Showing 30001 words to 33000 words out of 37326 words

Chapter 11 - WACECE ITA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hauwa M Jabo.txt

14 Jan 2025

2854

har wata tasan asirin
mijinta Allah wadaran halin farhaan, Kinga mijin
ki Dan gayu ne, so wallahi sai kin kasa kin tsare
yanda yan mata sukayi yawa idan ma Allah ya
tsareki bai miki kishiyaba to zai nemi mata a
waje amma idan kika gyara kanki kin gama
komai Dan maganin matannan kinasha kwalliya
duk ki riqayi kissa da kisinsina ki zama first
class gaki da gashi kiyi yanda kikasan mijinki zai
ji dadi, Dan girkinnan duk ki xama kece kan
gaba, wallahi nasan yan matan da suke son
mijinki ba adadi kuma duk sun fiki girma da
wayo, ko wacce tasan yanda zata sace zuciyar
namiji so ki zama very careful iffaat kam ta
sassauto da kishi tana sauraren jawabin qawarta
Aysha armiya'u mada lallai ita tasan inda duniya
ta Nufa kuma itace qawa ta gari....
Armiya'u tace ki duba yanxu ina kallo mijinki ya
shigo baki gaisheshiba kuma ko ruwa baki
kaimasaba bare abinci, iffaat tayi murmushi
batace komai ba
Armiya'u dai ta baiwa iffaat darasi kuma ya
shigeta matsalar batasan yanda zata fara bane,
bayan sunyi sallama ta tafi saiga farhaan ya fito
a daki dama jiran tafiyarta yake yaxo yayi tsaye
yana kallonta wannan yarinya akwai kwarjini sau
da yawa idan ta masa Abu ya tunkareta sai ya
kasa..yaga idan ma masifa zai mata aikin banxa
zaiyi don ba jin masifar takeyiba so gara ya
mata magana cikin ruwan sanyi....
Ya kira sunan ta tana kwance ta dago ta
kalleshi, ki tashi zaune batace komaiba ta miqe
zaune yace ki ijiye waya, zamuyi magana kafada
inajinka kawai.
Ya kira sunanta, Iffaat tace na'am ki ijiye waya,
sai ya bata tausayi ta ijiye waya ta fuskanceshi
dakyau yace iffaat abinda kikayi kina ganin kin
kyauta? Ta xaro ido mi nayi kuma? Kin fini sani,
aah Malam kada amin sharri ina zaune lafiya mi
nayi?? mi kika yiwa yaran mutane? Ta bone
kuwa wayanni yara kuma ?? Yace abokan aikina!
Uhum yy kenan abokan aikinka kuma? Ya za'ayi
nasan abokan aikinka? Iffaat wannan serious
issue ne, miyasa kika aikata hakan?? Nifa yaya
ban gane mi kake fadaba kamin dalla dalla
kawai, yaga zagaye zagaye ba nashi bane yace
yaran da kika yiwa aski da bille Kuma kika
dakesu....!!
[9:59PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??76
Na Hauwa M. Jabo
Au kace min karuwanka koda yake suma abokan
aikine tunda dasu ake iskancin no no no na
manta wayewace, ko ba wayewa bace?! ranshi
ya baci, sai ya share yaci gaba da magana
kinsan kuwa kan haka wata har qara ta shigar
kotu dagayar na rufe case dinnan,? iffaat tayi
dariya hadda kwalla, wallahi da ka bari an tafi
dani kawai kaga sai kaji dadin kawo su har cikin
gida kamar yanda ka saba,! shiru yayi aransa
yace wannan duk abinda aka fada tanada amsa,
shikam gara kawai ya nemi shiri gunta koya
sami sassauci dama laifin sane dabai nuna mata
shi wayeba da yanxu rawar ta chanxa amma
soon zata shigo hannu.. chan yace iffaat kinsan
kuwa ina tsananin sonki? Kinsan tun yaushe
nake fama da sonki cikin rayuwata? Please iffaat
kidaina wahala min da zuciya... Wani sanyi taji a
ranta inaga tinda tazo duniya bata taba jin
kalma mai dadi kamar wannan ba, amma bata
nunaba Sam, iffaat ki tausayawa rayuwa wallahi
wasu abubuwan duk rashin ki yake sa ina
aikatasu...¡!
