Showing 9001 words to 12000 words out of 46754 words

Chapter 4 - A WATA MASAURAUTAR (1 to End) Book Complete by Ummu Safwan .txt

18 Jan 2025

3596

ya d'aga masu hannu alamar sukyaleta."




Tonima dai ganin hakan yasa nayi saurin barin wurin, kar prince yasa a suburbud'eπŸƒπŸΌβ€β™€πŸƒπŸΌβ€β™€






















Writing by Ummu Safwan luv u all 😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR.....


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




writing by Ummu Safwan 07066214433


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




kinwuce k'awa. Kuma kin wuce aminiya. kinzama 'yar uwa a gareni." ZAINAB ALIYU MAIRIGA (ZEETAH) ALLAH yabar k'auna. hard'iya, da jikoki." Luv u so much😘😘😘😘😘








Page1⃣4⃣


Adnan tsaye yakasa tafiya."
Duk inda Rayuwarsa take tab'aci, jikinsa har rawa yakeyi,"
Gaba d'aya jijiyoyin kansa duk sun firfito. Idanunsa sunyi jajir."


Ganin halin dayake cikine yasanya, fadawansa sukayo kansa." suka kankamasa, sukasanyashi a mota, suka nufi gida dashi."


Dashigarsu gidan. bejira akabud'e masa mota yafitoba." dakansa yabud'e yafito, sai wani cincira yakeyi, kamar wadda zai tashi sama."


Dak'yar yasamu isa d'akinsa."
A kan makeken gadonsa ya kwanta, sai ajiyar zuciya yakeyi. yana tuna fuskar Bilkisu lokacin da take tufamasa yawu a fuska, a gaban bainar jama'a, kuma a gaban fadawansa."
Zunbur ya mik'e tsaye." Sai safa da marwa yakeyi, yana tunanin, waishi kamarsa prince." ace wata y'ar matsiyata, harta samu damar


fad'amasa mgna."


Bakinsa yacije ya kaiwa gado daushi."
" impossible. bazai yuyuba." Yazama dole nasan ko ita wacece?." Waye ubanta?." a fad'in duniyar nan." dame take tak'ama?." Dolene nasanya a abincika mun asalinta domin nasan ko ita
wacece?" Sanan na d'auki kwankwaran mataki a kanta."


Kai tsaye toilet yashiga, domin yai wanka koda zaiji sanyi avrayuwarsa."




Gimbiya bahijja sun sauka lafiya."
Motocinsu ne, ke tsayawa a harabar gidan sarkin kano."
Lokacin, Yayi dai dai da fitowar, yarima Fahad da prince Adnan zasu fita."
Tsayawa yayi yabi motocin da kallo, domin a xahirin gskya kowaye a cikin motar yabashi sha'awa. prince Adnan yasaki baki yana kallon waye zai fito a cikin motar."


yanayi motocin, da kuma yanayin wadda ke cikin motar, tabbas yasan yanaji da mulki da saurata."
Sai yadinga maganar xuci, inama shine a cikin wnn daular."


Sai mgnar Bilkisu tafad'o masa a rai."
datake cewa. "Idon mulki kake tak'ama dashi." to kasani, mulkin wata masarautar, yafi mulkin masarautarku."
Idon kuma sarauta kake tak'ama da ita."
To kasanya a ranka sarautar wata masarautar tafi sarautar masarautarku."


Ganin wad'an nan motocin kawai ya i'sa, yabawa kansa amsar, maganar da Bilkisu tafad'a masa."


Yarima Fahad yanufi motar da murmushin sa, a kan fuskarsa, motarda gimbiya Bahijja ke ciki, yanufa,
Domin shi tun shuguwarsu, yagane tambarin masarautar yola." Domin yana yawan zuwa yola sada xumunta." Allah yayiwa yarima Fahad son 'yan uwa, da kuma sada xumunta." Sab'anin prince Adnan, daba kowa yasaniba a cikin 'yan uwansaba."


Prince Adnan kuwa tsaye yayi yana kallonsu. Yaga waye zaifito a motar."πŸ™Š


Lokacin gimbiya Bahijja, fadawa suka bud'e mata mota." fitowa tayi, cikin shiga ta alfarma, wadda tafito mata da kyanta, da kuma mulkinta, fitowa tayi cikin k'asaita da i'sa da kuma mulki." sukuwa kuyanginta mata sai fifita sukemata suna jeramata sannu, had'ida yimata kirari."


Yarima Fahad naganin ta, ya shedata, domin shi rabonda ya ganta, tun lokacinda yakaiwa Ammi wata Zayara shekara shidda da suka wuce."


