Showing 6001 words to 9000 words out of 46754 words

Chapter 3 - A WATA MASAURAUTAR (1 to End) Book Complete by Ummu Safwan .txt

18 Jan 2025

3606

wuce kenan , taji fadawa na fadin, karya kike yar matsiyata bbu Wanda yadace yaxama sarki sai yarima adnan, don hka xubarda yawun bakinki.


Tamaida kallonta ga fadawa, tayi masu kallon sama da kasa,
Idon babba na mgna ya kamata kudinga bashi respect, bai dace ina mgna da shuganku kusanya mun baki,
Yakama kuje kukuyi ynda ake daraja babba,
Kodayake bnga laifinkuba, shugaban naku besan yanda ake mulki ko saurataba bare Ku yan kuransa,


Yunkurawa sukayi da niyar ladabtar da ita prince ne ya daga masu hannu, da karfi yace Ku kyaletaβœ‹πŸΌβœ‹πŸΌβœ‹πŸΌ






Written by Ummu Safwan
Luv u all😘😘😘😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR...
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
π€½π€½π€½π€Š


Writing by Ummu Safwan 07066214433


Pure moment of life writers (P.M.L.)






Page πŸ”Ÿ


Kamasa sukayi, suka sanyashi a mota, suka nufi gda dashi,


A bakin get direba yayi horn, maigadi ya budemasu get, suka shigar da motar sannu a hankali sbda kar yarima yaji ciyo, parking space suka nufa suka'ajiye motar, fadawa suka nufosa, suka kankamasa sai sannu suketa yimasa.


Nuni yayi da hannu, alamar susakesa. sakinsa sukayi, sai sannu sukeyimasa.


" tafiya yakeyi kamar wadda akayiwa kaciya, domin shi kadai yasan abunda yakeji a jikinsa.


Dakyar yasamu ya shiga gda.
Bebi takan kowaba, kai tsaye sakinsa ya nufa, yafada a kan makeken gadonsa, ya kwanta rumda ciki,
Sai a lokacin yakejin wasu hawayen wahala nafitomasa,


Tunani yakeyi, irin hukuncin da xaiyimata, tabbas xan hukuntaki, hukunci mai tsanani, xan ladab"tardake, wadda ko makiyinki sai ya tausayamki, xanunamki cewa babu wadda ya isa yataba, "yayan sarauta ya kuma xauna lfy,


Shikadai yake surutunsa, kamar wani zautance,


Bilkisu kuwa yana barin wurin, taja hannun safeenat suna dariya, tana fadamata yanda abun yafaru, sai dariya sukeyi,


"Mutane kowa fadin albarkacin bakinsu sukeyi, wa "dansu na jinjina mata, wa "dansuwa na ginta,


Mafiyawan masu xagin nata duka matane, wa "danda suka mutu a kan son sa.




Yau gdan cike yake da yan"uwa da abokanin arxiki,
Domin uwar"gida sarautar mata, wato hajiya nafeesa, ciki kegareta, wata bakwai, amma babu wadda yasani,
Domin tana ganin kamar rashin haihuwarta yanada nasaba, ga hajia maryam mahaifiyar adnan.
Gashi tadau burin duniya ta daurashi a cikin, lokacinda ta fahimci tana da cikin,sai ta tsiri tafiya garinsu, bata dawoba saida cikin yakai wata bakwai, don hka ko sarki,
bata fadama tanada cikiba, sai yau dayakai wata bakwai,


Sarki yayi murna sosai, don hka ya gayyato "yan'uwa da abokanen ar'xiki, domin atayashi murna.


Ba sarki ba, har maman su adnan tayi murna da samun cikinta,

Amma duk da hkan. hajia nafeesa, cewa takeyi, duk munafurci ne, ba"kin ciki takeyi, da cikin.


Ita dai batabi takantaba bare tabiye mata.


