Showing 6001 words to 9000 words out of 22202 words

Chapter 3 - Auren kisan wuta Complete Book By Zulaihat Sani Kagara.txt

zan batardashi a doron kasa baki daya, jamila tace nifa nagaji kasa shi yasakeni indawo wurinka, shiyasa tun farko nace maka nifa yaron nan bemin ba, amma kawani nace wai ai yaro ne shi kuma zeyi rikon amana,




Kuma dayaga anbashi kudi ze aikata abun da akeso, yayi"










Ai gashinan yanuna ma shi yaro ne,




Dan liti dayake bayanta tsaye, yaji kuma duk abinda tafada, bata ankara ba taji ya warce phone din, yafara magana da alhaji usman,








Alhaji usman barka da warhaka, alhaji usman yafara ma dan liti magana kaman zai cinye shi,






Kai dan mema kakeda sunana to wlh kakiyaye ni, ni nafi karfinka, kai ko?




To waima waye kai?


Daya wuce talaka har da zaka hada kanka dani, dani zakayi jayayya?


Wlh sai insa abatar min da danginku gaba daya, koka sakar min mata kokuma hukuma ta nemomin kai, wlh kuma inbiyasu sucanja maka kama,






Yadaka mishi tsawa, zaka sakar min mata kokuwa!








Dan liti yayi dariya πŸ˜„






Yace haba alhaji usman mai gwal, meyayi zafi haka?




Dafa dan yaron nan dan liti mai wanki mota kake magana, habawa ai kaman dan liti yazuma alhaji fetir ne, yahau bala'i,






Akarshe yace kajirani ganinan zuwa da kwalawa, wlh sai nakoya maka hankali, dan liti yasaki murmushi kefen baki,




Yace ina jiran zuwanku, inbaka gane gidanba kakirani, in maka kwatance,












Tofa 😳






Wai me dan liti yataka ne?






To mudai je zuwa








Taku har kullum yar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*




*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*






*PAGE* *17* */* *18*






*KAINUWA* *WRITERS* *ASSOCIATION*🌈








Dan liti na ajiye wayan ya zubama jamila ido, tace menene kawani zuba min ido, tamur guda mai baki 😏






Bakai wai me taurin kai ba, kana tala ina kai inaja da mai kudi, irin alhaji usman inbanda ma wauta irin na talaka, ina kai ina irina, yama zakayi dani tukunna, dakaki sakina harda canja min gida,








Yaro dakai kaima kasan ni ba sa'arka bace ni, dan ni nafi karfinka kamin yaro,






Dan liti daya gama kai kololuwa wurin bachin rai, dan a kalaman jamila kab, kalmar datake batama dan liti rai kenan, wato kalman yaro"






Yasaka idonshi cikin nata jamila taga yakoma mata kaman namijin zaki, gashi bata iya kallon shi ido cikin ido, sbd yana mata kwarjini, dasauri tasaukar da idanun ta k'asa,




Dan liti har yayi kaman ze mata magana, sai kuma yafasa shige daki, yana shiga kaya kawai yacire ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa, yajima yana wanka kafin yafito,




Yashirya chikin wani yadi, me arha irin dai na masu karamin karfi, yataje suman kanshi mekama dana larabawan misira, lol






Yafeshe jikinshi da turare, yasa hulan sa, yafito jamila tana zaune a parlon inda yabarta, nadin dai yasame ta kobi takanta dan liti bai yiba, ya wuce yafita daga gidan,






Bewani dade da fita ba yadawo, dauke da ledoji niki niki yayi kitchen dasu, yakara komawa yadauko wasu harda kwalaye, yagama shigowa dasu kaf,






Sannan yashiga kitchen, yahada musu abun karyawa, yasoya kwai yahada musu tea, yadauko nashi yadawo parlon, yana gama karyawa sai yaji wayanshi yana ringing, koda yadauko sai yaga alhaji usman ne ke kiran shi"






Yana dauka, se yaji alhaji usman yana cewa, ashe kai karamin mara kunya ne?




Matso raci kagudu ai daka kajirani, kaga abun da zanma, dan liti yace kwantar da hankalin ka, alhaji usman bari inmaka kwatancen gidana, sai kazo kai da rundunan yan sanda"






Atage dan liti yama alhaji usman kwatan chen unguwan su, ba'a wani dauki lokaci ba sai ga alhaji usman, da yan sanda Sunyi parking a kofar gidan dan liti,








Alhaji usman yaba yan sanda umurnin sushiga, sufito da dan liti, aikuwa sukayi yanda ya umurce su, sbd naira"






Koda suka shiga gidan sunsami dan liti zaune, a parlon yakalle su yayi murmushi, πŸ˜„ har kun iso?






