Showing 3001 words to 6000 words out of 38330 words

Chapter 2 - AUREN WATA TARA Book Complete By Hajara L Sdiq.txt

27 Dec 2024

2878

d'an tasha Dan uwarki Dan kin samu ma ana sonki Aiko daga yau bazaki k'ara gigin Marin wani ba ya fad'a yana zare belt d'in jikin wandonshi tuni cikin Zarah ya Dori ruwa Dan ba abunda ta tsana irin a tab'a lafiyarta Cikin Sauri Ta maza ta Ruga d'akinta Tare da sanya sakata ta rufe sai huci take.






" Salisu ko tsaye yayi ya na ta banka k'ofar ya ke kamar zai b'allata "Rabi ko shiru tayi Dan abunda yasa bata tanka ba Baba na bandaki tun daga Shigowar Salisu Kasancewar Tattare suka shigo da Zara da ido take masa nuni akan ya bari amma sai dura ashar yake ya na cewa yau sai ya raba Zarah gida biyu .






Baba ne ya fito daga bandaki cikin b'acin rai irin nasu na masu hakuri ya dakawa Salisu tsawa " Juyowa yayi Dan duk iskancinshi yana shakkar Malam saboda mutum ne mai kwarjini Sosai Malam ya shiga F'ada ta Inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sulalewa Salisu yayi ya bar gidan Inda ya koma kan Rabi ya ce.






"Wlh na.k'araga d'an iskan yaron nan ya shigo gidan nan zaki kuka da kanki Marainiyar Allah ku sakata gaba Kuyi ta musguna mata wlh kedai Rabi kiji tsoron haduwarki da ubangiji Dan sanya bak'inciki a cikin zuciyar maraya ba k'aramun Abu bane kina daukarsa wasa hakkin wannan yarinyar kadai ya isa ya hanaki kwanta kabari ko Dan a tunaninki duk abunda kike bansaniba .




"ina sane kuma ki kiyayi irin hukuncin da zan yanke nan gaba Dan Zarah ta fiyemun ke da kowa ma " Tsaki Rabi ta ja tare da Barin wajen ta na gunguni "Girgiza kai Baba yayi tare da Yin alwala Dan ya wuce masallaci ya Tada musu sallah.






Zarah ko ta nan tana hawaye har taji fitar Salisu da yanda Baba yayi musu saitadanji sassauci Amma dukda haka tsoron bud'e d'akin take Dan tasan Rabi duk abunda Baba yayi mata akanta zata huce Ga tana son taje tayi salla ta na tsoro Gashi yau batayi musu girki ba tasan ta bani ta na nan rufe ta kasa fitowa tanajin irin ruwan zagi da masifar da Mama Rabi ke Surfa mata tayi mata banza






sai da kanta taje tayi girki wajen 11 PM tukwana Zarah ta fito tayi alwala tana sanda ta koma daki tare da hade Sallar magriba da isha i tukwana ta nemu waje ta kwanta






Dan Daman batasa ran cin abinci ba tama girka sai Anga dama dama ake bata Ko idan Baba na gidan bare ba ita ta girka ba Cikinta na kukan yunwa a haka har bacci barawo ya kwasheta.






Washegari Tana kwance da Yamma tana bitar karatun Islamiya kasancewar Alhamis ce suna gida taji yaro yayi sallama tare da cewa ana kiran Zarah a waje "




Mama Rabi Ce dake waje ta ja tsaki tare da cewa "kaje kace bata nan " Baba ne da shigowarshi gidan kenan ya kalli yaron ya ce "je kace gata nan"






Fita yaron yayi yayinda Mama Rabi ke cika tana batsewa Kwalawa Zarah kira Baba yayi Bayan ta fito Ya ce "Jeki shirya Ana Kiranki kofar gida"




" to "tace tana kasa da kanta dan bazata iya musu da mahaifinta ba Tare da komawa ciki ta sanyo k'atuwar hijab d'inta Ta fito Mama Rabi na binta da harara Dan tana bakincikin taji ankira Zarah waje zance.




kamar yanda tayi tsammani shidinne sanye cikin wani bakin yadi gashi bak'i ga bakin yadi sai suka saje tsaki taja a ranta tana turo baki harta isa Inda yake tare da ja ta tsaya tana kauda kai .








"Nura ko cikin farinciki ya ce " Yakike masoyiyata Yaudai Ranar ta musamman ce a gareni tunda kika amsa kirana "Wani banzan kallo Zarah ta watsa masa tare da Jan tsaki ta ce "






"Malam idan ka gama zan wuce ina da Aikin da nake "a ah yi hakuri gimbiyar mata kinsan ke din ta musamman ce sai ana lallabaki Dan Allah Zarah ki amshi tayin Soyayyata tsaki Zarah taja ta ce " Inma kana wannan mafarkin Ka daina Dan bana sonka na fad'a maka ba sau d'aya ba basau biyu ba Amma ka nace ayi mutum ba zuciya ta fad'a tana Kara Jan tsaki tare da Juyawa ta shige cikin gidan ta na gunguni.






