshe namun daji sucinye mu,
tausayin kaina da na Æ´aÆ´ana ya kamani sai na rungume su na fashe da kuka.
ganin sunyi bacci na shin fiÉ—a musu abun kwanciyar su wato zanin goyon su,
na janyo hijabina na lulluɓe su,
na mike na soma tafiya..
kallon sama nayi hadari ya haÉ—u bakikkirin daga can kasa sai walkiya ake da rugugin tsawa da
alama dai anata zabga ruwa daga can da nisa,
ina tsaye ina tsinko abun da zan ci daga can nesa narika jin kugin ruwan nan yana karuwa
sosai ba kamar nasauran kwanaki ba ƙugi ne sosai mai matukar amon sauti sosai.
da sauri na juya na fito daga cikin bishiyoyin na nufi in da su Naseem suke kwance cikin
hanzari.
Daga can na hango ruwan yana wani irin gudu da kugi daga can da nisa yana wani sama da
kasa.
Huff na É—aga Nasmah na goya ta kana É—auki Naseem da gudu na juya ganin ruwan
yana haurowa a hankali inda muke yanata taruwa a hankali har ya wuce idon sawu na,
daga can cikin kogin kuma yana wani irin gudu yana yin sama da kasa sai ruwan ya haÉ—u da
junan sa ya fansalu sai yayi sama sannan ya koma kasa.
gudu nake da iya karfi na nayi bayan dutsai cikin sansanin tashin hankali galin ruwan ya iso
inda muke zama ya mamaye gurin wan da yake gudu daga can kuma sauran kiris yakaraso,
bayan dutsai da na ɓoyen ma tuni ruwan ya iso har gurin,
cikin kaɗuwa da tashin hankali nasoma hawa kan dutsan da ko a mafarki ban taɓa tunanin zan
iya hawan sa ba sai gashi na haura kan sa da goyo da kuma wani É—an a hannuna can kuma
saman sa sosai.
kan kace me ruwan yataho da wannan kugi da ambaliyar da yake,
gurin da muke zama yadawo tamkar cikin ainihin kogin hatta bishiyoyin nan sai da ruwa yahaye
kansu,
duk da girma da tsawon da dutsai É—in nan yake dashi sai da ya kusa haurowa sama in da nake
tsaye jikina na cirawa,
rumtse idanuna nayi nakuma buÉ—ewa cikin ruwan da yake wani irin gudu da kugi, ina ambaton
sunan Allah, yau kam nasan mutuwa ce yazo mana babu makawa ruwa ce zata zamo ajalin
mu,zata tafi da mu mu kuma mutu a cikin ta.
kankame Æ´aÆ´ana na kuma yi nagama sadakarwa na mika wuya ga mutuwa gaba É—aya.
wasu irin halittun ruwa narika gani daban-daban wani abun ma idan nagani rufe idanuna nake
da karfi har sai ya wuce kafin na buÉ—e,haka sukayi ta wucewa a kan ruwan,
wani abun da yadaÉ—a firgita ni da bani tsoro daga can najiyo guÉ—a mai karfi a can tsakiyar
ruwan guÉ—a mai tsawon gaske babu jan numfashi ko sauke wa,
ido na zuba sosai daga can in da guÉ—ar ke tashi sai dai banga komai ba sabo da sakanin mu da
nisa kuma da alama daga can kasa abun ke wuce wa.
sai narika jin kamar iska tana jana kuma karfin iskar tacikin ruwan ne,kuka na fashe dashi na
durkushe kan dutsai É—in na kankame jikina,ina ambaton sunan Allah.
har lokacin ban fasa jin iska na kokarin jana ba,
a hankali guÉ—an da ake yarika raguwa alamun yana yin nesa da ni,
iskar da ke jana kamar zai faÉ—ar dani cikin ruwan sai yarika sassauta, lokacin da na dai na jin
sautin guÉ—ar nan gaba É—aya iskar ta tsaya.
