Showing 21001 words to 24000 words out of 38330 words
Chapter 8 - AUREN WATA TARA Book Complete By Hajara L Sdiq.txt
ta ke amma Zarah na sauraronsu Taji abunda Suke fad'a saida takai daidai Inda takeson tsayawa tukwana ta ninke Alk'uran din Chuchu jira ta ke ta gama daman cewa ta yi"
"Gaskiya momcy kin hadu ta ko ina wlh bantaba Jin kiri'ar karatu mai dad'in wannan ba kina da murya mai zaki Dan Allah Ko zaki dinga yimun k'arin karatu Dan wlh hizif d'ina ko Talatin bankai ba "
"Da murmushi a fuskar Zarah ta ce " me zai hana daughter insha Allahu indai kina so daga yanzu ma saimu fara"
Cikin farinciki Chuchu ta ce "Wow ngd momcy a shirye nake yanzu ma mu fara"
Daga yasin suka fara Dan karatun ya tafi yanda suke so.
Washegari a tare sukaje suka bud'e account Inda ita Chuchu rakiya ce kawai tayi musu.
Tun daga ranar Zarah ta zama Malamar Chuchu kullum rabin shafi take Kara mata kuma sosai take fahimta idan ta bata hadda sai ta d'ora mata wani shakuwa Ce da abokantaka ta k'ara shiga tsakaninsu ta musamman hatta lecture din da bata ganeba wajen Zarah take zaunawa tayi mata bayani"
Sannan yanzu Chuchu ta nutsu ta koyi wasu daga dabi'un Zarah yanzu itama hijab take sanyawa dukda ba Koda yaushe ba da wasu kide kide duk ta rage ji
Zaune yake a garden d'in gidansa ya na shakar daddad'an iskan dake kadawa cike da ni'ima.
lilo din da yake kai ya na jujjuyasa har wani lumshe ido yake zazzak'ar muryarta Take dawo masa a kwalwa hatta karatun da yaji tanayi yaji ya na masa gizau ya rasa ya akayi ba tunda yaji muryar mai karatun nan take dawo masa ba a kwalwa Tsaki ya ja a ransa tare da saurin barin tunanin da yake.
Ya na nan zaune Jabir yazo yayi mamakin yau yanda fuskar abokin nasa a warware "Zaunawa yayi Inda suka shiga d'an hirar Kasuwancinsu"
"MD ne ya ce " Ina son a shiryamun tafiya America gobe "okay Kai d'aya za ashirya maka ko tare da Amera "
Sai sannan MD ya tuna da Amira tsaki yaja saboda haushinta da yakeji tunda ta tafi gidansu bata leko ba ya ce "
"Ni d'aya zaka shiryamun ta na gidansu"
da mamaki jaber ya ce.
"Wai kana nufin tun sanda ta tafi bata dawo ba kusan two weeks lallai Abokina ka na hakuri wlh wai meyasa ba zaka bi shawarar Ammy ba akan ka k'ara Aure Kaga dai na farko Auren nan naka da Amera shekara Tara kenan bata tab'a d'ora girki ba da niyyar wai ta girkawa mijinta abinci ba Sannan ita ba haihuwa ta tab'ayi ba bare ka ce zaka zauna da ita Dan d'iyanta sanin kanka ne kunje Asibiti yafi sau nawa ance matsalar daga gareta ne dukda kana boye mata why zaka zauna mace d'aya ta dinga baka wahala tunda ka Aure ta Banbancinka da gwouro Kad'an ne kana da kudi da komai da zaka mori rayuwarka da su MD kayi tunani"
"Nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce.
" bazaka gane bane Jabir bazan tab'a yiwa Amera kishiya ba Dan bata haihuwa da misalin ace nine bana haihuwar itama haka zata zauna dani sannan har yanzu banga wace macen da zance wai ina da ra ayin aura ba"
Numfasawa yayi saboda doguwar magana da bai saba ba sannan ya ce .
"Amera na da kishi sosai bazata iya zama da kishiya ba sannan ina son matata bazanso abunda zai b'ata mata rai ba hasalima ni a tsarin rayuwata ban tsara auran macen da ta wuce d'aya ba mace d'aya nake da ra'ayin zama da ita kuma Babu saki a tsari na karma ka k'ara zomun da irin wannan maganar"
"Shidai Jabir mamaki yaki barin fuskarsa zai d'aga baki yayi magana MD ya d'aga masa hannu dage kafada yayi tare da tashi Dan takaicin abokin nashi ya zauna mace d'aya na wahalsheshi.
