Showing 6001 words to 9000 words out of 37326 words
Chapter 3 - WACECE ITA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hauwa M Jabo.txt
bashi dariya kuma, Ashe
kawai abinda zaisaa wannan shu'umar kuka, yaji
dadi aransa ko banxa ya rage baqin cikin ta
kuma dama Dan ya bata wahala ya mata
hakan..
Sorry iffaaahh, na manta dana hana abaki
abinci, to mi kikeci kullum,?? bansaniba ta fada
a yatsine wato kai ka yahana a bani abinci,
wallahi Dana sani da ban mai kukaba duk a zuci
take maganar.!!
Kiyi haquri kinji, tana kallo ya kira kukunsa yace
a riqa girki da ita,tace bazanciba gida zaka
maidani, bai kulataba ya wuce abinsa.
Bayan kwana biyar farhaan ya sallami rufee,
Kwana na shida yazo da wata matar,
Itama yar gayuce irin rufee saidai wannan tafi
kyau, koda suka shigo iffat na goge Palo,
yarinyar ta kalleta ke kawo min ruwa mai sanyi.!
Ta fada a gajiye tafada kan kujera ta zauna iffat
ko kamar batajitaba, aranta tace dama matansa
biyu yaro dashi sai mata, baijira amsar iffat ba
Dan yasan halinta sarai batada kirki, yanda ya
gaji bazai iya fita nemawa ramsy hotel ba, ya
dauko mata ruwan ya kawo mata kixo mushiga
daga ciki kinga ana aiki anan ka shiga idan na
huta zan shigo ta fada alalace,
Ya wuce yabarta tana danna waya amma ranshi
baiso barintaba, kee mai aiki idan kin gama kizo
ki matsamin qafafuwana....
[3:00PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA.?? 15.
Na Hauwa M Jabo
Nan ma Tayi banxa da ita har ta qare aikinta,
tana neman ficewa palon, ta kalli iffat kizo ki
danna min hadda bayana kiyi min a hankali Na
gaji sosai, tana magana a wahalce irin ta gaji
dinnan, iffat nan ma ko ta mata banza ta fara
waqar ta badi ba rai soyayyar jigon rayuwa da
amana...... kusan kullum sai iffaat ta yi wannan
waqar Dan tana bala'en Sonta kuma baiti biyu
ta iya tun aqauyensu, ramcy taji shiru, ke kodai
kurmace ke? Kurmane kuma zaiyi waqa,! Kee
Ana magana kinyi banza da mutane, iffaat
Tamata kallon wulaqanci, shi mijin naki yace
miki aikina kenan danne dannen matansa??
Aikina biyune zuwa uku hajiya batace in ma
matansa tausaba.! ta miqe zaune Ke marar
kunyar yarinya, kina kallon mutane kamar kina
kallon kashi, wai ma Waye matar tasa? Zan miki
display a gidannan kuwa, iffat kam bata ko
kalletaba taja tsaki ta wuce dakinta, ramcy a
fusace ta tashi taje dakin farhaan, har ya fara
bacci ihunta ya tayar dashi, ya zaku ijiye mai
aiki Mara kunya a cikin gida yarinya har tana
mini tsaki.! Yadanja tsaki ya rasa abinda zaice,
aransa yace ki godewa Allah data tsaya akan
tsaki, bayason ta fahamci koshi iffat ba ragawa
takeyiba, cool down baby ba girman ki bane kina
fada da mai aiki in kin kula yarinyace, xata qara
magana ya janyota ya rungemeta.... nidai jabo
danaga abin zaifi qarfina sai kawai na bar musu
daki nayo waje.
