Showing 15001 words to 18000 words out of 37326 words
Chapter 6 - WACECE ITA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hauwa M Jabo.txt
Yaya farhaan, zan iya CE
muku duk yinin ranar abinda ta saurara kenan,
ta rasa mi yasa komai nashi burgeta yakeyi,
bama kamar idan taji dariyarshiba, itama saita
dara haka take zama ta miqe gafafu tayita
saurare tana dariya, wannan voice yasata
walwala ranar farahnax taso ta gane sai kawai
ta daina saurare dan bata iya delete ba,
Sai yanzu ta gane mi wannan takardar da goggo
ta bata tace yayyenta sunce ta kira take nufi,
Ta nemota a cikin kayanta ta saka amma wayar
tata ba kudi, ta je gun farahnax tace ta kira
mata wannan number, farahnax kuwa chatting
takeyi bazata iya bata wayantaba sai ta saka
mata recharge card na 1,500 ta saka mata
number tace ta kira, ta koma dakinta haka tayi
ta kira ba tareda tasan kiran yana shigaba saida
ta bar miss call 47...
Ameen bayan ya dawo yaga miss call da yawa
sai ya kira,
Tayi sallama, ya amsa yadauka mamarshi ne
Dan kusan muryarsu iri dayane, mama lafiya kira
haka ?? sai tace ba Maman shi bane ya tabbatar
da wrong number ne sai kawai yace wrong
number ya kashe, bai tsaya yaji abinda zataceba,
Itama dataga haka sai bata qara kiran number
ba,
***************
Kwanaki sun tafi iffaah ta waye iya wayewa
kamar ba Yar aikiba, wani lokaci Idan sunfita
tareda farahnax bazaka ganetaba cox tafi
farahnax kyau nesa ba kusa ba, saidai har yanxu
qauyancinta da yake nuturally ne sai bai
saketaba tana taba abinta, gata bakinta baya
shiru duk abinda ta gani saita tambaya gata a
waye a dressing amma a aikace har yanxu da
saura...
shekara ta zagayo iffat zata koma qauyensu Dan
sallah da azumi achan kamar yanda sukayi
alqawari run farko,ta rasa gane dalilin da yasa
ranta bayason komawa qauye kodan zancen
goggo ne da take cewa za'a saka mata ido a
qauye tayi zamanta birni! ko kuwa rabuwa da
iyayen farhaan da, ko mahaifiyarsa ta kalla sai
taji sanyi sabida tsabar kamarsu da farhaaah.....
[10:05PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 36
Na Hauwa M. Jabo
**************
Iffaah ta isa qauyensu cike da tunanin rabuwa
da da iyayen farhaaan..
Goggo tayi mamakin yanda ihhatu ta chanza tayi
kyau duk wani Abu da ake buqata a gurin mace
ihhatunta tana dashi saidai tunda iffaat taje bata
zuwa ko ina daga gida sai gida, ta natsu
matuqar natsuwa, ga yawan shiru shiru da
takeyi.
Ranar goggo ke tambayarta bata sami miji a
birniba, goggo ni har yanxu ba Wanda
yakesona,! Ta dafe qirji kardai birnin ma kin
musu halinsu kin kashe kasuwarki, zancen goggo
ya bata dariya, goggo Allah ne bai kawoba,
hakane kuma Dan yanxu naga kin tsama yan
mata, wallahi sai mai mota zaki aura kikaini
makka ko? Ta amsa da sosai kuwa ta fada tana
miqewa tashige daki, zan iya CE muku tunda
iffaah ta dawo qauye kullum sai tayi kuka, wani
Abu takeji ya tsaya mata a zuci ya tokareta ya
hanata sakat, bata iya aikin komai Idan wannan
abin ya motsa mata.. abinka da yarinta Sam
bata gane cewa soyayyah bace, bata gane kanta
Sam. sau tari takanje bayan gari ta sami bishiya
ta zauna taci kukanta har ta godewa Allah,
sannan ta dawo gida ba abinda yafi damunta illa
rashin gane takamammen abinda yake damunta.
Wayartace tayi qara, ta dauka farahnax ce.
Hello
Ta amsa tanajin dadi
Farahnax chikin dariya take maganar bayan sun
qare qaisawa, kee iffaat Yaya ya dawo dazu sai
tambayar ki yakeyi, qirjintane yayi bala'en
bugawa sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye,
na rashin dalili ta yi shiru.
