Showing 18001 words to 21000 words out of 46754 words

Chapter 7 - A WATA MASAURAUTAR (1 to End) Book Complete by Ummu Safwan .txt

18 Jan 2025

3594

Adnan ne yasanya a d'auketa, domin d'aukar fansar abunda taimasa,
Wata zuciyar kuwa na gargad'inta da bazai iya sanyawa a d'auke ta ba."


Bilkisu kuwa ya kulleta a d'aki yayi tafiyarsa, sai dai duk bayan a'wa biyu zaizo domin ganin koda tayi nadama tafad'a masa inda Abdullah yake,


Amma babu alamar nadama a fuskarta, sai dai ya tarar da ita tana games a wayarta hankalinta a kwance babu damuwa a tareda ita,

haushinta ya lunlub'eshi yace "wato ita wannan yarinyar batada niyar nadama tafad'i inda takai Abdullah kenan?"


Ya kai hannunsa zai fisge yawar dake hannunta k'irar 1phone tayi saurin b'oye wayar a bayanta,
Ganin zai iya murd'eta ya kwace wayar a hannunta , tatura wayar cikin rigarta,
shi kuma ganin ta tura wayar a rigarta, yayi mata wani kallo,
Yace "shed'aniya ni babu abunda zanyi dake, kidaina wani tura waya a riga, wato d'azun kinji dad'in nahad'a jikina da nake shine yanzun kike Neman nasanya hannuna a cikin rigarki, saboda kina jarabanbiya, to Allah yakiyayeni babu abunda nake iyayi dake, kitafi can kinemi dai dai dake, ninafi k'arfinki babu abunda zanyi dake,
Yaja wani dogon tsaki malama kifito mun da Abdullah nasakeki kikama gabanki ."


Ta kallesa taja wani dogon tsaki, tayimasa kallon sama da k'asa,
Tace "mezanyi dakai, dibeka, me gareka wadda harnake sha'awar had'a jikina da kai,
tanuna masa d'akinsa dayi wani kaca kaca da kaya tace " k'azami kawai."πŸ™„


Tace Abdullah bazan fad'i a inda yakeba domin har yanzun bangaji da ganinka cikin k'unci da bak'in cikin rashin ganin Abdullah ba."


Yace "a she kema zama bek'aremaki a gidan nan ba kenan,
Domin mundun bakibada umurnin a sake Abdullah ba nima kisani bazan tab'a sakinki ki koma gida ba,
Kuma kisani abincin da nake kawomaki daga yau na daina,
Sai dai kizauna da yunwa idon kikaji wuya zakiyi bayani da bakinki inda kikai Abdullah,


Ganin yanda yake magana sai wani cincira yake cike da b'acin rai da bak'in ciki, kamar ba Adnan d'in da tasani ba,
Dariya tashiga yimasa tana nunasa da hannu tana dariya harda rik'e ciki,


Haushi da bak'in ciki ya kuma lunlub'esa,
Ya d'aga hannu alamar zai daketa meya tuna oho sai ya sauke hannun yana cizon yatsa,
Sai yafita d'akin a fusace yaja k'ofar d'akin da k'arfi yasanya makulli ya kulleta yayi tafiyarsa."


Ganin ya kuma kulleta bayada niyar sakinta bare takoma gida,
Duk hankalinta yatashi tana tunanin jakadiya, tasan yanzun duk inda take tana cikin tashin hankalin rashin ganinta kwana d'aya dabatayiba
Idon kuma tayi yunkurin shedawa maimartaba to Tabbas hukuncine zai hau kanta watak'ila harta rasa rayuwarta, wadda idan hakan yafaru bazataji dad'i a rayuwarta ba."


zubur tamik'e tsaye da tuna da Safeenat tasan yanzun labari ya kai a kunnesu na b'atanta
Suma tasan tabbas basa cikin kwanciyar hankali a wannan lokacin."


