Showing 33001 words to 36000 words out of 37326 words
Chapter 12 - WACECE ITA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hauwa M Jabo.txt
shiga wanka sai mutum
ya manta da cewa ya shiga, taxo gaban madubi
ta Dan goga powder ta gyara fuskar batayi
kwalliya ba kada ya rainata da xuwa yaga ta
fara shafe shafe, taje ta Dora mai abincin akan
table ta dauko mai wasu kaya da taga idan yana
gida yake sakawa.....
Muje zuwa muji shin kulawar iffaat zata sa
farhaan ya chanxa ko kuwa halinsa dai!!
Idan bai chanxaba wane mataki anti iffaat zata
daika,?
Ya soyayyah zata guda tsakaninsu!? KU BIYO
YAR MUTAN JABO KUSHA LABARI....
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??83
Na Hauwa M. Jabo
Yana fitowa wanka ya saka tufafin data ijiye
masa ya feshe jikinsa da turare yadauki waya
ya kira abba ya gaya masa ya iso anjima zaizo
ya kawo mai report din komai, Abba yace ya bari
sai gobe idan ya qara hutuwa,ya kira mama da
umma da hajiya kulu duk ya gaishesu ya gaya
musu ya iso, iffaat ce ta shigo tace Au har ka
fito? Ya kanne ido yana Neman janyota jikinsa
yace nayi missing dinkine Dan shiga bayin da
nayi shi yasa nayi saurin fitowa, bata bari ya
kamataba ta zille, tayi murmushi, tace sai tsara
zance, nidai muje kaci abin ci tana gaba yana
Binta baya sun Isa Palo ta zasu fara chin abinci
farhaan yasa rigima shi dole sai ta bashi a baki
idan ba hakaba bazaiciba, aranta tace anya xan
juri Wannan shiriritar kuwa? Mutum da girmansa
yana Wannan Abu, yaji shirun yayi yawa yace
bari naje na kwanta, ta kalleshi da dara daran
idonta abincin fa? Ba kinqi bani abakiba, yanda
yayi ya bala'en burgeta kuma sai taji wani
sonsa ya ninku a zuciyanta Allah ya shirya min
kai mijina!, tace to bari na baka ya kuwa gyara
zama tafara bashi duk taje saka mai loma sai
rabi ya shiga rabi ya xube hakadai taga chi da
chokali shirititane ta ijiye tafara bashi da hannu
nan ma da gangan ya riqa chijeta wai ya dauka
kifine, suna tsaka da wannan drama saiga
maman Nargees ta dawo, ta wangale baki taji
dadi ba kadanba, ga dawowar farhaan ga kuma
abinda tagani wai iffaat tana baiwa farhaan
abinci a baki, hmmm.
Ta gaidashi, iffaat nason ta daina bashi shi kuwa
sai haaaaa yake mata baki yake irin na yara,
haka dai ta bashi sama sama.
sun gaisa yake mata godiyar xaman da tayi da
iffaat tace ba komai yiwa Kaine. Ta wuce kitchen
ta jera kayan data siyo ta wanke kayan da iffaat
tayi aiki dasu tsab sannan ta fito koda ta fito
sun tashi gurin duk yayi abinci tayi murmushi
tace sai kace an baiwa jinjiri abinci, ta share
tsab, ta gyare.!
Iffaat bayan sun qare chin abinci farhaan yasa
wata rigimar wai wallahi bayan sa kamar ya
bude Dan gajiya, taxo ta masa tausa, tace
bakyau ana qare chin abinci a kwanta Dolensa
yayita zagayawa a daki har yaji ya gaji kuma ya
hanata tafiya bayan ya qare ya kwanta bacci....
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA.. ??84
Na Hauwa M.Jabo
Bayan ya kwantane Ya nace saita mai tausa
gata bata iya tausaba haka dai tayi ta dannawa
tun yana wash wash har dai baccin gaskiya ya
kwashe shi, tana tabbatar da yayi bacci ta janyo
bargo ta lullubeshi, ta zauna akan madubi tana
kallonsa, tana tunani,
Dama ana cewa namiji daidai yake da jinjiri idan
kana mai abinda yakeso to ka gama dashi,
saidai ita kam nata mijin mayen mutane Allah
dai ya shirya matashi hakadai tayi ta tunani...
chan ta tuna da maman Nargees tayi sauri taje
Palo koda taje ta hada kayanta bayan ta gyara
palon, iffaat ta kalleta Dan Allah kiyi haquri
wallahi na manta kin dawo! Ya naga kin hada
kaya ina xuwa??