Hello hello iffo kinajina? Tanata magana amma
iffaah ta kasa bata amsa, qarshe ta tsinke
wayar, iffaat ta shige dan dakinta ta zauna ta
rasa mi yake damunta yan watannanin Miyasa
duk lokacinda take tunanin yaya farhan take
shiga wani hali??
Miyasa duk taji sunanshi sai taji faduwar gaba??
Miyasa taji tanason ta Ganinshi yanxu ??
Miyasa duk ta zauna labarin sa take sonyi??
Kai tambayoyinta sunyi yawa, batada amsar ko
daya. Tayi wani tsaki
Ba abinda yake daga mata hankali irin son ganin
farhaan da takesonyi, Wanda ji take kamar tayi
fiffike taje ta Ganshi,
Amma ba halin yin haka,
Su iffaat an fada tarkon soyayyah amma batada
labari har yanxu ba tasan miye soba..
[10:11PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 37
Na Hauwa M.Jabo
***********
Kwanaki sunja gaba har anyi sallah qarama,
iffaat zata koma gidan aikinta a birni, tun lokacin
da farhaaah yazo batayi waya dashiba jifa jifa
tana kiran su umma ta gaidasu, kuma farahnax
tana turo mata recharging wayanta.
Ta shirya tsab sai birni,
Su umma sunyi murnar zuwanta matuqa ko
banza umma nasonta Dan akwai bada labarin
ban dariya kamar me shi yasa daga umma har
Abba zaune sukeyi tana basu labari suna kwasar
dariya.
Wannan karo an samu chanxi iffaat ta dawo
amma ba komai tsakaninta dasu, musamman
umman farhaan kunyar su takeji! Da kuwa zaune
take tasasu gaba tana basu labari suna dariya,
gashi kullum tanada sabon labarin da zata
bayar, bata maimaici amma yanxu Dogon motsi
bata iyayi gabansu, Ashe akwai abinda zai iya
chanza wannan hatsabibiyar yarinya,?? Hmmm
sai soyayyah.. soyayyar da ita kanta batasan
tanayiba,
Kai amma ni jabo na jinjinama duk soyayyar da
tayi tasirin chanxa wannan yarinya koda ta qara
wayewa yanxu...
*******
Iffaat miyasa tunda kika dawo kika daina bamu
labari?? ta sunne kai qasa tayi murmushi ba
komai hajiya! Nidai wannan zuwa hutu baiyimin
ba yarinya duk ta susuce sai rama takeyi? Ko
wani Abu ya faru bakyason fada mana??
Laaa hajiya bakomai Abba yace ki kyaleta kinsan
fa ta qara girma hankali yana shigarta, duk aka
saka dariya,
Farahnax ce ta shigo tare da wata yarinya
kyakyawa zatakai 24yrs kyakyawace sosai, tana
shigowa tace kinganta, yarinyar mai amsa sunan
suhailah ta gaida su umma da abba a kunyace,
ta kalleni cikin fara'a tace Ashe ma qaramace
sosai gata kyakyawa kuwa saidai tafini kyau da
kike cewa munyi kama., umma tace ai kuwa
nima sai yanxu naga wannan kama da kuke
cewa sunyi, saidai yata iffaat tafi kyau, sukayi
dariya gaba daya iffaat ta gaisheda suhailah
umma tace kuje daki mana, suka wuce umma
tace na bisu mama na tashi na bisu, anan
farahnax take baiwa Suhaila labarina sunata
dariya, sai nadan saki jiki dasu dama wani lokaci
zaman kadaicine ke haifar mata da damuwa bata
saniba..
Suna tsaka da hira wayar Suhaila tayi qara, ta
dauka tana kashe murya, duk da cewa da English
suke maganar hakan bai hanani fahimtar dawa
take maganaba kuma mi suke fadaba, farahnax
tana bani labari amma hankalina Sam baya tare
da ita qirjintane ke dukan uku uku wani baqin
ciki Mara dalili takeji Wanda ya haifar mata da
rashin natsuwa lokaci daya, Daidai nan kunnenta
ya jiyo mata maganar da takasa tantance
sanadiyar rudewarta sai ganinta tayi a asibiti....!