Guraren maqreeb suka farka daga bacci suka
fito yunwa ta addabesu ya nema musu snack
suci, ramcy tace indomie take so tachi, kuku
kuma bayanan, to miye amfanin wannan
yarinyar? Basai ta girkamin ba, no ki barshi xan
girkamiki farhaan ya fada yana miqewa Dan
yasan iffaat zubar mai da mutunci zatayi, ramcy
dataga dai da gaske zai mata girkinne sai tace
ta fasa amma zuciyarta fall da tunanin miye
amfanin yar aikin, suna zaune suna hiransu suna
dariya iffaat ta taso tazo gabansu ta wuce, wani
warin datti ya daki hancin ramcy tace; kai amma
wannan yatinya na wari! Ta toshe hanci, iffat ta
waigo taceni nake wari? Farhaan yace ke ki
matsa ki baiwa mutane guri,an fada kina wari
qaryane bakya warin? Shima kallon banxa ya
mata yaci gaba da hiranshi, ran iffat ya baci
matuqa, ba'ataba fada mata hakaba wai tana
wari sai yau, ko qauye su dijee da rukayya ne
ake cewa suna wari ba wanda ya taba CE mata
tana wari ta wuce fauuuuuh kamar guguwa ta
tasooo, tana zuwa daki ta fara tunanin abinda
zatama matar farhaan ta rama, cox taji haushin
abinda ta fada mata, itaf ta dauka matarshice,
batasan matan banxa bane, tayi wata dariya
mugunta an samu idea ta miqe tsaye taje
kitchen ta dauko man gyada, tayi zaune duk ta
gogo gurin da ba carpet dashi tayis sai maiqo
yake yaji oil sosai, cox ta taba zubarda man
gyada a kitchen tafadi har sau biyu sai ta gane
cewa yana fadar da mutum, ita kanta da
tsantseni take tafiya har takai wani guri ta
zauna, ba'ajimaba kuwa saiga ramcy an fito da
kayan bacci kamar tsirara, tana fitowa daki tana
yatsine yatsine, sai wayanta tayi qara
juyawanda zatayi ta dauko wayan, kikajita
teeeeem ramcy anfadi qasa ansha qasa, ta fadi
saman hannunta tayi wata qara, iffat ta
gyalgyale da dariya, tazo kanta tana kallonta
tana dariya, ramcy kuwa sai kuka takeyi tace da
bana wari Dana taimakeki Amma ina tsoron in
saka miki warina .......
[3:43PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA..?? 16
Na Hauwa M. Jabo
Maimakon ta dagata din amma ina sai dariya
takeyi, ramcy sai kuka take tana ki taimakeni
iffaat taci gaba da wa qarta ta badi barai, tayi
sauri ta goge duk gunda ta saka mai,ramcy nata
kiranta ta taimakamata amma iffaat kamar ma
batajiba, hankalinta kwance, ramcy ta rarrafa
taja jiki ta dauko wayanta ta kira farhaan ta
gayamai faduwan da tayi da dariyar da house
girl dinsa tamata ba'ajimaba saiga farhaan da
Dr. Sunzo Dr. ya duba ramcy akace hannunta da
qafarta sun targade, farhaan yaje dakin iffaat
batanan yaje ko ina batanan kamar daga sama
ya ganta ta chiko dan kwali da fruit lambu taje
kenan, tana qarasowa ya wanketa da mari.!saida
abinda ta debo ya watse, Ke dan ubanki Mara
tarbiyar inace ke?? Mace ta fadi Dan bakida
tausayi idan baki taimaketa kin dagataba ai
bakya mata dariyaba, Dan Kinga ina gyaleki a
gidannan kike abinda kikaga dama, karfa ki
manta ke ba kowa bace illa yar aiki, kuma
wallahi zan riqa chin ubankine, wawuya Mara
tarbiya.!! Ya fada a hasale ya wuce daki gun
ramcy, ranshi a bace yaci gaba da rarrashinta...