Itama hakan. taganesa, sai kawai tasakar masa murmushi tanufosa."
Cikin k'asaita, take mgna, "yaya kafa ganni amma ka kyaleni bakaje kataroniba."
Shima murmushi yayi, yace "gimbiya Bahijja barka da xuwa." Bagashi natafo nayiwa k'aunata oyoyo ba."
Gaba d'ayansu sukasanya dariya."


prince Adnan dake tsaye yana kallonsu, yakasa k'arasawa a inda suke, sai k'okari yakeyi yaga fuskar kowace Fahad ke mgnada da ita."


lura yayi da fuskar,
Ai kuwa a take gabansa yafad'i."
Domin yarasa a inda yasan wannan fuskar."
Kuma tanayimasa kama da, wadda yasani, da fuskar."


Bekawo Bilkisu a rywarsaba, domin, yasan ita bakowa bace face 'yar matsiyata." bare yayi tunanin ta had'a wata a lak'a da masarauta."


Yarima Fahad ne yakatse masa tunanin dayakeyi, yace "Adnan baka ganeta ba ne,?"


Katsaya kasaki baki, da hanci , kana kallon mutane."


Sai a lokacin ya k'araso a inda suke, yace "yaya naganeta mana, ba Bahijja bace 'yar gidan Ammi?"


Yace "itace shine bazaka gaida ita ba?"
Kuma bazaka kirata da Anty ba." Sai dai Bahijja kai tsaye?"


Yanayimasa mgna amma rik'e yake da kunensa."


Yace "wayyo yaya sakarmun kunne."


Amma fa nga sati d'aya kawai tabani." Shine zance mata Anty."
Kuma fa dataxo kai, d'aya tayiwa mgna. Ni ko kallona batayiba."


Ya kuma jamasa kunne." Yace " maza ka gaida ita."
kace Anty ina wuni.sannan zan sakarmaka kunne."

Yace "to Anty ina wuni."


Bahijja tayi dariya cikin k'asaita, tace "lfy k'alau d'an k'anena."


Gaba d'ayansu suka Sanya dariya, suka d'unguma sai fadar maimartaba."


, amma banda prince Adnan domin yanada muhimmin abunda xai aiwatar yau d'in nan


















UMMU SAFWAN
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASAUTAR...


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by Ummu Safwan 07066214433


Pure moment of life writer's


1⃣5⃣


A guje yashigar da motarsa cikin makarantar, bexame a ko inaba sai ofishin shugaban makarantar.


Betsaya neman ixininba , kai tsaye ya afkamasa batareda sallama.


Malam Sanusi dake xaune a kan kujerarsa yana rubuce rubucen takardunsa.
Sai ganin prince yayi a gabansa ."


Abun yabashi mamaki matuk'a, ko dadai yasaba da rashin sallamar prince idon xai tafo wurinsa, shima abun yana damunsa sai dai ba yadda zaiyi idon yanason yaci gaba da aikinsa."


Kallo yabisa dashi yana murmushin dole yaimasa nuni da hannu, yace "zauna mana yarima."


Anan Adnan ya maida kallonsa a kujerar da malam sanusi yanuna masa domin ya zauna."
Yaja kujerar ya zauna, cike da i'sa da k'asaita,
Ya maida kallonsa a wurin shugaban makarantar,
Yace " wurinka nazo. Inason kayi mun aikin kud'i, tun daga miliyan d'aya har xuwa miliyan goma
Idon kuma kud'in sunyima kad'an, kana iya kafad'i konawa kake buk'ata, xan iya Baka, idon har kacika mun burina."


Malam Sanusi yayi murmushi yace "fad'i buk'atarka ina saurarenka Prince.


Prince Adnan yace " wata yarinya nakeso a kora, a makarantar nan, idon akayimun hka, nayima alk'awari duk abunda kake buk'ata zanyima, komai girmansa.


Malam Sanusi ya kalli prince yayi murmushi yace "idon wannan ne bakada matsala prince, fad'amun wacece?" Kuma meye sunanta?."


Prince yace"Sunanta Bilkisu Abdulrahaman yola


Jin prince ya ambaci sunan Bilkisu, yasanya malam Sanusi yayi saurin kallon prince a raxane,
Yace "a gaskiya wannan yarinyar bata koruwa a makarantar nan.


Prince najin hka, a nan take ya canxa fuska, yace "saboda me bata koruwa?" Ita wacece?" Kuma d'iyar waye?" Waye ubnta?"
Duka ya jeromasa wad'an nan tambayoyin.