Wayarta ta d'auka takira fadawanta tace tana buk'atar a sakar mata Abdullah yanzun nan,


Suka amsa mata da to angama ranki ya dad'e,


Suka sakesa, suna kewar juna domin d'an zamanda sukayi da Abdullah sunshak'u dashi sosai,
Wadda shi kuma Abdullah beso aka sakesaba ko dan saboda kalar abincin dayakeci irin na masarauta,


Sai yashiga tunani a zuciyarsa, gaskya betab'a ganin masarautar da fadawa suke daula haka, sai a wannan masarautar,


inama shima a maidashi cikin fadawan yaci gaba da rayuwasu,
da ya bautawa masarautarsu Bilkisu,
Domin zama taredasu ya fahimci me'ake nufi da sarauta,
Kuma ya fahimci k'aramci da daraja d'an Adam irin na masarautarsu Bilkisu


A haka dai yabar wurin fadawan,
yana kewarsu,
yana mai tsinewa Adnan a rayuwarsa domin yasan shine silar sanyawa a sakesa, domin yaga kwana biyu beganshiba, saikace a tare a ka haifemu."πŸ™„ Yaja wani dogon tsaki😏 yayi tafiyarsa."




Adnan yana k'ofar gidansu Abdullah yana kwantarwa da mahaifan Abdullah hankali a kan cewa insha Allahu gobe Abdullah zaidawo gida, ba b'acewa yayi ba yanan cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali,


Begama rufe bakinsaba sai ganin Abdullah yayi a gabannsu yana dariya, yayi kyau yayi k'iba har wani shek'i yake, yana masu dariya, yanufi mahaifansa ya rungumesu cikin jin dad'i, suma sai murna sukeyi naganin tilon d'ansu,


Prince baki yasaki yana kallon Abdullah yana mamakin kwana biyu, yaga yayi kyau kuma yayi k'iba.


Gefe yajanyeshe yana kallonsa cike da mamaki,πŸ€”


yace "Abdullah wai meke faruwa ne?" ina fatan muguwar yarinyar bata sanya anyimaka illah ba?"


Yakaiwa Adnan hararaπŸ™„ yace gaskiya ka daina cewa gimbiya Bilkisu muguwa, domin ita ba muguwa bace, illah maison alkhairi da daraja d'an adam,
Ni wlh a baya d'aukar da nake mata wata wuk'antanciyar 'yar talaka marasa galihu a she ba haka abun yakeba,


Adnan yasaki baki da hanci yana kallon Abdullah cike da mamaki,
Yace "gimbiya kana nufin Bilkisu 'yar sarki ce?"


Abdullah yace kwarai kuwa, 'yar sarki ce, wadda mahaifinta da masarauta gaba d'aya suke alfahari da ita saboda kyawawan halayennta da kuma daraja d'an adam."


Adnan yace " 'yar wace masarautarce?" Waye ubanta?" Kuma A wane gari suke gudanar da mulkunsu?"
Duk a jere yajerawa Abdullah wad'an nan tambayoyi,


Abdullah ya wurgamasa harara, yace " kobaka tambaye niba nad'aukoma labarai da d'umi d'uminsu,


Zakasan kowacece Bulkisu amma kabarni nashiga gida nahuta zuwa anjima sai muhad'u kasha labari."
Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa yabar Adnan a nan tsaye yashiga tunani,


Saida Abdullah yakai k'ofar gida ya waigo yaga Adnan tsaye yana tunani,
Yace gaskya prince baka kyautamun ba, dakasanya a kafito dani daga cikin daular mulkin gimbiya Bilkisu,
Domin gaskiya da bakai bane danace kamar kanajin bak'incikin ganina a cikin daular masarauta
Yana kaiwa nan yashigewarsa gida
Yabar prince Adnan tsaye yana tunani."






























Writing by
Fareeda
Bashir✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR...


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by
Ummu
Safwan


PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




page 2⃣4⃣ 2⃣5⃣




Prince Adnan kasa tafiya yayi a k'ofar gidansu Abdullah,
Domin gaba d'aya Abdullah mamaki yake bashi lokaci d'aya ya firgice masa har yake iya fad'a masa Magan ganu a kan Bilkisu,


Motarsa Yakoma ya zauna yana tunanin sauyawar da Abdullah yayi,


Kiran sallar azahar ne yafito dashi daga cikin motar, yanufi masalanci dake kusa da gidansu Abdullah domin yayi sallah,


Yasan dolene Abdullah yafito domin yayi sallah, daga nan yabafashi labarin kowacece Bilkisu, 'yar wace masarautace shine kawai abunda yakeso yasani a bakin Abdullah."


