Showing 42001 words to 45000 words out of 46754 words
Chapter 15 - A WATA MASAURAUTAR (1 to End) Book Complete by Ummu Safwan .txt
tadago kanta sama tana kallon mai kiran nata fuskarta cikeda mamaki,
nanfa safeenat tadinga lallab'ata akan ta tashi tatafi k'in zuwanta wurin ba girmanta bane,
Ahankali tamike ta isa wajen tatsaya, a tsakiyar filin, ido yayo kanta kowa kallonta yakeyi,
Sannan M.C yacigaba da magana,
Yace "muna da sharadin duk wadda yafito Wurin nan to munsan tabbas ya yarda da kansa,
don haka munada sharad'i?
Sharadin shine duk abunda akkace mutum yayi saiyayi ko kuma acishi tarar (70, 000 N)
Ya maida kallonsa a Bilkisu Yace "gimbiya kinyarda,?
Ta maida kallota ga safeenat,
Safeenat tad'aga mata kai alamar tace ta yarda,
Bilkisu ta kalli mc tace "nayar da Dan kudi bama tsalata bane, nan fa aka d'auki kuwa,
yace
sharadi na biyu, programs nafarko dole sai kinyi abunda akkace kiyi, idan bakiyiba zaki biya Tara,
Ko kuma a fansheki, ma'ana kuma wani daga cikin masoyanki subiya maki,
Tana tsaye ankabawa safeenat wani farin kyalle,
akkace ta daure mata fusaka da farin kyallen,
Ya kuma bada umurni akkan cewa duk namijin da yafito tsakar fili,
yacire ta kalmensa ya ajiye a kusa da ita,
bayan sun kammala ajiyewar,
Sai MC ya kalli Bilkisu dake tsaye d'aure da fuska,
Yabata umurni dataduk' ta d'auki talkami d'aya cikin tallakamin da aka ajiywmata a gefenta,
Nanfa tashiga gewaye tana lalaben inda talkaman suke,
can ta canki wani takalme,
tamik'awa MC sannan aka bude mata fuskarta,
MC yashiga diban k'afafun mutanen dake tsaye tsakar filin dan ganin ko takallemen waye ta cinka, Nan aka kasoma dibon k'afa ashe na yarima adnan ne tadauka, aikuwa mutane na fahimtar hakan suka suma kuwa,
M.C yayi gyaran murya yace, "Bilkisu da Adnan kawai yakeso ya gani a tsakar filin,
Zaharaddin yyi bak'in cikin rashin d'aukar takalmensa dabatayiba
MC yace a saurara, za'a sanyawa Bilkisu da Adnan wak'a domin sutaka rawa,
Adnan yaji dad'in hakan,
Ita kuma tad'auki niyar cewa Adnan bazai tab'a kada itaba,
bata iya rawaba amma takawa takeyi cikeda k'asaita saida ta tabawa kowa sha'awa amma banda zaharaddinka,
Sai programs na k'arshe,
M.C yace anason Adnan yayiwa Bilkisu kiss harna tsayin 30minut,
nanfa hall yayi tsit don kowa sonyakai yaga yanda hakan zata kasance
adnan yyi murmushin jin dad'i,
Yasoma lasar baki da gyaram kwalar Rigarsa za,asha banza,
Adnan yasoma matso Bilkisu naja baya, MC yace "wait Prince bara nak'irga goma idan bata yardaba zamu cita tara,
idan kuma akwai mai fan sarta toh am waiting, nanfa yafara k'irga d'aya Bilkisu naja baya prince nabiye da ita har da ta kai karshen bango, Prince nabiye da ita,
Datagade ba sarki sai Allah sai tayi tsaye, ta kulle idonta tana jiran taji saka mako abunda prince zaimata,
Shi kuma har yaruk'o hannunta, yaji ance na nafansheta, nan take prince yayi saurin waigowa domin ganin waye ya katse masajin dad'i, sai yayi arba da Zaharaddin a tsaye yana murmushi, nanfa yaji kamar yamutu amma sai ya yamutsa fuska alamun ko ajikinsa
Amma taciki naciki nan dai akaci gaba da programs daga bisani aka tashi kowa yawatse.
safeenat ce takeyiwa Bilkisu dariya tana fad'in "yau wata datasha lebo,
Bade ta kulataba sai harara databita da ita, tareda fad'in " Allah yafishi,
safeenat tace bawani anaso ana kaiwa kasuwa, ai koke bakiji dadiba itade batace mata uffanba
Suna fitowa Zaharaddin yabiyo bayan bilkisu suna tsaye yanamata k'orafi akan cewa danmi bata dau takalmensaba?"