abun tun sassafe sai yamma can kafin ruwan yafara sassauta gudun da yake, yana sassauta
yana yin kasa-kasa,
a hankali yarika yin kasa yana wuce wa har ya dawo in da yake,
Numfashi mai cike da zallar tsoro na sauke a sannu narika bin gurin da kallo har zuwa gurin da
muke zama,
yashin ya daÉ—a wankuwa yayi fari soll sai dai har lokacin da jikan ruwa sosai a hankali nafara
kiciniyar sauka daga kan dutsan nayi matukar mamakin yadda akayi na iya hawa saman
dutsan,
daƙyar na iya sauka kasa.
a hankali narika takawa in da kafata har yana lumewa cikin saka sabo da har lokacin da dam
shin ruwa,
a hankali na matsa can gefe in da shima akwai damshin sai dai ba kamar in da muke zama ba.
ranar a nan muka kwana cikin ciyawa,
sai dai ban yar da na rumtsa ba dan gani nake kamar ruwan zai dawo....
Washegari da safe gurin ya daÉ—a sha ya tsantsame sai dai har lokacin da É—an damshin sai dai
ba kamar na jiya ba,
sai da rana yafito sosai kana
a hankali na É—auko su Nasmah muka dawo gurin zaman mu,
ido na kurawa kogin nan ganin yadawo yan da yake da, kamar bashi bane jiya yayi ta hauka
Allah mai iko.
É—an kwalin kai na na kunce na shin fiÉ—a a kasa kana na zaunar da Naseem a kai ina faÉ—in
"Zauna kada ka sauka kasa kaji gurin da sanyi".
da sauri na kunco Nasmah da take ta musu-musu tana kuka a abaya,
na zauna na basu abincin su,
sai dai har lokacin bata fasa kananan kuka ba,
jijjiga ta nashiga yi ina faÉ—in
"Yi hakuri Nasmah nasan wan ka kike so kuma nasan ruwan nan akwai sanyi kibari rana
yadaÉ—a yin zafi idan ruwan yayi É—umi sai na muku".
nayita jijjiga ta.
zuwa can an jima
jin rana yadaɗan yi zafi sosai sai na tuɓe su na dubi Naseem da ke zaune yana ta wasa da
yashin gurin nace
"Zauna na fara yi mata wanka sai na ma ka ko".
na mike da ita a jikina na isa gurin ruwan da muke wanka, ruwan yada É—a yin fari soll,
kasan cewar rana ya taso ruwan har yana kashe ido sabo da tsabar hasken da ya kara,
a hankali na fara yi mata wankan ina yi ina kawar da kai na daga kallon ruwan saboda kashe
min ido da yake, tamkar hasken ranar a cikin ruwan yake.
koda na gama yi musu wankan.
babu jimawa sukayi bacci,
mikewa nayi na koma gurin ruwan domin yin al'wala, na sun kuya ina ta kare fuska ta da hasken
rana ke haska cikin ruwan yana kashe min ido, na saka hannu cikin ruwan a hankali na É—ibo na
fara yin al'walar, na kuma mai da hannuna a karo na biyu, da sauri na ciro hannun jin na taɓa
wani abu, sai kuma na mai da hannun a hankali jin kamar dutsai ne na taɓan, a raina nake ai yana cewa
ai dutsan yashi ne,
na cusa hannuna nakuma É—ibo ruwan sai na haÉ—o da yashi da wani farin dutsai, ina É—ago
hannuna hasken rana ya haska dutsan tamkar wutan lantar ki mai hasken gaske. da sauri na
rumtsa idanuna jin hasken har cikin jijiyoyin idanuna, cikin hanzari na watsar da yashin gefe ina
mammatse idanuna, nayi al'walan da sauri na bar gurin...
koda yamma tayi da nazo yin al'walan la'asar lokacin rana tayi sanyi hasken ruwan yaÉ—an ragu,
ina saka hannuna cikin ruwan nakuma É—auko dutsai É—in,
A hankali na É—ago shi narika juyashi a hannunna dutsan fari soll mai kyau da shi sai kyalkyali
yake duk da kuwa babu hasken rana,
narika kallonsa gwanin ban sha'awa.