Shiru kakeji har a'ka kammala sallah bega Abdullah ba, dibe dibe yashigayi koda zaiganshi amma beganshi,


Yanke shawara yayi yashiga cikin gidansu kai tsaye yayi masa dabarar da zai fanyace masa komai a kan Bilkisu,


Domin yanda yaga kan Abdullah namasa rawa ko aika yaro yayi yakirashi yasan bazai fitoba."


Kaitsaye yanufi gidan tare da sallama,
Mamarsu Abdullah ya tarar tsakar gida tana arwala,
Ya durkusa k'asa ya gaida ita, ta amsa masa cikin fara'a da sakin fuska,


Tace "Adnan dawowa kayi ne?" Yaufa bazaman lafiya amininka yadawo,
Adnan yayi murmushi ya sosa kai, yace "Ummu yana ciki kuwa?"


Ummu tace "yana d'akinsa shiga katashesa lokacin sallah yayi yana kwance,


Adnan ya mik'e yashiga d'akin Abdullah dake kwance saman makekeyar katafarsa yana shak'ar barci,


Adnan yashiga tashinsa yana bunbugar k'afarsa,


Abdullah yabud'e idonsa a hakanli yakai dibonsa ga maitashinsa yana cikin jin dad'in barcinsa,
Ai kuwa yayi ido biyu da Adnan
Zurbur yamike zaune yana mai kallon Adnan
Yace "dama nasan kaine, domin babu mai katsemin jin dad'in duniya sai kai,
To yanzun da katasheni me kakeso naimaka?"


Adnan yayi murmushin dole domin a xahirin gaskiya maganganun da Abdullah yake fad'a masa sunayimasa ciyo a rayuwarsa amma baya nuna masa, saboda yana buk'atar yabashi labarin Bilkisu wadda ya dad'e yana nema."


Danne zuciyarsa yayi, yace "sorry abokina tashi lokacin sallah ne yayi kana kwance kanata shak'ar barci,
Kuma kasan kwana biyu nayi missing d'inka,
Bilkisu ta d'aukemun kai."


Jin ya ambaci sunan Bilkisu Abdullah yamik'e zaune yana murmushin jin dad'i a fuskarsa,
Wadda yabawa Adnan mamaki."


Abdullah yace "wlh kuwa nima nayi missing d'inka abokina bari nayi sallah kasha labari da d'umi d'uminsa."


Adnan yayi murmushin dole, yace "yawwa my friend ayi mana addu'a."


Dariya yayi ya d'auro alwala ya shinfid'a darduma tayar da sallah,
Adnan na kallonsa."


Bayan ya idar da sallah ne Ummu tagabatar masu da abinci,
Damun shinkafane yasha kayan lambu da busanshin kifi,

Adnan yakai dibansa ga abincin, yaga kalar abincin da Addah take dafa masu duk ranar juma'a,
Filet d'in abincin yajawo a gabansa yana mai had'iyar yawu,
Soma cin abincin yayi yana mai kallon Abdullah domin ya matso yafad'a masa asalin wace ce Bilkisu,
Yana gudun yafayiwq Abdullah maganar,
Yace yafasa gayamasa, domin ya fahimci dawowarsa wani rashin mutunci yakeji dashi,
Besan abunda ya hango a masarautar su Bilkisu ba,
Wadda shi a masarautarsu basu dashi."


Ya kuma kallonsa yace "abokina baka bani labarin zamanda kayi da fadawa ba?"


Abdullah yayi dariya yace "bari kawai prince nasha wuya,
Kuma daga baya nasha dad'i, domin kuwa abincin damukece tare da fadawa kamar abincin da sarki yakeci,
Bari kawai prince ai mulki da daraja d'an Adam na masarautar su Bilkisu,
Sannan kullum cikin farin ciki muke kwana mutashi cikinsa sab'anin nan,


Prince yayi saurin katsesa zuciyarsa nayimasa tafasa, yana yabun kirkin wata masautar da batasuba, kuma abunda yakeso yafad'a masa bashi yake fad'a masaba😑



Yayi karfin halin yimasa magana yace "friend abunda nakeso nasani shine,
Wace ce Bilkisu?"
Kuma a wane gari take?"
Waye mahaifinta?"


