Showing 30001 words to 33000 words out of 46754 words

Chapter 11 - A WATA MASAURAUTAR (1 to End) Book Complete by Ummu Safwan .txt

18 Jan 2025

3602

Fadawa basujira umurninta ba sukayi saurin dakatardashi,
Suka had'a baki gaba d'ayansu, suka
Dakata d'an talakawa.
Mundad'e muna sanyamaka ido kana bibiyarmu tun a kan hanya,
Meke tafe dakai?"


Bilkisu tayi saurin dokawa fadawa tsawa, tace "banason hakan banason ana wulak'anta d'an adam a gabana,
da talaka da mai kud'i duka Allah ya haliccesu, indai ina taredaku karna kuma jin kunyiwa kowanne mutun wannan kalamin,
Kubarshi ya k'araso nace, domin naji abunda ke tafedashi,


Bilkisu na magana amma kallonta yakeyi cike da sha'awa, bedamu da abunda fadawa sukayimasa ba,


Ya k'arasa kusa da ita yace "gimbiya Bilkisu halayarki suna burgeni suna kuma bani sha'awa,
Saboda kyawawan halayarki yasanya nake bibiyar rayuwarki domin ganin nacinma burina a kanki na aurenki,


Da farko sunana Zaharandin Mansur nid'an minister garin nanne,
Tun lokacinda nad'ora idona a kanki Allah yasanyamin sonki a rayuwata,


Bilkisu kyawawan halayanki sune suka kuma dasamun wutar sonki a rayuwata,
Harnakai bana iya ganin kowace mace a duniya sai ke,

Pls Bilkisu ki amshi soyayya ta wlh nayimaki alk'awarin bazan tab'ata wulak'antakiba
Zankula dake zanriritaki a cikin Mata,
Zaki zamo tauraruwa a cikin taurari,kuma nayimaki alkharin bazan tab'a yimaki kishiyaba, pls Bilkisu ki amshi soyayyata.


Bilkisu kallo tabishi dashi cike da mamaki ganin yanda ya katse sai zuba zance yakeyi,


Tajuya ta kalli fadawanta take tsaye suna kallonsa,
Tayi masu nuni da suyi tafiyarsu saitanemesu, suka shiga motarsu sukayi tafiyarsu.


Ta maida kallonta a xaharandin tayi murmushi tace "nagode da k'aunar da kanunamin,
Hak'ika naji dad'in soyayyarka gareni,
Domin inason mai sona a duk inda yake,

Ta kalli agogon da ke hannunta, tace kayi hakuri sai wani lokaci domin yanzun lokacin cin abincina yayi,
Gashi kuma yanzun nadawo daga tafiya,
Tajuya zata shige gida kenan,
Sai hango Prince tayi a tsaye a bakin motarsa tareda Abdullahi
Adanunsa sun kad'e sunyi jajir, jikinsa wani cincira yakeyi yana rawa, saboda b'acin rai,
Abdullahi ne rik'edashi yana lanlashinsa had'ida bashi magana,


Bilkisu ganinda tayimasa a tsayen saida gabanta yafad'i, domin tasan ba alkhari bane yakawosa,
Ya k'arasa wurin zaharandin yarik'emasa kwalar riga yana fitar da huxuci kamar wani zaki,
Yanafad'in " meyakawoka wurin matata?"
Wani dalili zai sanyaka zuwa neman aure cikin aure,
Domin Duk maganganunda kake furtamata a kan kunnena yake.


Ya kuma cacumo masa riga, saida idanun zaharandin suka firfito waje, akan jinzafin rik'on da Adnan yayi masa,


Yace gargid'i nake maka ba umurniba,
Duk lokacinda nakuma ganinka a k'ofar gidan nan,
Ko kuma na kuma ganinka tareda Bilkisu saina b'atarda kai daga lokacin ba mai kuma ganinka."


Ganin rik'on da prince Yayiwa zaharandin yana neman kashesa,
Cikin yanayin tashin hankali tak'arasa kusa dashi
Tasanya hannunta tabuge hannun prince daga wuyan rigar xaharandin
Tace "sakesa Adnan waime hakan?"
Idan ka kashesafa?"


To bari kaji zaharandin shine Mijin da zan aure, kuma shi nakeso a rayuwatah,
Kuma kasani daga yau duk wani abu yasameshi,
Kaima baza'abarkaba sai anhukuntaka,
Domin furucin dakayi yanzun shi zai d'aureka har lahira.


Da kuma kake i'k'irarin ni matarkace waye ya d'aura mana aure dakai,
Allah ya tsareni da aurenka dana aureka k'ara na tabbata banyi aureba,
Domin babu komai ataredakai sai tsabar mugunta,
Da kuma wulak'anta talakawanka."