Malam Sanusi shuru yayi, yana tuna abunda sarki Abdurhaman yafad'a masa gameda Bilkisu,
Ya d'ago kansa ya kalli Prince yace "kayi hakuri prince bawai don nak'i aiwatar maka da buk'atarka bane, a'a, ina mai Neman afuwarka, akan wannan buk'ata taka, sai dai idon zaka canza da wata zan iya aiwatar maka da ita, amma banda wannan.


Prince ya kalle malam sanusi, ransa a b'ace, yace "tambayarka nayi waye ubanta?" Dabata koruwa a karantar nan?"


Malam Sanusi yace "gaskiya bansan kowaye ubntaba, don hka kaje kayi bincike koda xaka samo labarin ubnta ko waye shi.


Bai kuma bi takan malam Sanusi ba,mik'ewa yayi, yafito ofishin a fusace, anan ya had'u da Abdullah abokinsa, yace " waye yatab'a mazaje?"
Prince yyi murshin da yafi kuka ciyo, yashiga fad'awa Abdullah ynda sukayi da malam Sanusi,
Ya kalli Abdullah yace. Abdullah inason kabin cikomun asalinta dana iyayenta,
Abdullah yace " bakada matsala a kan wannan."


Prince yayi murmushin jin dad'i sannan yashiga motarsa yawuce gida."






Bahijja zama yayi dad'i a wurin hajia Nafeesa,
Zamane Wadda take taka tsantsan da abunda zai b'atawa hajiya nafeesat rai,
Domin kuwa Bahijja akwaita da gudun zuciya, gata batada yawan magana, idon safiya tawaye abunda ke gabanta shitakeyi, tana gudun zuciyar hajiya nafeesat.


Yarima Fahad kuwa bayada wurin zama yanzun sai b'angaren hajiy Nafeesart,
Domin sunshak'u da Bahijja, Shak'uwa mai tsanani har yakai baya iya cin abincin kowa a gidan sai wadda Bahijja tadafa masa,


Shak'uwa mai tsakanin tashiga tsakaninsu har yakai kowa a gidan yanajin dad'in kasancewarsu a hkan,
Musamman maimarta sarki Bashir dayake addu'a Allah yasanya soyayya ce a tsakaninsu. Domin hakan shi zai k'aramasu dankon zumunci tsakaninsa da sarki Abdulraham."


Wani yammaci ne, Bahijji tafito domin shak'atawa a nan harabar gidan,
Zama tayi akan kujera, tana karatun mujalla, saitajiyo k'amshin turaren Fahad a bayanta,
Juyawarda zatayi sai ta ganshi ya tsura mata ido ita kawai yake kallo,


Ganin da tayimasa yana kallonta yasanyata jin kunya, ta sunkuyarda kanta k'asa


Shikuwa ya zagayo inda yake fuskantarta, yace, "gimbiya barka da hutuwa sarauniyar mata.


Kunyace ta lunlubeta ta rufe fuskarta da jaridar dake hanunta tace " yawwah yarima Allah ya taimakeka ya kuma tsare mana lafiyarka.


Murmushin jin dad'i yayi, yasamu d'aya daga cikin kojeran ya zauna, suna fuskantar junansu,


Yace "gimbiya Bahijja kinkosan abunda ke tafe dani a daidai wannan lokacin?"


Tayi murmushi tace, " ranka ya dad'e bansaniba, amma kunnuwana, saurarenka suke, suna jiran suji abunda zaifito daga daga bakinka,


Yayi gyaran murya, yace "Bahijja tun lokacinda nasanya idona a kanki naji nakamu da soyayyarki. a kullum dake nake kwana dake nake tashi a rywatah,
Bahijja kitaimakamun ki karb'i soyayyata, idon kikayimun hkan zanji dad'i a rayuwata."


Magana yakeyi kanta a sunkuye yake, duk kunya takamata musamman dayace sonta yakeyi,


Ganin tak'i kulashi, yasanyashi sauka daga kan kujerar dayake zaune, ya runsuna k'asa ya tallabo fuskanta da tafin hannunsa, ya tsura mata ido, cikin shauk'in so da k'auna. "Bahijja magana nakeyi amma kink'i kulani, kodai bakya sona ne?"


Kasa had'a ido tayi dashi, sai dai ta kuma sunkuyar da kanta k'asa, tana maijin kunya.


Yace "Bahijja ki amsa mun maganata koda zanji sanyi a rayuwata.


Rufe fuska tayi da tafin hannunta,
Yin hkan datayi saida abun yabashi dariya.


Yace "yanda kike tafiyarda da rayuwarki, Bahijja kike k'ara burgeni, nakejin sonki a rayuwata, Bahijja ilove you.
Ki taimakamun kice mun I love you, yin hkan shizainuna mun nasamu karb'uwa a rayuwarki.


