Showing 3001 words to 6000 words out of 22202 words

Chapter 2 - Auren kisan wuta Complete Book By Zulaihat Sani Kagara.txt

insha Allah, ai kuwa washe gari dan liti yakira alhaji usman, yagayami shi wurin da zasu hadu,








Yaje yasame shi alhaji Usman yace dan liti, dan Allah alfarma nake nema awajeka, kuma nasan baze ga garekaba, sai dai zaka jishi yamaka girma,








Tunda kai yarone wanda hakan betaba faruwa da kaiba, zanbiya ka konawa ne pls "






Alhaji duk dadai ni yaro ne amma nasan halacci, ka kyautata min, to kaga kuwa har inni dane yaka mata insaka maka duk da babiyanka zanyi ba,








Yanzu kafada min mekake da bukata,










Sonake Ka auri matata!










Dan liti yazare πŸ‘€ yace in me?












Wai fans wata matar alhaji Usman yake nufin dan liti ya aura ne?


Hehehe nimadai πŸ€·β€β™‚πŸ€·β€β™‚










Muje zuwa








Yar mutan Kagara 😎
*AUREN* *KISAN* *WUTA*










*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*










*PAGE* *9* */* *10*










*DADICATED* *TO* *FIRDAUSI* *AMINU*










Alhaji banfa fahimce kaba, yaza ayi in auri matar ka? Aina aka taba yin aure akan aure?






Kuma alhaji kaduba kaduba wannan al amarin, yaza ayin dan yaro dani in auri matar ka! ai takusan haifata koma ta haifan,






Alhaji usman yayi murmushi, duk tamba yoyinka suna kan hanya, kuma kanada gaskiya akan abin da kafada, to nafarko dai matata dana cema inanufin munrabu da itane, nakeson ka aure ta,








Nawani lokaci sai kasake ta tadawo wurina, saboda yanzu tazama harabiya ta inason ne ka halatta min ita,






Saboda Saki uku ne tsakanin mu, kuma dakace zata haifeka, ko kuma takusan haifanka, to ai ba uwar gidana bace, amarya ce "










Kuma ita ina ganin baza tafi irin ashirin da hudu ba,






Dan liti yace inna fahimce ka auren kisan wuta kenan kukeson yi ko?








Alhaji yadafa shi yana mecewa yauwa dan liti, ashe kagane,






Haka nakeso!






Ina fatan zaka bani hadin kai,ba dadewa zakuyi tare ba, kuma nizanyi komai, kuma inbiya ka ,seku zauna daya daga cikin gidajena "










Yayi ko?






Dan liti yanesa yace to wai alhaji, kaman yaushe kuke tunanin za'ayi?




Yauwa yanzu dai ka amince? Badamuwa ai duk yiwa kaine, kuma hakama jahadi ne, yiwa kai ne "






Zan yi insha Allah, Kai nagode nagode dan liti, gaskiya kagama min komai, dama nasan bazan taba shan wahala akan kaba,








Ammafa akwai sharadi !








Dan liti yace to ina sauraran ka, alhaji yace in anyi auren, sati uku zatayi kasake ta, inajin ka alhaji sannan karka kuskura karabar min mata, ko hannunta banyarda karike ba,






Dan liti yace nikam meye matsala ta da πŸ€·β€β™‚da duk abin da kalissafo,


Taimako na fa kuka nema bani nanemi auren ba, balle yabani sha'awa, indan tanine kasa ranka a inwa banida matsala da hakan,








Nidama karake yadawo sati daya alhaji danni takuramin za ayi, har sati uku "








A'a yihakuri dan liti, yakai sati ukun kar jama'a sugane, to shikenan Allah yabamu sa'a, alhaji yace amin,




Yabama dan liti kudi yace yasamu na kashewa, dan liti yayi godiya,






Har sunrabu alhaji usman yashiga motar shi shikuma, dan liti yana tsare abin hawa, alhaji yadanna mishi horn, yadawo yace ai namanta dan liti yaufa saura sati daya ta fita idda,






Yan kazauna cikin shiri, nikuma nanda kwana biyar, zankawo maka kayan da zaka rinka zuwa, wurinta dashi,yace to alhaji, Allah yakaimu yace amin.








Alhaji usman yana zuwa, gida yakira baby j yayi mata bayanin yadda sukayi da dan liti, dafarko bata yarda ba, tace ita bazata iya auren kowa ba inba shiba,








Alhaji usman yahau washe hakora, yaji shifa akeso haka dai yata lallashi har ta amince "








A yau ne jamila tafita idda, a yau dinne dai alhaji usman yashirya ma dan liti, haduwa da baby j.








