Showing 21001 words to 24000 words out of 46754 words
Chapter 8 - A WATA MASAURAUTAR (1 to End) Book Complete by Ummu Safwan .txt
ganin yayi tabud'e idanunta,
zurbur tayi tamik'e zaune tanaimasa kallon tahuma, tace "to Allah yakamaka, mekakeso ka aika mun?" Rayfen d'ina zakayi kome kake nufi?"
Shi kuma kunya duk ta lunlub'esa, amma sai ya wayance ya mere baki, yace mezanyi dake?" dibeki, dan Allah malama kitashi na maidake inda na d'aukoki,domin inada abunyi, yana kaiwa nan yanufi hanyar waje yabarta a nan zaune."
Ganin yafita, itama ta mik'e tabi bayansa, ta tarar dashi har yashiga motarsa ita kad'ai yake jira,
Tana zuwa wurin Taja tayi tsaye jikin motar taki shiga,
shima ita yake kallon cike da mamaki,
Saida suka d'auki kusan minti 30 yaga batada niyar shiga motar,
Bud'e murfin motar yayi yafito yana huci, yace "dan Allah malama idan bakitashi tafiya ba, ki kauce kibani hanya na wuce, domin ni inada abunyi,
Bata kallesaba kuma bata d'aga daga inda takeba,
Ganin zata b'atamasa lokaci yaja hannunta yabud'e murfin motar ya turata a ciki,
Yazagaya mazauninsa yashiga yatayar da motar suka bar gidan,
Kallonsa takeyi cikin k'asaita mulki tace "a she kasan abunda nake nufi?"
Ya zama Dole abud'ewa gimbiya mota idan tazata shiga,
Be tankamata ba domin ya fahimci neman magana take dashi, yaci gaba da tuk'in motarsa."
Hanyar makaranta yanufa da ita, zai ajiyeta a inda ya d'auketa,
Tsayarda motarsa a cikin makarantar yayi daidai da gaba d'aya d'alibai sunfito lacture motar prince na tsayawa sai a kan idon Safeenat dake zaune tayi tagumi tana tunanin Bilkisu
Atake gaban Safeenat yafad'i da tahango Bilkisu a cikin motar prince,
Wata irin k'ara tasaki tazubar da littafan hannunta, wadda taja hankalin d'aliban makarantar gaba d'aya a gareta domin ganin meke faruwa?"
Wurin Bilkisu tanufa da gudu, ta rungumeta tana zubar da hawaye,
Kallo d'alibai suka bisu dashi, suna mamakin ganin Bilkisu tafito a motar prince, domin suna da labarin b'acewarta yau kwana biyu kenan,
Safeenat tamaida kallonta a wurin prince dake tsaye a bakin motarsa,
Tanunasa da yatsa idanunta cike da hawaye, Tace "wannan azzalumin ne yad'aukeke?"
Wlh Allah saiya sakamaki,
Ta kuma rungume Bilkisu tana kuka tace "sister ina fatan beyimaki komaiba.
Bilkisu ido cike da hawaye ta kalli Safeenat ta kuma juyawa ta kalli mutanen dake kallonsu jira sukeyi suji dalili,
Tace " jama'a kudibesa,
tayimasu nuni da prince dake tsaye cike da mamaki,
Ko wannesu ya maida kallonsa a wurin prince
Tace shine yasace ni,
da kansa bawai sanyawa yayi a saceniba,
a matsayinsa na d'an sarki meye hukuncinsa?"
Kowa shuru yayi, rike da baki, yana kallon prince cike da mamaki,
Ta kuma matsawa kusa da shi ido cike da hawaye tace " nace banasonka, kakirani a waya, katuramun sak'on text duk a kan nayi hakuri nasoka, domin ka fahimci cewa ni 'yar sarkice,
Nanumaka bana ra'ayinka, bana iya soyayyah dakai, shine kasace katafi dani gidanka domin kayi rayfen d'ina,
To Allah yafika azzalumi mai mugun nufi, Allah zaice gaba da tsareni daga shairinka,
Aikuwa a nan d'alibai kowa yasaki baki da kunne, suka had'a baki sukace fed'e🤔 to Allah ya kyauta
Amma dai prince kabamu mamaki🤔 kowa ya kama gabansa yana fad'in albarkacin bakinsa,
Safeenat tamatso kusa gareta ta dafa kafad'arta tace sister ina fatan beketa maki haddiba?"