Zani gida mana aikina ya qare gashi tun ba'aje
ko inaba har an fara mantawa dani, iffaat tayi
dariya tace wallahi ba komai mukeyibafa ! nace
wani Abu kukeyi?
Naji dadi sosai wallahi nan dai maman Nargees
ta qara bata wasu shawarwari sannan tace duk
da haka ta riqa ja masa aji ba komai bane jiki na
rawa zata masaba, tayi dariya taso ta bari
farhaan ya tashi ya sauketa amma tace ya gaji
kuma ta hanata itama ta kaita wai idan ya tashi
bata ba zaiji dadiba, uhummm maman Nargees
dai ta gyara aure sosai ta tafi...
Bayan maman Nargees ta tafi iffaat kayan da
aka shigo daso ta musu muhalli bata budeba
Dan tasan bata aikesaba!!
Ta gaji Dan aikinda tayi ta zauna tanata tunanin
yanda xuwan farhaan ya chanza ta tayi
murmushi tasan dai har yanxu bazata iya bari
suyi wani abubua Dan tsabar kishi irin nata, bari
tayi wanka har zata shiga bayi sai tace bare taje
S.P ta dauko Yar figaggiyar rigar wankanta ta
saka taje ta fara wanka,.
Ashe farhaan ya tashi yana kallonta ta window
yana murmushi yanda take wasa da ruwa kamar
kifi, Yaji bari yaxo shima ayi dashi tana cikin
ruwan kawai jin tayi mutum ya fado ciki da yake
tafi shi iyawa shi farkon ruwan yake tsayawa ita
ko har gurin xurfin take tafiya..
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 85
Na Hauwa M. Jabo.
Tana ganin yazo kusa da ita kunya ta kamata
Dan kayan sai a hankali komai na jikinta suna
nunawa gasu irin masu hade da wandone, yayi
qoqarin kamata amma yana xuwa kusa da ita ta
gudu ya kuwa biyota sai ji yayi kamar ana jansa
tuni ya nemi nutsewa a ruwan tana mai dariya
sai taga da gaske yakeyi yanda yake dukan
ruwa, ba shiri tama manta da wani kayan jikinta
da boyon da takeyi kada ya ganta tayi sauri ta
rungume shi ta janyoshi bakin ruwa farhaan duk
ruwan dayasha bai hanashi jin laushin fatar
jikinta ba jikinsu ya hadu sun kawo bakin ruwa
amma farhaan da iskanci yayi lamo a jikinta yaji
fresh fata ba irin ta gardawan yan matansa ba,
ta kalleshi ta jijjigashi ya bude ido a hankali tace
mai sannu ko? Ya harareta ya murguda baki
yanda yake murguda baki ya bata dariya ta
kuwa dara, yace dariya ma kike min ko bayan
kin wahaladda ni, tace to ai Kaine kasan baka
iyaba ka biyoni, ya qara narkewa a jikinta to
yanxu ka fita waje kamin nazo yace ba inda zaije
saima ta koya masa yanda takeyi, tayi tayi
amma ya nace ba inda zaije sai ta koyamai
yanda ya maqalqaleta ne ba yafi damunta tace
to sakeni sai muje! Yace wayo zaki min ki gudu
tace zan koya maka amma ba yanxuba yace
shiko idan har bazata koya mai yanxu baisaidai
su kwana chikin ruwa, Tace to, ya maqalqaleta
har suka kai gurin sannan ya saketa, ta fara
nuna mai farhaan kam kallonta yakeyi ba kallon
abinda take koya masaba....
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 86
Na Hauwa M. Jabo.