Mik'ewa tayi tsaye, rufe da fuska, tace "
Fahad I love you, I really luv u ,
Tana kai nan taruga a guje tabar wurin


Murmushin jindad'i yabitadashi, tak'ara shiga ransa domin yanason mace mai alkunya.


A hka dai soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin yarima Fahad da gimbiya Bahijja."






A b'angaren prince Adnan kuwa, bayan kwana biyu dayin mgnarsa da Abdullah, saiga Abdullah yakira shi a waya, yake shedamasa dacewa ya binciko masa ko wacece Bilkisu,
Murna yashigayi sukace sai sun had'u a makaranta sauran bayani


A gurguje yashirya domin tafiya makaranta, sauri yakeyi domin yasamu abdullah yafad'a masa wace Bilkisu?"


A makarantar yasame Abdullah a tsaye yana jiransa, k'arasowa yayi a kusa dashi suka tab'a suna kiran sai maxaje,

Prince yace to ya Abdull bani labarin 'yar matsiyatar nan,
Abdullah yace "wai kasan ko d'iyar waye?"
Prince yace "ina zansani saika fad'a
Abdullah yace to bad'iyar kowa bace face d'iyar matsiyata, kuma talakawa ne, nabugawa a jarida😊 don ance ubnta yama mutu, basuda kuwa,daga ita sai uwarta suke zaune a gidansu,
Don hka nake baka shawarar kadaina wahalarda kanka a kan 'yar matsiyata, kafita daga harkanta kashareta kawai, tunda kafahimci ita bakowa bace,


Prince yayi dariyar mugunta, yace gud story naji dad'in wannan labari Abdullahi.kafin narabu da ita saina nunamata kuskuranta, kuma sai nunamata yanda xata dinga girmama shuwa gabanni, musamman sarakuna, da kuma 'ya'yan sarakunan."


























UMMU SAFWAN
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR...


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




Page 1⃣7⃣




Gudu yake kamar Zaitashi sama, sai tunanin marin da Bilkisu tayimasa a gaban bainar jama'a


kaiwa sitiyari mota duka yayi ya burxarda da wani iska mai zafi a bakinsa, idanunsa sunkad'e sunyi jajir. Sai gudu yake zubawa a kan titi, ganin gudun dayake ba'a hankanlinsa yakeyinsaba yasanya
Abdullah yayi k'arfin halin yimasa magaba, "don Allah prince katafi a hankali mana, kadiba ga yanda jini yake zuba a k'afarka, duk kawani fita hanyacinka akan wannan matsiyaciyar yarinyar, wai ynxun ina muka nufa ne kabiyo ta wannan hanyar."?


Betankawa Abdullah ba, sai gudu yake shararawa, Abdullah duk ya tsorata da ganinsa cikin wannan halin.


Sai ganin yayi.
yayi parking a dai dai k'ofar gidansu Bilkisu, waya yad'aga yakira fadawansa, yayi masu kwatancen a inda yake suzo susamesa.


Ya mayarda kallonsa ga Abdullah yace, "yau zannuna mata na i'sa nakoresu a garin nan,kora ta wulak'anci, kuma zan a zabtar dasu har saitayi nadamar marina datayi a gaban bainar jama'a,
Itama zan wulak'antata kamar yanda tayimun a gaban bainar jama'a.


Yana rufe bakinsa saiga fadawa sun iso kowanesu jira yake abashi umurni.
Runsunawa sukayi suna kwasar gaisuwa, kallo yabisu dashi d'aya bayan d'aya, yayi masu nuni da gidansu Bilkisu,
Yace "kushiga gidan nan kufitomun da duk wani abu dake cikin gidan nan, tareda bil adaman dake rywa acikinsa, duk a fitomun dasu yanxun nan."


Fadawa suka afka gidan, suka tararda jakadiya zaune tana yankan a aifa, sai ganin fadawa tayi gabanta, kallonsu tashigayi cike da mamaki, ita dai tasan ba fadawan masarautarsu bane, tomeye had'insu da wad'an nan fadawan? Tashiga yiwa kanta tambayoyi. Saiji tayi anwatso mata a kwatin kayansu a k'afa, cike da mamaki take kallonsu tana fad'in "lfy"? Meyafaru"? Me mukayumaku"? Basu saurare taba sukaci gaba watso masu kayansu a waje."


Bilkisu kuwa na makaranta, batasan abunda ke faruwaba. Kuka takeyi, safeenat sai hakuri take bata, gameda abunda prince yayi mata.
Mekewa tayi tsaye cikin yanayin damuwa tace sis zantafi gida kaina ke yimun ciyo, bazan samu damaryin test d'in nanba domin kona tsaya bazan iya rubuta komaiba.