Ta kalleshi ta watsa mai harara Malam Dan
kawai yan matanka sun gudu shine zaka lallabo
gurina ka min wayo ko? To kayi letti
bazakasamu hakanba,
No iffaat ni ba sai na sami komai a wajenkiba
just kawai ki amince dani maisonkine, mudaina
rigima nagaji. wallahi ina axabtuwa da rashinki,
guntun tsaki taja, ta koma ta kwanta ta dauki
wayanta ta danna recoding duk abinda yake fada
tana dauka har ya qare batace dashi komaiba,
ya qare yazo kusa da ita tayi sauri ta kashe ya
dafa kafadarta ta watsomai ido miye haka wai?
Ta bani dariya miji ya taba mata tana miye
haka!?
Yace ba komai yakai hannunsa akan gashinta ya
shafa yace kizo na gyara miki gashin ki!
Kallonsa kawai tayi yanda ya chanza ya bata
tsoro ta yinqura zata tashi ya danneta ta koma
kwance ta kalleshi wai mi kakesone Malam? Ya
kawo bakinsa daidai da kunnenta ya mata rada
saida tsikar jikinta ta tashi yace ke nakeso
iffaat, tace Banganeba! ina nufi matata nakeso!
Tofa yau akeyinta gata kwance duk ya dabai
bayeta, yana zauna qasa hmmm kawai tace bata
ce komaiba tana jinsa yana Dan mata wai waye
a qirji alamar yanason ya aika hannunsa ciki,
Yya farhaan ina zuwa bari nayi fitsari. Ya gane
guduwa takeson tayi sai yace muje na rakaki,!
Burinta dai ta tashi zaune ya daga mata ta tashi
zaune muje mana. Ta harareshi nama fasa
xuwa. Murmushi yayi yace idan kina tsiwa kinfi
kyau.! aransa yace sai kin shigo hannunna
yarinya ya miqe ya shiga daki,
Iffaat kam dadine yake Neman ya hallakata
dama Ashe yanasonta? Da tasani ta tambayeshi
tun yaushe yakesonta tayi murmushi ta shafa
gashinta, ta tuna shine mutum na farko daya
fara gyara mata gashinta! Ta qara murmusawa
ta tashi tayi sallah...
Goben ranar farhaan ya ya fitowa office wata
budurwarsa ta kirashi tace su hadu wani guri
kamar bazai jeba sai kawai ya wuce gurin iffaat
kuma tana sukul bayan ta fito lecture sai ta
duba latitude dinta taga farhan yananan kusa da
skull dinsu, har ta qara shiga lecture ta fito bai
motsa daga gunba tayi refreshing still yana gun
tayi zooming sosai taga gurin a qafa ta tattaka
koda taje ta qara refreshing taga itama tana
gurin nisansu Kadan ne, koda ta daga kai sai ga
motarsa da wata mota,! Tayi tsaye ta rasa
yanda zatayi, ta duba ba kowa a gurin, sai mai
gadi, tanuna ma mai gadin gurin hotonsa tace
yaga wannan yace eh yana ciki.! tayi shiru ya
zata shiga gurin aka nuna mata dakin tana
kallon dakin amma ta kasa qarasawa sai ta fito
Dan tasan baqin ciki kawai zata gani idan ma
taje din tana hanyar dawowa sai taga police
station tayi murmushi wallahi yau farhaan sai ka
kwana a Gidan yayan sanda direct gurin su
taje........