Data gane kallonta yake tace a bari sai gobe
yace ai bai gwada ya ganiba ko ya iyaba, ta
riqoshi tana nuna mai ya bata wahala ba
kadanba amma fa shima yasha ruwa....
Hmmm , soyayyah cikin ruwa dadi wallahi, tana
Neman fita ya kamo gashinta saida tayi qara
tana waigowa ta zabgamai cizo shima saida yayi
qara tace ka tsani gashinnan nawa kodan ina
aske na yan matankane kakejin haushin nawa.!?
ya tun karo ta da qarfi tuni tayi wani super a
ruwa ta gudu yasan idan ma ya bita wasu
ruwan zaisha sai ya gyaleta, ko banxa tayi
tsokana bare ta sami abin fada, yana kallon ta
ta fita ruwan ya qurawa halittarta ido iffaat
akwai chinya, ga uban hips dinnan ta take
juyashi kamar me yayi murmushi ya lashe lebe
aransa yace Allah yayita bani sa'arki, har ta
wuce ta juyo taga yana kallonta tasan dama zai
kalla yanda ta saka wannan kayan haka tamai
bye tayi sauri ta wuce ya Dade a ruwa yana
tunani sannan ya fito ya shiga gida koda yaje ta
shiga kitchen daura abinchin dare, yaje ya saka
tufafi ya biyo ta kitchen ya rungumeta ta baya,
yayi kissing din wuyanta. Tace Dan Allah kaje ka
kalli ball dinka gashichan an fara. Yace au
korana ma kikeyi ko??
Ta baxan tafiba, tace yi haquri mana, yace kibar
girkin anjima sai mu fita muci tace itakam ba
inda zata chin abinci. Haka yayita damunta
kuma ya qi sakinta, saida yaga ta daure fuska ya
kama kanshi, ya dan samu tana sake mai idan
ta daure mai ai ya shiga uku yace tayi sauri ta
qare yana jiran ta,
Ayanda iffaat takeda saurin aiki yana burgeni
cikin lokaci kadan zatayi aiki ta qare dama tasan
farhaan akwai chin amala kamar Dan yarbawa
cox lokacin da tana mai aiki kusan kullum sai
anmai amala, ita kuma lokacin komai aka bata
chi take dukda bata gane abincin amma haka
take chinyiewa, to itama amala ta hada mai da
miyan agusi yaji kayan ciki yana qamshin
attarugu da carry ta hada mai fruit salad ta
kawo ta ijiye...
Uhummm su farhaan fa za'a fara dandana dadin
aure...
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??87
Na Hauwa M. Jabo.
Bayan ta qare girki ta ta fito yanata mata sannu
murmushi kawai tayi, ta shiga bayi ta watsa
ruwa tayo alwula sannan ta fito shima yayi
alwula ya tafi masallaci ta zauna saida ta qare
kwalliyarta tsab sannan tayi sallah, nima ta
burgeni Allah ya qaro min yawan gashi nasamu
na kuri irin iffaat... Ta fito tsab da ita taje Palo
farhaan ya dawo kenan ya ware hannu irin taje
dinnan ta murguda masa baki abin ya bashi
dariya ita iffaat komai sai ta murguda baki...
Akaxo chin abinci nanma yace baxai iyaciba
itama tace bazata iya Chiba tofa sai Yaya wai
sai dai ya bata ta bashi haka sukayi kuwa
wannan karon bata batamai tufafi sosai ba, Dan
tana kallon yanda yake bata sai itama tana yin
hakanan suna chi yana bata labarin Thailand har
suka kammala suka tashi suka Dan zaga palon
Dan abincin ya fada musu, bayan sun qare
iffaat ta zauna farhaan yaje ya bude kayan da ya
siyo abinda yafi bata dariya hadda kayan baby
kuma bana babyn farahnax bane wai na babyn
da zasu haifane nan da wata Tara a yanda yace
murmushi kawai tayi ta tattara kayan ta saka a
wardrobe ta dawo ta zauna, yayi miqa kixo muje
ki kwanta mana, ta yatsina fuska kaje kawai
zanzo, habadai kizo muje kin gaji, tayi fari da ido
kaje mana idan naji bacci zanxo, ya dawo ya
zauna ni bazan kwanta idan bakiba...