Magana yaji anayi a bayansa yaji anafad'in "akanmi zata d'auki takalmenka tabar na mijinta?'
Nan suka juya gaba d'ayansu dan ganin mai yin magana,
Zaharandin ya kallesa yace 'toh kai kuma miye naka nabiyomu a Nan Adnan?"
Prince yayi murmushi yace "nabiyoka ne domin inyimaka kashedi a kan karabu da Bilkisu domin nikad'ai nakeda ita, banason inason abu naga wani na Sonsa, Dan haka kakiyayi kanka,
ko nasanya a b'atar min da kai, b'acewa ta har abada,
Domin kadaina ganin kanka wai d'an minister ne,
kod'anda shugaban k'asane kai zan iya sanyawa a b'atarmun da kai.
Bilkisu tayiwa prince kallon sama da k'asa "tace kai malam yimun shiru,
wacece matarka?'
Allah yatsareni danazama matarka,
Tanuna xaharandin tace, "kaga wannan shine mijina,
Wanda ya amsheni a hannun azzalumi irinka,
Tun Kamin ta iyar da maganarda takeyi saiji tayi an watsamata mari,
Ta dafe kunci
Tace "kamareni?" akan nace bana sonka?" toh nafad'a nace bana Sonka Adnan,
shikuma abunda yatsana a rayuwarsa kenan ta duniya,
bilkisu tace bata sonsa.
Nan Yadinga kallonta idonsa yarik'ed'e yayi jajir,
ya hango shatin hannusa,
a inda yamareta ya kwanta mata akan kyakkyawar fuskarta,
Ta kuma kallonsa ido cike da hawayeTace "nace bana sonka zata kuma yin magana yad'aga mata hannu alamar tayishuru yajuya zaitafi idanunsa surikid'e, sunyi jajir sai zubar da hawaye yakeyi,
Zai wuce kenan saiganin sukayi ya yanke jiki ya fad'i k'asa a some,
nan take Abdullah yayo Kansa suka tallabesa aka sanyashi a mota suka nufi asibiti dashi,
Hankalin Bilkisu duk yatashi sai zubarda hawaye takeyi,
zaharaddin yace akan wannan jakin zaki tada hankalinki?"
yama mutu mana,
shiyasa lokacin dayayi hadari naso yamutu,
kenifa saboda kiyayyar da nake masa yasan, natura akad'eshi a mota mufuta, Domin tun farko bana sonsa,
Bilkisu tabishi dawani kallo wadda saida ya firgitashi, sannan ta d'aga masa hannu tace
Ya i'sa zaharandin, dama kai azzalumine maci amana?"
Ashe zaka iya kashe rayuwa?"
kuma d'an uwana?", toh bara kaji daga yau kada ka kuma yimun magana natsaneka, bana sonka banason ganinka azzalumi kawai, nan ta tohfa masa yawu tawuce.
Koda aka i'sa asibitin prince besan inda kansa yakeba,
Likitoci tai makon gaggawa suka basa,sannan akakira sarki yazo han kalinsa a tashe yashigo asibitin,yana tambayar ba,asin abunda ke faruwa ga prince, nan sunkace suma basu saniba gani kawai sukayi ankawosa,
Nan likita yayi sarki magana, akan cewa yana son ganinsa, suna shiga yafayiwa sarki bayani kamar haka,
"zuciyar Adnan ce yake keson bugawa saka makon wani abu dayake so baisameshiba Don haka ayi saurin basa abunda yakeso, idan bahaka ba, zai iya rasa rayuwa.