ran mata ya bace ga duka ga zagin chin
mutunci, ta fashe da kuka, ta fito harabar gida
ta rakube wani guri tasa kanta a cikin chinya ta
fara kuka, kuka take sosai cox ranta ya bala'en
baci ba'ataba samun nasara akantaba irin
wannan wato duk dabarar da zatayi dan ta rama
abin da ya mata ta sai taji yana bata tausayi
bazata iyaba, shegiyar matar ya kamata ta qara
yiwa wani sharrin, haka taci gaba da kuka har
farhaan ya fito zaikai ramcy asibiti ya sameta
anan ya zabga mata harara ya wuce abinshi, har
sukaje suka dawo tana kuka sai ta bashi tausayi
yaje ya ijiye ramcy ya dawo, kewai mi kikeyi
anan,? ki tashi ki shiga ciki kinzo kina ma
mutane kuka, tayi banza dashi yayi yayi tun
yana fada fada har ya dawo rarrashinta, har ya
gaji taqi daina kuka kuma taqi tashi, ya gaji ya
koma chikin gida, iffat dai ta gaji da kuka tayi
bacci anan, har gari ya waye guraren 9 farhaan
zaije skull yaganta anan kwance ya rasa yanda
zaiyi da ita sai kawai ya dauketa a hankali
yakaita Palo saman kujera ya shinfidar, ita kuma
ramcy tana Palo zaune saman keken guragun
da aka bata, tamai kallon tuhuma waye ka
dauko, sheeeeeeee, ya dora yatsansa akan
lebensa yace kada tashi, banganeba yar aikice
kake dauka, yace batada lafiya, jiya sabida
abinda na mata akan ki waje ta kwana. Ramcy
tace then so what Dan ta kwana a waje, ya bata
amsa da then so keep quiet kada ta tashi nace!
Tamai kallon tuhuma farhaan ka gaya min WACE
CE ITA??
[3:44PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA..?? 17
Na Hauwa M.Jabo
Ya kalli ramcy kallon bangane mi kike nufiba, ya
tambayeta WACE CE ITA?? Eh wace ce e ita.!!
Wace ce ita kuwa bayan house girl dina, yayi
guntun tsaki, ki kula kada ki tayar da ita bacci
ba tada lfy, ya bata amsa ya fita abinshi, house
girl ce hadda wani daukota,aranta tace yanda
tasan farhaan da gyangyami ba yanda za'ayi ya
kula wannan qazamiyar yarinya, yarinyar da ko
qirqar danki yanxu takeyinsa.
Ta gungura kekenta ta koma dakin farhan.
Farkawan iffaat keda wuya taganta a saman
kujera itada tayi bacci a waje taja tsaki ko wane
aljanine ya daukota ya kawota nan oho? taje
lanbu abinta ta nemi abinda zai qosar da ita taci
ta haye wata qatuwar bishiyan mangoro mai
sanyi bata dadeba ta fara gyangyadi da taga
zata fado sai ta daura Dan kwalinta tayi yanda
bazata fadoba.
Farhaan yayi baqo kuma bayason yaga ramcy
dan ba kowa yasa yana neman mataba, sai
kawai ya janyoshi lanbu dama wasu takardune
zasu cika tare, kusan awa uku sunanan suna
aiki. bayan sun qare suna tadi suna dariya, sai
kawai sukaga abu kaman ruwa saman kan baqo
amma ruwan yellow ne har dai ruwan suka jiqe
takardun da suka cija gabaki daya, takardun da
da suka sha wahala kamin su sami signed su
chika, sun miqe lokaci daya suna kallon sama
cike da mamaki da tsoro coz sun gane ba ruwa
bane fitsarine hadda diminsa... farhaan ne ya
hangota tana sharar barchi, wato fitsarin kwance
takeyi, yaja tsaki kunya da takaici suka isheshi
kawai yaja abokin sa zo muje ciki, abokin yace
minene?? wallahi wani hatsabibin MONKEY muke
dashi, shine ya mana fitsari Dan Allah kayi
haquri muje ciki kayi wanka ka chanza kaya, sai
kuma ya tuna ramcy tana ciki bayason ya
gantane shi yasa yama kawoshi nan ga wannan
sakaran abinda ta musu, yaqara jan wani tsaki,
ya zaiyi dole tasa ya bude mai dayan sashen
gidan yayi wanka yadauko mai kayan sa ya
saka, abokinsa yanata dariya abin ya bashi
dariya matuqa yace farhaan wannan monkey da
gani Dan iskane, farhaan ya murmusa ai
hatsabibancinsa yafi wannan, ta ciki na ciki
bayan ya sallami baqo yazo lanbu yaci qaniyarta
sai kawai yayi karo da ita gefen bishiya tana
wasa da qasa, abinda ya gani ya bashi tsoro
matuqa idonta sunyi suntum kamar jabo tayi
kuka.!