To zamu iya tafiya, yayi gaba yan sanda da abun yabasu mamaki, sbd shi ko ajikin shi dinnan, yadda zakaga anzo kama mutun, yafara zazzare ido 😳 yana bada hakuri"








To shi wannan ko a kwansa, sukace kome yataka ohu πŸ€·β€β™‚ suka bishi abaya, yana fita yasakar ma alhaji usman murmushi, yadare motan yan sanda, alhaji yabishi da ido"






Alhaji usman yace, towai ni wannan yaro me yataka ne?




Yaro sai ji dakai, kaman wani dan sarauta, kumafa kafin in mashi matata ya aura ba haka yake ba,






Kar daifa, sai yaji andafa shi azabure yadawo setin shi, dan duk maganan dayake yi a zuciya yakeyin ta, shi yasa memaji magana police officer ba,






Police yace alhaji me kake tunani ne tun dazu, sai cema nake mutafi, mutafi tunda munkama shi,




Alhaji usman yace eh wlh wani dan magana ne yatafi dani, police yace to Allah yasawa ke, sukashi ga motan alhaji usman din suka bisu a baya.






Tafanin jamila tana ganin, an tafi da dan liti, sai taji jikin ta duk yamace ita dai batasan meyasa ba,








Suna isa police station, aka tasa keyan dan liti chikin, akasa shi bayan kanta, alhaji usman yace to me kuke jirane ? Kulallasa minshi har seyayi laushi,






Wani daga chikin yan sanda, yace alhaji muna jiran oga ne, kuda keshi inji ni base kunjira d p o ba,




Sukace kadaiyi hakuri alhaji yanzu zakaga yaka raso, alhaji usman beko saurare suba, yaciro waya yakira d.p.o. har yatsinke ba'a dauka ba,






Alhaji zefara masifa kenan, sai yaji karan motan dpo, yana parking yanshi suka sara mai ya amsa, suka sanar dashi zuwan alhaji usman ai sai yahau wangale baki,




Yaka rasa chiki da sauri, dan yasan yau kam aljihunsa ze chika taf,






Yaka rasa suka gaisa da dpo yace alhaji usman kwana biyu, ya aiki?


Lafiya kalau dpo, dpo yace wai lafiya kuwa ? Naganka a wurinmu?






Alhaji usman yace bari kai mutu mina, wai yaro karami ze raina min wayau, to muje office,






Suka shiga chiki office din, dpo yabuka chi alhaji usman yayi mishi bayani, yako bashi bayani filla filla, yana gamawa dpo yasa akawo mishi,








Mai laifin office dinshi, seko ga dan liti antaso keyar shi, har chikin office din dpo, koda suka shigo idon dpo yana kasa yana rubutu,




Yana dago fuska yana cewa, kai ne me taurin Ka....... i






Ai a zabure yamike, ya zaro ido 😳😳




Yana nuna dan liti












Tofa ai nima da gudu nayar da birona saboda yanda naga dpo duk yada burce daga ganin dan liti, ai zenaji ya'yan hanji na sun kada, ai sai nadiba πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€








Muje zuwa










Yar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*




*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*








*Edited by:πŸ’žMrsπŸ’žMansoorπŸ’ž*








*PAGE* *19* */* *20*






🌈 *KAINUWA* *WRITERS* *ASSOCIATION*🌈








D. P. O chikin tashin hankali ga gumi daya gama jik'a mai face, yace "kalifa"






Alhaji usman daya gama, k'uluwa yamik'e yace "meye haka kuma d.p.o? Daga ganin me laifi se kawani rud'e, kuma naji kace mishi kalifa, shifa wannan sunan shi d'an liti, shine fa yaron dana kawo wurinka ku gyaramin shi kuma kusa yasakar min mata"






D.p.o yajuyo yakalli Alhaji Usman yace "kasan waye wannan kuwa"?