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 88
Na Hauwa M. Jabo.
Okay.! zauna muyi kallo ya zauna suna kallo har
guraren 1 na dare iffaat idonta gyam akan TV ko
motsi yanayi yana satar kallonta amma batada
niyyar tashi, ya fara gyangyadi, ya karbi remote
ya kashe dole sai sunje sun kwanta, iffaat kuwa
ta fuske tace yaje xatazo yaga dai batada niyyar
tashi sai ya wuce yace yana jirinta tace mai OK,
iffaat dai anan ta gyangyade sai bacci da asuba
farhaan ne yaxo ya tayar da ita bacci yana Dan
shashafata har ta bude ido tamai murmushi ta
tashi taje tayi alwula tayi sallah ta dawo Palo
zata kwanta farhaan yasha gabanta yace idan
dai dannine ki kwantar da hankalin ba abinda
xan miki murmushi kawai tayi ta rabashi ta
wuce, taje taci gaba da baccin ta qarfe 9 ta
tashi ta hada mai breakfast ta shirya a D table
ta dawo tayi kwanciyarta sai goma ta tashi da
yake ba lecture ta Dan dima abincin a taje
taganshi yana sharar bacci wanka ta shiga ta
fito ta dandasa kwalliya ta saka wasu arnan
kaya cikin kayan da tasiyo ita kanta tasan tayi
ta fesa turare taxo kusa dashi ta shafa
kumatunsa a hankali ya bude ido ya kalleta
tamai murmushi ya janyo ta jikinsa sosai yayi
kissing dinta a kumatu, tadan goce ka tashi
muje kayi wanka, yayi miqa hadi da salatin
annabi ya miqe yaje wanka bayan ya fito tazo
tayashi goge jiki da shafa mai, daxai chanxa
kaya sai ta miqe xata fita ya janyo ta ina
xakije,? ta Sosa kai xan dauko abune a Palo yayi
murmushi aranshi yace mata da mijinta amma
tana guduwa. Ya saketa bata dawo ba saida ta
tabbatar da ya saka kayan sannan ta shigo.....
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 89
Na Hauwa M.Jabo
Ta kalleshi ta riqe kunkumi iyeee kaganka
kuwa.!? Kayi kyau kamar sabon ango, ya kalleta
ya kanne ido yace ai angonne ko kinmanta har
yau baisha maiba,! Ta gane mi yake nufi sai ta
basar da zancen muje kayi breakfast kaje ka
gaida su Abba da umma, yace to my princess,
sun zauna ta kawo breakfast nan ma yasa
rigima har yanxu bai warwareba sai ta bashi a
baki, haka ta riq biye mai tana bashi yana chi
idan ya cijeta tace sai ta rama haka zata samu
wani guri shima ta chije shi har suka kammala,
ta rakashi har mota ta dawo ta tattara kayan
gudu gudu cox tanada lecture 12 gashi 11:30 ya
wuce ta qare ta wuce skull.
*********
Zaman iffaat da farhaan dai xan iya cewa lafiya
lau duk wani kula dashi tanayi ba abinda za'
nuna mata tun daga kwalliya har girki da tattalin
miji saidai har yau taqi bada hadin kai farhaan
yayi yayi amma taqi..
Ranar dai ya tirketa tana baccin rana a daki
yaxo ya dabai bayeta ya fara yan shafe shafensa
chan ta farka ta bude ido ta kalleshi tace miye
haka?? Yace mata sunnace haka, tace sunna
kuma? Yace eh bakisan annabi yace duk Wanda
ya aikata Wannan sunnatawaba daidai yake da
Wanda yayi jihadi ya kashe arna dububa. Ta
kalleshi ta kyalkyale da dariya har saida tayi
kwalla, sannan tace Yy farhaan watana hudu
gidannan watanka uku muna kwana daki daya
gado daya bargo daya bakasan da a kashe arna
ba sai yanxu farhaan kam ya fara nisa ba wani
jinta yakeba tuni tasa qarfi ta tureshi gefe ta
miqe zaune ta kalleshi rai a bace wallahi kada
ka qara kuskura kace zaka kusanceni! Ya kalleta
ido sun wani Kada haba iffaat mi yasa kike min
hakane? So kike na koma abin farko da nakeyi?
