Showing 27001 words to 30000 words out of 37326 words

Chapter 10 - WACECE ITA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hauwa M Jabo.txt

14 Jan 2025

2858

na Neman wata daya Gidan
farhaan baya kulata itama bata kulashi amma
rashin xamansa gida na damunta ko ina yake
zuwa Allah masani kuma bata gane takunsa,
Ranar tana zaune dabara ta fado mata yanda
zata gane ina yake tafiya, bayan ya dawo
gantalinsa na dare ya kwanta bacci, dama
batayi bacciba tana jiransa ya dawo ya ijiye
wayansa tana tabbatarda yayi bacci ta dauki
wayansa ta shige bayi ta kulle ta danna power
off screen din yayi duhu ta duba da kyau sahun
hannunsa ya yake zana pattern dinsa bataci
wuyaba tana zagaya yanda taga sahun
hannunsa yabi tayi sa'ar bude wayar pattern
dinsa ba wahala ma, tana budewa ta fara aiki,
farko saida ta budamai Google account sannan
taje play store tayi downloading din latitude
tamai register dama tana dashi ta dauko
wayanta tayi sending request ta karba shikenan
ta gama da wannan duk inda yake matuqar data
dinsa a kunne take zata Ganshi baya buqatar
GPS latitude din, ta shiga SMS bata sami
komaiba taje contact ba wani number da bata
yarda dashiba harda searching na sunayen yan
matansa data sani amma babu ta duba logs nan
ma babu da qanqaro WhatsApp a kulle yake
kuma da pin number kawai zai bude bata
wahalda kanta ba taje gallery ba wasu hotuna
daga nashi sai iyayensa sai kuma na margayiya
Suhaila, gasunan sunfi 100 wani qololon baqin
ciki da kishi ya taso mata ganin hotunan da
Wanda suke tare da Wanda rake ita kadai amma
ba nata ko daya kamar ta goge amma kawai
saita fasa har zata fita sai taga wani folder ta
shiga akwai wani aciki ko wanne an rubuta
empty haka tayita dannawa saida ta wuce folder
14 sannan takai gunda aka rubuta Mrs
PURHUUN, ta shiga ciki hotunan tane aciki daga
kan wayanda ya mata lokacinda ta fara koyon
gayu gun Yar baqa Dana zuwa qauyen da yayi
wasu ma ya saka su a cikin frame mai heart
wasu kuma itada Suhaila ne amma an gutsure
Suhaila ko farahnax wasu ma batasan ya
dauketa suba irin tana zaune dinnan tana shirme
ko kuma tana surutunta tun kamin ta qare
wayewa gasunan dai kala kala, mamaki da jin
dadi suka mamaye mata zuciya ganin ya damu
da ita hatta hotunanta a wayar, sai wani video
da ta gani rawar da suka tabayine itada
farahnax a daki sukayi video ko ina ya samu
ohoooo tana tsaka da kallo taji yana qwanqwasa
bayi tsoro da tashin hankaline suka
baibayeta.....
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 69
Na Hauwa M. Jabo
Tace Idan da kana dukana ada yanxu akwai
banbanci wata qila ada ina gyalewa ko kuma ina
ramawa to ka sani yanxu akwai banbanci, ni
matar aurece inada yanci kuma nasan yancina
so ka kiyaye hannunka daga Taba matar aure.!
Ta sake mai hannu da qarfi Ta wuce abinta ya
bita da kallon Mamaki hadida zargin abinda ya
kawota yi anan ya akayi tasan yana nan ya daki
iska baima jira karuwarshiba ya fito da qarfi
koda ya fito bata ba labarinta ya shiga mota
gudu yake kamar ya ya hira sama koda ya isa
gida bata isoba yayi kusan 30mnt sannan ta iso
da ledojin abinci a hannu.! Tana zuwa ya daka
mata tsawa ina taje? Ta kalleshi dukda taji tsoro
amma bonewa tayi, ta danqaramar uwar harara,
kamar ma bada ita yakeba, tana Neman guri ta
zauna ya fincikota ke badake nake maganaba, ta
kalleshi ido cikin ido tace mai inda yaje chan
taje? Mi kikaje yi achan nanma ta bashi amsa
abinda kajeyi achan shi najeyi.? Idonsa suka
kada sukayi jaaa sun firfito waje iffaat kinsan
abinda kike fada ya qara fincikota ya mannata a
garu kinada auren nawa zakije gurinnan ? Ko kin
manta ke matar aurece. Taji tsoro iya tsoro
amma ta daure ta bashi amsa ta kalleshi idonta
cikin nasa tace, au auren akan mace kadai yake
kenan kaima ai kanada auren nawa kaje gurin
nan ko kaman ta kanada aurenane akanka? Idan
kuma akwai banbanci tsakanin mu let me know.