Shine fa, taga shiguwar, Prince cikin fushi, yana tafiya kamar wadda kwai yafashema a ciki,

Ai kuwa babu abunda tashiga fadi, sai dan "bakin ciki, mai irin rayuwar uwarsa, yaji labarin inada ciki, shine ya shigo rai "bace,
To komai ba"kin cikinka, sai na haifi muslimu a gidan nan, domin shima ya hau karagar mulki,


Masifa taketayi ita daya, kamar wata xaranriya,




Shi dai prince yana dakinsa, duk abun duniya ya damesa, sbda bakin ciki ko kayan jikinsa be cireba,


Sai mganar zuci yakeyi,
Kamar ni prince d'an d'an sarki a'ce, wata "yar matsiyata take yiwa abunda taga dama? xunbur ya mike tsaye, kamar wadda wani abu ya tsikara, sai safa marwa yakeyi,
Yana tunanin, ita wace ce?
Dame take ta'kama?
Waye ubanta a garin nan?
Dolene nayi bin cike a kanta, domin na tabbatar da ko ita wace ce😑

Koma yayi ya kwanta, rumda ciki, idanunsa sun rikede sunyi jajir , sai tunani yakeyi, ta ina xaifara bincin.


Sannan idon yagano asalinta wane hukunci zaiyi mata?
Wadda saitayi dana sanin, saninsa, a' rywa












Written by Ummu Safwan. Luv u all😘😘
πŸ‘‘ Your πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR....


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by Ummu Safwan 07066214433




Pure moment of life
Writer's (P.M.L)




Page 1⃣1⃣


Tunda daga lokacin, Bilkisu basu kuma haduwa, da prince Adnan ba.


"Itama hakan yayi mata dad'i, domin tasamu kwanciyar hankalin ga karatunta,


Amma duk da hakan, kwana biyu da bata sanyashi a ido ba tajita duk ba dad'e, sai tunani takeyi,
"ko lfy ya daina xuwa makaranta? Wata xuciyar kuma nafada mata, kudai abunda taimasa ne, yasanya shi rashin lfy, harya daina xuwa makaranta,


"Xaune take ita d'aya tana tunanin prince. gani take kamar abunda taimasa bata kyauta masa ba.


Kwance tashi bawuya a wurin Allah. Bilkisu harsun kammala jarabawarsu lfy, kuma suna saran, ayimasu hutu, ranar friday, amma har ynxun bata sanya Prince a i'donta ba,


Yau juma'a takasance ranar hutu, Bilkusu da jakadiya suna har had'e kayansu domin tafiya gda, suna kammala had'a kayansu kenan sai Safeenat ta shigo domin suyi bankwana da Bilkisu,


Bankwana sukeyi amma kowan censu kuka takeyi, basa sun rabuwa da junansu,


"Jakadiya tsaye tayi tana kallonsu, domin kuwa itama sai da suka bata tausayi,kukan da sukeyi na rabuwa da juna, sannan tayi karfin halin yimasu mgna
"Kuyi hkr safeena, ai hutun ba mutuwa bane, kamar gobe ne xakuga kundawo.




Hka suka 'kare kuke kukensu naxasuyi missing din junansu.

Jakadiya ce taja a kwatin kayansu suka nufi tasha, domin shiga motar da xata kaisu yola.


Tareda Safeena suka nufo tashar, saida taga tashin motarsu, suna dagawa junansu hanntu, sannan tajuya tanufi gda, ido cike da hawaye, tana mai kewar Bilkisu,


Motarsu na dagawa, takira maimartaba ta sheda masa da cewa gasu nan, sun taso yxun.


"Maimartaba murna ya shigayi, yatura a kiramasa Ammi mahaifiyar Bilkisu,


Shiguwar Ammi keda wuya, yashiga fadamata gimbiya Bilkisu tayomasa waya motarsu ta taso, gata nan isuwa,
don haka a shirya mata, duk wani abu da akasan tana bukata, kuma a sanya masu kula da dakinta, su kakkab'e mata kura, a gyramata shi,


Ammi murmushi tayi,
"Tace angama ranka ya dad'e yadda kace hka xa'ayi.


