Showing 33001 words to 36000 words out of 49670 words
Chapter 12 - HAMDAH part 2 Complete Free pages By Rasheedat S Director .pdf
iso kusa da su,
wasu matasa Fulani ne guda biyu suke kiwon shanun,suna tsaye can gefe sai dai na lura basu
san da zuwa na gurin ba duk da dai sakanin mu da ɗan tazara,
a sannu na isa gindin wata bishiya na zauna kana na sauke su Naseem,
nayita rarrashin su Nasmah har sukayi bacci.
muna nan zaune a gurin har yamma sai sannan makiyayan nan suka fara kaɗa
shanukan,sunayin gaba,
Ganin haka na mike da sauri na ɗauki su Nasmah narika bin bayan su duk inda sukayi ina biye
da su,idan suka tsaya na tsaya idan suka cigaba da tafiya nima na bisu.
haka dai mukayi ta tafiya har naji badaɗi gashi babu halin nace zan tsaya na huta sutafi su
barni,
tafiyar nake ina matsar ƙwalla sabo da tsaɓar gajiya gajikina da ya daɗa kara yin tsami,
muna nan muna tafiya har guri yafara rufawa.
can naga shanun sun tsaya kana a sannu naga sunayin kwana can na hangi bukkoki gefen
bukkar cikin wani gurin da a ka zagaye shanun suka shiga, nan makiyayan suka fara ɗaure su,
a sannu na karaso gurin sai na tsaya gefe da garken shanun ina ta raba ido,
Fulani mazaunan gurin sunata harkokin su wasu daga kusurwa daban-daban suna ta ɗaure
shanukan su da alama suma yanzu suka dawo daga kiwo,
numfashi na sauke tare da yin murmushi cikin zubda ƙwalla gani na acikin mutane wan da
nagama fidda sammanin yiwuwar hakan,
a hankali na tako na tsaya kusa da garken shanun....
wani dattijo ne yafito daga cikin wani gidan da ke gefe da garken shanun,
kana yashiga cikin shanun cikin girmama wa da ladabi matasan makiyayan nan suka shiga gai
dashi cikin girmamawa,ya amsa cikin sakin fuska
kana yashiga tayasu ɗaure shanun.
jijjiga Naseem da yake ta musu-musu a bayana nashiga yi dan nasan yagaji ko kuma jikin sa
ya masa tsami dan yabugu sosai,ina matse ido hawaye na zuba,
tuni Nasmah ma ta saki kuka, sai na cigaba da gargiza su ina hawaye,
yan da nake girgiza sun hakan yasa hannuna ke girgiza zafi har cikin raina.
da sauri dattijon nan yafito daga cikin garken shanu yana ɗan waige-waige da alama dai kukan
yaran yaji yasashi fitowa duba da yan da yake ta ɗan waige-waige,
nan idanunsa ya sauka kanmu da mamaki yake kallona kana yace
"Ke wanene me kike yi a na?".
yayi maganar idanunsa a kaina cikin hausar sa da bata tsaya ba,
banyi magana ba sai masar ƙwalla nake,
"Ke wanene nace me yasa mi yaron?".
cikin zubda ƙwalla nace
"Munfaɗi ne shine yaji ciwo kuma yunwa suke ji".
"Yunwa?".
yafaɗa yana kallo na".
na gyaɗa kai na alamar Eh, yaɗan yi shiru yana kallona,
kana ya kalli su Naseem da Nasmah da kyau sannan yace
"Garin yaya kuka faɗi haɗarin mota ne ina zaku je??".
yajero min tambayar
nace
"Acan kan tudu muka faɗi kuma Yola zamu".
shiru yakumayi alamar nazari kana yajuya tare da faɗin
"Kubiyo ni".
ai ko da sauri na bi bayan sa.
ya shiga gidan tun daga bakin kofa yake faɗin
"Sumaye Sumaye Sumaye".
wata yarin yar dake zaune a tsakar gidan ta mike tana faɗin
"Inna wuro Bappa na kira".
wata dattijo war mata tafito daga cikin bukko da sauri tana amsa kiran sa,
tare da faɗin
"Gani nan Malam".