Yanda idan ka'aikata badaidaiba za'a maka
hukunci haka nima za'amini so miye
banbanci?? Wani baqin cikin kishi ya turnuqeshi.
Muryansa na rawa yace iffaat tell me the Truth
mi kikajeyi a gurin nan ? Ya bata tausayi yanda
ya sassauto, nace abinda kajeyi shi najeyi.
Sakinta yayi ya fuskanceta dakyau iffaat mi
kakajeyi a gurinnan Har kika ganni? Tace abinci
naje siya,
Ya manna mata arniyar harara, daga yau na
soke baki ba fita sayen abinci idan dai ba
makaranta zakijeba baki ba fita, abincin kuma ki
shiga ki girka da kanki!!
Tsaki tayi ta wuce shi,
Farhaan ya tsargu matuqa yauda ta kamashi da
wata ai bai isa ya shigo gidannan ba..
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 68
Na Hauwa M. Jabo
Gari ya waye ma amaren farhaan yana jiran
amai breakfast amma shiru har 12 yunwa ta
isheshi ya duba ko ina ba alamar girki sai
hayaniyar mutane, Yakama hanya ya fita abinsha
bai dawoba sai guraren daya na dare bata
damuba cox yan ganin amarya da qawayenta
sunanan sunyi girki sun debe mata kewa, bayan
sun tafi sannan ta fara tunanin ina yaje!? Daya
na dare ya dawo daya shigo tamai kallon
tuhuma tana Palo bai kula da itaba ya wuce
dakinta,
Koda ta shiga ya shiga wanka ta zauna bakin
gado har ya fito ta kalleshi yana goge kai alamar
wankan xxxxxx yayi. Ta fuskanceshi da kyau,
tace ina kaje yau? Gurin abokaina ya bata amsa
yana chire doguwar rigar dake jikinsa dagashi
sai towel bata taba ganinsa hakaba sai yau tsoro
yakamata ta tashi ta koma palo, ranar dai batayi
bacciba zuciyarta cike da tuhume tuhume, sai
guraren asuba bacci yayi awon gaba da ita bata
farkaba sai guraren 12 Subhanallahi yau tayi
lettin lecture dole taje ta nemo abinci ta tashi ta
fita direvan bayanan an ma fita da motar da ake
kaita skull da ita tayi tsaki tafito ta taka sosai
sannan ta sami mai adaidaita sahu ya dauketa
koda taje Al nasiha restaurant abincinda takeso
ya qare aka mata kwatancen wani guri inda zata
sami abincin ta qara tsayawa chan saiga mai
adaidata sahu ta tsayar dashi suka tafi sun isa
gurin tace ya jirata ta fito tana zaune tana jiran
a hada mata abincin taji ance farhaan, wani rass
taji mace ce ta kira Sunansa ta juyo ta kalleta
ga dukkan alamu tasan ta amma ta manta ina
tasanta Dan kamar ta qara fari yanxu, ta kashe
kunne taji tace Tana xuwa yanxu. Iffaat tace ina
xataje oho? Tana fita tabi bayanta Tana kallo ta
tsallaka titi sai taga ta shiga wata villa a gun,
tayi tsaki, ta dawo abinta ta karbi abinchinta ta
shiga adaidata sunxo daidai villa taga motar da
ake kaita makaranta....