[12:04AM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 38
Na Hauwa M. Jabo
Tana bude ido taga Su umma sun zagayeta Yar
budurwar na zaune gefenta itada farahnax, sai
nan ta tuna da abinda kunnuwanta suka jiyo
mata, LAAA KINGA NA MANTA IFFO BANGAYA
MIKIBA, KINA QAUYE AKA YIWA YAYA FARHAAN
BAIKO DA SUHAILA..!!!! Hawaye ne suka wanke
mata fuska shaaaaar, idan bata mantaba
Wannan maganar itace qarshe maganar da taji
sai yanxu da ta farka ta ganta a asibiti, ta
motsa hannu taji yayi nauyi ta qurawa Suhaila
ido mi yasa taji tana Sonta aranta?? Amma sai
take ganin kamar ba sontane takeyiba tsanarta
takeyi,?? Tanajin Suhaila har cikin ranta amma
kuma tsanarta tayi yawa a zuciyanta. tana tsaka
da tunani umma ta dafataa ta mata sannu, ta
kalli umma tace hajiya miya faru?? Ya akayi
mukazo asibiti?
Umma ta bata amsa da kin samu sauqi dai ko?
suna haka sai ga nurse tazo ta dubata aka
tabbatarda yanxu ba abinda yake damunta, illaa
kawai ta rage tunani....
Ta tashi zaune anan farahnax ta bata labari
muna tadi dake nake gaya miki an yiwa Yaya
farhaan baiko da Suhaila sai kawai naga kin
danne kai kina juyawa kika miqe tsaye sai kuma
naga kin kika fadi sumammaiya, Suhaila ta katse
wayar mukayo kanki muka kira umma taxo aka
saka miki ruwa amma ko motsi daga qarshe sai
Abba yace a kawoki asibiti, farahnax tace miyake
damunki iffo?? Tunda kika dawo gida kika chanja
ko su sukace miki ki riqa yi mana haka? Wallahi
iffo banajin dadin ganin ki a haka, Dan zaman da
mukayi na Saba da tsokanarki da labaranki
Masu dadi, shiyasa ma na kawo Suhaila itama ki
bata labarai sai Kuma haka ta faru, please ki
saki jiki damu ke Yar uwarmuce kinji.!? Aranta
tace da nasan abinda yake damuna Dana fada
kodan samun natsuwar xuciyata..
Ta kallesu tayi murmushi ba komaifa, sai tayi
shiru hawaye suka gangaromata,umma ta matso
Ku bar min yarinta ta qarajin sauqi sannan Ku
fara mata jarida. Dukansu suka saka dariya har
iffaat din saida tadan murmusa.
Saida ta kwana daya da yini sannan aka
sallamesu.
**
sun koma gida umma da farahnax suka sa iffaat
gaba sai ta fadi abinda yake damunta. Amma ta
murje ido tace bakomai koda yake ba komai din
tunda ita kanta batasan abinda yake damunta
ba, nifa tinda ta dawo Hutu banga dariyarta sau
ukuba, umma tace nimadai banganiba umma
ranar abbanku yace a kirata ta bashi labari
amma tazo ba wani labari,
Iffaat!! Na'am hajiya! Ki mana magana zama
damune kike gajiya dashi ko kuma wani yake
quntata miki ko kuma wani Abu yake faruwa a
qauye??
Kawai sai ta fashe da kuka, kuka mai tsuma
zuciya, ita kanta batasan sanadin kukanba,
sukayita rarrashi har tayi shiru, ki fada mana
minene idan mune mu gyara muryan ta a dishe
tace wallahi Baku bane hajiya, nima wallahi
bansan abinda yake damunaba haka kawai idan
ina zaune sainaji raina ya baci ko kuma na
riqajin inason wani Abu amma bansan ko miyeba
qunci yamin yawa hajiya ta qara fashewa da
wani kuka, sukayi chirko chirko, chan iffaat tace
mamarta takeso .....