yace
"Zo ga wani bakuwa nan tazo kuma wai yaron ta ya faɗi a kasa kuma yana jin yunwa bashi
abinci yaci".
tace
"Subhanallahi kawo shi nan mugani garin yaya?".
namatso in da take tana kokarin karɓar Naseem dake ta zandara ihu, garin cirosa sa a bayana
sai ta bige min hannun,
yarfe hannun nayi tare da faɗin
"Wayyo Allah hannuna".
tace "Ayya Allah kam sansu ke ma hannunka na siwo ne?".
kai na gyaɗa cikin zubda ƙwalla nace
"Eh da muka faɗi ne nima na buga hannuna".
kallon yarinyar dake zaune a gefe tayi tace
"Zo Mero kikarɓa mata yaron hannun ta".
yarin yar ta matso da sauri ta karɓi Nasmah,
tace
"La Inna wuro itama taji ciwo".
Inna wuro tace
"Oh wani irin faɗuwa ne haka sai kace haɗarin mota".
tafaɗa tana roko hannuna tare da cigaba da faɗin
"Ko dai haɗarin mota kukayi ne".
yarfe ɗaya hannun nayi nace
"Wayyo Allah na".
Inna wuro tace
"Malam itama ta buga hannun ta inaga tayi targaɗe a hannun".
"Nima dai haka nace kamar wan da suka faɗi a mota".
yamatso kusa da ni yana faɗin
"Naga hannun".
naɗago haka na mika masa yarike yana ɗan jujjuyawa,
rumtsa idanuna nayi da karfi ina faɗin
"Wayyo Allah wayyo Allah".
yace "Sannu kinyi targaɗe ne".
sai ya saki hannun
"Bari nakawo magani nasha maku".
Bappa yafaɗa yana shigewa cikin bukko,
ni dai yarfe hannun narika yi ina matsar ƙwalla.
yana shiga yafito da wasu robobin mai guda biyu, ya dawo in da nake.
Inna wuro tayi sauri ta ɗauko taburma ta shin fiɗa tace na zauna,
na zauna shiko a kan kujera ƴar tsuguno ya zauna kana yaruko hannuna yaja yaja yajijjiga shi
da ɗan karfi, kara na sake cikin jin azaba har cikin kokon zuciya ta, ina shushshure kafafu kasa
kamar zan saki fitsari a jikina.
kana yabuɗe ɗaya daga cikin roban mai daya fito da su ya lakato maganin ciki yashafa min a
hannun da tuni yahaɗa zufa,kana ya saki hannun yana yimin sannu.
Inna wuro tace
"Sannu zakiji daɗi har kiyi bacci".
kai kawai na gyaɗa mata ina matsar ƙwalla, na matsa baya na jingina da jikin garu ina rike da
hannun da ɗaya hannuna...
ya karɓi Naseem yashafa masa maganin dake cikin ɗaya robar a duk kanin ciwukan jikin sa,
yana yi yana ɗan mammatsa jikin sa har ya gangaro kasan kafar sa ai ko yana rike guiwar kafar
sa yakara sautin kukan sa yana kankame jikin sa,
kafar yarike da kyau yaja sai ga kafar tayi kass,
Maganin da yashafa min a hannu yashafa masa a kafar yana faɗin
"Gocewar kashi ne".
kana ya mikawa Inna wuro shi ta karɓe shi tana girgiza shi da yi masa sannu,
nan ya karɓi Nasmah itama ya sha fa mata bayan yagama dudduba jikin ta ko itama da buguwa
ko gocewar kashin a jikin ta,sai dai ita ba a samu gocewar kashin ba sai dai buguwar kawai...
Ina zaune nayi jugum zuwa lokacin kam alhamdllh zafi da zugin da hannuna yake min sai
raguwa yake,
ido na zubawa su Naseem da ke jikin Inna wuro sunyi shiru sunata rarraba ido,
Bappa kuwa tun da yagama shafa mana maginin yamike yafiya sai yanzu yashigo rike da
kwarya a hannunsa,
ya karaso in da muke ya mikawa Inna wuro kwaryar yana faɗin
"Basu susha dan su daɗa jin karfin jikin su".