Karfe takwas na dare, alhaji uaman yayi parking kofar gidan su baby j, yakira ta awaya cewa suna waje shida dan liti "










Dama tayi wankanta taci ado, dama su jamila ba ayi makeup dinba ma ya akakare, balle kuma anyi, tashiga dakin inna dan tafada mata wani yazo nemanta awaje,










Tasameta zaune kan sallaya tana karatun kur'ani, tazauna seda takai aya tashafa, sannan tace inna wanine yake sallam dani awaje, to jamila kuma har yasan yau kika gama idda πŸ€”






Jamila tace eh Inna tawurin maryam yabiyu shiyasa yasan nagama din, to Allah Yasa mudace, tace amin inna kije amma karki dade fa, insha Allah bazan jima ba,








Koda jamila tafito taga batasan alhaji usman da wannan motan ba, tana karasowa, yabude mota yafito ya wani hade rai, yace baby j saboda nace miki wani zezo wurinki ne,shine kikasha makeup haka?






Hnmmmm ni har akwai wanda ya isa inyimai kwalliya, sama da kai, kawai fa dan kacemin tare zakozo ne shiyasa nayi,






πŸ˜„ yauwa baby j tawa, tare fa muke da dan liti din, bazan iya barinshi yazo shi kadai bane, Shiyasa nadauko shi muzo tare ayi hiran tare dani"








Dan bazan iya bari yaro dan yanjini yatsaya min dakeba, zuciya ta zata buga, Jamila tayi murmushi tace karka damu karubuta ka ajiye, Jamila takace.








Waiyo nikaina wlh har kinsa naji wani sanyin dadi a raina, dole inmiki kyauta, bari inmiki transfer yanzu kuwa, take yamata kuwa dubu dari uku, tayi godiya yace to bari inbarki dashi yanzu nasamu kwarin guwiwa,








Tafiya gida, dan liti yafito alhaji yace karfa kadade, kawai basaja ne abun dan dai aganku tare ne, kawai.






Dan liti yace badamu wa insha Allah,




To ga dan liti ga baby j..............










Muje zuwa












Yar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*




*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*




*PAGE* *11* */* *12*










Koda alhaji usman yatafi, yarake subiyu wani irin kalo Jamila takwashe dan liti dashi, tace amma kai kam anyi mayan son kudi, saboda kwadayi abun duniya shiyasa kana yaronka dakai,






Ka abince aure na na sati uku, hnmmmm yanzuma intambaye ka, kasan me akecewa in anje tadi?




Dan liti dayayi tsaye yana kallonta, yagirgiza mata Kai alaman besani ba, tace kaga illan talaka ko ga kwadayi ga dakikanci, dan liti shi dai yazuba mata ido yana kallonta,




Tace to ina jinka bakazo zance bane?




To fadi inajinka, dan liti dai yana tsaye yanade hannunshi a girji, yana mata wani irin kallo , wanda koni yar mutan Kagara, banace nasan fasaran wannan kalon ba"






Haka jamila taci gaba da fada mishi magan ganun duk daya mata dadi, shi dai nashi ido,


Jamila tace kadai san badade wa zanyi ba inmukayi aure ko, yace eh nasani tace nifa sati ukun da alhaji yadiba, yamin yawa gaskiya,




Dame zaka rikeni nasan duk alhaji usman dindai shi zeyima komai, Kai saboda talauci shiyasa kayarda da auren kisan wuta ko?




Dan liti yace a'a kawai dai, alhaji usman ne yanemi alfarma, kuma ya cancacci inmasa ne, shiyasa nayar da,




Suna chin haka saiko ga malam, tai mishi sannu da zuwa, dan liti yaduka har kasa yagai sheshi, ai malam yaji dadi,ya amsa mishi cikin mutunci da jindadin gai suwan da yayi mai,




Sabani wasu samari, basaba iyayen budurwa girmansu, kuma malam farat daya yaji yana son yaro, yakwanta mishi, tana ganin malam yashige tajuya tana shigewa gida, tana cikin tafi ne tace zaka iya tafiya,








Sai wani lokacin shi dai dan liti dakallo yabita, abun ma dariya yaba shi, yajuya yatafi




Dan liti besha wuyaba wurin neman auren, jamila saboda daga malam har inna, Sun yaba da tarbiyan shi da nagarta, ga kuma natsuwa,






Koda malam yanemin dan liti yaturo magaba tansa, dan liti baban abokin sa musa yasama, yafada mishi yadda sukayi da malam,