[12:04AM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 39
Na Hauwa M. Jabo
Umma ta nunfasa tace idan wannan ne
damuwarki karki damu xamu nemo miki mamarki
duk inda take, ta danyi shiru amma jifa jifa
takan zubarda hawaye, bayan kwana biyu, muna
zaune palo nidai kamar hoto ko nace gunki
kawai cika wuri nakeyi. Suhaila ce ta shigo ina
ganinta naji qirjina ya wani buga, da Leda a
hannu, tana murmushi ta gaida umma tace nazo
dubiyar mara lafiyane suka saka dariya ai ga
tanan taji sauqi, ta zauna tamin ya jiki, na amsa
mata inata kallonta har tadan tsargu, suhaila
tace iffaat wallahi kinyi kama da qanwar
babanmu sosai saidai tafiki haske amma hatta
gashinki irin natane ke ko murmushinku iri daya
tafiyarku ma iridayace ke hatta maganarku iri
dayane ke komai naku iri daya, duk aka saka
dariya har iffaat din ganin yanda Suhaila ta
jajirce da bayani, sai kun sami lokaci kixo muje
gidan mu ki ganta a gurinta nake zaune, iffat ta
amsa da insha Allah....
*****
Iffaat dai bata gane karatu yanxu, gashi an mata
nisa sosai abubuwan da bata yisuba a lesson
take samu a namatasu, karatun ma haushi yake
bata yanxu, zaman gidan ya gundureta, idan har
aka zauna Idan ba hirar farhaan akeyiba bata
taba samun sukuni a rayuwarta, wutar sonsa
kullum Dada ruruwa take a zuciyarta amma har
yanzu bata gane cewa she is fall in love ba...
Yar baqa qawarta tayi tambayarta har ta gaji sai
tace ba komai, to batasan mi yake damunta ba
bare ta fada,
Zaman birni ya gagare iffaat, kusan kullum saita
xubar da hawaye wace irin rayuwace wannan?!
ta matsa musu akan ita sai ta koma gurin
iyayenta ta gaji da zama anan, aka buga sama
da qasa amma taqi amincewa har suka gayawa
abba,
Ranar yasa aka kirata ya tambayeta ko ana
mata wani abinne tace ba abinda ake mata,
iffaat bamu daukeki a matsayin Yar aikiba a
matsayin Yar cikinmu muka daukeki wannan
dalilin yasa har muka damuwa da damuwarki,
muka sakaki makaranta Dan kema ki sami gata
da yanci irin Wanda ko wacce yarinya take samu
a gidan mahaifinta, iffaat kamar jiran abba take
ta fara kuka kamar ranta zai fita, Abba nagode
da dawainiyar da kukayi dani Allah ya saka da
alkhairi, abba wallahi ni kaina bansan abinda
yake damunaba rayuwata bata min dadi ba
abinda yake burgeni a duniya komai haushi yake
bani, banason naci gaba da wannan hali na
damuwa kuma na sakaku akan shakkun kanku,
wallahi kun min komai a rayuwa kuma na gode,
wata qila Idan na koma qauyenmu tunda nasan
yayyena suna zuwa nemana wataqil Idan nagan
su in sami sassauci.
Amma Dan Allah Abba Ku mayar dani gida taci
gaba da kukanta......
Tofa muje zuwa muji anya zata iya rayuwar
qauye? Yama za'ayi ta gane cewa soyayyah ce
take damunta...??!
[11:44PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 40
Na Hauwa M.Jabo
Abba Ku taimakamin ku mayar dani gidan mu,
jikin kowa yayi sanyi yanda take kuka kamar
ranta zai fita ta basu tausayi koni Jabo ta
matuqar bani tausayi Dan saida nayimata qwalla,
tabbas So bala'eeee ne, yana zautar da mutum
ya rasa mi yake masa dadi yama rasa gane
kansa,! zaiyi loosing din control dinsa ne gaba
daya, ko manya ya suke fafatawa da soyayya
bare yarinya Yar shekara 15 irin iffaat da har
Yanxu batada wani wayo bare har ta gane wane
hali take ciki....
Abba yace To ki daina kuka iffaat za'akaiki gida
dama Dan kada ya zama mune muke shiga
haqqinki ba tare da mun saniba amma tunda
kince bakomai kin zabi hakan shikenan, dukansu
basu ji dadin tafiyar da iffaat zatayiba, amma ba
yanda suka iya dole su saka mata ido, farahnax
ma ta sameta a dakinta tana kwance bayan ta
hada kayan ta, yanxu iffo tafiya zakiyi ki
barmu?? Muka miki dan Allah da har bakya iya
zama damu?? Ta kalleta tace sister wallahi ba
haka bane bakumin komaiba, kawai rainane baya
min dadi kuma bansan dalilin hakanba, kuyi
haquri Dan Allah, anan dai sukayi hirar qarshe,
koda iffo taqi sakin jikinta...
sun mata goma na arziki suka bata kudi masu
yawa sannan akasa driver yakaita har qofar
gidansu.