Inna wuro ta amsa
tare da faɗin
"Dama yanzu nake shirin aiken Mero taje ta tatso musu madarar".
ta aje kwaryar ta mike da sauri ta shiga bokkar dake gefe da mu tafito da kwarya da ludayi guda
biyu,
ta raba madarar biyu ta mika min rabi kana ta zauna tana ɗibawa da ludayi tana baiwa su
Naseem,
ai ko suka karɓa suna ta sha,
A hankali na ɗibo nadarar cikin lodayi nakai bakina,
lumshe idanuna nayi jin ɗumi da garɗin madarar ya ratsa ni,ai ko na gyara zamata sai gashi na
shanye madarar tass har ina tanɗe baki...
Bappa ya fito da shirin tafiya masallaci ya dube ni yana faɗin
"To ni zan tafi masallaci yanzu ina zakuje tun da naga kun gama shan madarar?".
kaina a kasa nace
"Yola zanje".
suka haɗa baki da Inna wuro wajen faɗar. "Yola??".
Bappa yace
"To ke da zakije Yola me ya kawo ki rugan nan Yola da yake tacan gefe Yola da yake tacan
mezai sa kibiyo ta nan?".
ko mai ban ce ba sai kasa da kai na da nayi.
da sauri ya juya yanufi kofa yana faɗin
"Bari na tafi kar na rasa sallah".
a hankali na mike nace
"Ni ma zan yi sallar".
Mero ta mike da sauri ta zubo min ruwa a buta ta mika min tare da nuna min banɗaki.
na je nayi sarki kana nafito nayi al'wala,
koda na fito na samu Inna wuro ta shinfiɗa min sallaya Mero kuma na rike da Nasmah sai wasa
da gashin kanta daya cukuikuye take,
bayan na idar da sallar ina zaune kan taburma tuni su Naseem sun yi bacci,sai na gyara musu
kwanciya kan taburman na rufe su da abun goyon su.
Mero da Inna wuro ma duk lokacin sun shiga yin sallah..
ina zaune jigum...
Bappa ya shigo da sallama,
na amsa kallon in da su Naseem suke kwance yayi kana yace
"A'a ya zaki kwantar da yara a wannan gurin sanyin ke bakyajin sanyi?".
murya ya ɗagaga yashiga kiran Mero,
da sauri Mero ta fito yace
"Kira Sumaye tazo ta ɗaga yaran nan anan ya za'a barsu cikin sanyi".
da sauri Inna wuro tafito tana faɗin
"Ai kwanciya sukayi ne".
ta dube ni tana cigaba da faɗin
"Ke ma in kin gama ki taso a sanyin nan".
ta ɗauke su ta kaisu ɗaki.
numfashi na sauke wai yau mu ake ce wa mutashi a cikin sanyi kar sanyi ya kamamu Allah
sarki rayuwa bayan acikin ta mukayi rayuwar wata biyu da ɗori..
A sannu na mike nabi bayan su muka shiga cikin bukka.
abakin gado gado irin na Fulanuka in da aka kwantar da su Nasmah na zauna.
tace idan ina jin bacci na gyara na kwanta a gefen su,a hankali kuwa na gyara dan kuwa baccin
nake ji...
Washegari da safe bayan mun karya da lafiyayyen tuwon gari miyar ɗanyen kuka wan da yaji
man shanu, muka kara da kunu.
Bappa ya shigo da madara acikin kwarya mai ɗumi ya bawa Inna wuro yace ta bawa su
Nasmah,
guri ya samu a gefe ya zauna kana ya dube ni sannan yace
"To yanzu kam gari ya waye bakuwa idan kika fita zaki sami motar tafiya Yola dan daga nan
babu wani nisan kirki sosai".
Kai na akasa na amsa da to,
mikewa yayi yashiga bukkan sa ya fito da robar maganin da jiya ya shafa mana,
ya dawo ya zauna yaɗau ki Naseem yana shafa mishi maganin a guraren da yaji ciwo yace
"Amma kam dai haɗarin mota ne wannan sai yau na daɗa ganin raunukan ashe da yawa ko
ɓarayi kuka haɗu da su a hanya suka yi muku duka haka,dan yanzu ɓarayi rashin imanin su
gaba yake har yara ma basu bari ba".