A hankali na mika hannu na É—auko É—ayan da É—azu nayi wurgi da shi na haÉ—a su ina ta juya su
cikin sha awa,
nakuma saka hannuna cikin ruwan nayi ta laluɓo duwasun ina ciro su sai da naciro guda takwas
na haÉ—a da biyun hannuna suka zamo guda goma,
bayan na gama al'walar na koma gun su Nasmah a kan abun goyon su na zuba duwasun,
ina zubawa kuwa da sauri har suna rige-rigen É—auka sukayi ta wasa da shi,
nima ina idar da sallar na zauna nayi ta tayasu wasan da duwasun gwanin ban sha'awa da kyau
da É—aukar ido.
dariya nayi ganin yanda suke wasa da duwasun su É—auki wannan su wurga sai subi sukuma
É—auko wa,
nace
"Kuma yayi muku kyau ko ai dutsan mai kyau ne nima wlh yayi min kyau kuyi wasan ku da shi".
nafaÉ—a da murmushi ina daÉ—a tura musu duwatsun gaban su...
Washegari ko da rana yafito dukan su na kwasa naje musu wanka Nasmah na goye sai na fara
yi wa Naseem ko da na gama mishi, sai na saka hannuna nayita laluma cikin ruwan can na ciro
dutsai É—in guda É—aya na dunkule shi cikin hannuna na cusa masa cikin hannunsa ina faÉ—in
"Gashi na karo muku abun wasa dun kule shi a hannunka kar ya kashe mana ido".
na kunce Nasmah na goya shi itama nayi mata wanka kana na laluɓo mata guda ɗaya na saka
mata cikin hannun ta nace
"Kema ga naki".....★
Zaune muke muna cin kayan itatuwan dana sinko mana shiru nayi tare da kasa kunne daga can
da nisa nake jiyo muryar kukan shanu,
da sauri na mike tsaye ina cigaba da baza kunnena ina son gane in da kukan shanun yake
fitowa,
duk da daga ji yana da nisa da mu sosai,
wani irin farin ciki ne da murna ya lulluɓe ni,
dan na tabbata shanu bazai zauna shi kaÉ—ai cikin daji ba sai da mutum.
cikin tsananin farin ciki da murna na sunkuya da sauri naÉ—au ki Nasmah ina faÉ—in
"Kuzo muje naji kukan shanu a tacan wata kila mu sami É—an uwan mu bil adam a gurin".
ina É—ago zanin goyon su duwasun da suke wasa da shi suka zubo kasa,
banko bi ta kan su ba na goya Nasmah da sauri na É—au Naseem da sauri nasoma tafiya.
har nakusa fita daga cikin bishiyoyin sai na juyo ina juyowa kuwa,
na hango duwasun suna wani irin walkiya kasan cewar lokacin rana yafara tasowa,
Naseem dake hannuna kuwa tsalle yarika yi yana nuna duwasun da hannu yanata kokarin
zame wa a hannuna,
murmushi nayi nace
"Oh Naseem dutsunan wasan ku ko bari naje na É—ebo muku".
na juya da sauri na ko ma gurin É—ankwalin kaina na ciro naÉ—ibi duwasun duka na zuba cikin É—an
kwalin na É—aure na rike a É—ayan hannuna,
na mike da sauri muka kama tafiya.
ta in da nafi zato da tunanin tanan kukan shanun ke fita na É—au hanyar da sauri.
sai dai munyi tafiya mai nisan gaske amma ban ga wani alamun shanukai ba hasali ma kukan
su da nake É—an ji yanzu na dai na, har na fara tunanin wata kila ma kunnena ne yajiye min ba
dai-dai ba.