Muje zuwaa
[10:07PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 77
Na Hauwa M. Jabo
Ta je gurin yansanda ta sami babban su tace
tanason yan sanda hudu ya tambayeta dalili
batasan abinda xataceba tace wanine yake bata
mata qanwa kuma ta rabasu sunqi rabuwa shine
takeson akama- matasu duka biyu taga kamar
baxasu bataba tana dubawa sai taga gun cirar
kudi anyi Sa'a ATM yana cikin jaka ta chiro kudi
tazo ta miqewa Dan sandan jiki na rawa ya
karba ya bata kwalawa hudu tace kuma kada
abada belinsu karma a bari suyi magana taje
tanuna musu gun tayi sauri ta dawo skull,
policawa kuwa sun cika aikinsu suka kama
farhaan da budurwarsa dama iffaat tace kada a
sakeshi kuma kada a sauraresu dukansu sai taxo
gobe zata karbesu kuma kada a bari yayi
magana da kowa!! farhaan kam Dan baqin ciki
har kuka yakeyi mi yake faruwa dashine tunda
yake ba'ataba kamasahiba sai yau an
wulaqantashi ba kadanba.. tsanar bariki ta shige
mai zuciya yayi nadama, yayi yayi abari yayi
magana amma ina sunqi kulashi tunanin sa daya
iffaat yanda zata kwana ita kadai..! Uhum,
itakam hankalinta kwance tanajin dadi koba
komai tamai rashin kunya da safe ta chaba ado
na gani na fada ta saka kayanda ita kanta tasan
tayi da saka glss dinta ta wuce skull bayan ta
fito lecture taje gurin yansanda, tace yazo beline,
aka fito da farhaan da matar tace a maida matar
sai an qare case din farhaan aka maida matar
wata jaka da ita sai jalkuna, yana ganinta ya
rude ya ma rasa abinda zai fada kamar gaske
tace ma yansanda Dan Allah a bata belin sa
mijintane bazai sakeba ayi haquri.!! ya kalleta
cike da mamaki iffaat waya gaya miki inanan?
haka kawai ya samu damar ce mata..! tace naji
a jikina kaje abinda ka saba an kamaka.! Ta
kalleshi but so happy wallahi Allah ya qara
maganin irinku kenan masu bata yayan mutane..
Sosa kai yayi, police din yace kai kanada
wannan baby mixakayi da waccan ashawon
kalleta haddadiya da ita kunya ta rufe shi da
haushin dansanda ina ruwanshi da matarsa.. ta
cika takardu aka saki farhaan sun fito ita dashi
ta kalleshi ta nunashi da hannu, kalleka Dan
Allah namiji har namiji amma ba halin kirki.! Tir
da hali irin naka, idonta suka ciko da kwalla
amma da yake ta saka glass sai baxai ganiba
nayi nadamar kasan cewa tare dakai a matsayin
matarka. Kullum cikin tunanin kana ina mi
kakeyi!!? kallonta yake tamai kyau iffaat baby ce
shima yasani kullum qara cika takeyi tana wani
fresh murmushi yayi ya janyota jikinsa ya
rungume yana bata haquri, tayi tayi ta kwace
kanta amma ta kasa sai ta barwa Allah.......
Dagyar Tasamu ya saketa hawaye ta gani a
idonsa tausayi ya bata, ta bude mai mota ya
shiga itama ta shiga taja suka tafi,mamaki yake
ya akayi ta iya mota? Waya koya mata? waima
waya gaya mata yana gurin baiso ta saniba
Sam har suka Isa gida bata kalleshi ba tana
tauna chewing gum a hankali suna Isa gida
kuma sai yaga motarsa......
[10:14PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 78
Na Hauwa M. Jabo
Ya kalleta chike da mamaki yaga batama kula da
mamakinsaba sai shima ya basar.! sun shiga
gida ta kawo mai abinci abinda bai taba samuba
tunda ya aureta yasan ba ita ta girkaba amma
duk da haka yaji dadi ya zauna yaci yana chi
tace, nasan police station ba abincin kirki shi
yasa na kawo maka wannam, lokaci daya har ya
hargitse, tayi dariyarta ta mugunta ya dago ya
kalleta tace kaima ka dandana kwana Gidan yan
sanda ko? Ta qara yin dariya tace dadi ko??
Baice mata komaiba ina tambaya.! ya kalleta
wai ya akayi kikasan ina chan ? Tayi murmushin
mugunta tace sabida ni na saka a kamaka..!
Ya zare ido Kamar ya? Tace Kamar haka.!
Please kimin bayani ya akayi kikasan ina gurin?
Wallahi Nina tura a kamamin kai, kuma yanxu na
fara duk lokacinda na ganka da wata mace
wallahi saina kulleka. Mamaki yakeyi dukda cewa
yasan iffaat fiye da hakama zata iyayi amma ta
bashi mamaki, miyasa duk motsinsa akan
idonta,? Ya akayi kikasan gunda nake zuwa?