ƙwalla naji ya cika min ido tuno da yadda akayi muka ji ciwon, cikin zubda ƙwalla nace
"A'a ba hatsari ko dukan ɓarayi bane faɗowa mukayi daga kan wani tudu".
da mamaki Inna wuro tace
"Ikon Allah garin yaya?".
Bappa yaɗan sakai ta shafa masa maganin yana faɗin
"Garin yaya a ina kuka sami tudu ku da kuke mota ba tafiyar kafa ba kuma kince ba haɗari
bane".
nace
"Eh acan cikin daji acan ta wani guri da nisa zamu zan sauka a kan tudun shine na zame shi
kuma ya suɓuce a hannnuna ya gungura yafaɗi kasa ita kuma tana bayana tare da ita muka
isa kasa shine na faɗo a kan hannuna".
gaba ɗayan su suka zuba min ido alamun na zartata da kuma magana ta kana Bappa yace
"Menene yakai ku cikin daji da har kuka kai ga jin rauni??".
kasa nayi da kai na ina wasa da ƴan yatsu na yayin da gudun hawaye na suka tsananta cikin
rawar murya da kuka ke son kwace min.
a hankali nafara basu labarin rayuwa ta tun daga farko har yau da nake zaune a gaban su.
Salati Inna wuro ta sake gaba ɗaya jikin ta yagama yin sanyi har sai da taɗiga ƙwalla cike da
tausaya wa rayuwar mu,
Bakin zanin ta takai tashare ɗan guntun kwallar da ya fito mata tana faɗin
"Ikon Allah lallai kinga rayuwa rayuwar ki abun a duba ne, me kika tsare wa mutanen nan da
zasu jefaki cikin wannan mawuyacin hali, har ya shafi yaran da basusan kansu ba bare susan
mecece duniyar, wannan wani irin zalunci ne".
Inna wuro ta karashe maganar tana jan hanci.
Bappa kuwa kai ya jinjina cike da dattako
sannan yace
"Allah mai girma da ɗaukaka,
lallai Allah shi ke kare ba wansa a duk inda yake, yatsare ku yakuma kare ku da sharrin
namomin daji masu cutarwa har kuka fito batare da cutar wan wani dabba ba,".
shiru Bappa yayi tare da zuba min ido na ɗan wani lokaci zuwa can kuma sai ya girgiza kan sa
sannan yace
"Mutane dai ko da yaushe burinsu su zalunci ɗan uwan su ko ribar me zasu ci da yin hakan?."
yayi maganar yana mike wa,
da sauri Inna wuro ta ɗago tana duban sa,
in da buta yake yanufa yasun kuya yasoma al'wala yana idar wa ya mike, yashige bukkar sa.
numfashi Inna wuro ta sauke,
tare da mai da duban ta kaina
tace "Allah ya tabbatar da alkhairi".
Amin nace batare da sanin inda batun nata ya dosa ba.
bayan Bappa nabi na kallo ganin yayi al'wala kuma lokacin sallah baiyi ba...
Muna nan zaune can yafito rike da jarbi a hannunsa bakinsa na motsi alamun lazumi yake, in
da yatashi ɗazu yadawo ya zauna,
numfashi yaja ya sauke tare da yin gyaran murya sannan yasoma magana
"Hakika asiri akayi miki mummunar asiri ma kuwa,
wanda ya sa akayi asirin da wanda ya ai kata sihirin babu imani azuciyar su,
bakin sihiri ne mai matukar duhun gaske, rashin imanin wan da ya ai kata abun yakai yakawo,
dan kuwa asirin ba zai taɓa karyewa ba har sai shi bokon da yayi asirin ya muku,
mutuwar sa shine lakanin karyewar asirin,
tabbas wan nan yacika mugu mara imani,
babu kuma wan da yasan ranar mutuwar wani sai Allah, Allah Ya takai ta ma dan basuso abun
ya tsaya iya haka ba, yana ai ki da babaken aljanu marasa imani,
sunso kiyi gaba can da nisa basuso kitsaya iya nan ba,
sai dai sun mance Allah baya bacci duk kuma wan da ya dogara da shi baya taɓewa addu'a
kuma makarin mumini sam addu'a bata faɗuwa kasa,
da yar dar uban giji bazakiyi gaba ba kamar yan da suka so, zamu gwada musu karfin ayar
ALHAH!".
cikin matukar mamaki da kaɗuwa nake kallon Bappa to wacece Ni da har wani zaiyi min asiri,
ni dai nasan anyi min kazafin da har na mutu bazan taɓa mancewa da shiba,
to wacece ni da har wani zai nimi yin asiri a kai na.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un".
nafurta daga zuci har kan laɓɓana.