Wannan kuma ya rage naka ko yanxu waya sani
ko ana lallabawa dubunka ce bata cikaba na
kamaku, ko kuma anji tsoron cell shiyasa ake
kama kai amma dai badan iffaat ba kuma ba
Dan tsoron Allah ba.!.
Ta wuce Palo ya zauna saman gado yayi tsaki
wannan yarinya mayaudariyace wallahi, ta
koramin yan mata kuma ta hanani kanta kuma
gata kamar aljana duk abinda nakeyi tana gani,
yayi tsaki yadan kwanta akan gadon qafafunsa
suna qasa ya dafe kai miye abinyi??
Da gaskiyar ta Dan tsoron cell naqi Neman
matana amma yakamata na bari Dan Allah
badan kowaba. Yayi ajiyar numfashi...
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 90
Na Hauwa M.Jabo
Ya biyo ta Palo tana sauraren waqarda kusan
kullum saita saurareta koda waqar hausa bata
burgeshi amma har ya haddace wannan wai
kuma baiti dayane yakejin tana maimaitawa
kullum shine na badi ba rai soyayyah jigon
rayuwa ana cewa " itadai soyayyah maiyi bai
samun sauqi, a jini take yawo wasu gunsu tana
hanin aiki, na shiga cikinta ta xafar tamkar doki,
na shaida sone mahadi gun rayuwa"ya kalleta
yayi murmushi iffaat sarkin rigima normal
xatamai duk abinda yakeso amma da xaran ya
buqaceta sai taqi, ya zauna kusa ida ya daura
kanshi akan chinyoyinta yana wasa da jelar
gashinta, yace yakamata amin tafsirin wannan
baitin waqar kullum shine a bakinki tun kina
qarama nakejin kina yinsa, tace kace dai tun ina
Yar aikinka nakeyinsa, tayi murmushi, nidai jabo
da zasu ce na musu tafseer din wannan baitocin
waqar da zanyi page 100 dashi amma basu bani
damaba, iffaat ya kira sunanta ta kalleshi mi
yasa kike guduna? Tace gudu kuma? Yace eh
mana, tayi murmushi tace Sabida lokacin auren
mu ba'ayi su dinner, su party su lunching ba
wani Abu da akayi kaga kuwa kamar ba'ayi
aurenbane ya miqe zaune yanxu kinason ayine?
Tace eh ayi, shine matsalarki?? Eh to yanxu dai
shine na farko, yayi murmushi wallahi duk
abinda kikeso xa'amiki ya miqe zaune ya shiga
dakinsa ya kira abokinsa wannan da iffaat tayi
wa fitsari farhaan yace monkey din gidansune,
yamai bayanin komai kuma yana son ayi komai
cikin satinnan..
Bayan kwana biyu farhaan ya kawo mata IV
yace ta rabawa qawayenta taji dadi sosai ta
shiga rabo, duk Wanda ya tambayeta ba tayi
aureba sai tace na jin dadin aurene wannan.
tayi qayyar mutane farhaan ma haka su umma
dai kam saidai su saka musu ido Dan sunga abin
nasu wasane farahnax taxo su ZZ duk an hallaro
Yar baqa ma haka hatta su dijee da rukayya
ba'abarsu a bayaba.....
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 91
Na Hauwa M. Jabo
Abin sai Wanda ya gani, farhaan har tausayi
yake bani wai wannan kudin da ya kashe duk
Dan cika umurnin Mrs purhuuun ne, anyi komai
cikin jin dadi da kwanciyar hankali su mama kam
sai fada sukeyi wannan bidi'a haka aure na
Neman shekara amma sai yanxu ake wani
qaqale qaqale iffaat kam taji dadin komai d
farhaan ya mata hatta kayan aure saida ya mata
sabbi akwatuna kamar dai sabuwar amarya koda
ai sabuwarce tunda har yanxu, wane yare da
sukecewa ((dast na khurde )) budurwar kenan
wacce batasan mazaba,
An sallami kowa cikin aminci inda amarya da
ango suka dawo gidansu farhaan kam hadda
shan maganin qara qarfi irin yau za'a suburbudi
iffaat...