Murmushi yayi ya kalli matar tasa cikin so da kauna, yace don hka nkesonki Ammin yara, domin kinabin umurnina koda kuwa hkan beyimki dadi ba


Itama murmushi tayi. tace dole ne nabi umurninka mijina,domin samun farin cikin ka, koda kowa hkan shi xaisanya rugujewar nawa farin cikin,


Maimartaba kallonta yakeyi cikin so da kauna , sai jawota yyi a jikinsa, yana sunsunar duk ilahirin jukinta da sha humra mai Kamshi, yasanya bakinsa a nata yashiga tsotsar lamb'anta, yana shafata tako ina a jikinta, bakinsa cikin nata, yake cewa wai meyasa Ammin yara bakya tsofa? kullum sai yarinya nake ganin kina k'ara komawa.


" Janye jikinta tayi a hakanli daga nasa, tana kallonsa da murmushi a fuskarta, tace ai kaine baka tsufa, ranka ya dad'e, kullum yaro kake komawa. ko da yaushe dawata salon sabuwar soyayya kake xomun mai rikitani, wai meye sirin? Ranka ya dad'e?


Kara jawota yyi a jikinsa yana fadin tafo nafadamki sirrin. kokarin xarcewa,nga sunayi a guje ni Ummu Safwan nabarmasu d'akin don karnaga abunda yafi karfin idonaπŸ‘, maimartaba da Ammi ba'a tsufa😊




Gimbiya Bilkisu sun sauka lfy, saukarsu kenan, takira maimartaba tasheda masa da sunsauka,
Ai kuwa nan take yakira direba yabada umurni da aje da sauri a d'aukota a tasha,


Motocine tare da fadawa suka tafo daukarta, ganinta tsaye cikin tasha, saida tabawa fadawan mamaki, lallai samun irin gimbiya Bilkisu sai antona

A nan take suka nufota suna kwasar gaisuwa,
"Ita kuwa hannu ta d'aga masu, alamar sutashi batason hkan.


Mota tanufa suka bude mata kofa tashiga tareda jakadiya, suka nufa gida.


Da i'sarsu gida, fadawa sai kwasar gaisuwa sukeyi, wasunsu kuwa sai bngajiya sukeyi mata, wasu nayimata kirari.
"Allah yatsare mana ke kinbiya, ya tsare gabanki ya kuma tsare bayanki, barka da xuwa sarauniyar mata Gimbiya Bilkisu mai gadon xinari.


Shigarta pallon kenan ta hango, Ammi da Bahijja da kuma prince abdull, sai kallonta sukeyi cikin murna da farin cikin dawowarta, kallo tabi kowa dashi tana murmushi, kowa sai tunani yake a wurinsa xata fara xuwa.


Ita kuwa tayi tsaye, tak'i k'arasa shiga cikin pallon, b'ata fuska tayi tana kallon kowa,
"Suma ita suke kallo suga a wajen waye xata fara xuwa.


A can ta hango maimartaba na sakkuwa. ai kuwa a guje tanufesa tana dariya da murna tanufesa, ta rungomesa.


Shima sai dariya yakeyi cike da murnar ganinta.
Kowa sai mamaki yakeyi, musamman Prince Abdull dayasan tafi shakuwa dashi a kan kowa a gdan.
















Writing by Ummu Safwan luv u all😘😘
πŸ‘‘ πŸ‘‘ πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR.. .


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
π€½π€½π€½π€Š


Writing by Ummu Safwan 07066214433




Pure moment of life writer's. ( P.m.l)




Page1⃣2⃣


Kowa kallon mamaki yabita dashi, musamman prince Abdull, da ya sheryamata kwarya kwaryar walimar dawowarta.


A nan me martaba yabada umurni da akawowa Gimbiya Bilkisu,
Abubuwan motsa baki, a nan take a kacikawa gimbiya gabanta da abubuwan ciye ciye. Gaba dayansu sarki yabada umurnin duk su sauko a'ci abinci gaba d'aya.

Kowa ya sauko, a ka xunxuba abincin, kowa ya faraci, amma bnda gimbiya Bilkisu,
Maimartaba ya maida kallonsa gareta.
"Yace gimbiya meke faruwa ne? Ko abincin ne bakyaso? Ynxun nasanya akawomki wadda kike bukata.


"Turo Baki tayi, tana shagwaba, ni Abba lkcin cin abincina baiyi ba, tadiba agogon dake daure a hannunta na gwal, a shagwab'e tace Abba dibafa kagani ynxun 6:30 kuma Abba kasan sai 7:00 nakecin abinci.