Shikenan iffaat ta baro gidansu farhaan.....
********
Iffaat a qauyen su,
Ashe yanzu bala'en yake bata saniba, yanzu
take qara shiga damuwa yanzu take gane cewa
ganin iyayen farhaaan rahamane gareta, amma
kuma still bata gano hakanba, ganin su da
takeyi yana raqe mata qunci matuqa, ta
sukukuce kamar ba itaba kai duk Wanda yaga
iffaat sai yayi mamakinta bata magana, Yar gayu
kam da take burin zama ta Riga ta zama, saidai
so silent yanzu take yanxu. goggo har tana tsoro
kardai ba abin kunya tayo aka korota birnin ba!!
*******
Watan iffat biyu a qauye ba walwala kullum
fuskar nan a turnuqe kamar ta dijee dama dijee
haka take ba sakin fuska su iffaat ne masu
dariya, yanzu kam iffaat ta zama Yar baqin rai
fiye da dijee..
Ranar iffaat ta tashi da ciwon cikinta har Yanxu
goggo batasan ta fara period ba tasha magani
ciwon ya fada mata tana zaune cikin runfar
qofar dakinta da Dan tsinke a hannunta tana
tsane a qasa taji sallama ta amsa batareda ta
dago kaiba tsul goggo ta fito daki tana washe
baki na dago kai na kalleshi, ke ihhatu bakiga
yayanki yaxoba, koda na Dade ban ganshiba
hakan bai hanani ganeshiba Yaya nane! Taje
gunsa na fada jikinsa tna kuka shima dai yayi
gwalla, suka zauna saman tabarma,
Yaya Ameen yake cewa goggo kinsan kuwa ba
nan nakeda niyyar zuwa ba sai naga na biyo ta
kusa danan nace bari na shigo qauyen namu in
gaisheki, Ashe rabon naga Yar mamane kullum
zancenki take mana, nayi murmushin jin dadi
Dan uwa Rabin jiki ciwon cikinta tuni ya ware sai
murna takeyi tana xubar da yan hawayen
murna..
Nan take Ya kira Mama ya gayamata ai gani ya
sameni yanxu mama murna kamar ta kasheta
yau taji autanta munyi magana ta ita inatajin
dadi,
Anan aka kitse akan gobe Yaya zaizo ya fafi dani
daidai nan na Dan shirya, goggo ranta baisoba
don iffaat ce rufin asirinta gata ba da bare
jika.....
[11:48PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA 41
Na Hauwa M. Jabo
Tun da safee iffaat ta shirya kayan da take
buqata sai rawar jiki takeyi duk da har yanxu
zuciyanta a qunci take hakan bai hanata
zagwadin ganin mahaifiyarta ba, goggo ta
sakata taje tayi ban kwana da mutanen , taje
tayi bankwana dasu, wasu nata mamakin
natsuwarta kowa na fadin albarkacin bakinsa,
taje gidan qawayenta dijee da tsohon ciki abin
sai Wanda ya gani, tana tsaka da ban kwana
akace mata yayan ta yazo zasu wuce, a gurguje
tayi sallama ta dawo gida...
Ranar goggo tayi kuka kamar ranta zai fita tana
ganin kamar hanyar samunta duk ta to she
kenan... ta manta samu da rashi na Allah ne....