Washe gari MD ya bar k'asar Bayan Yaje yayiwa Ammynsa bankwana ya wuce america.
Amera ko jin shiru mijin nata bai kirataba saida ta gama shiriritarta da yawonta iyayenta ko y'an komai kayi daidai ne cikinsu ba Wanda zaice shirya ki koma gidan mijinki.
kiranshi tayi a waya taji layinshi na k'asar baya shiga Ta na kiran na America taga ya shiga amma baya d'auka sai sannan ta gane ya tafi america kenan .
Aiko cikin rana tsaka ta d'auko akwatin kayanta cikin K'ananan kayan da ke jikinta ta d'ora mayafi tare da fitowa cikin Sauri iyayen da ke palour duk kallonta sukayi dadynta ya ce "
" ina zuwa da tsakar ranar nan my merah"Tana Sauri ta bar palourn ya ce "Dad America na tafi gidan mijina bye saimun dawo " .
ta na gama fad'ar haka tabar palour ta na fita ta kwalawa driver kira cikin Masifa da bala i ta rufeshi da fada akan zai bata mata lokaci shidai hakuri ya dinga bata Dan tun tana gidan ba mutunci garetaba ka tab'ata yanzu kayi ta aikinka Kai tsaye Airport ya wuce da ita.
Koda ta isa America sosai Tasha fama kafin ta shawo kan mijin nata Dan ya nuna mata b'acin ranshi a fili kuma yayi zuciya da jikinta sosai hakan ya dinga damun Amera saida kyal ta samu ta na kuka ya hakura Dan tasan logar mijin nata ba abunda ya tsana sama da kukan mace .
ranar dai amera ta d'an daure ba raki ba komai har Dan kanshi ya rabu da ita ya rasa wani irin mutum ne shi shekara Tara da Aure amma har yanzu baitab'a sanin gamsuwar da maza kecewa sunayi ba a tattare da matan su.
Karatun su Zarah sosai yake gudu Dan yanzu haka harsun fara exam sosai suka maida hankalinsu ga karatunsu Masha Allah sun gama Exams lafiya sai kuma jiran result Inda kowa ya tafi gidansu dominyi Hutu dazasu rabu su Ukku saida sukaji ba dadi Chuchu hada hawaye A haka dai suka rabu akan zasu dinga waya Bayan sunyi musayar number"
Chuchu tunda ta koma sosai Ammy taji dad'in irin shigar data ganta da ita ta hijab sosai taji dad'in sauyawar dabi'un na y'artata Wanda tun farko tasan sakacinta ne .
Tunda Chuchu tazo bata da labari sai na Zarah nan Tabawa Ammy labarin karatun da Zarah ke koya mata yanzu har sunyi hizif Talatin sosai Ammy tayi murnar Haduwar y'artata da mutanen kwarai Itama har cikin ranta taji wannan zarar ta kwanta mata a rai sanyawa tayi ta kira mata ita Aiko cikin Sauri Chuchu ta kira mata ita Zarah na d'auka cikin d'oki Chuchu ta ce.
"Momcy ga Ammy na zakuyi magana" ta fad'a ta na bawa Ammy wayar ".
cikin nutsuwa Zarah ta gaishe da Ammy'inda Ammy ta amsa mata cikin Fara'a tare da yi mata Godiya akan Karatun da take koyawa Chuchu"
cewa tayi" ba komai Ammy Ai anzama d'aya "sosai Ammy taji Zarah ta kwanta a ranta Dukda bata ganta a fili ba Amma a d'abi'unta da yanayin yanda taji muryarta sai taji ta na sha'awar Had'a zuri'a da ita a ranta ta ce "
"inama ina da wani d'an da zai sota Bayan MD da na had'asu da ita Dan tasan MD kam yayi nisa ta ma hakura da masa maganar Karin Aure Dan tasan ba yi ba zaiyi.