Tace sabida ina iffaat, baice komaiba aransa
yace Ko ta saka a riqa bibiyarshine? Kallonta
kawai yayi Dan gaskiya tamai yawa,!! yana
zaune wayanshi tayi qara ya daga abbanshine
ya gaisheshi anan abba yake gayamai zai
aikeshi Thailand, kuma ya tafi da matarsa,
bayan ya qare waya ya mata bayani ido bude
tace baxataba karatunta zai sami matsala kuma
tafiya har wata biyu ko uku, yaso ya tafi da ita
wataqila ma achan su shirya amma taqi.
Farhaan yama Abba bayanin abinda ta masa
bayani Abba yace ba komai...
Tunda tun cikin Daren yabar gida yaje Kaduna
yana shirye shiryen tafiya, mai sami kansaba har
ya tafi,
Farhaan dai an tafi Thailand yabar iffaat ita
kadai a gida an kawo mata wacce zata tayata
zama kamin mijinta ya dawo...
Tunda matar maman nargees tazo ta kula iffaat
abincin take siyo musu, tanason tayi magana
amma dai tana tsorooo ace tayi shishigi.....
[10:19PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 79
NA Hauwa M.Jabo
Kusan sati daya da tafiyar farhaan amma still
siyo abinci take ta kula iffaat akwai saurin sabo
kuma batada matsala amma kuma batason
shishigi, ranar suna zaune sai matar tace yau
nayi mafarkin Dan wanke, iffaat tace Allah ko! Ki
bari anjima idan na fita sai na siyo miki, matar
tace aah gara dai mu girka kayan mu ko mi kika
gani, iffaat tace gaskiya ban iyaba, sai na koya
miki ko bakyaso tace tanaso, anan iffaat tabata
labarin cewa tunda take bata taba girkiba, matar
nata mamaki ace mace bata iya girkiba, haka dai
matar ta dage ta koyama iffaat girki kunna gas
yanda akeyin komai tace akwai books na girki ta
siya, tace mata, wallahi girki shine mace duk
kyanki da yanga idan baki iya girkiba baki cikaba
bakida daraja a gurin miji, matar dai ta kula
iffaat gayun banxane bata iya komaiba, a labari
iffaat take fadamata cewa ai idan taga mijinta
yana magana da wata ubanta takeci ta mata
aski da bille matar tayi dariya sosai wai bille,
tace to aike iffatu ba haka akeyiba baki
kyautatawa miinkiba ya za'ayi yaqi Neman
mata, kina gani maxan yanxu ko kin kyauta tasu
ya kuke qarewa bare baka kyautata musu,
wallahi kiyi hankali ki San ciwon kanki ki fara
dafe mijinki sosai sannan idan kin Ganshi da
wata sai kisan abinda zaki mata, amma haka
kawai baxaki hanashi abinda yakesoba ke baki
biya mai buqatansaba ki hanashi ya nema!! Ai in
gaya miki kina zaune saidai kiga kishiya, ta dafe
qirji kishiya!!? Sosai kuwa kishiya, Allah ya
rabani da kishiya, Yan zu maman Nargees ya
zanyi,? Ya zakiyi kuwa illa ki koyi girki ki iya
kwalliya koda naga kwalliya ke ajin farkoce ki iya
shagawaba idan yana gida ki manne masa duk
motsinsa akan idonki, iffaat ta kwashe da
dariya.! Miye abin dariya? Tace ba komai, haka
dai tayita gaya ma iffat abubuwan ta bata
sirrikun mallakar miji wani abin iffaat tayita
dariya tana mamaki, bayan ta tashi taje ta
kwanta a nan ta fara tunanin maganganun da
ake fada mata gaskiyane dole ta fara saba masa
da kanta sannan taje chin uban na waje....
[10:30PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??80
Na Hauwa M. Jabo
To amma ai ba laifinta bane? Shine bai
nemetaba! Wata zuciyar tace yaga fuska bare ya
nemeki? Aike ya dace ki kwatanta kiga yanda
zai dawo hannunki, wata zuciyar tace kawai ya
rainakine yana jiran kikai kanki ya qare dake,!