"tanunasa da hannu tace "Allah yafishi,
Allah ya kwaceni a hannun azzalumi irinsa,
Amma kasani bazan barkaba har saina d'auki fansar saceni dakayi kwana biyu batare da hakkina ba,
Prince mutuwar tsaye yayi yana mamakin makirci irin na 'ya mace, yanuna kansa cikin sarkewar murya yace " rayfen nizanyi rayfen d'inki?"
Me gareki wadda zaibani sha'awar da zaisanya nai maki fed'e?"
To bari kiji ni har yanzun banganki a mace ba.
Amma idon hakan kike buk'ata zan aikata maki basai kin had'a dayimun k'azafiba.
Idanunsa sunkad'e sunyi jajir alamar ransa yab'aci sosai, yashiga motarsa yayi tafiyarsa
Tok'i yake yana tunanin tuzarcin da Bilkisu tayimasa a bainar jama'a,
Ya kaiwa sitiyarin mota doka, had'i da Jan wani dogon tsaki,
Tambas zand'auki mataki a kanki Bilkisu,
Ba 'yar uwata kikeba ko ciki d'aya muka fito dake saina d'aukar maki mataki mai muni,
Wadda yafi fed'e ciyo."
Writing by
Fareeda
Bashir✍🏻
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
A WATA MASARAUTAR...
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
Page 2⃣8⃣ 2⃣9⃣
Gudu yake a kantiti kamar ba'a hanyacinsa yakeba, Allah ne kadai yakawosa gida lafiya,
Aguje yashigo da motarsa ya ajiyeta parking space, a can ya hango Bahijja da Fahad suna tattauna maganar aurensu,
Ganinsa dasukayi yashigo ba a hayyacinsaba duk Kansu sukashi mamaki meke damun?"
Fahad yace "kwana biyun nan yarasa abunda kedamun prince kullom cikin k'unci yake ba fara'a a fuskarsa, duk yashigo gida baya kula duk wadda ke masa magana, yanzun diba kigani yanda yashigo gidan nan kuma a haka zai rab'amu yawuce batare da yayi makowa maganaba a cikinmu
Bahijja tace "wlh kuwa nima hakan nakeganinsa kullum cikin damuwa,
Basu gama rufe bakinsuba yanufosu idanunsa sunkad'e sunyi jajir,
Kallon tuhuma suka bishi dashi gaba d'ayansu, suna jiran suji tabakinsa.
Ya k'ak'aro murmushin dole, yad'an saki fuskarsa yace "amarya da ango kunan zaune ashan soyayya,
Fahad betanka masaba,
sai Bahijja ce tace masa "zaunan kowa yayi aure yabarka,
baka daniyar yin auren, sai fama kake da bak'in rai tsakankanin nan gidan nan kowa maganarka yakeyi anrasa abunda ke damunka,
Sai a lokacin Fahad ya kallesa yace,
Idan kaga dama memartaba na nemanka.
Ya kalli Fahad yayi dariya domin a yanayinda yayi masa mgana ya fahimci fushi yakeyi dashi.
Ya kuma maida kallonsa a Bahijja yace Anty Bahijja na tambaye?"
Bahijja tace "ina saurarenka Adnan Allah yasa nasan amsar tambayarka,
Yace "waini ina k'auwar nan taki Bilkisu?"
Bahijja tace "Allah sarki Bilkisu baiwar Allah, tana nan lafiyarta k'alau anan garinma take karatu,
Adnan yace ce wata yarinya ce mukahad'u da ita a makaranta naji ina mutuwar sonta,
Kamarku d'aya da ita sak,
Duk damuwarda kukaganni nashiga kwana biyun nan, duk a kantane,
Ina tunin a raina cewa kamar Bilkisu ce domin kamarku haryab'aci, kinsan tunlokacin da Bilkisu nak'ara rabona da ganinta.
Fahad yace "ina zakasanta tunda bakason zumunci,
Farkon ganinka da Bahijja ai kasa ganeta kayi sai daga baya sannan kaganeta,
Adnan yayi murmushi a zuciyarsa yanason ya tabbatar da Bilkisu 'yar uwansa ce?" Itace k'auwar bahijja kuwa?"
domin yasan kalar hukuncin da zai d'aukar mata, dan yayi alk'awali da rayuwarsa tunda tayimasa k'azafin yatashi yin rapean d'inta,
A gaban bainar jama'a to tabbas tunda hakan takeso zai aikatashi a kanta, ko kuma yayi mata abunda yafi rapean ciyo."