Ta juya wurin zaharandin da yayi tsaye yana kallonsu idonsa yayi jajir d'in wahala,


Tace "my love yi hakuri shiga motarka kayi tafiyarka, sai munhad'u a makaranta gobe saimu iyar da maganarda mukeyi,
Tabud'e masa murfin motar
Tayimasa nuni da hannu da yazo yashiga
Yaji dad'in irin karamcin da tayimasa a gaban Adnan,
Murmushin dole ya k'ak'aro yazo zaishiga motar yace "my one and only kikulamun da kanki,


Naji dad'in kulawarki a kaina luv u
Tace "luv u 2


Yashiga motarsa yayi tafiyarsa yana mai d'aga mata hannu
Itama hakan.


Duk abunda sukeyi a kan idon Adnan, jiyake kamar ya had'iye zuciya ya mutu saboda bak'in ciki.


juyawa yyi yanayiwa Bilkisu magana yana fad'in "Bilkisu tsaya kiji abunda ke tafedani alkhairi ne wlh ba muguntace taka woni wurinki ba.


Ko sauraransa batayiba tayi tashegiwarta gida."


















Writing by Fareeda Bashir✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

A WATA MASARAUTAR......


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by
Ummu
Safwan




PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




Page 4⃣5⃣ 4⃣6⃣








Sai ganin xaharandin
tayi cikin motar fuskarsa d'auke da murmushi,
Ya bud'e murfin motar yafito fuskarsa cike sa fara'a,
Yake cewa gimbiya barka da fitowa tund'azun nake zaman jiramki domin naga kyankyawar fuskarki koda zanji dad'i,

Bilkusu ta kallesa sama da k'asa, tace "nagode zaharandin da kulawarka gareni amma kasani idan ina tafiya ba'a tareni a hanya, ina fatan hakan yazamar makashine na k'arshe


Xaharandin yace insha Allah gimbiya hkan bazai kuma faruwaba,
Nasan makaranta kika nufa kushigo mutafi nima can zantafi,


Tayi murmushi tace "nagide zaharandin a k'asa nakeso natafi,


Ya durk'usa k'asa yana rok'inta, yanafad'in gimbiya kiyi hkr kishigo nak'arasa da ke,
Banaso kina tafiya a k'asa kamun ki kai makaratar duk namijin da yaganki nasan sai ya kalleki ni kuma yi hakan zai ya yimun ilah a rayuwata,
Pls Gimbiya Dan Allah badan halinaba kishigo nak'arasa dake makaranta,


Ganin ya had'ata da Allah yasanyata shiga mortar suka nufi makaranta,


Tafiya sukeyi sai fira yakemata tun bata kulashi hartasoma bayarmasa,
A nan ta fahimci zaharandin mutum ne mai yawan barkwanci, a haka har suka isa makaranta,


Shigarsu makarantar yayi daidai da fitiwar prince daga class,
Kallo yabisu dashi cike da tashin hankali da tsantsar kishi a fuskarsa,


Bilkisu ta hango prince tsaye ya tsura masu ido yana kallonsu, saida gabanta yafad'i, amma kuma ta dake tabiyewa Zaharamdin yaci gaba da bata labari tana dariya,


Jikinsa ne yasoma rawa alamar b'acin rai zuciyar maza ta motsa,
Abdullah yayi saurin matsowa kusa dashi ya rik'ashi ya zaunar dashi, yana bashigana,
"Pls Adnan ka sansauta nuna kishin hka akan Bilkisu, wadda batasan kanayi,
Idan ta fahimci da kana kishinta hakan, to tabbas na tabbas zatadingabi ta wannan hanyar domin ganin ta musguna maka,

Adnan yadafa Abdullah yamik'e tsaye, yace "Abdullah son Bilkisu da kishinta suna neman sukashe, bakaji yanda nakejiba a zuciyata idan nasanya idona naganta tareda zaharandin,
Jina nakeyi kamar nahad'iye zuciya na mutu, zansanya a d'aukemunshi, tabar ganinsa,
domin ya daina d'aukemata hankali, har saina dasa soyayyata a zuciyarta harmuyi aure


Abdullah yace "haba abokina kazamo namijin duniya mana a fagen soyayya, idan kasanya aka d'aukesa tomekayi kenan?"
hakuri zakayi kafafata dashi harkasamu ka kwato soyayyarka awurin Bilkisu dingayi,

Duk maganganunda sukeyi a she akan kunnen Safeenat,
Tazo wuce, takusa dasu, basu d'ura da itaba,
Sai gani sukayi tarab'asu ta wuce, had'ida yimasu wani kallo na nuna alamar duk abunda kuke fad'i najishi a kunne na,
Tanufi wurin Bilkisu cike da mamaki ganinta tana magana da xaharandin harda dariya.