Malam tanko yace to madalla abu yayi kyau, Allah yasanya alkhairi, dan liti yace amin, dan liti yace ammafa abba bazawara ce, masha Allah, kakoyi koyi da ma'aikin Allah,








Hakan yayi kyau, kuma nizan jagoranci al amarin, zamu je tare da kannaina, insha Allah, dan liti yayi godiya,






Biki dai yakan kama, ansa rana sati biyu masu zuwa, kuma malam tanko baban musa, shine waliyin ango,








Alhaji usman yagama komai yayima jamila setin akwati hankare da kaya, yayima dan liti shima seti goma, na fitan biki,








Yakuma ba dan liti gidan da zasu zauna, chiki da parlon da toilet dakuma kitchen, yakuma chema su malam karsuyi komai, shizeyi mata duk abunda iyaye kema yaransu,








Sukayi godiya.








To ranadai bata karya sai dai uwar diya taji kunya, a yau ne dubban jama'a suka sheda daurin auren dan liti da jamila, akan tsadaki naira dubu goma,




Dubu goman ma alhaji usman ne yace ga dubu goman, yabayar saboda iyayenta sunsan ango beda kudi, wankin mota yakeyi kawai, karsuzo suchiga wani tunane shiyasa yabada dubu goma,






Ankai amarya gidanta, kowa yatafi tunda bazawara ce, koda tarake ita kadai bata damuba, hasalima tafison hakan saboda suna makale da juna da alhaji usman a waya,






Yana kara jadda damata, karta yarda yace zeyi wani abu da ita, ita kuma in yafadi hakan sai taji ranta yabaci,




Tace mishi ita ko mazan sunkare mezatayi da wannan yaron, ai ba abunda ze iya yimata, in tafadi haka shikuma alhaji Usman sai yaji wani sanyi dadi,










Basubar waya ba har taji shigowan dan liti, tace gaba dawayar ta hankalinta kwance,




Shikuma yayi kaman besan meta keyiba, sai da suka gaji dankansu sannan suka hakura,




Ta tashi tashiga toilet tayi wanka ta dauro alwalla, koda tafito humra kawai tashifa tasaka dogowan riga tayi sallah,




Ta idar tanaciki karatu kur'ani taji wanyan dan liti yana ringing a parlon, tagane da alhaji yake wayan, saboda taji yana cewa insha Allah bazan kusanci taba har mucika sati ukun,




Alkawari na dauka, to madala alhaji ka kwantar da hankalin ka ba abunda zefaru,






Haka rayuwa yata tafiya, duk cefanen da dan liti zeyi ahaka zai lalace, jamila bazata girkaba, sai dai tafita tasayo abunda zataci, tunda kullum alhaji usman cikin tura mata kudi yake,




In dare yayikuwa to ka idane dan liti na parlon ita kuma tana uwandaka harda murza key kuwa, kuma duk lokacin da sukaga dama suke wayansu ita da alhaji usman, dan liti betaba daga ido yakallesu ba,






To yau dai jamila taciga sati uku a gidan dan liti, kuma a yau ne alhaji Usman yake cikin farinciki shida baby j dinshi, saboda yau suke tunanin dan liti zesaki jamila !










Tofa πŸ€”


Hnmmmm mudai je zuwa yanzu aka fara πŸ‘








Yar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*




*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*






*PAGE* *13* */* *14*










Tun safe alhaji usman yake kiran dan liti, amma wayansa a kulle, yaje wurin wanki motanshi yayi sau biyar amma kowan lokaci zance daya ake fada mishi, bezoba"




Tundai alhaji usman bedamu ba har yakaiga hankalinshi yatashi, fiye da tunanin mai karatu, inyakira baby j itama zancen daya ne bedawo gidan ba, tunda yafita sallah asuba,




Alhaji usman yacire hulan kanshi yashare zufan daya tsastsafo masa, yayi tagumi πŸ€”to waini me yaron nan yake turamin yine, kodai wani abune yasame shi?