Alhaji Usman yace ma d.p.o"karka raina min wayau mana, waye shi kuwa? daya wuce d'an liti mai wanki mota"








D.p.o yace "Alhaji dan Allah kafita min daga office, dan tsayuwarka anan wallahi zan iya rasa kujera na, saboda haka kafita pls"πŸ‘








Ze sake magana d.p.o yaba yaran shi umurni sufitar dashi, tunda ko yaji haka yafigi babban riganshi yayi gaba, haka yatafi fuuuuuu, kaman zetashi sama, yazo sauka daga matattakala aiko yataka gefin babban rigan shi yayi taga taga ze wuntsila, Allah yatai make shi.




Bekai k'asa ba, yana tafe yana kumfan baki,




D.p.o yace Kalifa "have a set pls, d'an liti ya zauna, d.p.o yajuyo ya kalle ni, yace "to me d'auka tabaza zaki fita ko sai nasa yara sun chilla min ke kagara? "




Ai saina fiddo ido waje 😳 senaga yad'auki waya zekira, ai a 360 nad'iba πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€sai waje.




Najima a lab'e bayan wasu awanni naga d'an liti da d.p.o sun fito suna hira, murmushi chike face d'insu, suka shiga motan d.p.o suka bar wuri , basu tsaya ko ina ba sai gidan d'an liti"






D.p.o yaba d'an liti hannu, sukama juna sallama, har d'an liti yabude k'ofa yajuyo yace "hope baka mance abun dana fad'a makaba ko?"






D.p.o yace "na isa inmance, d'an liti yace good" yashige gida, yasamu jamila tayi wanka ta baza gayu, sai kamshi take fitarwa, gidan ma tas tag'yara ko ina tazuba turaran wuta, gidan duk yad'ume da k'amshi.








Tana zaune parlon tana kallon wani film har ya gitta ta yadawo "kebaki iya gaisuwa bane ?"








Tace "me ake kira haka?"




Yayi smile yace "Malam da Inna dai sunyi k'ok'ari sosai, wurin baki tarbiya kowama yasan hakane saboda sudai bayin Allah ne masu dogaro da tawakali,






Nasan wannan rashin d'a'an naki, a wurin nusarin nan ne me katon chiki kika koyo shi" jamila tamik'e chikin fushi"Kai har ka isa katsaya gabana kana zagar min Miji a gabana,






Wallahi kayi k'arya, waye kai? Mekake dashi?




Harda zakayi jayayya da Alhaji Usman!"




"D'an wanki mota dakai yaro sai taurin kai" d'an liti yadaka mata wani irin gigitacciyar tsawa, seda takoma ta zauna saboda tsorata, yace "kinsan Allah duk ranan da kika kara kirana yaro"








"Wallahi wallahi zan miki aikin yarinta kinji nafad'a miki"yajuya yashige d'aki abin shi.




Yabarta da sanyin jiki, tana nan zaune taji motsin shi a toilet, tamik'e tashiga d'akin, aiko tana dubawa taga wayan shi a gefen gado, bajira komai ba ta d'auka takira number Alhaji Usman,






Bugun farko ya d'auka, yace "ka saketa ne?"




Jamila tace "nice fa,Baby j kece to ya'ya ya sake kine?"


Tace 'a'a, wai ya kukayi ne?Hnmmmm ai kedai bari Baby j niban san menene alak'an yaron nan da d.p.o ba wallahi,






Kina ga yadda d.p.o ya rikice kuwa, daga ganin d'an liti,kuma wai ni Alhaji Usman me gwal, d.p.o yake cemin infita in bar mishi office, kar insa a kore shi, a aiki "








"Wai fa akan d'an liti ze rasa aikin sa kijifa" suna chikin wayan ne jamila taji, an finciko ta d'an liti da fitowan shi kenan daga wanka, yana d'aure da towel, ya had'a ta da bango yamatse ta da jikin shi, sega idon 😳jamila kamar zasu zube k'asa,










Taji matsa ga kuma tsoro, yace "mena gaya miki? ke gaki me kunnen k'ashi ko? To wallahi bazan d'auki iskanci a gidana ba, bazan kafa doka ak'i biba"






Jamila da dak'yar magana nan yafito tace "kayi hak'uri nadai na, ciki b'acin rai d'an liti yace"wallahi daga yau kar ink'ara ganin wayana a hannun ki"








Tace "to", ya wurgata gefe Allah Yya taimake ta bata fad'i ba,










Wai waye adon tafiya!