a gajiye na ja na tsaya tare da waigawa baya a raina nake faÉ—in
"Zan koma kawai gara rayuwar can ya fiye min na ko ina acikin dajin nan".
ga mamakina sai naga nayi nisa sosai dan ko katon dutsai É—in nan bana hangowa na juya da
zummar komawa bakin kogin sai kuma na hakura ganin nayi nisa sosai.
gashi kuma yamma ta fara yi sai na zauna kawai a gurin a nan gurin muka kwana washegari da
safe ina zaune ina É—an gyangyaÉ—i dan jiya ban samu nayi bacci ba dan acikin sun kuru muka
kwana, kukan shanun nan irin na jiya shi ya farkar da ni firgigit na nimike da sauri.........!★
*Na jiya da gobe na baku*í ½í±Œí ¼í¿»í ½í¸†
Mommyn Twins ce
Zunbur na mike tsaye jin da gaske ba wai ko kunne na bane ke yi min karya kamar yan da jiya
nayi tunani,
da sauri na É—auki Nasmah na goya ta,
sannan na É—auki Naseem na rike shi,
na É—auki É—an kwali na da na É—aura musu duwatsun wasan su na rike a É—aya hannuna.
cikin sauri mai haÉ—e da gudu narika bin hanyar da nafi sammani da tunanin tanan ne kukan
shanun ke fi.
nayi ta tafiya idan naji shanun sun dai na kuka sai na tsaya na huta idan duka cigaba sai na
mike da sauri nacigaba da tafiya,
haka nayi ta tafiya ina yi ina hutawa duk san da shanun sukayi shiru idan suka cigaba da kukan
sai nima nacigaba da tafiya ta in da nake jiyo kukan su daga can nesa sosai.
nayi tafiya har na godewa Allah.
ina zaune a gindin wata bishi ina hutawa gaba ki É—aya jikina yayi sanyi dan tun É—azu da shanu
sukayi kuka basu kuma ba,
har nafara cire rai da sake yin kukan nasu zunbur na muke jiyo sautin su daga can kasa kuma
yanzu nafi jin murtar nasu yafi kusa dani akan na É—azu.
da sauri na mike na soma tafi
É—an tafiya kaÉ—an nayi da sauri naja
burki ganin rami a gabana,
in da nake tsaye kuma tudune mai tsawon gaske,
dan saura kiris na zurma kafata kasa.
daga can kasan shima duk daji ne da bishiyoyi,
daga kan tudun in da nake tsaye ina hango shanukai É—in can da nisa suna ta kiwo kasan cewar
a kan tudu nake.
kallon kasa nayi mai uban nisa da tsawo
"Taya zan iya sauka a nan gurin".
nafaÉ—a ina daÉ—a kallon kasan.
a hankali nafara bin gefe tacan ɗaya ɓarin gefen dama na,
ganin tacan É—in bai kai in da nake tsawo sosai ba,
a hankali nafara sauka ina takawa a hankali,sam naki yar da na kalli kasa sai naga ya daÉ—a yi
min nisa kaina kuma sai yarika juyawa sabo da nisan sa,
nayi rabin saka daga saunin sai kawai kafata ta sule na zame muka rika gungurawa kasa tuni
su Naseem suka saki kara mai karfi,
kan kace me Naseem ya suɓuce a hannuna ya ganaga can yafaɗi kasa,
Nasmah da ke baya na kuwa mukarika gungurawa da ita, cak numfashi na ya tsaya dan ganin
ina kokarin isan kasa da baya kamar an juyani sai kawai na faÉ—i da gefe a kan hannuna.
kara dukan mu muka sake da karfi cikin azabar jin yadda na faÉ—i kan hannuna tamkar hannun
zai ɓalle yabar jikina.
nayi-nayi na tashi na gagara tashi nafi minti goma kwance ko kyakkyawar motsi na kasa, ina
kallon
Naseem yashe a can gefe yana ta zandara ihu,
Nasmah ma sai ihu take tana goye a bayana har lokacin...