****************
Guraren 6 na yamma suka Isa zaria birnin
zazzau amma iffaat anyi bacci a mota so bata
gane garinba, direct unguwarsu aka wuce da ita
gyallesu, iffaat sun tararda mama tana ta gyare
gyare tarbon autarta, tana ganina taxo ta
rungumeni tana yan hawaye, nima hawayen
nakeyi Yaya Ameen kuwa yanata dariya, yace
mama murnace haka harda kuka haba miye aciki
Dan ba iffaah tunda nida Yaya Ali mumanan,
dama kullum ta damesu da zancen iffaah
autarta, mama ta harareshi ai kowa matsayinsa
daban, taja autarta suka wuce daki suna
marmarin ganin juna,
a takaqaice zuwan iffaat yayimusu dadi babban
yayan su mai suna Yaya Ali shine babba kuma
Allah ya azzurtashi matuqa tun bayan rabuwar
mamansu iffaat da babansu ta dawo birni gurin
yayanta dama chan su yayyen iffaat gurin yayan
mamansu suke suna karatu so basuyi zaman
qauye ba iffaat ce kawai gurin mamar kuma da
suka rabu da baban sai ya kwace ta da qarfi da
yaji... Yaya Ali Allah ya azzurtashi sosai bayan
business da yakeyi tareda qanin mamanshi yana
aikin Kaduna in short dai suna shanawa wannan
gidan ma da suke ciki shiya Gina ma mamashi...
Iffaat ta kalli gidanda suke ciki aranta tace
wannaan gidan kenan gadansune zatayi duk
abinda take so bawanda zai hanata rayuwa
sabuwa jin dadi sabo komai sabo saidai batasan
bazata iya chanza kuntacciyar xuciyartaba....
Lol.
[11:57PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 42
Na Hauwa M. Jabo
Rayuwa gidan mahaifiyarta Yana mata dadi
matuqa tana samun gata ta kowane fanni,
Sai yanxu ta gane cewa wannan garin garinsu
farhaaah ne, koda ko za'a kasheta bazata bata
gane gidan su farhaaan din amma dai ta gane
makarantarda aka sakata da tana gidansu
farhaaan nan guraren PZ ne. Yanxu kuma Hall
Mark international school aka sakata kuma duk
gurare dayane...
mama ta samo mata mai lesson Yana mata a
gida, islamiya ma tana zuwa anan unguwarsu ta
gyallesu,
saidai a tunanin iffaat xuwa gidansu gun
mahaifiyarta zai sa ta daina damu wa batasan
ba anan gixo yake saqaba ita zuciya kawai
burinta takai ga wannan abin da takeso idan ba
hakaba kuwa ba zaman lfya..
*****
Wata rana maman iffaat take tambayarta lfy
bata walwala? Tace ba komai mama. Mama tace
kodai bakyajin dadin zama damune?
Laaaa mama wallahi ba haka bane nafison nan
da ko ina har gidansu..... Sai kuma tayi shiru sai
mama tace har gidansu waye?? Ba kowa mama,
hmmmmm.
nidai da yawa mama nakanji banajin dadine
saina riqajin kamar inason wani abu Amma
bansan ko miyeba haka zan kasance chikin
damuwa.... iffaat tama mama bayanin abinda
takeji, tace wani abin mama sai idan na tuna
yaran gidan da nayi aiki,! Sai nayi tajin raina
yana wani iri, kawai mama shine ba wani abubw
kuma inaga kamar sabone ko mama, mama tayi
murmushi tace Eh inaga sabon ne kawai.
mamadai ta gano cewa iffaat wani take so
amma itama mamar bata fahimci ko wayeba
Kuma iffaat din har yanxu batada wayon da zata
san cewa ta fada tarkon soyayyar farhaaan ne,
mama da ta fahimci halin da yarta take ciki sai
ta dada janta jiki ko zata mantar da ita wannan
mugun ciwo da yake addabarta..
Sau da yawa idan iffaat ta shiga daki ta fara
tunane tunane sai taga kamar ba ita bace.. taci
kuka taci kuka har ta godewa Allah....
***
Wata rana iffaat bayan ta fito a class sai ga
wasu yan samari sun wuceta tana jikin class
suka fara mata hy yan mata ji mana,! iffaat
kamar bata jisuba, sukayi iskancinsu suka gaji
suka wuce bata ko daga kai ta kallesuba, har
sukaje suka dawo suka qara mata tayi banxa
dasu....
Bayan sun wuce tana zaune sai ta fara tunanin
iskanchin da aka mata ta gyale, anya nice iffaat
kuwa? Wacce Ko ba'akasa dani nakan siya,
nakan sayi fada da kudina bare a tsokaneni,
waima wayannan yaran zasu min iskanci na
gyalesu tayi tsaki kamar an tsira mata allura, ta
tashi ta fito tsakiyar makaranta don nemansu,
fitanta keda wuya tayi karo da malamai suna
kora a koma class juyawanda zatayi head