Maimartaba yayi murmushin jin dadi,
" yace tabbas gimbiya hakane. na manta,Allah yayimaki Albarka. tayi dariya tace amin Abba nah.


Ta maida kallonta ga Bahijja "tace Anty Bahijja dake da yaya Abdull naga kunyimun k'iba dayawa, gaba dayansu suka sanya dariya.


Sannan tamike tace "Ammi bara nayi wanka kafun nashirya lokcin cin abincin nawa yayi.


Gaba dayansu, Kallo suka bita dashi, suna mamakin tafiyarta makaranta be canza mata rayuwa ba.


Kai tsaye d'akinta tanufa, mamaki tashiga yi, ganin ancanza mata komai na d'akin, murna tashigayi a Zuciyarta tana godewa maimartaba domin tasan shine yasanya ai'mata komai, domin yafison a koda yaushe yasanyata farin ciki.


K'arewarta wanka keda wuya, yyi dai dai da lokacin cin abincin nata, a gurguje ta shirya cikin wani matirial, pink&blu. Yaimata kyau sosai.


Sankowa takeyi sannu a hankali kan bene, domin ta halarci wurin cin abinci, ta taran da Bahijja, da kuma maimartaba zaifita fada,
Kallonsu tayi gaba dayansu tayi murmushin jin dadi da farin ciki, yau gata a gida, a gaban iyayenta da kuma 'yan uwanta.


Maimarta ne yayi gyaran murya yace "gimbiya Bilkisu anfito?


Murmushi tayi, ta sunkuyar da kanta k'asa, tace Allah yakara maka lfy, nafito domin naci abinci, na
huta,
Ganin fitowarta yasanya maimarta komawa ya xauna, yafasa fita fada.
Sai kallon gimbiya yakeyi yana murmushi, domin duk a cikin 'ya 'yansa Allah yafi d'ora masa son gimbiya Bilkisu, ga biyayya, ga kuma kyauta, bata kyamatar talakawanta.


Bahijja tayi kyaran murya, tace "yauwa Bilkisu, jiya a masarautar kano sun aikowa da Abba sa'ko, akan cewa matar sarki Bashir, tanada ciki har natsawon wata bakwai.


Bilkisu batace komaiba, face ya mutsa fuska da tayi. tace "mamansu fadila? Ko kuwa wannan jarabanbar matar tashi?


Gimbiya Bahijja ta kalleta tayi murmushi, tace "ba mamnsu Fadila ba. d'ayar.


"Kice jarabanbar kenan.


Ita dai gimbiya Bahijja komai batace ba, domin idon da sabo, tasaba jin irin wad'an magan ganu, a bakin gimbiya Bilkisu.
domin tuntana k'arama, idon sukatafi da ita can, kusan kullum saitasha doka a wurin Hajia Nafeesat, tana dukanta tana xaginta, tana cema mai bak'in hali irin na mahaifiyarta.
Shine mafarin tsanarda tayiwa Hajiya nafeesat.
dalilin da yasa batason xuwa gidan kenan.
Don ita harga Allah ta manta dasu.
Koda taje kano karatu gaba d'aya ta manta da sunada wata alak'a a tsanin masarautarsu.


Gimbiya Bahijja tace "har Abba nafad'in muje tare dake, kinga Idon hutu ya k'are, kinfuta da zuwa da jakadiya sai dai kawai ki xauna can gidan.


Tunkafin tarufe baki,tace " taf. Allah ya kiyaye ni.
Tana fad'in hkan, kamar tayi kuka, a nan kowa yasanya dariya harda maimarta, yace karkiyi kuka gimbiya bbu wadda zai tilasta maki abunda bkyso, Karkiyi kuka share hawayenki.


Murnushi tayi tace "ngd Abba nah


Dariya tabawa kowa, daga nan kowan nensu yatashi yanufi d'akin barcinsa.




Kwance tashi asaran mai rai. Gimbiya Bilkisu har ta kammala hutun ta.


Shiri takeyi domin komawarta mkranta.
Maimartaba ne ya aiko kiranta.
Ajiye kayan sake han nunta tayi, tanufi wurin maimartaba, domin jin kiran dayake mata.