Jiki na rawa ta tsayarda mai adaidaitan tace
Tana xuwa qirjinta kamar ya fito Dan tsananin
tashin hankali wata zuciya tana kije wata na
fadin kada kije, haka ta shiga gurin taje gun
Masu coffee ta nuna musu hoton farhaan
mutumin ya gaya mata dakin da yake zama
kullum, taje dakin da qarfin guiwa za'ayi kashin
kai wallahi!
Ta bubbuga farhaan ya taso ya bude mata,
tsaye yayi yana mamakin mi tazo yi anan gurin
ya kalleta mi kikeyi anan ta watsa mai harara
abinda kakeyi shi nakeyi ta shiga dakin ta duba
ko ina ba mace, tazo ta kalleshi karuwar taka
bata Iso bane??
Keeee waike bakida hankaline?? Mutum bai isa
ya fito shaqatawa ba sai ace yaje gun karuwai
wall.......
Sheeee ta katseshi da Dora hannu a lebenta...
da kunnena naji kana waya da karuwarka kana
taxo ka iso tazo kuyi iskancin da kuka sabako??
Ya daga hannu zai wanka Mata mari tuni ta riqe
hannunsa,...
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??71
Na Hauwa M. Jabo
Ta sadaqar kawai har zata danna power Off ta
kulle wayar sai ta tsaya tayi clear din duk abinda
ta bude tabar wayanda ta gani ta danna power
off ta bude bayin, Tana jiran ya fara masifa akan
me zata Taba mai waya amma taga ya shiga
bayin baima kalleta ba tana ganin haka tayi sauri
ta ijiye masa kayan sa tana ijiye wa ko hannu
bata daukeba alarm ya fara bugawa na sallar
asuba.
Allah yasota da ya buga Tana bayi ai da asirinta
ya gama tonuwa, tayi murmushi yana fitowa
itama ta shiga tayi alwula tayi sallah......
**********
Aiki ya sami iffatu duk yinin ranar Tana biye
dashi a latitude duk inda yaje Tana biye dashi
haka tayita saka mai ido har kwana uku ta gano
gurin da yake xuwa kullum ta gano gunda yake
yawon dare, hatta gurinda yake parking din
motarsa ta gane so zata fara aiwatarda aikinta
akansa.
Farkon abinda ta farayi ta Riga ta gano gunda
yake parking kuma tasan lokacinda yake xuwa
gurin, saida ta tabbatarda yana office ta kira
driver tace yakai motarta gurin ya ijiye tamai
kwatance ya kuwa je ya ijiye farhaan an qare
aiki akazo gantali tashin hankali abinda ya fada
kenan lokacinda ya hango motar ta, ko miya
kawo wannan yarinyar anan gurin?? Ya fara
tunanin ko tazo nemansane ya tafi akan tazo
nemansa ne kawai, bai tsaya bata lokacinsanaa
jikinsa na rawa yabar gurin bayan ta duba taga
yaje sai kuma taga ya bar gurin ya nufi hanyar
nasiha restaurant Tana ganin haka Tama driver
dinsu magana akan yaje da sauri ya dauko
motar bayan ya ijiye motar a gida dama tayi
kwalliya kamar wata amarya, yana dawowa ya
ganta kuma, ya kalleta kwalliyan ta ya sakashi
zargi,! To Ina taje miye na kwalliya ma! Cox bata
taba masa irin wannnan kwalliyar ba, Yanason
Ya mata magana amma yana tsoro, yasan
zatace shima mi yajeyi a chan? Ko kuma tace
ina ya ganta? Tinda bai gantaba gara ya bari
har y kamata da kanshi, haka ya zauna yana
tafarfasa har yayi bacci Dan baqin ciki ranar ko
fitar dare baiyiba..
Goben ranar sai baije gurin ba daga office ya
dawo gida kuma idan ya dawo saiya ganta gida
zaune ba inda tajee har kwana uku ranar na
hudu yaje gurin tana ganin haka ta tura driver
yaje yayi parking din motarta daga kan hanya
hanya ta yanda dole dole yaga motar tazo tayi
kwalliya abinta ta kame bayan ya fito hotel din
yaga motarta, mamaki ya kamashi, tana kallon
duk wani moving dinsa a latitude yana yawo
hakan ya tabbatar mata da nemanta yakeyi a
gurin tayi murmushi ya fito wajen gurin yayin
parking yana jiran ta fito kusan awa daya yana
jiran ta tafito amma bata ba labari, ya gaji. ya
riqa ya tabbatar da cewa nan gurin tazo yaja
mota Kamar wani mahaukaci.....