*ASALIN* *LABARI*










Muje zuwa










Y'ar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*








*BY* *'YAR* *MUTAN* *KAGARA*






*EDIT BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*






*PAGE* *21* */* *22*






🌈 *KAINUWA* *WRITERS* *ASSOCIATION*🌈








Asalin Labari




Malam haruna wani bawan Allah ne, Wanda shi kwata kwata duniya bata dame shi ba, yana da d'alibai da yake k'oyar wa a kofar gidan shi, bayan sallan asuba da magrib ake karatun saboda malam haruna yana zuwa kasuwa.








Yana da shagon sai da kayan masarufi, idan ya koyar da karatu da safe sak ya tafi kasuwa, da yamma in ya dawo da yamma sai ya d'ora ma d'aliban shi kuma, saboda in ya shiga gida bayan sallan isha'i, ba ya fitowa sai asuba k'a'idan malam haruna kenan.








Yana tare da matar sa inna Ramatu da ya'yansu uku, Jamila itace babba sai karima sai autan su Ibrahim.








Malam Haruna yana k'ak'ari wurin k'yauta ta ma iyalan sa, kuma ya tsaya akan karatun yaran shi, shi yake koyar dasu shi yasa su jamila suka haddace alkur'ani.






Da sauran littattafan addini sosai, malam haruna duk da bai yi karatun boko ba, bai hana shi jajircewa wurin ba Ya'yan sa ilimin boko ba, shi da kansa ma yake kai su kafin ya tafi kasuwa.








Makarantan kud'i ya sa su saboda yana son suyi karatu mai zurfi, to a nan ne jamila ta had'u da k'awaye biyu Hadiza Aminu da Maryam Yahya.








A lokacin da suka shiga nursery ne Allah ya hada jinin su tare suke zama, cikin school duk inda zasu to tare zaka gansu.






Har suka shiga aji shida a primary, basu ta'ba fad'a ba ko sa'insa a tsakanin su ba.






iyayen Hadiza da Maryam suna da rufin asiri dan ko abinci dasu ke zuwa da shi kasan gidan su ba laifi.




Jamila kullum cikin kai korafi take wajen malam na cewa su basa kai abinci mai dad'i kuma ba'asa musu naman kaza a cikin abincin su.






Malam da yaji haka, to ranan da abun da Jamila take so zai dawo gida.






Saboda gobe su tafi da shi makaran ta, inna takan ce "malam kafasan halin d'an yau! me yasa kake k'ok'arin yi musu duk abin da suke so ne?






Malam yakan yi murmushi, yace " wato Ramatu hikiman yima yaro abin da ya nuna ya nason, hakan wata hikima ce.






Na k'ara ma yaro k'aimin da naci ne a wurin karatu, saboda kai babba kafin ka aikata abin da yaro yake so, zaka nuna mai cewa ai karatun da yake yi ne yasa ka saya mai ko ka mai.








Shi yasa ki kaga ina biye musu saboda k'okarin da suke dashi, tun fa da suka shiga makaranta boko basu ta'ba cin na biyu ba.






Haka ne malam Allah dai yasa mudace, yace " amin".






Su jamila suna daf da zana jarabawan kammala firamari, Hadiza Aminu tafara rashin lafiya hankalin su Jamila ba k'aramin ta shi yayi ba, lokacin da suka samu labari.








Suna tashi a ranan sai ga baban yazo daukan ta, kafin ta shiga motan ta fara ba babanta labari ciwon k'awar tasu.








Kafin babanta yace wani abu, sai ga malam Haruna shi ma ya tsaya a mashin d'insa, suka gaisa anan ne baban Maryam yake ba malam labarin ciwon Hadiza.










Aiko malam naji yace " su tafi gidan kawai, suka shi ga mota shi kuma malam yadebi karima da ibrahim, saboda jamila tabi motan baban Maryam ne.










Baban Maryam yana yin parking, yafito yace " to ku fito mana kun coge a mota baku zaku mana jagora ba?








Jamila dai takasa hakuri Maryam da har tabude kofa zata fita, Jamila tayi saurin kamo hannun ta Maryam ta juyo tana kallon jamila menene haka ? zan fita kin wani fizgoni kuma kinsa su abba na jiran mu.








Jamila tace " wai kina nufin nan ne gidan su Hadiza Aminu?






Eh mana nan ne.






Me yafaru a'a, bako mai d'an ban ta'ba zuwa bane kawai, OK to fito mu shiga ko da suka fito su kaga hankalin iyayen nasu bai tare dasu maryam taja hannun Jamila suka shige da sauri.