Adnan yabita da kallon mamaki,
Yajuya ya kalli Abdullah yace masa "ina ganinfa duk maganganun da mukeyi Safeenat tajisu,
Abdullah meye mafita?"


Abdullah yace wannan ma wata damace dazamu biyo tawurinta mu fahimtarda ita, saita tashawo maka kan Bilkisu,
Adnan yace "idan mukatashi daga makaranta musameta gida saimuyi maganar,


Safeenat kallon mamaki tabi Bilkisu dashi,
Tayimasu sallama, zaharandin yace k'awarmu barka da zuwa,
Ita kuwa Bilkisu zuwan safeenat tayimashi sallama,
Tarik'a hannun safeenat suka nufi class,


Safeenat fuskarta cike da alamar tambaya,
Bilkisu ta lura da hakan tace "sis kobaki tambayanba yanzun zanfad'amaki domin
Naga hkan a fuskarki,


Safeenat tace "ina sauraranki, meye had'inki da zaharandin Mansur?"


Anan Bilkusu tashiga bata labari tunfarkon had'uwarsu harkawowa yanzun da tagansu a tare,
Tacigaba da cewa wlh Safeenat babu soyayyar zaharandin ko kad'an a rayuwata,
Domin baya d'aya daga cikin mazan danakeso na aura, ina kulashi ne domin na musgunawa Adnan dan na lura dazarar yaganni taredashi jiyake kamar yahad'iye zuciya ya mutu,


Safeenat tace "tabbas prince sonki yakeyi domin nadad'e da gano hakan ataredashi, kinkoga kuwa kunyi maching dashi,


Bilkisu tace "Allah ya tsareni nayi aure wacan maigirman kan tsiya,
Wadda me d'auki talaka a bakin komaiba saidai abunda wulak'an tawarsa,
Keni wlh banmafa yarda dashiba akwai abunda yakeson k'ullawa shiyasa yabiyo ta wannan sigar wai sona take, kuma nasan Allah yafishi,
Takuma kallon Safeenat tace "ga alamar tarkonsa yafara kamaki, kinsoma yarda dashi.
Safeenat tayi murmushi taja hannunta suka shiga class,


Bayan antashi daga makaranta Adnan da Abdullah sukayi zaune a mota suna jiran fitowar Safeenat tareda Bilkisu,
Domin subi safeenat gida dansuyi magana da ita ta fahimta,


Sai hangosu sukayi sunfi Zaharandin yabud'e masu mota sunshiga yaja suka bar makarantar,


Prince yacije Baki, ya duki sitiyarin mota,
Had'ida kallon Abdullah yace "wlh Bilkisu sutake takasheni, ita bata lura da sonda nake mata takeyimun wannan wulak'ancin, amma nasan maganinta,


Yaja motar yabi bayansu."

























Luv u all😘. Writing by Ummu safwan✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘


A WATA MASARAUTAR.....


πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘




Writing by
Ummu
Safwan




PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S




Page 4⃣3⃣ 4⃣4⃣


Abdullahi ya rik'ashi yashi gardashi mota, saboda b'acin rain abunda Bilkisu tayimasa be iya tuk'a motarba,
Saidai Abdullah yaja motar suka tafi."


Gida Abdullah ya nufadashi,
Yashigar dashi d'akinsa ya kwantar dashi a kan gadonsa,
Adnan sai zubar da hawaye yakeyi idan yatuna irin abunda Bilkisu tayimasa a gaban zaharandin,


Abdullah sai hakuri yake bashi,
Yana kuma lallashinsa,


Adnan ya kalli Abdullah idonsa jajir,
"Yace wlh Abdullah a kan Bilkisu komai zan iya aikatawa Zaharandin, dama tun a makaranta nake ganin take takensa a kanta, Ashe dama sonta yakeyi?"
To be i'sa yaja dani a fagen soyayya ba,
sai dai nasanya a b'atar dashi b'acewa ta har abada,
Ba d'an minister bane shi koda d'an shugaban k'asa ne be i'sa yayi ja yanya dani a fagen neman aure ba, musamman a kan Bilkisu.


Zubbur yayi yamik'e tsaye,
yanufi hanyar waje yana wani huci,
Abdullah yayi saurin rik'o hannunsa yace "prince ina zuwa haka?"