A haka har lokacin hutunsu ya k'are suka koma makaranta sai farincikin ganin juna suke nan aka d'ora daga Inda aka tsaya har suka cinye second semister Bayan sun koma wani hutun suna dawowa suka shiga aji biyu
a lokacin ne kuma Hafiz zai tafi karo karatu England ranar da yazo mata bankwana school duk yayi sanyi Kallonshi tayi ta ce .
"ya Hafiz naga duk kayi sanyi" Dagowa yayi tare da kallonta ya ce"kawai tafiyar nan da zanyi sainakejin gabana na fad'uwa kamar bazan dawo na taddaki ba sai nakejin kamar wani Abu zai shiga tsakaninmu ko wani zai raba mu Wanda bazan tab'a iya jurewa hakan ba"
"Cikin tausasa murya Zarah ta ce " ka daina wannan tunanin ya Hafiz babu Wanda ya isa ya shiga tsakaninmu kaid'in ka zamemun wani bangare na jikina kayimun abunda ba kowa yayimun a rayuwa ba ka tsayemun a karatu na ni d'in y'ar halak ce ba butulu ba ya Hafiz bazan tab'a butulce maka ba insha Allahu zaka dawo muyi auranmu ta fad'a ta na rufe fuska"
Sai sannan Hafiz ya sauke ajiyar zuciya Tare da sakin rai sunjima suna Hira kafin yayi mata bankwana cike da kewar juna suka rabu "
Koda ta koma hostel duk tayi sanyi Samun Chuchu tayi ta na cika ta na batsewa tare da Harararta.
"d'an murmushi Zarah tayi ta ce " yau kuma wa ya tab'o mana chuchun yaya"
tana cigaba da turo baki ta ce "Ke ce mana momcy" wara idanu tayi ta ce.
"Ni kuma to me nayi" Wancen mutumin mana da kika tsaya dashi kwata_kwata ba class d'inki bane yanzu asmy ke Cemun wai dashi aka sanya miki Aure kinji yanda Naji wlh kwata_kwata bakuyi match ba momcy ke Matar manya ce Wlh Harna fara kishi Dan da yaya na kika dace ba wancen bak'in ba....βπΏ
_07026166536_
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. π―ββοΈπππ*
1, *MU GANI A ΖASA...*π₯
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ΖWAI..*π₯
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*π₯
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*π
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*π©ββ€οΈβπ¨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huΙu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Ιaya N300
*DOMIN TURA KUΖIN KAI TSAYE*π
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biyaπ
0810 433 5144
Masu tura katin MTNπ
0814 179 9224
Ζ³an Ζasar Niger zasu tura nasu anan.π
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huΙu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Ιaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* π₯π₯π₯ππ©ββ€οΈβπ¨
_*Miss Hajo*_π€πΏ
[8/29, 14:32] β€οΈβ€οΈβ€οΈ: π¨ββ€οΈβπ¨ *AUREN WATA TARA* π¨ββ€οΈβπ¨
```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*
π
ΏοΈ............*19 & 20*
"Bata fuska Zarah tayi Jin shirmen da Chuchu take Dan a shirme ta dauki maganar wata maganar ta kawo musu Dan son barin zancen.
Tunda Hafiz ya tafi kullum cikin waya suke da Zarah tare da video call
Yau Zarah ta tashi da ciwon ciki hakan ya nuna mata zuwan perioud dintane sosai take murkashi akan Gado Dan su Asmy suna lecture Duk ta had'a zufa a haka har suka dawo suka sameta sosai suka shiga tashin hankali musamman Chuchu da batasan da larurar Zarah ba Dan kwanakin baya ciwon ya d'an lafa.
Da damuwa ta ce " subhanallahi me yake damunki momcy"Asmy ce dake mikar da Zarah ta ce perioud dintane yazo mu maza mu kaita Asibiti bari na taro napep "
Da mamaki Chuchu ta ce " Daman haka yake yi mata?
"Eh haka take Asmy ta fad'a tare da saurin fita Dan ta taro napep inda Chuchu ta shiga Jerawa Zarah Sannu.
Asibiti mafi kusa suka nufa Inda Asmy tayiwa Dr d'in bayanin abunda ke damun Zarah allura akayi mata Bayan Bacci ya kwasheta ta na tashi taji da sauki haka suka koma hostel Chuchu dukda tsorata Dan ita duk perioud din da take bata tabajin ciwon ciki ba Saidai taji kasala.