Ko da suka shiga sun samu Hajiyan Hadiza a parlon zaune, Hadiza kuma tana k'wance a k'afan maman ta tana tsula shagwaba, ita kuma maman ta sai faman lallashi take.








Suka gaishi ta da fara'a ta amsa musu tana tambayan su school kun zo gai da k'awa ne?








Su kace eh, a ka cika su da kayan motsa baki da na sha sai da su kayi dam su kaji cikin su ya d'auka, suka tuna iyayen su najiran su a waje.






Sukace "zamu wuce, Hajiya tace to wa yakawo ku?


Su kace "ai baban mu suna waje Hajiya ta rik'e baki πŸ€”ka jimin shak'iyan yara sai Kuka barsu a waje?






Amma dai baku k'yauta ba tana fatan ne tana shiga d'akin baban Hadiza, sau gasu sun fito tare suka gaishe shi ya amsa yana musu dariya.








Ya shigo dasu malam suka gaisa Hadiza tazo ta gaishe su suma sukayi mata ya jiki.




Basu wani d'auki lokaci ba suka tafi, cike da abubuwa kuwa suka tafi maman Hadiza ta had'a musu kayan makeup masu k'yau baban kuma kud'i ya basu.








To daga lokacin Jamila tasa ma ranta itama tunda baban ta ba mai kud'i bane to ita kam ba zata auri talaka ba itama tana son tazama Hajiya.








Masha Allah a yau ne su Jamila aka kammala primary school, sai shirin zuwa gaba da primary.












Muje zuwa










'Yar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*






*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*








*PAGE* *23* */* *24*










🌈 *KAINUWA* *WRITERS* *ASSOCIATION*🌈








Tunda su jamila aka shiga s. s. One tafito da halin ta na k'yaman miji tala k'arara, har fad'ima k'awayen ta take," itafa miji me kud'i take so ta aura, sukuma k'awayen dayake su irin rayuwan jamila sunsaba dashi se bedamun su.








Haka sukaci gaba da karatun su, gashi gaba d'ayan su anaji dasu school d'in,saboda ilimin su,shugaban makaran ta ba k'aramin alfahari yakeyi dasu ba.,








Afanin malam kuwa, ba k'aramin dad'i yakeji ba, akan yadda yarin yarsa tadage tana karatu ba tare da tabashi kunya ba, a kullum yana al fahari da result d'in jamila,








Shi yasa kullum abun da takeso shi yake yimata, kaya kuwa na zamani to ko yarin yan me kud'i sai haka, a bun ba kud'in bane zuciya ce,shi kam malam yatsare ma iyalin shi komai,








Anan ne jamila tasamu daman yin kwalliya yadda take so,










Gata dama Allah ya mata diri mai kyau, ya tsun hannun ta kawai abin kallo ne, saboda zara zara ne, skin d'inta kuwa ko kul'ba se haka, gata fara tas idanuwan ta kuwa har wani d'au kan ido sukeyi,


Tsabar farin su gasu dara dara, gashin idonta yir yir gonin sha'awa, ga suma idan jamila ta warware maka gashin kanta zakasha mamaki, dan har gadon bayan ta,




Na sha nunta kuwa a tsastsa ye suke, tan tsama - tantsa ma kaman zasu faso riga sufito,






Mazau nanta in tana tafiya zaka rantse itace ke karkad'a su, kuma ba haka bane halinta tane,


A haka Allah yabasu sa'a suka kammala secondary school lafiya tare da result me kyau,






A lokacin ne suka fara kula samari, inda hadiza ta had'u da saurayin ta har ya kaisu ga aure, Jamila da maryam kuwa suka samu reshen karatu a federal polytechnic suna karan ta english,








Jamila tahad'u da samari kala kala, amma bata ta'ba sauraran wani ba, saboda Allah yayita da tsoro ita dai tana son me kud'i,amma kuma tsora suke bata,










Suna daf da kammala poly ta had'u da Alhaji Usman se taji ya Kwanta mata, a haka suka shinfid'a soyayyan su mai tsabta,






Ba k'aramin kud'i Alhaji Usman yake kashe ma Jamila ba,har account ya bude mata a U. B. A,








Yana tura mata kud'i, ita" kuwa koda wasa bata ta'ba gigin nuna masu inna da malam kud'in da yake bata ba,






Tun Alhaji Usman na damun ta da zance turowa, har ya shirya rana d'aya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login