Tana ganin sa ta kauda kai sai ya yazo gurinta,
ya tsuguna umma tana gaisheki tace kiyi haquri
zaginda ake miki,kinji tace in baki waya kuyi
magana, cox yasan duk abinda za'amata taji
haushi baikai a zagi margayin babantaba, yayi ta
mata surutuai ko motsi batayiba bare ta bashi
amsa har ya gaji ya tafi.
Da yamma ta shiga gidan tasan farhaan
bayanan sai ramcy zaune a Yar kekenta ta
guragu tana cin Apple tana ganin iffaat tasha
mur ta toshe hanci, iffaat saida taxo daidai ita ta
wanketa da lafiyayyen mari, ta tureta saman
kujera ta fadi, ta take qafar da aka daure ta
murza sosai, koda batada nauyi saida ramcy ta
saki wata qara Dan azabar da taji, ya kalleta irin
kallon nan nata na wulaqanci, idan mijin naki ya
dawo kice ya kasheni, ta koma lanbu abinta.
Farhaan ya dawo ya tararda ramcy a qasa tana
kuka ya tambayeta tace ba komai gida kawai
takeson ya maidata tana tsoron ta fada yaqara
daku iffaat idan yafita ta kasheta haka ya maida
ramcy gida....
su iffaat sarkin gaba tun daga ranar bata qara
yiwa farhan maganaba ta daina aikin da takeyi,
burinta kawai a maidata gida, amma ina ba hali,
Ranar tana zaune a sabon dakinta wato lambu
cox yanxu kullum tana gun dare da rana ko tsoro
bataji, dama tsoro bashida muhalli a zuciyar
iffaat tana zaune ta hango wata qofa, koda taje
ta daga an sa sakata an kulle ta bude sakatar
tana budewa qofa ta wangale saiga ta taganta
waje,....
[10:15PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 18
Na Hauwa M. Jabo
Dama an hana mai gadi ya barta ta fita, itama
an hanata zuwa gurinsa ba gunda take zuwa
daga aiki sai aiki...
Sai yau cikin ikon Allah gata waje, Ta kalli gidan
da tafito kallon sosai, gidane na gani na fada,
kusan duk unguwar ba gidan dayakaishi tsari da
girma, tayi yan kalle kallenta, ta samu guri ta
zauna anan taga yan mata nakai da komowa ko
wacce kayan jikinta abin kallone fuska duk fenti
ta kalli yanda suke tafiya kamar basason taqa
qasa, aranta tace lallai birni birnine bata taba
ganin yan birniba saiyau. Amma ita iya sanin ta
karuwai ne basa yawo da gyale, amma taga
wayannan manya dasu amma basa saka gyale
kodai karuwanne?, haka dai aranta tayi ta saqe
saqe har guraren yamma sannan ta koma cikin
gida.!
Tana shiga taga farhaan da wata mata, aranta
tace matansa uku kenan, lallai suna qoqari,
Bata takansuba dama bayi tazo, wucesu tayi ta
fita abin ta bawanda ta ko kalla balls gaisuwa,
budurwar ta kalli farhaan waye wannan?? Yace
watace,! to WACE CE ITA?? Mai aikice, amma
batada ladabi shine kota gaida mutane, look
hafsa! ba ruwanki da masu aikiin gidan mu
please, ke kullum kikaxo sai kin kawo Qatar
masu aiki haba, Bawai komai bane illah bayason
rigimar iffaat yanxu sai ta zubar mai da
mutunci, ya qara da cewa kuma ma kurmace
bata iya magana Dan ki fita hanyarta, tace Allah
sarki,
Yaja budurwarsa ya wuce daki da ita, kwanan
hafsa biyu a gidan. ranar iffat ta dawo daga
kallon mutanen unguwa da takeyi da yake tun
lokacin ta daina mai magana tadaina yini gida
hatta aikin ta dainayi, ta fado ba sallama, sai
hafsa ta kalleta a yamutse ke Dan kina kurma
baki iya ishara da hannuba Ko uyayenki basu
koya miki gaisuwa bane? Kai Allah wadaran
halinki, ran iffaat ya baci amma guduwarta data
korota tafi mata tsayawa masifa Ta kalleta
kawai ta mata tsaki ta wuce bayi abinta, Dan
abinda takeji ya matseta!! ta qare ta fito tana
waqarta ta badi ba rai soyayyah jigon
rayuwa......., nan ma hafsa ta qara magana,
wallahi sai na sa farhaan ya koreki duk masu
aikin gidannan suna gaisheni amma bandake
Mara kunya kawai, waike kurmako?? da ganin
idonki nasan ba kurma kikeba iskancini kawai
kurmace ke waqa .dama farhaaan duk masu
aikin da yake mafi yawa yan matanshi suke sa
yana korarsu, wasu kuma baqin halinsu kesa ya
koresu, iffaat har zata tankata nan ma sai ta
mata kallon banxa tayi tsaki ta wuce abinta.