Tundaga lokacin abun Zarah ya k'ara worse a halin yanzu har suma ta ke Asibitin da suke zuwa Dr d'in harya ganesu wani zuwa da sukayi ya cewa Asmy .
"a Gaskiya ko yarinyar nan ta na samun sauki tofa dole sai wani Abu ya shiga tsakanin ta da wani?wara idanu Asmy tayi ta ce.
" What Dr kenan yanzu ba maganin da za a bata"Babu maganin ciwon nan kamar yanda na fad'a hakan ne kawai maganin da zan baku shawara tayi Aure zata daina "
"Ajiyar zuciya Asmy ta sauke ta ce " mungode dr"Ranar sun koma hostel Asmy ta kalli Zarah lokacin ta na kurbar tea ta ce.
"Sis waikinsan me dr ya ce Ko kina daina ciwon cikin nan sai kiyi Aure sainakejin inama saida akayi aurenki da Hafiz kafin ki fara makaranta Dan wlh ciwon nan naki ya fara bani tsoro da safe fa har suma kikayi"
"Cike da damuwa Zarah ta ce " Ni kaina ciwon nan ya na damuna karkiga idan perioud d'ina ya matso irin fad'uwar gaban da nakeji Asmy Aikin gama ya Riga ya gama dole ne nayi hakuri har na k'arasa karatu na Shima ya k'arasa nasa"
Tsaye ya ke waya na K'are a kunnansa daga ka gansa ka San ranshi a matuk'ar b'ace yake tashin hankali k'arara a fuskarsa ya ce.
"what ka na nufin an sanya an kashe Alh sammani?banji me akace daga d'ayan b'angaren ba saiji nayi cikin Sauri ya ce.
" gani nan zuwa k'asar yanzunnan ka sanar da DPO abunda ke faruwa a maza a tari abun da wuri kafin Su gudu a tabbatar an kama su"
Ya na Gama fad'ar haka ya katse kiran Tare kiran PA dinsa ya ce a shirya masa tafiyar gaggawa daga Inda yake tare da Escort dinsa suka wuce Aiport ba tare da ya koma ma gida ba yayi wa Amera bankwana Dan Zuwan emergency ne.
Kasancewar kwazo da dagewa da kuma ilimin addini ya sanya aka bawa Zarah Amera ta makarantar Sauri take sosai Dan zasuje wata musabaqa ta students din makarantu a Polytechnic Kaduna Sosai tayi kyau cikin Zumbuleliyar Hijab d'inta har k'asa mai hannu maroon"
Tare da daura Nik'ab tare da Asmy suka tafi Dan tayi mata rakiya Chuchu ko ta na gida Dan weekend ne kuma yawaici a kd takeyinsa.
Kasancewar a motar makaranta suka tafi cikin k'ank'anin lokaci suka isa Inda aka fara gudanar da Musabaqa ko wasu makarantu har akazo kan makarantar su Zarah Inda Zarah ta wakilcesu cikin muryarta mai dad'in sauraro tare da qiri'arta ta fara karatun da aka tambayeta duk Inda aka janyo saita k'arasa batare da gargadaba ba Kuma zallar tajwid take fitarwa Sosai ta burge mutane da dama dake wajen.
Motocin Escord dinsa Guda goma suka sanya motar da yake ciki tsakiya shi kadai ne a motar sai driver .
sunzo daidai zasu gitta ta poly MD yajiyo karatun muryar da ta kasa barin kwalwarsa cikin Sauri ya cewa "Driver ya tsaya"
tsayawar yayi yayinda sauran motocin ma suka tsaya gabaki d'aya ya mayar da hankalinsa ga zazzak'ar muryarta karatun da yake jiyowa har wani lumshe ido yake Sosai muryar ke shiga ta na ratsa duk wani sassa na jikinsa suna nan tsaye ya na sauraronta muryar da tabbas ya San muryar da yaji ce a lokacin da yake waya da Chuchu.
sosai yaji ya na son cigaba da sauraron karatun daga mamallakiyar wannan zazzakar muryar saida suka kwashe minti Talatin tsaye kafin ta gama karatun sai sannan MD ya dawo hankalinsa.
ji yake kamar ya dawwama cikin sauraron muryar ta Cikin Sauri kuma ya tuno da abunda ya kawosa Umartar driver yayi da yaja su tafi.