Tayi tsaki. Miye mafita idan bata mantaba Aysha
armiya'u mada ma haka tace mata farahnax ma
da taxo haka tace mata a skull ma idan suna
tadi zancen kenan daya kyautatawa miji, ga lada
ga la'ada. Tayi murmushi ta janyo wayarta ta
dauko hoton farhaan tana kallo tana zooming
batasan lokacinda tayi kissing din bakinsaba tayi
jimm gatada miji har miji amma manemin mata!
Lallai ta bala'e bazata wani gyarashiba ya
kamata ta dandana masa Zumar ta sannan ta
kasa ta tsare idan ta kama ta raka anan ne idan
yaqi dainawa taci gaba da chin ubansu..
100% ta aminta da haka so tana jiran dawowar
farhaan ne taga yanda zata fara, kunya takeji
anya zata iya? Taya zata fara!? da shedana da
wasa zata cusa kanta, har komai ya daidaita, ta
lashe lebenta tayi murmushi ta rungume pillow
Allah ya shirya min kai Yy farhaan.. Haka dai
madam iffaat tayita tunani har bacci ya dauke
ta,...
*************
suna waya akai akai amma dai ba wani chanxi
data nuna mai, shikam hadda cemata yake yayi
missing dinta takanso tace bawani Dan tasan
yana tare da yan matansa amma kuma sai ta
share...
kwanci tashi har farhaan yayi wata daya a qasar
iffaat kuwa lokacin ta gama iya girki nikaina jabo
idan tayi girki badan kada aga kwadayinaba
wallahi dasai naci, amma ba hali, girkinta haka
yake qamshi kamar me maman nargess hatta
yanda ake tafiya gaban oga saida ta koya mata
da yanda ake shagwaba a narke jikin miji duk ta
koya mata cox practice sukeyi maman Nargees
ce iffaat iffaat ce farhaan sai tace ta fita waje
tana shigowa maman Nargees taje ta rungume
ta tana mata wani Abu iffaat Dan dariya har
hawaye takeyi, anya zata iya yin haka kuwa??
Maman Nargees kuwa sai qarfafata takeyi, har
dai taji zata iya, ga iffaat gwana gashi dama ba
auki zatayi dadin kakkarya jiki....
Daidai wannan lokacin farahnax ta haihu ta
sullubo yarta kyakyawa kamarsu daya da
farhaan idan kaga Yar kace ta farhaan ce Dan
kamar har ta baci da iffaat ta tura mai hoton
baby ya gani yace da babyn Suhaila ta rayu da
itama yasan kamar shi zata dauko iffaat dai
batace dashi komaiba, yace amma insha Allah
ina dawowa zan samo wata zaki tayani nemowa,
tayi kamar bata gane mi yake nufiba, tace eh
mana duk inda ake siyowa kaima ka siyo yayi
murmushi ya basar Da maganar....
[10:33PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 81
Na Hauwa M. Jabo
Anyi suna lafiya ansha shagali taga yanda ake
soyayyah gurin farahnax ranarda mijinta yaxo
tana wani mai shagaba tana narkewa abin dariya
yake bata, kuma gaban kowa zata mai haka
saidai a bata guri badai ita ta basu guriba
abinsu yana burgeta, farahnax takance niko
sister iffo zanso naga ranarda zaki daina halin
ki, takanyi murmushi baatace mata komai. duk
abinda sukeyi tana recoding a kanta kuma shima
yana shiga cikin list dinta zata ma farhaan dinta
fiye da wannan idan ya dawo...
Duk kudinda abba yake xuba mata da wayanda
farhaan yabar mata taje ta siyo arnar nyte dasu
ta siyo English wr masu zafi ita kanta tasan dole
ya girgixa idan ya gansu gashi yana sonta dole
kuwa yayi sha'awarta..