[7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 72
Na Hauwa M. Jabo
Tana ganin yabar gurin dama driver yana gurin
tamai waya tace yayi sauri ya dawo da mota
gida yayi gudu sosai farhaan kam traffic ya tsare
shi a hanya ga uban go slow ya biyo ta PZ shi
kuwa driver ta by pass yabi kamin farhaan ya
kawo tudun wada tuni an dawo da motar gida
yana shigowa gida yaga motar, yana huci Kamar
kasa tana zaune a Palo ta saka fura gaba
tanasha yana xuwa yasa qafa yayi ball da furar
gaba daya ya finciko gashin kanta ya wurgata
saman kujera, yazo Dai dai da ita zai kasheta da
mari ta wani riqe hannunsa da qarfi, tayi tsaye
saman kujerar wallahi idan ka mareni ba mijina
bane ko waye kai sai na rama...
A fusace yace ke Dan ubanki ubanwa kike yiwa
kwalliya kina kina fita?
Ta watsa mai harara tace ubanda ya
chanchanchi na yiwa kwalliya shi nake yiwa.! Ya
daki iska ya juya yana huci iffaat ni kike yiwa
rashin kunya?? mi kike zuwayi a Zaria hotel? Mi
kikiye achan?? tsaki ta masa ta diro daga
kujerar ta kama hanyar dakinta ya biyo ta
kinsan Allah wallahi idan bakiyi magana zan iya
kashe ki iffaat wallahi xan sallantar da
ruwuyarki..!!
tashin hankali lallai farhaan yafi iffaat kishi
hadda zancen kisa ta bala'en jin tsoro ta juyo ta
kalleshi taga yanda yayi wani iri dashi, tayi sauri
tabi gefensa ta fita bata tsaya ko inaba sai
Gidan su farhaan tana zuwa ta fada jikin umma
tana kuka... Akayita tambaya amma ba amsa
umma ta kira farhaan tace maxa yaxo tana
Neman sa ya kuwa zo, umma ta fara tambayar
sa mi ya mata haka duk ta firgice shiru yayi ya
kasa magana umma ta dakamai tsawa ya mata
bayanin komai tsaki tayi, rudadden banxa wai kai
mi yake damunka ne? Ko kunya bakajiba Dan
Allah kace ka ga mota amma baka gantaba
kuma ka dawo ka tarar da ita gida, haba wane
irin shirme ne wannan umma wallahi har
kwalliya fa takeyi.! Umma tace to mace a Gidan
mijinta batayi kwalliya idan batayi kwalliya ba mi
kake son tayi kaji shiriritar banxa, kai waya gaya
maka haka ake kishi da hauka, ka bari sai ka
tabbatar sannan ka yanke hukuncin waima kai
uban me kakeyi a Zaria hotel? Da har kaje kayita
ganinta? Ya Sosa kai iffaat data narke jikin
umma ta dago ido ta saci kallonsa ya duqar
dakai, yace umma baqi nake saukewa a gurin.
Tayi tsaki wallahi ka shiga taitayinka. kada ka
qara daga mata hankali da haukarka kaji na
gaya maka sannan duk abinda kakeyi ka bari sai
ka tabbatar sannan ka yanke hukunci farhaan
kam ya rasa bakin magana umma ba fahimtar sa
zatayiba tonon asiri ne ma zai yiwa kansa idan
yace zaiyi ma umma bayani har ta gamsu,!!
akace ta tashi ta bishi ta sa kuka ita bazatajeba
dole umma tace ya tafi gobe ya dawo ya tafi da
ita,
Na gaya muku iffaat fa taji tsoro matuqa taji zai
kaita lakhira...
Dole ta chanxa wata hanya...
Muje zuwa muji hanyar da zata komawa.
[9:32PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??73
Na Hauwa M. Jabo
Farhaan kuwa zaune ya kwana yana ta tunane
tunane, kamar ya hade rai ya mutu Dan baqin
ciki...