Zarah ko Bayan ta gama karatu kabbara kawai ake daga karshe dai ita ta ciyo musu na d'aya Wanda hakan yasa makarantar suka kara alfaharin da ita Dan sannan ne karo na farko a Musabakar makarantu state din da aka fara ciwo musu na d'aya Zarah ta samu kyautoci da dama daga wajen manyan da suka halacci wajen.
Koda za a koma A motar makaranta kin shiga sukayi Dan suna son su biya gidan su chuchu Dan tun d'azu ta ke kiransu akan d'an Allah Ammy tace suzo Mai napep suka Tara Inda sukayi ciniki da shi akan ya kaisu G R A.
Gudu sosai suke shararawa a titi yayinda waya na K'are a kunnansa DPO ne ya ce .
"Ranka ya dad'e sun Kufce mana Yanzu haka Suna Hanyar da kake bi karka yarda su tsere zaka gansu a mashin sun rufe fuska su biyu suka rage sauran sun gudu"
Cikin masifa MD ya Ce "Aikinme kuke har zaku kasa kama k'ananan y'an iskan da basu da aiki sai kashe jinin y'an uwanmu musulmi bil'adama ".
tsaki yaja tare da katse kiran yace driver Kara gudu "Sunzo daidai Wani round about MD ta Cikin glass ya Hango su cikin Sauri ya zage glass din tare da fiddo bindigarsa Ya saitasu ji kake tassss ya harbesu a gefen hannu d'ayanma haka Shi kanshi MD rumtse ido yayi Dan wannan ne karo na farko da ya tab'a harbi a rasuwarsa.
Hakan yayi daidai da isowar su Zarah wajen Akan idonsu Harbin ya afku saida basuga mai Harbin ba Sosai suka rude Zarah ta kankame Asmy tare da fasa Kara Dan iya tsawon rayuwarta bata tab'a ganin irin wannan ba Mutane filis a kasa jina jina akan idonsu aka harbesu.
Ita kanta saida Asmy ta girgiza karkame juna sukayi tare da karanto duk addu'ar da tazo bakinsu dan basu tabajin anyi harbi a gabansu ba lura da hakan mai napep din ya juyo ya ce
"Ku nutsu Wannan abun ba Bak'on Abu bane a Saidai kawai Allah kyauta"
Asmy ce tayi k'arfin halin cewa "da gangan fa aka harbesu suna Tafiyarsu Dan zalinci ,"
girgiza kai napep din yayi ya ce " a Lamarin k'asar nan sai dai addua MD ne a cikin motar kuma ina kallonsa ta cikin glass shi yayi harbin Kunga ko a kudin sa ba abunda aka isa ayi hatta gwamnatin a hannunsu ta ke Saidai hakuri kawai "
MD Zarah ta maimaita a cikin zuciyarta lokaci guda taji wata irin matsanancin tsanar mai sunan a rayuwarta ta tsani mutumin da baisan darajar d'an adam ba bazata tab'a mance da sunan ba mutumin da ya tsaidasu a Zaria da zasuje Banki.
Sosai taji wata irin tsanarsa dukda bata sansa ba a fuska Amma taji a duniya babu mahalukin da ta tsana sama dashi cikin rud'u ta ce "mai Napep juya damu ka maidamu tashar motar Zaria"
Juyasu mai napep din yayi har lokacin Zarah A rude ta ke Har suka isa Tasha Inda suka hau motar Zaria Dan komawa school jikinta bai bar kyarma ba
"Ajiyar zuciya ya sauke daga zaunen da yake tare da maida bindigar ma ajinta a take nan motar y'an sanda suka ido DPO da kanshi ya lek'a ta glass tare da sarawa MD ya ce.
" da ana samun irinka a cikin k'asar nan da an zauna lafiya Allah ya k'ara tsarewa sannan ya k'ara girma yanzu zamu wuce dasu police station ko asibiti bazamu kaisu ba harsai azaba ta ishesu sun fad'a ogansu dake sanyasu wannan aikin".
"Jinjina kai MD yayi tare da cewa " kar ayi Sakaci dasu a matsesu har saisun fad'a ko waye duk bayanin da