Gurfane take gabansa ta sunkuyar da kanta, kasa "Allah yataima keka, Allah yak'ara maka lfy gani, naji ance kana nemana.


Maimartaba yayi kyaran murya, yace "Gimbiya Bilkisu nakiraki ne domin na shaida maki cewa, tareda Antynki Bahijja xaku tafi. domin zataje tadiba lfyar Hajia Nafeesat, sbda kinsa zumuntar dake tsakanin mu da sarki Bashir.


Ta d'ago kanta cikin biyayyah ta kalli maimartaba
"Abba ba wai zank'ibin umurninka bane a'a ba hakan nake nufiba. sai dai Abba kasan a motar haya xan koma, kuma ita Anty Bahijja bata shiga motar haya Abba,
Banason mutafi tare da ita a motar gida. yin hkan shi zaisanya agane koni wacece,kuma banason abunda zaisanya a gane ko ni wacece Abba kadiba mgnata.
Ta kuma durk'usawa, "tuba nakeyi Abba idon nab'ata maka rayuwa kayi hkri.πŸ‘πŸΌ


Kallonta yakeyi, yana murmushi jina jinjinawa hali irin na Bilkisu,
Yace "karki damu 'yata. Nasan bakifad'i hkanba domin kib'atamun rywaba. Tashi kitafi Allah yayimki Albarka.


Tace " Amin Abba.
Ta koma taci gaba da shirinta domin komawa makaranta












Writing by ummu Safwan luv u all😘😘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR..


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by Ummu Safwan 07066214433




PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S


this page is dedicated to my lovely doughter Fareeda shu'aibu Jos, Allah yabar k'auna, luv u so much😘😘😘😘




Sarki Bashir mahaifinsu Adnan, da Ammi mahaifiyarsu Bilkisu uwa d'aya Uba d'aya ne,"


Kada ku manta da Ammi mahaifiyarsu bilkisu 'yar sarki ce,"


da masarautar kano. da masarautar yola. suna da kyan kyawar fahimta."
da sarki Abdulraham, da Sarki Bashir abokanen junane."
don hka sarki Bashir yabawa sarki Abdulraham Auren k'auwarsa Ammi,"


Kunji alak'ar zuwan Bahijja garin kano,"


Amma Bilkisu da Adnan babu wadda yasan juna a tsakaninsu.
sabda tuntana k'arama tadaina xuwa gidansu saboda jininsu be had'u da hajia Nafeesa ba."


Motocine birjik harabar gidan, za'ayiwa gimbiy Bahijja rakiya, kwaliya tayi kalar ta gidan sarauta."


tasanya alkimba, sai tafiya takeyi cikin k'asaita da mulki,"
Fadawa kuwa sai zuba mata kirari sukeyi,"


Ammi ce a gefenta, tarakota,sai jamata kunne takeyi, tace


"Bahijja kikula da kanki, kiyi taka tsantsan da mutanen gidan, domin kinsan xaman da sukeyi da hajiya nafeesa, kiguje abunda xai kai ya komo a gdan," sannan kizama maiyiwa kowa biyayya,
musamman hajiya nafeesa daxaki tafi wurinta,"
Bahijja tayi murmushi, tace
"Ammi kada kidamu insha Allah babu abunda zaifaru. kinsan tsuhuwa mai ran k'arfe Addah tana nan bata mutuba. don hka bazan samu matsala da kowaba a gidan ba har naje nadawo,"


Ammi tayi murmushi, tace "nayarda dake Bahijja, Allah yatsareku ya kuma kaiku lfy, Bahijja tace "Amin Ammitah."
tashiga mota suka suka tafi,"




Gimbiya Bilkisu tareda jakadiya sun sauka lfy."
Saukarsu gda kedawu Bilkisu takira wayar Safeenat tafad'a mata tadawowarta makaranta.
Safeena kuwa tashiga murna da jin dadi, domin tayi missing din babbar k'awarta Bilkisu."


Ranar Monday, takasance kowa ne d'alibi sauri yakeyi domin halartar shiga Aji, gudun karsuyi latti,"
Bilkisu ce tareda Safeenat tafiya sukeyi cikin sauri, domin su shiga Aji, kar malam yariga su shiga."