Nidai sai kallo nake wai iffaat ce take tanadin
kayan da za'a sakawa miji, batada matsala gurin
kwalliya ta iya kayanta tana biye da group chat
duk abinda akace yana saka ni'ima saitaci tasha,
duk wannan tanadin na PURHUUN dinta ne,
Ranar tana zaune a Palo ta qare gyara gunba
yatsunta sunyi kyau abinta, tayi zaune tsakayar
daki saman center carpet tana kallo taji
tsayuwar mota ta dauka maman Nargees ce Dan
taje siyyah kasuwa kuma kayan sunada yawa da
zata siyo, ko motsi batayiba taci gaba da
kallonta daga bayan ta taji mutum ya Dora
wuyansa akan kafadarta ta wani zabura da qarfi
amma qamshinsa ya bayyana mata wayeshi!
farhaan ne batasan lokacin da maqalqaleshiba
tana dariya yayi surprised dinta ba kadanba
mutumin da akace zaiyi wata biyu koma fiye
amma yau kwana 48 ya dawo, farhaan kam
murna yakeyi yauga iffaat dinsa a jikinsa kuma
da ra'ayin kanta, ta sakeshi ta riqe kunkumi tana
dariya tace, wai Kaine naka gani ko kuwa
mafarki nakeji, yace sosai nine farhaan na dawo
na gaji da rashinki kusa dani koda kuwa kasheni
zakiyi gara ina ganinki tayi dariya na Isa na
kashe yayan farahnax, yayi dariya dhima ya
janyota jikinsa uhum su farhaan an sami yanda
akeso....
[11:34PM, 5/14/2015] .: WACE CE ITA..??82
Na Hauwa M Jabo.
Ya jata kujera Suka zauna tace Bantaba tunanin
zaka dawo yanxuba shine ko waya kaqi gaya
min ai da sai ko girkine a maka, mamakine ya
cikashi shikam gara da yayi tafiyar nan tayi
missing dinsa, hadda su girki,! ana wani mai
murmushi shida idan yaga dariyar ta to tabbas
tamai mugunta ne take dariya....!! .
mai gadi ya fara shigowa da kaya niqi niqi yana
ijiye wa gefen qofa, ya rungumota sosai jikinsa,
Abu daya ta manta bata tambaya ba idan miji ya
dawo sai yasha ruwa sannan zaiyi wanka yaci
abin ci ko kuma sai yayi wanka sannan yaci
abinci, ta rasa yanda zatayi kamar taje kitchen
ta ma maman Nargees waya ta tambayeta sai
tace bari kawai ta masa yanda ta iya, ruwa ta
kawo masa da drink ta zuba masa yace
hannunsa ya gaji saidai ta bashi a baki, dariya
tayi ni ban Iya baiwa ko yara abinciba bare
manya, yace ai nima yarone a gurin ki ko
bakyaso,? murmushi tayi aranta tace shima yaxo
da nasa kwandon iskanci, tace inaso mana,!
Yace to ki baiwa babyn ki ruwa ta kuwa taso ta
tsuguna gabansa ta bashi ya kwankwade yace a
qaro ta qara mai ya kwankwade yace a qaro
tace aah ya Isa,yayi murmushi idan dai ke zaki
bani xan tasha har sai na shanye duka,murmushi
kawai tayi batace komaiba, tace muje kayi
wanka, yace iyeeeee duk ni kadai gaskiya dole
duk sati na riqa yin tafiya tunda idan na dawo
gata ake min, ta waigo ta Dan qaramai harara
ta murguda baki, saida ya tuna da ita a yanda
take da tamai gata gwanar murguda baki,tuni
yayi tsitt kamar ruwa ya cishi, suka shiga bayin
zata fito yace kixo muyi wankan tare mana tace
ni nayi daxu kai kayi yace to kixo ki wankemin
bayana hannuna baya kaiwa, kallon sa kawai
tayi ta wuce abinta duk shekarunda kayi kana
wanka wa yake wanke maka bayanka!
Shikam murna da dadi ya ma rasa abinda zaiyi
dan murna, iffaat ta rasa mi zatayi girki zata
masa ko kwalliya zata tsaya tayi, sai kawai ta
Yanke shawarar girki, ta shiga ta duba duk wani
abinci idan tace tayi shi zata bata lokaci sai
kawai tayi sauri ta hadamai danbunb cos cos
da busashen kifi yaji ganye, duk Wanda
Yaji qamshin girkin to zaisan cewa abincin ma
zaiyi dadi dambun cos cos dan taga yafi sauri
dama farhaan idan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login