Sarki natsaye yana saurarem likita, yana yimasa bayani, gaba d'aya hankalinsa baya jikinsa saboda tashin hankali,
Marmartaba yayi lilita godiya yafito, cike da mamakin meye prince yakeso hkan Wanda besamuba haryake neman narasa rayuwarsa,
Bilkisu kuwa gaba d'aya hankalinta yatashi da ganin fad'owar da prince yayi
Aguje tashiga napep tabi motarsu prince a baya, sai kukatayi tana mai tausaya masa halinda yashiga a kanta,
A harabar asibitin me napep d'in ya ajiyeta,
Aguje tak'arasa d'akinda aka kwantarda prince d'in, tura k'ofa tayi tashiga."
βπ»writing by
Ummu
safwanβπ»
ππππππππππ
A WATA MASARAUTAR....
πππππππππ
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S
page 5β£1β£ 5β£2β£
Hango Prince tayi a kwance cikin mawuyacin halin, sai wani numfashi yake fitarwa, kamar ransa zaifita,
Kuka tafashe dashi, tanufi gadonsa,
Cikin yanayi mai bantausayi,
Ta durk'usa dai dai gadonsa, tana kuka,
Ta rikomasa hannu taga baya motsi,
Ta kurma I'hu, wadda yaja hankalin likita tareda maimartaba sukayi saurin shugowa d'akin, suka tararda ita sai girgiza prince take tana kuka, tana fad'in
"Dan Allah Adnan karka mutu wlh inasonka,
Katashi a d'aura mana aure, nadad'eda fahimtar kyakyawar niyarka a kaina, inasonka Adnan kai kad'ai nakeso,pls Adnan katashi karka mutu kabbarni,
Adnan dake kwance cikin mawuyacin hali, wanda ko iya motsi bayayi,
Yanajin sautin kukan Bilkisu nayimasa yawo a kannen,
Bud'e idonsa yayi, ya d'aga hannunsa ya rik'o hannun Bilkisu ya rik'esa gam,
Yanda bazata kuncemasa ba,
Ya mayarda idonsa ya rufe, hawaye na zubar masa a gefin fuskarsa,
Bilkisu Tashiga share masa hawaye a fuskarsa,
Tana fad'in pls Adnan karka mutu kabarni wlh inasonka,
Karka mutu kabarnu sai munyi aure mun hayayyafa,
Likita da Maimartaba sai kallon mamaki suka bisu dashi,
Fahad da Bahijja ne suka turo k'ofa suka shigo,
Suka tarar da Bilkisu a kusa da Adnan sai share masa hawaye takeyi itama tana kuka,
Kuma idonsa a rufe, amma hannunsa rik'e da hannun Bilkisu, kamar Wanda za'a kwace masa ita a gudu,
Fahad yakai dibansa ga maimartaba yace
"Abba me likita yafad'a gameda abunda kedamun Adanan?"
Abba ya maida kallonsa ga Fahad yace " doctor cewa yayi,
Zuciyarsa zata iya bugawa, har yakaida rasa Rayuwarsa idan ba'abashi abunda yakesoba,
Maimartaba ya dafa Fahad, cikin yanayin bantausayi,
Yace Fahad nayi mamakin maganarda likita yafad'amun a kam Adnan,
Nidai a iya sanina Ku uku ne Allah ya mallakamun a rayuwata a matsayin 'ya'yanah,
duk daga cikinku bbu wadda yatab'ata Neman wani abu najin dad'in duniya yarasa a wurina,
Yau ga Adnan ya kwanta ciyo saboda yana Neman wani abu a rayuwarsa besamuba,
Fahad menene shi?"
Menene d'an uwanka yake nema yarasa wadda har yake Neman rasa rayuwarsa?"
Fahad ya kalli mahaifinsa, idonsa cike da hawaye saboda tausayin mahaifin nasa,
Yace "Abba nasan baka ragemu da komaiba a rayuwa, duk abunda mukeso kanayimana shi in dai har kud'i na sayensa,
Amma Abbah na alak'anta ciyon Adnan ga Bilkisu,
Fahad yanuna Bilkisu
Likita shima ita yake kallo,
Domin Adnan yanason Bilkisu kamar rayuwarsa, gani yakeyi kamar baza a aura masa Bilkisuba,
Sai sannan likita yayi magana yace "tabbas ciyon Adnan yanada alak'a da Bilkisu, idan akayi dibon yanda aka kawosa ko numfashi bayayi, amma jinta da yayi a kusa dashi, yasa haryake iya bud'e idonsa,
Ya kuma jayo hannunta ya rike da hannunsa,
Abba yayi murmushi irin nasu na manya,
Yace doctor yanxun meye mafita?"