Yace Anty Bahijja don Allah kid'an nunamun photo nan Bilkisu a wayarki nagani, domin na tabbatar da k'auwatace tashiga birnin zuciyata.
Dariya sukashiga yimasa gaba d'ayansu,
Fahad yace Ashe soyayya ce take neman ta zautarmun da d'an uwa, muka rasa gane kansa a gidan nan,
Bahijja ya takamomasa photo nan Bilkisu tanuna masa tace kaganta nan, Allah yasa dai itace tanemi zarar dakai,
Yayi dariyar da tafi kuka ciyo shekad'ai yasan abunda ke zuciyarsa,
Ya amshi wayar yashiga diba photo nan Bilkisu,
Ganin photo Bilkisu dayayi ya tabbatar da ita d'in daice, yayi saurin mik'ewa tsaye yana fad'in tabbas itace itace wlh,
Gaba d'ayansu dariya suke masa a ganinsu ya zare a soyayyar Bilkisu.
Cikin dariya Bahijja tace zauna mana Adnan muyi magana.
Sai a lokacin ya nemi wuri ya zauna,
Tareda cewa Anty Bahijja kuna kama da ita sosai,
Inason natuna da wani abun shin Ku biyu ne 'ya'ya mata a wurin Ammi ko?"
Bahijja tace kwarai kuwa, mu uku ne 'ya'ya a wurin Ammi yaya Abdulraham shine babba sai ni, sannan kuma Bilkisu ita k'arama a d'akinmu wadda gaba d'aya halinta ya babbanta da nakowa a familynmu,
Saboda kyawawan halayanta maimartaba yafi sonta a cikin 'ya'yansa.
Yacije baki yace Anty Bahijja inason Bilkisu kuma aurenta zanyi,
Wlh idan bansamu Bilkisu ba zan iya rasa rayuwatah.
Kitaimakeni Anty Bahijja kibani Bilkisu.
Dariya sukadinga yimasa gaba d'ayansu lokaci d'aya duk yafita hankalinsa a kan soyayya,
Fahad yadafa kafad'arsa yace "ka kwantar da hankalinka Adnan indai Bilkisu ce kasanyawa rayuwarka tazama matarka,
Yanzun katashi katafi kaji kiranda maimartaba yake maka daga can kafad'amasa k'udirinka a kan Bilkisu.
Mi'kewa yayi yanufi sashin maimartaba, a zuciyarsa kuwa yana Addu'ar Allah yasa kudirinsa ya cika."
Writing by
Fareeda
Bashir✍🏻
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
A WATA MASARAUTAR..
👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
3⃣0⃣ 3⃣1⃣
Dashigarsa sashin maimartaba,
Ya tarar dashi zaune rik'e da jarida a hannunsa yana karatu.
Sallama yayi masa jiki ba gwari yashiga cikin d'akin,
Yanemi wuri ya zauna a k'asan
gefin k'afar maimartaba , ya sunkuyar da kansa k'asa,
yace "Allah yataimakeka Allah yakara maka lafiya ranka ya dad'e gani yarima Fahad yace kana nemana.
Maimartaba ya maida kallonsa akan Adnan yaga duk yarame masa yayi bak'i.
Sannan yayi kyaran murya yace "Adnan waimeke damunka?" Kwana biyu na lura dakai bakacikin hankalinka?"
Meke damunka wadda mu mahaifanka bazaka iya fad'a mana shiba,
Tun shekaran jiya nasanya d'an uwanka Fahad yakiramun kai domin mutattauna akan tafiyar da zamuyi a gobe zuwa yola, domin nemawa Fahad auren Bahijja,
Amma dazarar antukari d'akinka sai aji kofa a rufe harka fita."
Ina kake zuwa?"
Meke damunka wadda a matsayinmu na mahaifanka bazaka iya fad'a mana Shiba?"
Adnan yasunkuyar da kansa k'asa yace "ranka ya dad'e tuba nakeyi,
Munkun fara jarabawa karatu ne yake hanani sukuni kwana biyu nan, kayi hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwaba, tuba nakeyi.
Maimartaba yayi murmushin jin dad'i
Yace "meye shawararka na tafiyar da zamuyi yola gobe Neman auren Fahad da Bahijja?"