Yakara gwada kiran layin, yananan dai arufe, jamila tana zaune a parlon, tamagaji da kuka tsabar Kuka har idonta yakunbura,, sai kawai taji ana bude kofa ganin dan liti, ne yasa tamike tsaye tahau masifa,




Wai kai dame kake takama ne? Dazakama mutane wulakanci, inbanda wulakanci meye nafita kaki dawowa gida tunsafe, kuma kasan yaune wa'adin zamana a gidanka yazo karshi,








Ai tanemanka a waya ba asamunka, tanayi tana murguda mai baki 😏


Batama lura da irin kallon dayake mata ba, sai zuma masa masifa takeyi, yanadai ta kallonta saida talafa dan kanta tayi shuru, se yabi ta gefenta yashige daki,






Aiko jamila kaman jira takeyi, tamishi dakin tana ruwan bala'i, shidai Komai beceba, tace aidama matsalan talaka kenan, kamai rana shikuma yamaka dare,






Sai girman kai ka iya Kai bakowan kowa ba, bakada ko sisi, mtswww fuuuuuuu tabar dakin takoma parlon, tadauki wayanta kiran iPhone 8 "






Takira alhaji usman yana dauka tafashe mishi da kuka, shikuma yabi yagigice yace meyafaru ne baby j,






Taja majina tace ya yadawo yanzu, ai seyazabura kikace yadawo?


Eh yadawo yanzu nan, yabaki sakin?


A'a be baniba ko magana beminba, amma lallai yaron nan yanason yaja dani, yana inane?




Yana daki, kinsan menake so dake baby j, karki kuskura yaron nan yataba minke pls, haba my man aini takace kaikadai, meze iya yimin, dan yaronnan habadai aini nawuce saninsa,






Dan liti dake daki kwance a kan gado, duk yana jinta, amma kalmanta nakarshe, shiya harzuka shi, yamike har jijiyoyin kansa sunyi rada rada, saboda bacen rai "






Jamila tana cikin wayanta da alhaji usman, taji kaman daga sama an warce wayan, tajuyo a fusace da niyar rashin mutunci, amma ganin yanayin face din dan liti ta tsorata, saboda bata taba ganin shi a haka ba"






Yau yazama mata kaman wani namijin zaki,






Tace meye na ansan min wayana?




Ko kallonta beyiba yabude wayan yacire sim card din yasa a baki yataune, ai jamila naganin haka, tayi chikin shi amma yana juyowa ai setaja burki,






Ya watsar da taunanne sim card din, yajuya zuwa daki Jamila harda saurinta wurin binshi, tanazuwa dakin sai bata ganshiba, taji motsinshi a toilet, tayi saurin shiga dai dai shiganta dai dai yana jefa wayan, chikin ruwa"










Jamila tasa hannu a kai πŸ™†πŸ»






Tace waiyo ni Allah na yajuya yafita, yabar ta nan, tafiddo ido waje 😳






Tabiyo shi parlon wai kai mekake ji dashi ne? Mekake takama dashi ne?




Daga tai mako dama ance inkaga mutun a rana,to ka kara ingiza shi ciki, daga taimako menene mijina beyima ba?




A rayuwa yamaka suntura yabaka kudi, ya baka muhalli, duk wannan bai maba sai kaci amana!






wlh ninafi karfinka inma sokake kataba jikina, wlh jikina yafi karfin yaro karami irin ka, a zabure yamike, yanunata da yatsa, yace idan kikakara cemin Yaro wlh zannuna miki true color na,








Jamila babu abinda take kallo sai kirjin shi, da kezuwa sama yadawo kasa saboda bacin rai,




Nisanki ne?





Yashiga daki ya kwaso kayanshi, jamila kawai ganinshi tayi da kaya, yada face yace ke dasauri ta dako rinannun idanunta, dauko maya finki kibiyo ni,






Tace inbiyo ka ina?




Inazaka kaini karab suka hada ido, setaji bakinta yagaza furta komai, kawai tamike tashiga daki ta dauko mayafinta, da kuma jakan hannu wanda acikine tazuba su ATM card dinta dadai sauran abun bukatunta"








Tafito tasame shi a tsaye yana ganinta, yakama hanyan kofar gida, itama tabishi jamila tana fita taga me adaidaita najiransu, da kallo tabi dan liti,








Shi kuma tagefen ido yake kallonta, yasaka jakanshi aciki yashiga, itadai jamila kallon shi kawai takeyi, beko juyo yakalleta ba, yace inkingama kallon zaki iya shigowa,








Tacinnu baki tace to ni mezan kalla anan, be kalletaba ma balle yasan tana yi,






Tana shiga mai keke napep yaja sukabar wurin, basu tsaya ko ina ba sai wani gida, me adaidaita yayi parking,




Dasauri jamila tajuyo tazuba ma dan liti ido, shima yajuyo yana kallonta!..........