Abdullah yayi dariya yace "Bilkisu Abdurraham yola kenan, haifanfiyar 'yar yolace,
Mahaifinta Abdurrahaman yola shike mulkin garin yola ma'ana shine sarkin garin yola,

Najiya a bakin fadawanta cewa mahaifin Bilkisu duk a cikin 'ya'yansa yafisonta, domin kyawawan halayenta da kuma daraja d'an Adam,
Kuma Batada girman kai irin ba 'ya'yan sarauta,
Asalima bataso a san cewa ita 'yar sarkice,
Wannan dalilin ne yasa taxab'i karatu a garin, domin babu wadda yasan ko ita wace ce bare adinga bata girman da zai hanata karatu cikin kwanciyar hankali."


To kaji tak'aitancin tarihim gimbiya Bilkisu."


Magana yakeyiwa Prince amma hankalinsa gaba d'aya yatafi tunanin Bilkisu,
Dayaji cewa 'yar sarkin yola ce,
To 'yar wacece a cikin matan maimartaba?"


Tunawa yayi da fuskar Bahijja, tabbas tun farkon ganinsa da Bahijja yaga tanayimasa kama da fuskar dayasani,
Sai a yanzun yagane bada kowa take masa kamaba face Bilkisu,
Kodai d'akinsu d'aya da?"


Zurbur yamik'e tsaye sai maganganu yakeyi kamar wani zaranre,


Yana fad'in tabbas k'auwar Bahijja ce,
Domin sai a yanzun yatuna Bahijja tanada k'auwa wadda take bimata, domin su biyu ne 'ya'ya mata a wurin Ammi,


Kuma yasan Bilkisu tun tana k'aramarta ganeta ganeta kawaine beyiba,
Yaja wani dogon tsaki wadda sai da Abdullah yazabura ya mik'e tsaye,


Yadafasa yace "prince lafiya kake kuwa?"
Naji kana wasu maganganu dangane da Bilkisu kodai kunada alak'atane da masarautar su Bilkisu ne?"
Domin da alamar hakan a fuskarka,


Adnan yace ban tabbatarba sainayi bincike,
Ya d'auki key d'in motarsa yayi ficewarsa, yabar Abdullah a tsaye yana mamakin d'an uwanka amma bakasan d'an uwanka bane, saboda rashin sadarda zumunta tsakaninka da d'an uwanka babu wadda yasan juna saida idon kun had'u a hanya katuru kudinga yiwa junanku rashin mutunci saboda babu wadda yasan juna a tsakaninku,
Allah yabamu ikon sada zumunci."


Abdullah yayi murmushin jin dad'i yace "Allah yasa idan kabincika kagano 'yar uwarka ce,
Danafi kowa jin dad'i domin gaba d'aya zan tattara kayana nakoma masarautarsu Bilkisu da zama."😊




















Writing by
Fareeda
Bashir✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR....


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by
Ummu
Safwan




PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




page2⃣6⃣ 2⃣7⃣


Prince tafiya yake hankalinsa gaba d'aya baya jikinsa,
Sai tunanin Bilkisu yakeyi yana mamakin rayuwa irin nata,


Bilkisu kuwa tun lokacinda tasanya fadawanta suki Abdullah take dibun prince shima yazo yafitar da ita cikin wannan gidan, amma shuru takeji bezoba,


Durk'ushe take tana mai zubar da hawaye, idan tatuna halinda jakadiya take ciki a yanzun na rashinta datayi,
tana tausaya mata domin tasan hankalinta a tashe yake yanzun,


Tsayowar motarsa tajiyo, da sauri tayi tashare hawayenda ke zuba a fuskarta, domin karyaga nadama a fuskarta,


Tashi tayi daga tsugunnen datake tayi saurin hawa kan kujera ta kwanta tarufe idonta alamar barci takeyi,


Tanajinsa lokacinda yasanya key yabud'e k'ofar d'akin yashigo ya ganta a kwance tana barci cikin nutsuwa,


Matsowa yayi kusa da ita ya tsora mata ido yana kallonta cike da tausayi, ganin yayi takoma masa Bahijja sak, murza idonsa ya kumayi domin ya tabbatar da gaskyar ita d'ince ko kuwa gizau take masa, ita d'in daice yagani kwance tana barci cikin kwanciyar hankali,.
Sai gani yayi tak'ara masa kyau da gwarjini, ya kai dibunsa a agogon gwal dake d'aure a hannunta yaganshi da tambarin masarautar yola, a nan take tausayinta ya lunlubeshi ya durk'usa saiti kujerar da take kwance yasunkuyar da kansa dai dai saiti bakinta ya kaimata kiss a baki, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login