Inna wuro ma salati ta saka tana faɗin
"Ikon Allah lallai mutum abun tsoro ne Allah ka shiga saka nin nagari da mugu"...
sun jinjina lamarin sosai tare da tausaya min kwarai da gaske...★
Tun daga wannan ranar bacci na yadawo rabi,
dan kuwa daga zaran dare ya tsala Bappa zai cewa Inna wuro tata tashe ni yace nayi al'wala
nayi salla, yakuma bani Kur'ani nayi ta karatu har sai asuba tayi idan nayi sallar asuba sai na
kwan, nan ne zan yi bacci mai tsawo.
A ɓangaren sa kuwa shima babu dare ba rana kullum zaka gansa cikin yin Sallah da karatun
Alqur'ani,
Bappa babban malami ne kuma limami acikin ɗan rugar tasu,yana da ɗalibai magidan ta da
yake koyar da su kullum duk bayan sallar asuba,
sai ya zamana da yanzu ya kara musu lokutan darasi bayan sallar isha zasu yi da asuba ma
suyi.
zuwa wannan lokacin targaɗen hannuna ya warke. da duk raurukan jikin mu dan kullum Bappa
sai ya shafa mana magani.
★★★★
*After 3 month*
★★★★
Zaune muke a bakin gado bayan Inna wuro tayi musu wanka ina shafawa Naseem mai Mero na
gefe tana yiwa Nasmah kwalliya da kayan kwalliyar ta sai dariya nake musu ganin yan da take
ta zana mata fuska da kwalli irin kwalliyar su na Fulani.
ina gama shafa masa na mike na ɗauko kayan su guda ɗayan nan wanda dashi mukayi ta
rayuwa a daji,
kullum idan na sa musu idan yayi datti sai na cire musu na wanke,yagama koɗewa har ba a iya
gane kalar kayan saboda yayi fari wani gun ma duk ya yayyage.
shekaran jiya Bappa ya siya musu yadi irin na Fulanuka yaba da a ɗin ka musu,
yace idan aka ɗin ka musu wancan ɗin na dai na sa musu waɗan nan kayan sun mutu.
na mikawa Mero kayan Nasmah nace
"Gashi idan kika gama mata kwalliyar sai ki sa mata".
tace
"To adda HAMDAH ba Bappa yace a daina sa musu waɗan nan kayan ya tsufa ba".
nace
"Eh to ai ba a amso na gun ɗinkin bane shi yasa zan sa musu wannan ɗin".
tace "To bari na gama mata kwalliyar sai na goye ta muje gun telan mu karɓo".
Nace to.
sallama Bappa yayi daga can waje, Naseem najin muryar sa yakama salle yana mika hannu,
dan yanzu sun saba sosai dan ko masallaci zai je yarika kuka kenan sai yaje da shi,
in ko zaije duba shanukan sa sun dawo daga kiwo sai ya ɗauke shi sutafi tare.
in ko Bappa na waje ya ɗan jima bai shigo gida ba sai yaɗau hanyar kofar gida dan yanzu
tafiyar sa ta ya fara kwari.
ganin yana ta tsalle yana nuna kofa da yin kwalaɓe yana faɗin
"Pappa Pappa".
sai nayi murmushi ganin karfi da yaji yana son yayi magana,
Inna wuro dake bakin kofa tayi dariya da faɗin
"Yana kiran mutumin shi ɗaga murya da karfi bai jika ba".
nace "Ai kam gashi nan sai tsalle yake kamar zai tashi sama".
Mero tace "Yi sauri Adda ki gama sa mishi kayan sai na kai shi".
nace to, hannuna na kika ta baya na janyo