Docter yace "mafita d'ayace a aura masa Bilkisu,
Gaba d'aya d'akin suka amsa da tabbas ahakan shine mafita,
Bilkisu na durkushe a a gab gadon Adnan, hannuta rike da na Adnan tad'ora kanta a kan k'irjinsa tana sauraren numfashinsa dan ganin takeyi da zarar tad'a daga daga wurinsa mutuwa zaiyi,
Tana sauraren duk maganganun da sukeyi harda anty Bahijja amma bata kulasuba ita dai burinta Adnan yatashi karya mutu ya barta,
Shi kuwa likita sai kokarin yake yaga fuskar Bilkisu, yaga wacece wannan Bilkisu wadda Adnan d'an sarki yakeso har yake neman rasa rayuwarsa a kanta,
Ganin batada niyar d'ago fuskarta bare ya ganta,
Yace to gimbiya kitaimaka kiceto rayuwar Adnan,
Sai anan tad'ago fuskarta sukayi ido biyu da doctor,
Doctor yace Bilkisu dama kece Adnan ya haukace a kan sonki?"
Doctor yamaida kallonsa ga maimartaba, yace ranka ya dad'e wannan itace
Wanda ta taimakesa tabashi kininta aka Sanya mashi lokacin da mota ta tureshi,
Amma ta rok'emu da cewa don Allah karmu fad'i sunanta, ta taimakesane domin Allah,
Ai kuwa maimartaba yashiga sanya mata albarka,
Bahijja ta matso kusa gareta ta rungumeta cike da jin dad'i,
Bahijja tace wannan kad'an daga cikin kyawawan halin Bilkisu,
domin a kwaita da jink'ai da tausayin, da kuma taimakawa duk mai buk'ar taimako,
Saboda kyawawan halayanta Abbanmu yake alfahari da ita cikin 'ya'yansa,
Duk abuda ake fad'a a kunnen Adnan,
Jin dayayi likita yace jinin Bilkisu ne aka sanya masa, sai ya kuma jin wani tausayinta dawani sonta yana k'ara shigar masa a cikin zuciya, jiya yake gaba d'aya ciyonda kedamunsa bayajinsa,
Mik'ewa yayi tsaye yanufi Abbansa ya rungumesa yana fad'in Abba Bilkisu Abba ka auramun Bilkisu, idan narasa Bilkisu zan iya rasa rayuwatah,
Mai martaba yashiga jinjiga bayansa, kamar wani yaron goye,
Yana fad'in ka kwantar da jankalinka insha Allahu Bilkisu takace, zata kuma zama matarka da yarda Allah,
Yasaki Abba yanufi wurin Bilkisu dake tsaye kusa ga Bahijja ya durk'usa wurin k'afarta
Yashiga yimata magiya,
Pls Bilkisu kisoni ki k'aunaceni wlh inason so nagaskiya ba nawasaba
Ki manta da abunda yafaru a baya shairin shaid'an ne, son gaskiya nake maki, pls Bilkisu Dan Allah kirabu da zaharandin wlh idan ina ganinku a tare zan iya rasa rayuwata,
Bilkisu ta runsuna k'asa ta d'ago Adnan sama ta tsura masa ido cikin so da k'auna,
Tace kadaina duk'amun kana Neman soyayyata na dad'e da Amincewa da kai, da kuma soyayyarka,
prince inasonka, kuma zan aureka kadaina d'aga hankalinka a kaina nitakace har abada,
Adnan yaji dad'in kalaman Bilkisu jiyaye kamar ya rungumeta, amma yaji nauyin yin hkan,
Murmushi yake sakar mata naso da k'auna,
Sannan yace "nagode beautynah had'ida yashafo fuskarta,
Likita naganin hka yace "dama ciyon Adnan na Bilkisu ne,
Kuma gata kusa gareshi ya warke, don haka na sallameshi, gaba d'aya d'akin suka sanya dariya,
Bahijja tace prince basu ciyon love,
Sukadinga yimasa dariya,