Ya janyo wayarsa ta bude hotunan ta yana kallo
tabbas yasan yana son iffaat babban abinda
yake damunsa idan ya tuna WACE CE ITA.. Yar
aikinsace fa wannan gani da yake mata har
kullum shi yakesa baya darajata, amma yasan
yanasonta babban dalilin da yasa ya qara
aminta da auren Suhaila Dan sunyi kama da
iffaat ne, hakadai yayita mulmula saman gado
kamar an xuba lemu a paranti sai zagayawa
yakeyi yana juyi wata zuciya tace idan ma Yar
aikinkace ai matarkace yanxu yakamata ka bata
haqqinta na matarka, ko ka sami sauqi, chaiiiiii.
qarshe ya tafi akan iffaat bazata taba aikata
hakanba amma xaiyi magana da driver dinta yaji
gaskiyar magana,.
Hmmmm nidai jabo Bantaba tunanin farhaan
yana son iffaat hakaba ba sai yau Ashe shima ya
kamu bamuda story,
Haka gadon ya masa fadi yasaba da kwanciya
tare da ita koda ba abinda sukeyi amma yana jin
qamshin jikinta, yanajin dadi amma yau babu...
Tunda qarfe 8 yaje daukota umma tace sai ya
dawo office sannan yazo ya dauketa..
Yinin Ranar dai bai gane komaiba gashinan sai a
hankali, har ya taso ya dawo office yazo umma
tamusu fada musamman shi, sannan suka tafi,
iffaat dai taji tsoro fa yanda ya mata ya firgitata
ba kadanba, amma bata nuna masaba
So ta yanke shawarar bazata qara kai motar ta
gurinba...!! Iffat Kura ga tsoro ga ban tsoro.!!
******
Farhaan ma haka bai qara xuwa Zaria hotel ba.
Bayan yayi bincike ya gano shirinta dariya kawai
yayi, lallai wannan yarinya akwai rigima..
Yanxu ta saka masa ido sosai a latitude tana
yawan ganin yana zuwa wani guri so abinda ta
farayi shine ta sami mai adaidata sahu ta
biyashi tace kawai ya bishi na kwana biyu yaga
mi yakeyi a gurin ai kuwa an kawo mata labari
wata yarinya yake dauka gurin tasa aka duba
mata gidansu yarinyar da komai nata, ta riqa ta
shirya abinda zata mata ta kiyaye lokacinda
yake sauketa ya wuce. ta sami almajirai su biyar
tace aiki zasu mata farhaan na sauketa ta riqa
ta tare hanyar tasa yaran suka tareta har ta fara
xaginsu iffaat taxo ta wanketa da mari tace
wayannan almajiran sun fiki daraja Yar iska
yarinyar.! mamaki ya cikata hakadai iffaat tace
ta shiga wani kongon gida zasuyi aiki, ta turje
sai tasa almajiran nan suka durata cikin kongon
gidan taso tayi taurin kai sai taga batada mafita
illa miqa wuya, bayan sun shiga iffaat ta zauna
saman wani bulo tabata almakashi tace ta yanke
gashin kanka ta fara gaddama iffaat ta qara
waske banxa da mari saida bakinta ya fashe da
jini ba shiri yarinyar ta karba ta aske iya yanda
zata aiya iffaat tace bai mataba haka tasa reza
ta mata tall kobo almajiran sai dariya suke nima
jabo dai na dara cox mace ba gashi batayiba!!
bayan ta mata gwandal tace saura Abu biyu
kuma, matar ta fara kuka tana tataimaketa iffat
tace ta rufawa kanta asiri ta bari suyi aikinsu
idan ba hakaba zata qara mata wani
punishment,mata kuwa sai kuka take tana roqon
iffaat tayi haquri amma iffaat ko kallonta
batayiba tasa almajiranta suka danne mata ita
ta mata bille guda biyu a fuska sannan ta fito
da bulalarta ta zaneta saida ita kanta ta gaji da
dukan nata sannan ta barta tace idan an
tambayeki wa ya miki haka kice iffaat ce ko kice
Mrs PURHUUN..... ta fita tabarta nan tana
kuka.....