hafsa kamar an tsikareta dama idan kayi masifa
akayi banza dakai yafi haushi, ta janyo iffaat ta
wanketa da mari....
[10:22PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 19
Na Hauwa M. Jabo
Habawa!! iffaat bata dubu girmar matarba Dan
kobata kaiba zata kai 25yrs ita kuwa yanxu take
Shiga14, itama ta wanketa da wawan mari
daidai shigowar farhaan, kee iffaat lafiyanki?
hafsa ta riqe kumatu tana mamaki, yau yar aiki
take dukanta, tasan tafi qarfinta Dan ubanta
mashhurin mai kudine itama kawai tanason
farhaan ne take biyoshi har gida amma tafi
qarfinsa, yana zuwa daidai ita hasale a ya
wanketa da mari biyu masu kyau saida ta fadi,
ya nunata da yatsa, ina Dada jaddadamiki ke ba
kowa bace illa mai aikina kuma bazan maidaki
gidankuba anan zaki ci gaba da zama, kinamin
bauta, idan kikayi ba daidaiba am always ready
na babbalaki,dama sabida umma nake raga miki
so naga ba amfanin haka, qara in nuna miki ni
waye, stupid girl kawai ya, rungume hafsa yana
bata haquri, hafsa ranta yayi fari Sol Dan yayi
hukuncin da ya mata dadi, ta kuwa narke a
jikinsa farhaan mai farin jinin yan mata.
Ta miqe tsaye taja ta toge ta rasa abinda zatayi
ta rage haushi kuma ta bashi haushi ya
sallameta amma ina kwakwalwanta baya aiki ko
kadan hasalima tausayinsa takeji,
***
Tafita daga gidan taje waje kallon yan mata,
wata yarinya da take yawan gani tana wucewa
yarinyar ta shiga ranta har takeji ina mazata yi
qawance da ita, wata zuciyar tace a haka zatayi
qawance dake kina duqun duqun, ta kalli jikinta
ta tuna tafi wata daya a gidannan amma duka
wankanta uku, kamar yan makarantar su jabo
basa wanka daga frdy sai frdy..
Ta kalli kanta aranta ta fara imagine irin
gasunan tare da yarinyar suna driving a mota
Habawa ta gyalgyale da dariya hadda buga qafa
a qasa, har ta manta da an mammareta ita
kadai kamar zararriya, lallai idan har tayi
qawance da yarinyar chan Yar baqa ta qare
qawance a duniya, tana nan zaune taji kamar
maganar farhaan saida hanjin cikinta suka juya
dan kuwa shine, lallai kamin ta ruga ta shiga
gida zai iya hangota, kamar monkey dinda ya
kirata haka ta Dane bishiyar da take zaune
gurinta farhaan yazo daidai bishiyar ya zatsa
yana danna waya.....