Sannan daga k'arshe suka fito gaba d'ayansu zasu tafi gida,
Likita yacewa dady yana son magana dashi a office d'insa,
Dady yasame doctor, doctor yasoma cewa dady
,
"Allah ya taimakeka ranka ya dad'e dama shawarace zanbayar gameda Adnan,
Tunda dai har wadda yakeso itama tana sonsa mexai hana ayi bikinsu a cikin satin nan,
Saboda yanayin ciyonsa,
Idan ya kuma shiga damuwa haryakai da fad'uwa to tabbas komai yana iya faruwa dashi,
Shiyasa nake ganin maganin ciyonsa ayimasa abunda yakeso wato a aura masa Bilkisu cikin satin nan,
Maimarta ya kalli doctor yace "nagode likita da shawararka kuma insha Allah Adnan zai kawo maka IV aurensa cikin satin nan,
Doctor yayi dariya yace Allah yanuna mana danafi kowa jin dad'i,
Sannan maimartaba yafito office d'in likita ya tararsu a mota suna jiransa tareda fadawansa suka d'unguma suka nufi gida,
Bilkisu saida ta nuna alamar bazatafisu gidansuba ita dai gida zata koma wurin jakadiya,
Adnan yarik'e mata hannu gam,
Yana fad'in bazata kuma zama a wannan gidanba,
Shikenan tadawo gidansu,
Inda zaharandin be isa yasanya k'afa yatako wannan masarautarba,
Haka dai tabiye masa suka nufi gidan Nasu,
Saboda tana gudun kartayi jayayya dashi ranshi ya b'aci harya kai ciyon zuciyarsa yatashi yafad'i yarasa rayuwarsa,
Agurguje
Bayan komawarsu gida,
Maimartaba yakira sarki Abdulrahaman, mahaifinsu Bilkisu, yasheda masa da duk abunda yake faruwa,
Gameda Adnan da Bilkisu,
Yashiga ruk'onsa a kan yajanye k'udiriinsa na cewa Bilkisu saita kammala karatu, sannan ayi aurensu, ya taimaka yaceto rayuwar d'ansa Adnan ayi aurensu,
Adnan yayi alk'awalin zaibarta tayi katun, tun daga nan har k'asar waje,
Babu abunda ya d'agawa maimartaba mahaifin Bilkisu hankali, dayaji mahaifin Adnan yace "Adnan yana iya rasa rayuwarsa idon besamu Bilkisu ba,
Shikuma ya tsani a sanadiyarsa wani ya rasa rayuwarsa,
Yanisa yacewa Bashir mahaifinsu Adnan,
"Wannan batsala bace,
Zankira ita gimbiya Bilkisu naji nata ra'ayi akan hkan,
Sukayi sallama akan cewa zuwa anjima zasu kuma yin mgna,
Bilkisu na kwance a d'akin Bahijja,
Adnan ya sanyata a gaba sai shagwab'a yake mata,
Bahijja sai dariya takeyimasa tana fad'in Ashe Adnan da Bilkisu an iya soyayyah,
Saiji tayi wayarta na ringing, tayi saurin kai hannuta ta d'auka saiganin kiran Abbantane tayi murmushi tayi,
Takara wayar a kunnenta
Had'ida yimasa sallama,
Maimartaba cikeda murna da jindad'i, jin muryar gimbiya Bilkisu,
Nan suka gaisa, yashiga fad'amata yanda sukayi da mahaifin Adnan metagani,
Ta Amince ayi auren nasu?" daga baya tayi karatun kobata amince ba?"
Bilkisu tace Abba na Amin
Allah yasa hakan shiyafi alkhairi,
Abba yace "Amin gimbiya,
Anan sukayi sallama da ita,
Yakira sarki Bashir mahaifinsu Adnan yashaida masa, ya Amince da buk'atarsa,
Anan suka yanke shawarar sanya ranar biki sati maizuwa,
Bilkisu takira safeenat tana fad'amata duk yanda akayi,
Safeenat tashiga murna tareda sheda mata gobe tana nantafe