[9:38PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 74
Na Hauwa M.Jabo
Yarinyar taji jiki matuqa sai kuka takeyi, babban
baqin cikinta billen data mata cox gashi zai fito
nan gaba amma bille bazai baceba har abada ta
fara tunanin WACE CE ITA?? Mrs PURHUUN
kuma?? waima da wane dalili ta mata haka??
Ta gaji ta rarrafa taje gidansu tana kuka..!
Ran iffat yayi sanyi farhaan na dawowa ta
kalleshi ta kwashe da dariya ya juyo ya kalleta
yace lafiya? Ta wani daga ido alamar dawa
kake? Yace hmmm yasan tabbas akwai abinda
takema dariya, sai daibai bazai kulataba.
Iffaat haka ta riqa bin farhaan a latitude saida
tama yan matanshi shida aski hadda su ramcy
ko ina hafsa take ohoo taso ta aske hafsa ta
mata bille....
*******
Ranar sun fito lecture ta hadu da wata tsohuwar
qawarta Aisha armiya'u mada. Sun Dan yi skull
tare da ita tanason iffat sosai bayan sun gaisa
take bata labarin tayi aure tanata tayata murna
hardai tace zataje gidanta bayan lecture sunje
gida akan hanya ta siya mata abinci Dan iffaat
har yau bata iya girkiba hasalima bata taba
girkiba saidai dafa tea, hatta kunna gas har yau
bata iyaba....
Bayan sun qare chin abinci suna tadi saiga
farhaan ya shigo, armiya'u ta gaidashi ya amsa
iffat kam ko motsi tadai kalleshi kawai, bayan ya
wuce ta kalleta tace iffaat wannan ne mijinki?
Tace eh kinsan shine? Tace Eh nasanshi, iffaat
aranta tace wallahi zan miki bille kuwa. Ina kika
sanshi? No tunda dadewa sunyi soyayyah da
wata cousin dina but Allah bai qaddari
aurensuba, iffaat tace eyyah aure nufin Allah ne.!
Eh hakane har an bar zancen amma iffaat sarkin
kishi abin yana cinta.
Chan tace ya sunan cousin din taki? Tace hafsa,
amma sun rabu yanda tace min wai yasa house
girl dinsa ta mata wulaqanci abin dai ba dadin ji
wallahi...
Nidai nace ko baka son mace ai ba haka ya dace
kayi Dan ka rabu da itaba....
Ka gaya mata bazaka auretaba sai a zauna
lafiya iffaat tayi murmushi wato abinda ta mata
ya rabasu da farhaan lallai aikinta yayi kyau..
A munafunce tace Allah sarki kinsan mazan
yanxu sai a hankali , tanason ta sami
information a gurinta,
Kuma ai farhaan ya damu da ita har ya bani
labarinta, armiya'u najin an fadi haka sai ta saki
jiki dama tana tsoron tayi siririn baha ya
zamana batasan da zancen ba.....
[9:45PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 75
Na Hauwa M.jabo
Armiya'u tace Wallahi kuwa hafsa taso farhaan
kamar rayuwarta ta bashi kanta sabida tana
gannin kamar zai aureta, kai ai hafsa tayi jinyar
rabuwa da farhaan, iffaat ta gyara zama tace ai
yace min tanada jarumta sosai, armiya'u tace
uhum Ashe dai kinsan komai kena,? nama daina
jin tsoron fada, iffaat tace eh duk ya fadamin
yace har matarsa ta farko tananan yana tare da
ita yace har gida yake kawota.! armiya'u ta
gyara zama za'ayi gulma ai iffaat in gaya miki
yanda hafsa ta bani labari mijinki akwai tsananin
buqata kuma yanason jarumta matuqa gurin
harka, idan kika kiyaye haka wallahi zaki
sameshi a hannu shiyasa ma hafsa ta daga tuta
duk cikin yan matanshi yafi ji da ita, idan kika
kiyaye sai yanda kikayi dashi.!
Iffaat dai duk da qunan da zuciyanta keyi bai
hanata saurareba, wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login