Banida wani buri a rayuwata illah naga na aurar daku lokaci d'aya dakai da d'an uwanka, amma kai har yanzun ba kasamu matar da kakeso ba,
Mamynka tasha nema maka 'ya'yan k'awayenta amma gaba d'ayansu bbu wace tayi maka a rayuwarka,
Adnan yakuma sunkuyar da kansa k'asa yace Allah ya taimakeka ai nesa tazo kusa,
Murmushi jindad'e yayi, yace "Allah yasa cemun zakayi kasamu matar aure, danafi kowa jin dad'i,
Sai na had'aka da d'an uwanka na aurar daku gaba d'aya.
Adnan yayi murmushin jin kunya, yace "kusan hakan ne ranka ya dad'e,
Maimartaba yace "Alhamdulillah.
'Yar waya?"
A wace unguwa take?"
Waye mahaifinta?"
Adnan yayi murmushi ya sunkuyar da kansa, yace Allah ya taimakeka k'auwar Bahijja ce Bilkisu, tare muke karatu da ita, kuma munfahimci junanmu tana sona Nima inasonta, Abba ka taimakamun karnasa Bilkisu.
Maimartaba yace Alhamdullah abu yazo gida kenan, amma naji dad'i sosai Allah yasa abukanin arzikinkune.
Murmushi yake yana cike da jin kunya ya amsa da Amin Abba,
Mikewa tsaye yayi zaitafi d'akinsa, yace Abba natafi sai da safe,
gobe tafiyar safe zakuyi kuwa?"
Maimartaba yace "tafiyar safe nakeso muyi in Allah ya yarda.
Allah ya tsareku Abba ya kuma kaiku lafiya dawo mana dakai cikin koshin lafiya.
Cike dajin dad'i Abba ya amsa da Amin Adnan.
Yafito yanufi d'akinsa shekad'ai yasan abunda ke cikin zuciyarsa.
Shigarsa d'akin yacire kayansa, yana mai dariyar mugunta yana fad'in gimbiya Bilkisu kenan kinshigo hannuna zanwula k'antaki yanda naga dama, domin ba d'igon sonki a cikin zuciyata ko d'aya,
kuma dole kiyi biyayya saboda kina k'arkashin inuwar aurenah,
Zanyi amfani da wannan damar na aure ki domin nad'auki famsar abunda kika aikatamun a gaban bainar jama'a.
Ya kuma yin murmushin mugunta, yacije baki, yace "nalura da idanunki saikin buk'atar d'a namiji,
da wannan zanyi amfani, na azabtardake azaba mai tsanani, saikinyi danasanin aurenah rayuwarki."
Yayi kwanciyarsa yana tunanin mugunta iri iri a rayuwarsa."
Maimartaba sarki Bashir mahaifinsu Adnan yasauka garin yola lafiya,
Inda yasamu tarba da karramawa a masautar yola,
Yayi farin cikin karramashi da akayi,
Daga nan yashiga fad'awa mai martaba abunda ke tafe dashi."
yazo neman auren Bahijja da Bilkisu,
Sarki Abdulraham yaji dad'i kuma yayi farinciki da zuwan nasa,
yace " aidakayi zamanka ba saikazoba ko aike kayi ya wadatar, kuma Bahijja da Bilkisu 'ya'yankane duk yanda kazartar da hukunci a kansu dai dai ne, ba saika taso tun daga kano zuwa yola nemawa Fahad da Adnan aureba.
Amma wani hanzari ba guduba, 'yarka Bilkisu karatu takeyi bansaniba ko Adnan zai iya jiranta harta kammala karatun nata sannan daga baya sai ayi bikin nasu, a lokacin ta mammals karatun nata.
hakan naga yafi.
Sarki Bashir yayi murmushin jin dad'i yace Bakomai hakan da katsara yayi dai dai zanje na shawarci Adnan idan yanada ra'ayin barinta karatu bayan anyi auren saitaci gaba da karatun dama kuwa makarantarsu d'aya.
Murmushi sarki Abdulraham yayi yace "hakan shine daidai idan ya amince sai ayi auren gaba d'aya,
Nima zankira Bilkisu domin naji ra'ayinta a kan hakan,
A haka sukayi sallama suka rabu cikin farin ciki da kewar juna.
Bilkisu kwana biyu hankalinta ya kwanta ta natsu karatunta tasanya a gaba, domin sunkusan fara exam, tsakaninta da prince sai dai kallo, itama mamaki yakebata domin gata gashi sai