mutuniyar kuwa ko a jikinta Dan tasan batada
tsarki, su farhaan anxo ana lalabe lalabe iffaat
ta dakatar dashi ta hanyar gayamai batada
tsarki kuma ta gaji ya barta tayi bacci, ga injin
dinsa ya riga yadau zafi, farhaan Dan takaici ya
rasa abinda zaiyi sai daukar key yayi ya fita yaje
kozai samu gunda xaiyi aiki yanda yayi tsingau
dinnan, iffaat ta gane ina ya nufa amma Sam
bata kulashiba.
farhaan bayan ya tafine yaje kuma yakasa
Neman matan banxar, haka ya samu daki ya
kwanta yanata juyi har bacci ya daukeshi bai
farkaba sai guraren 3 Subhanallahi, ya tashi da
sauri ya dawo gida koda yaxo ya tarar da iffaat
zaune tana kallo abin ya bashi mamaki kallon
iffaat cikin dare....
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??92
Na Hauwa M. Jabo
Yana shigowa ko kallonsa batayiba, duk kunya
ta kamashi, gashi ma abinda yajeyi ya kasa
aikatashi ya Dan Sosa kai yace bakiyi bacci ba!?
Tace nayi faarkawa nayi yanxu, yaga kamar
batayi fushiba sai ya matso kusa da ita zai
zauna tayi xunbur ta tashi kada ka kuskura ka
matso kusa dani tamai kallon raini kamar taga
wani kashi,
Ta kalleshi ai shi mai hali baya barin halinsa
tunda ka saba da Neman mata wallahi ba abinda
zaisa ka daina, ya xa'ayi na iya bacci bayan na
auri miji manemin mata, ido cikin ido ta kalleshi
tace farhaan nayi Dana sanin aurenka, nayi
baqin cikin kasan cewa tare dakai, babban abin
godiya ga Allah shine ba'abinda ya shiga
tsakaninmu, bare ayi xancen hada zuri'a na
tabbatar da yarana sai sunyi baqin ciki da
samin uba mazinaci irinka.!! Amma yanxu kaga
Hankali kwance zan nemi wani miji nayi aurena
kuma wallahi saina fadawa umma halin da kake
ciki..
Farhaan zuciya tayi xafi waishi take gayawa zata
nemi miji tayi aure, yaso ya mammaketa amma
sai ta wuce shi nan ya zauna yana Allah
wadaran halinsa yayi tsaki yafi sau dubu ya kasa
shiga dakin har bacci ya saceshi, iffaat kam ko
dar bata ga bacciba gari ya waye kamar kada
tamai breakfast Amma ta daure ta hada mai
taxo tasa qafa ta shureshi ya tashi, ta kalleshi a
wulaqance tace to aje ayi wanka a tsarkake jiki
ayi sallah, a karya aje gun Neman wasu matan,
aranshi yace wai dan wulaqanci da qafa xata
tayar dashi yaji bala'en haushi Dan kuwa da
atayar dashi da qafa gara a gyaleshi, kuma ga
magan ganun banxa tana gayamai ya kalleta
waike waya gaya miki Neman mata naje?! Cikin
isa da tsabar rasjin kunya Tace sabida ba
namijin kirkin da xai bar gidansa 12 na dare ya
dawo 3 sannan yace ba gun banxa yake
zuwaba, bare kaida akasan halinka na Neman
mata....
Farhaan dai ya kasa magana yayi wanka ko
karyawa yakasa yi ya Dan saba tana bashi a
baki yau kam yasan koxai mutu bazata bashi
abakiba,
Haka ya dawo office guraren yamma ta qare
girki tayi kwalliyarta kamar ba itaba.
..
[8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??93
Na Hauwa M. Jabo
Tamai sannu da zuwa, ya amsa bayan ta juya
ya kalleta mace kamar hawainiya sai chanxa wa
takeyi, yaje yayi wanka.
ta kawo mai abinci Dana safe