Prince yace "wurin dady zan tafi, nafad'a masa yasanya ranar aurenmu nan da sati biyu,
Domin nahuta da rad'ad'in sonta dake andabata a rayuwatah,


Abdullah yarik'e hannusa yace "idan kayi hakan mekayi kenan?"
Prince kazamo namijin duniya mana, kajajirce kasamo soyayya gimbiya Bilkisu da hannunka,
har lokacinda ta yarda ta amince, tasoka, a sannan saikuyi auren,

Domin na hango k'iyayyarka tsantsarta a idon gimbiya Bilkisu,
Wadda mundun kayi amfani da damar da kake da ita ka domin aureta,
to tabbas komai zai iya faruwa bayan aurenku.


Pls Adnan ka kwantar da hankalinka mubi komai a sannu har kasamo soyayyarta da kanka ta yarda dakai sannan kuyi auren sai kunfiyin zaman lafiya da jin dad'in rayuwar aurenku.


Sai a sannan Prince yaji dad'i, hankalinsa ya soma kwanciya, sai ya soma tunanin ta ina zai fara gyara kura kuransa?"
Da musgunawar da yadinga yiwa Bilkisu, wad'anda yasan har abada bazata tab'ata mantawa dasuba.


Ya kuma mai da kallonsa a Abdullah yace " Abdullah ta ina zan fara Neman soyayyar Bilkisu?"
Harta yarda dani ta kuma amince dani har muyi aure?"


Abdullah yace "wannan nabarmaka daga yau zuwa gobe kayi tunani kasamo mafita,


Tashi tsaye yayi yacewa prince "zantafi gida sai dai gobe idan mun had'u a makaranta,
Kashigo da wuri domin Kasan munada test k'arfe 8:30am


Prince yace" ai dole nashigo da wuri kodan saboda naga sahibatar zuciyata,


Abdullah yayi dariya yafita had'ida jamasa k'ofa yace "Prince Adnan ankamu dayawa a soyayyar Bilkisu.


Bayan Abdullah yafita,
Prince har zaishiga toilet domin yin wanka,
Sai ganin Abdullah yayi yadawo a guje yana fitarda numfashin gudun dayayi,


Prince cikin gid'ima ya tambayesa Abdullah lafiya?" Meke faruwa?" Naga kadawo a guje hakan?"


Abdullah yakai zaune dafe dakai, yacewa prince "inafa lafiya ina fita yanzun naci karo da wannan masifanfen sojan,
sanye da kayan sojoji, da k'atuwar bindiga rataye a kafad'arsa.


Yanuna prince da hannuπŸ‘‰πŸ» Wlh duk abunda yasameni da kai zanyi kuka,
saboda saidana fad'a maka bazan fitoba amma katilassamin saida nafito yanzun ga irinta nan abunda nakewa gudu yafaru. ya d'ora hannu a kaiπŸ™†πŸ»β€β™‚ shikenan yanzun kasheni zaiyi."

Adnan mezaiyi inba dariyaba,
Yacewa Abdullah "mutafi ka nunamun kowaye wannan sojan dayakeso yafirgitarmun da Amini,


Abdullah yakaimasa hararaπŸ™„ Yace "saidai kai kafita,
kagansa amma ni daga nan babu inda zankuma matsawa.


Prince safe da ciki yana dariyaπŸ˜‚ yace "to fad'amun a dai dai wane wuri kaganshi?"


Abdullah yace "daka lek'a waje,
zaka ganshi zaune a kan kujera, da bindiga a hannunsa.


Prince yafito yana dariya,
Mahmud ya hango abokin Fahad sanye da kayan sojoji
Adnan yayi murmushi yak'arasa wurinsa, had'ida yi masa sallama, ya mik'amasa hannu suka gaisa,

Adnan fuskarsa cikeda murmushi yace " yaya mahmud,Ashe dama kaine ka firgita aboki?"
Aduk lokacin da yayi ido biyu dakai saika firgitashi har saiyasaki fitsari,


Mahmud yayi dariya yace "wannan abokin naka shikuwa menaimasa hakan?"
wadda yasanyashi jin tsorona harda fitsari?"


Adnan yana dariya yafad'amasa duk abunda Abdullah yafad'amashi a kan shi,


Mahmud dariya yashigayi, yace "tuni namanta dashi, nayi cigiyarsa kwana biyu domin nabashi kayansa bangansaba, yanzun haka jakar kayansa na but d'ina dasu nake yawo, ina cigiyarsa ko zanganshi amma ko alamarsa babu,
Namayar da kayan na'ajiye a but d'ina."


Adnan yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login