Heheheh chasssssssπŸ’ƒ












Muje zuwa












Takunce dai har kullum yar mutan Kagara πŸ€“
*AUREN* *KISAN* *WUTA*






*BY* *YAR* *MUTAN* *KAGARA*






*PAGE* *15* */* *16*




🌈 *KAINUWA* *WRITERS* *ASSOCIATION*








Yahada rai yakoma kamar betaba dariya ba, yace mekike jira?


Tace insauka inje ina?


Wai ma mekake nufi danine, daba zaka bani takaddana ba, dan liti yasauka yabiya mai adai daita, yasakai yashige chikin gida, Jamila tajuya taga bawasu jama'a sosai, ai dasauri tabishi chiki "




Koda tashiga gidan bataga kowa ba, tabi tsakan gidan da kallo gidane madai dai chi, chiki da parlon da toilet da kuma kitchen, duk a chiki,




Ita kanta jamila gidan yaburgeta, tajima a tsaye tana sakar zuci, can setaga dan liti yafito daga parlon, yawuce ta yaje yarufe kofa, yadawo






har ya wuce ta yadawo inkingama tsayuwar ki kinshigo kirufe kofa, yashige yabarta, Aikuwa kaman yace fara masifa tace dawa Allah yahada ta inba da dan liti ba,






Tafara surfa bala'i tun tana tunanin ze fito har dai tahakura,






Tana nan tsaye taji kaman kafanta ze yarda ita, se kawai taduka wurin ta hau rusan Kuka 😭 mai chin rai,






Dan liti dake parlon har chikin ranshi yake jin kukan, tun yanajin sautin kukanta da karfi har, yafara jinshi kadan kadan, har yaji shuru yadaina jin kukan,




Yafito yaganta ta hada kai da guwiwa, daga gani kasan barcin wahala yadauke ta, ya girgiza kai yakoma har yakai kofan parlon, sai yatuna garin fa akwai sanyi,




Yadawo yadauketa cak, yaji shabal ba nauyi kamar baby, yayi murmushi yace sai siwa ba nauyi, seson girma kaman kembo bedireta ko inaba sai gado,






Har yayi tunani ko yacire mata kaya yasa mata na barci, yace to ma nawa a wanne koda Me zata kwana "






Haka yabarta yakoma parlon yakulle kofa, yacire kayanshi yashiga wanka, koda yafito turare kawai, yasa yasa rigan barci, ya hau gado yaja bargo,






Karfe biyu dan liti yamike, yaje bayi ya dauro alwalla ya hau darduma yafara sallah, jamila tafarka fitsari karfe uku, taga dan liti yana sallah, tayatsina baki 😏




Bata dai cemishi komaiba, tayi dube dubenta taga wani kofa tayi tunanin shine kofan toilet din, ta murda tashiga,


Takama ruwa tafito takoma barcin ta, chikin barci taji kamar ana tadata, tabude ido a hankali, karab kuwa suka hada ido meyene ina barci zakawani sani gaba kana kallo,




Yayi murmushi yace mezan kalla anan, tashi kiyi sallah!




Jamila taciza lips dinta, lallai yaron nan yama rai nani, wato meze kalla a jikina ko tasa hannu tagoge kwallan daya zubu mata,






Bayan ta idar da sallah tabude jakan hannunta taciro kur'ani, tafara karatu, har dan liti yadawo daga masallaci,




Yahau gado yana sauraren zazzakan muryanta, har dai barci yadauke shi, yayi nisa da barci shi, ita kuma jamila lokacin tashafa addu'a,






Tacire hijab kenan setaga wayan dan liti yana haske, kaman kira da har zatashare sai ta duba kan wayan taga anrubuta alhaji usman, tazaro 😳




Dasauri ta dauka, tafashe da kuka tacen bangaren, alhaji usman jiyayi kaman yayi tsuntsu yazo yashake wuyan dan liti, har sai yasakar masa mata,






Tsaya kisaurare ni kina inane?


Ina yakaimin ke?


Naje gidan banganki ba pls baby j kifadamin inda yakaimin ke, karki yarda yacefa ze tabaki,




Tace haba dai my man kaima kasan nafi karfin yaron nan, inada kaman ka meze iya yimin, ai nafi karfinshi, yamin yaro"






Alhaji usman cikin tashin hankali yake mata magana, wai ina yakaimin ke ne?






Ni yaron nan zema ha inci to lallai saina nunamishi waye alhaji usman, besanni bane daga tai mako waini zema bariki,






Talaka dashi dan wanki mota har zeja dani, ni banmasan meyake nufi ba, dan daji dashi da ga gani bemayi ko boko ba,






Talaka dashi zeja dani, inyayi wasa dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login