Tafiya sukeyi sai ganin d'alibai sukeyi suna nunasu da hannu, Safeenat bata lura da hkanba Bilkisu ce kawai talura.
maza da mata kowane nunansu yakeyi, Bilkisu ce tayi k'arfen halin yin mgna, tace


"sister lfy naga kowane sai nunamu yakeyi da yatsa.πŸ‘‰πŸ»πŸ‘‰πŸ»
Safeenat takai kallonta a gun mutanin taga tabbas hakane nunasu akeyi.
tacewa Bilkisu, "bara ga sister zainab a can xaune barana tambayeta kowani abu ke faruwa bamu saniba."
Ai kuwa kafin ta rufe bakinta, sai ganin prince Adnan tayi a gabansu.


Kallon Bilkisu yakeyi sama da k'asa, sannan yace mata "hiii. y'ar matsiyata, to gani naxo gabanki." xanyimki wulak'ancen da babu wadda ya isa yarama maki a makarantar nan." xan wulak'antaki wulak'anci mai tsanani."
kina tsammanin Zaki tab'a yarima d'an sarki kuma kikwana lfy?" to k'arya kikeyi 'yar matsiyata."
kinsanyani jinya ta tsawon sati biyu,ke kuma zansayaki ta shekara d'aya."
sannan daga k'arshe nayi amfani da mulkina da sarautana nasanya a koreki a makarantar. Ba kuma a hka zanbarkiba har saikin d'an d'anni azabar bauta, bauta kuma irin ta k'as k'antun bayi." Zan nunamaki babu wadda isa yaja da yarima Adnan ya kuma zauna lfy."
Kinjawa kanki, kin kuma jawa iyayen, domin harsu bazan barsuba, har sai sunyi nadamar haihuwarki a rayuwarsu."


Yana kaiwa nan, yayi nuni da hannu. a nan take fadawa suka zagayesa,"


Safeenat ce hankalinta duk yatashi, tashiga magiya tana bashi hakuri."


Bilkisu dake tsaye idanunta sun kad'e sunyi jajir, bakomai take tunaniba illah tayi lorzing din darasinta na yau, kuma gashi yau Monday.


Tajuya ta kalli Safeena sai faman bashi hakuri takeyi amma yayi beres da ita.'
su kuwa d'alibai da fadawa duk sun xagayesu, saikace wad'anda sukayi sata,"


Ai kuwa rayuwarta ta kuma b'aci, a nantake ta dokawa safeenat tsawa. Tace "ya isa Safeenat, kidaina bashi hakuri, yazo yyimun duk abunda yagadama." Tunda anfad'a maka sarauta haukace." Ko anfad'amaka, tunda kana yarima d'an sarki kataka kowa yadda kaga dama."
To k'arya kakeyi, babu wani abu da ka i'sa kayimun,"
Sanan kuma babu wata masarauta da ta i'sa nayimata bauta."
Jinya kuma bakayi komaiba". Don sai nasanyaka kayi jinyar shekara 10 kana kwance."
fadawa sukace "karya kikeyi 'yar talakawa baki isa kisanya yarima yayi jinyaba."


juyawa tayi ta kallesu sama da k'asa, ta xubar." Sannan


Tajuya ga Prince Adnan tace masa, a hkan kake tak'ama da mulki?" To tabbas baka cancanci kazama yarima ba."
Kaje ka diba kundin tsarin mulki a chapter 9067 zakaga ynda ake tafiyarda mulki, ba irin naka narashin adalciba, nason kataka talakawanka yanda kaga dama."
Kallonsa takeyi ranta a b'ace."
Tace koda yake banga laifinkaba idon nayi tunanin rashin ilimi ne da jahilci ke d'awainiya dakai,"
don hka babu abunda kake iya yimun, tana kaiwa nan taja wani dogon tsaki, ta tufa masa yawu a fuska, taja hanun safeenat
suka bar wurin,"


Kallo yabita dashi, yashiga goge yawun da ta tofamasa a fuska, yana mamakin ta yadda takecin galaba akansa."




Fadawa xasuyi yunk'urin rek'eta prince

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login