Nayi ta yunkurin tashi na kasa da kyar na kai É—aya hannuna na kunce zanin goyon ta kwanta
gefe tana cigaba da tsala ihu duk jikin ta ya kwakkwar jane,
hannuna da na faÉ—i a kansa na É—agosa da kyar kana da kyar na iya mike wa zaune.
yayin da hannun da na faÉ—i a kansan ke min wani irin zugi da raÉ—aÉ—i,
da kyar na yunkura na mike ina É—ingishi nazo gun da Naseem yake kife a kasa yana ihu,
na zauna na É—ago shi da É—aya hannuna mai lafiyar,
nashiga kakkaɓe masa jikin sa ina jijji gashi,
shima duk ya kukkuje a.
Nasmah ta rarrafo tana kuka ta zo in da muke na janyo ta na cigaba da rarrashin su,
duk abun da nake cikin dauriya kawai nake dan nima duk jikina a kukkuje yake,zafin raunukan
jikina bai kai na hannun da na faÉ—i a kan sa ba.
duk raunukan jikin yaran sai jini yake fidda wa.
rungume su na yi tare da fashewa da kukan azabar da hannuna yake min, ko matsi nayi da
hannun sai naji zafin har cikin raina.
Mun jima zaune agurin jin tamkar karamin zafin ake a hankali na lallaɓa da kyar na mike,
na kamo Naseem da hannun na mai lafiyar na É—agoshi da kyar na iya goya shi, dan shi yafi
Nasmah jin ciwo.
ina matse idanuna hawaye na zuba cikin jin azaba,
sannan na É—auki Nasmah na rike ta
a ɓarin hannuna mai lafiyar,
gefe na na waiga in da É—ankwali na dana É—aura musu duwatsun wasan su yafaÉ—i can gefe
shima na isa na É—au ka da hannuna mai ciwon,
Jin wani irin zugi da hannun yayi min sai na sake É—ankwalin kasa,
na juya ina faÉ—in
"Naseem Nasmah bazan iya É—auka muku abun wasan kuba hannuna yana min ciwo idan na
samu wasu zan É—iba muku a hanya".
a sannu na soma tafiya ina É—aga kafata ahankali-ahankali,
sai kuma na tsaya a raina nake faÉ—in
"To yanzu idan na tafi na bar É—ankwali na anan a ina zan samu abun da zan É—aura a kaina idan
na cire hijabi na na rufe su Nasmah da shi?".
nayiwa kai na tan bayar,
idanuna na rumtsa nasan idan na É—auka hannuna zai min zafi.
a raina nake ayyana na kunce Duwatsun na zubdasu sai na É—auki É—an kwalina nasan shi bazai
min nauyi ba.
na koma in da yake na É—auki É—an kwalin ina kokarin kuncewa nayi nayi na kunce na kasa
saboda da hannu mai ciwon ne jin hakan yana daÉ—a kara ramin zugin hannuna ne sai na bari.
na zaunar da Nasmah a kasa Sannan naÉ—an kunce zanin goyo na cusa É—an kwalin sakanin
bayana da jikin Naseem,sai na mayar na É—aura,
kana na É—auki Nasmah muka fara tafiya a hankali.
dan yanzu bana iya tafiya da sauri dan duk jikina ciwo yake min ga su Naseem har yanzu suna
ta kuka.
Idan muka É—an tafi kaÉ—an sai na sauke su na huta kana muku ma ci gaba,
Abun mamaki munyi tafiya mai nisa amma har lokacin bamu iso in da shanun nan suke ba,
daga can saman tudun da muka gangaro da nake hango su banyi zaton zanyi irin wannan tafiya
mai ni haka ba kafin na iso su.
a haka dai nayi ta tafiya har na