[10:29PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 20
Na Hauwa M. Jabo
Yaci gaba da wayansa saida ya qare kamar zai
daga kai ya ganta amma hankalinsa na gun
budurwar da yake tsarawa a waya, bata gane mi
yake cewaba Dan da English yake magana, ya
wuce kamar da second 30 ta sauko ta shiga
gidan da sauri ta kulle qofar lanbu taje gurin
zamanta tana addu'a da Allah yasa bai gantaba,
idan ya ganta tunda yace bazai maidata gidaba
ya zatayi, zai kulle qofarne ya hanata fita ko ina
gashi tanason tayi qawance da yar baqar
yarinyar da take gani tana wucewa. Tana nan
zaune Tana Zane a qasa ya kwala mata kira taje
ta turbude fuska, yace taje hafsa na kiranta,
batamai musuba ta wuce shima yayi mamaki
sosai yanda ya wasketa da mari batace
komaiba, aransa yace kodai ya fara nasarar
natsar da itane, hafsa a Palo zaune, wai ta dan
qasa mata qafafuwanta da ruwan xafi, ( inaga ta
kusa fara period ne coz yan chinar skull dinmu
haka sukeyi kuma zakiga sun Dan sami sauqin
ciwon cikin) na watsa mata harara, banganeba,
tamin bayani shiko gogan yana tsaye ya
rungume hannuwansa, nikaina jabo nayi
mamakin iffaat data amince da aikin, ta zauna ta
riqa juya ruwan turinisu suna dukan qasar qafar
hafsa har suka huce ta zubar ta dauko wasu ta
mata daqowar da hafsa zataye ta hanbare iffaat
ta fadi xaune ruwan suka zube a jikinta duk ta
jiqe amma ruwan ba wani zafi sosai, farhaan ya
kallesu baice musu komai ba, yaci gaba da
kallon ball dinsa, karo na uku ta dauko ruwan
zafin da gangan iffaat ta juye matasu a qafafu,
hafsa ta tsallara ihu, iffaat ta miqe tsaye da qarfi
tayi gefe farhaan yazo da sauri yana duba qafar
ba abinda tayi a Zahiri amma tana zugi daga ciki
iffaat tayi tsaye tana jiran hukuncin da farhaan
zai yanke mata da sauri ya kira Dr. hafsa sai
aikin kukatakeyi, yana rungume da ita tanata
ihun, yace iffaahh. Ta watsomai idonta da gani
tadan tsorata ya akayi haka?? Ta fuske kamar
da gaske, naje zan juye ruwan sai kawai tasa
qafa zata shureni saita shure ruwan suka juye
mata a qafa, harga Allah ya yarda cox yaga
yanda ta shureta karo na farko, ya jinjina kai,
duk da baiji dadiba amma yasan iffaat batada
laifi,......
Dr yazo ya dubata ya bata
magunguna, tace zata koma gida kada yar
aikinsa ta kasheta, baiji dadiba cox duk cikin yan
matanshi hafsace kawai take iya jure jarabarshi,
cox ita sonshi takeyi so duk wahalan da zai bata
tana jurewa sauran kuma, kudi kawai sukeso,
Yakaita gida, ya dawo bai kula iffaat ba ya wuce
dakinsa sai yanxu ya kula dakin yayi kacha
kacha ya kwala mata kira, ke zaman me kike a
gidannan?? Kalli dakina kalli toilet dina! Miye
amfanin kine??
[10:33PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 21
Na Hauwa M. Jabo
Dole kiyi aikinda aka kawoki kiyi idan har
kinason amaidaki gida, so zabi ya rage naki, ko
kiyi aiki a maidaki gida ko kuma kiyi ta zama
anan har qarshen rayuwarki. taga gara tayi
aikin ya maidata gida.
***********************
Yau watan iffaat biyar a gidansu farhaan inda
sabo yaci ace ya saba da halinta ya kawo
budurensa daidai har 8 suna chin uban juna Ita
dasu, kuma ko wacce sai tayi nasarar daukar
fansar abinda suka mata ta hanya kala kala,
kuma farhaaah Sam baya ganewa, ita
Har yau ta kasa gane cewa ba matansa bane
matan banxa ne da taga sunfi hudu sai kawai
aranta tace auri saki yakeyi, irin na wani alhajin
qauyensu da akace auri saki yakeyi, kullum
sukaje Gidansa kallon TV sai suga sabuwar mata
a gidan akace auri saki yakeyi, anan ta gane
halinsu daya da farhaan...
*********
Yau dai iffaat an tashi ba lafiya zazzabi yake
damunta da wani gwauron ciwon ciki, har bacci
ya dauketa tsakar bacci ciwon ya tayar da ita
taji danshi danshi a qasanta dubanwa da zatayi
sai taga jini Habawa ta fashe da kuka koda ta
tashi ya mata kache kace a jiki Ashe ya Dade da
zuwa bata kulaba, tayi Sa'a farhaan yana palo
yana kallon ball ta fito a hargitse tana kuka, ta
nuna mai jininta