Safeenat tace "sis Allah ya sauwak'e, idon kikaje gida kisha magani. Ynxun da munfito gani nan zuwa naga jikin naki.

Bilkisu tace "to sis ngd saikin shigo."
Tawuce tatari mai adai2 sahu yakaita gida.
da shigarsu kwanar unguwarsu ta hango mutane, sunyi cincirundo a k'ofar gidansu mamaki tashigayi tana tambayar kanta lfy"? Taka mutane haka a k'ofar gidansu?


K'arasawa tayi domin ganin me kefaruwa, sai ganin kayansu tayi anawatso masu a kofar gida,
Jakadiya sai kuka takeyi tanabada hakuri amma basu saura ra mataba,

Bilkisu nazuwa wurin gaba d'aya kallo yadawo Kanta, ganin fadawan prince tabawa kanta amsar wadda yasanya suyimasu irin wnn wulak'ancin, batabi takan kowaba sai wurin jakadiya tanufa dake durkoshe tanabawa fadawa hakuri,
Durkusawa tayi tad'ago jakadiya tsaye tace "Ammi meye abunbasu hakuri a ciki? Ki kyalesu kawai suyi abunda sukeso.
Tana mgna amma idanunta sun cika da hawayen bak'in ciki.
Yau ita gimbiya Bilkisu itace ake wulak'antawa a gaban bainar jama'a😭
Tana rungume da jakadiya suna kuka."


sai tab'i taji anayi a bayanta, juyawarda zatayi ganin prince tayi tareda Abdullah sunayimata dariyar k'eta.


Kallo tabisu dashi sama da k'asa,
Prince yace " ni nasanya a yimaku hakan, domin bana muradin ganinku a k'asata, bakeba ko mai kama dake nagani saina sanya ankoreta a garin nan, bareke. Na tsaneki banason ganin fuskarki bare mai kama da fuskarki.


Kallon tsana tabisa dashi, tana mai zubarda hawaye, tace "banada niyar mugunta amma kaine mutum na farko da zansanya a axabtar dashi a zaba mai tsanani,
banada niyar amfani da damata domin wata manufa marasa kyau, amma Kaine mutum na farko dazaka sanyani yin hkan,
Kasani na tsaneka tsanawa mai tsanani. Ka wulak'antamu a gaban bainar jama'a kaima ka saurare naka hukunci gobe.
Tana kaiwa nan Safeenat tafito cikin a dai dai sahu, ganin Prince tsaye tabawa kanta amsar tambayar dazatayi,


Bilkusu tayi karfin halin yimata mgba tace sis tsayar mana da mai a daidaita karya tafiyarsa.
Tsaidashi sukayi takama hannun jakadiya tasanyata a ciki, sanan tadawo d'aukar kayansu, ba komai tad'aukaba sai jinkar takardunta, sai kuma a kwatin kayansu, tasanya a bayan adaidai ta.
Mutane sai kallonta suke suna mai tausaya mata.


Dawowa ta kuma kiyi, tanufi gefenda makwanciyarta take tsaye tana zubarda hawayen tausayinsu domin sunyi matuk'ar sabawa da ita


Cikin yanayin kuka ta nufo Bilkisu ta rungumeta tana kuka, Bilkisu tayi k'arfin halin yimata mgna, tace
"Hajjah daina kuka zandawo gareku bada jimawaba, abunda nakeso dake yanxun kisamu yara sukwashe maki duk wani abu dake wurin nan, nabaki shi kyauta, sanan ta Nuna wani k'aton frege tace wanan kuma a kai sa gidan liman nabasashi."
liman dake tsaye cikin yanayin tausayi yanufota yana godiya, domin tun zuwan Bilkisu a unguwar duk ranar juma'a saitasanya ayimasu abincin sadaka duk wanda yazo sallah a masalancin to saiyaci abincin Bilkusu yana mai sanyamata albarka, sannan shima liman d'in duk zai sallar juma'a dasabon d'unki yakeyi wadda Bilkisu take d'unka masa.
Abunda yasa suka saurarawa wadda yayi mata hkan, ganin fadawa dasukayi da kuma Prince da ke tsaye domin sunsan halin prince ba imani ke garesa ba.


Sanan tanuna wasu durum2 na ruwa tace liman a kai wad'an nan masalanci a dinga zuba ruwan alwala."


Tana kaiwa nan tajuya tanufi wurin prince dake tsaye yana kallonta sai a lokacin yafara tausayamata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login