Baba na ganin shigowarta rai bace ya ce "Lafiya y'ar Amanar Baba waya tab'amunke naga ranki bace " Cikin shagwabarta da tunda aka haife take da ita ta ce .






"Baba Nura ne kuma nace masa yadaina zuwa wajena yak'i dainawa" Girgiza kai Baba yayi tare dayi mata murmushi ya ce "in banda abunki Zahra'u meye aibun Nura yaro mai hankali da sana'arsa da komai "






Zarah ji take kamar tayi kuka ta ce "Ni Baba bana sonshi kuma ni da ba Aure zakamun ba Duka nawa nake" Dariya Baba yayi ya ce "to shikenan y'ar Baba kwantar da hankalinki ai ba a dole a soyayya Yawwa daman zuwan da nayi kauye jiya na sayar da akuyata Dubu sha Biyu Yanzu haka daga wajen malamin naku nake harma nakai kud'in sun bani receipt ya fad'a yana nuna mata receipt din" .






Cikin farinciki Zarah ta d'ago ta ce "Kaii amma nayi farinciki nagode Baba Allah saka da alkhairi ya k'ara budi nagode Nagode"






" Ameen y'ar kirki "ya fad'a yana Mikewa Mama Rabi Ce ta mik'e cikin Masifa ta ce




" Amma dai Malam kasan Irin faman da muke a cikin gidannan kullum cikin cin tuwo Miyar kuka muke Maimakon da kud'in ko y'ar shinkafa ma auno mana Shine zakaje Ka biya asara Har dubu koma akan Saukar da bama ta kirki ba aka bibiya izif biyar bazata kawoshi a ka ba wlh abunda kake Malam ba adalci bane na tabbatar cikin yarana Khairat ko Safiya acire Habiba da Salamatu tunda ba yaranka bane Babu wacce zaka biyawa Har dubu goma idan zasuyi sauka amma ita y'ar gwal din ka lale Naira na dukan Naira har dubu goma ka biya mata".






girgiza kai kawai Baba yayi Dan ba a komai ya fiye mata ba ya ce "Suma cikinsu Wata ta dage tayi saukar taga ko sama da dubu goma idan ban bayarba yaran da kin lalata su islamiyar ma na sanyasu amma ba zuwa suke ba Shine har zakizo kina kushe karatun yarinyar da ta shekara da shekaru tana gangariyar karatu ta gama sauka gashi yanzu har tayi harda Wanda iya tsawon rayuwa baxan iya tuna ince ga ranar da Zarah bataje makaranta ba ince Salamatu da Habiba ba sun girmeta ba cikinsu ba mai izif Biyu cikakke gwarama khairat shine zaki hadata da su wannan Abun da kike za a iya daukarsa a hassada ce "






" Sosai maganganun baba suka b'atawa Rabi Tai masifa ta shiga surfawa Inda ta shiga ba ta nan take fita ba hada kuka wai yayiwa diyanta gori Baba bai kulata ba ya ficewarshi tana ganin fitar Baba ta sauke ruwan masifarta akan Zarah saida tayi mai isarta itadai Zarah bata kula tab'a sai aikinta da ta kama .






suko su Habiba ko akansu ita da da Salamatu suna Chan suna wayar batsarsu da samarinsu Bayan Mama ta gama masifarta daki ta shiga Inda ta samesu kowanne da earpiece suna Waya sai huci take Salamatu ce ta katse wayar tare da cewa.






"kema Mama ki daina tada hankalinki akan komai meye akayi akayi wata banzar Zarah kina da mu " Tsaki Rabi taja ta ce "ba dole na damu kaina ba yarinya duk tazo tana neman muku zarra Kuna nan zaune bakinku primary amma yarinyar nan shegiyar da bala i na da komai Amma saida har ta gama secondry school sannan gashinan har tana hardar alk'ur ani amma ku shaggun ko izif d'aya cikakke bana ce zaku kawoshi ba ga shegen farinjini tsiya yarinyar nan Duk ta na neman ta rikitamun lissafi "






"Habiba ce ta turo baki tare da cewa "kema Mama meye abun damuwa anan har waccen figaggiyar yarinyar y'ar shekara 16 zata dameki sannan da kike maganar Karatu har wani amfani ke gareshi a zamaninnan Mama Me muka nema muka rasa Muma dai daidai gwargwado muna da namu farinjinin tunda manyan yaran da suke zuwa wajenmu da kud'in da ake kashe mana ma kadai ya isa ki gane munyiwa yarinyar Chan zarrah Mama"






"Kullum maganar kenan kuna tare da manyan yara yau a sauke ku a wannan mota gobe a saukeku a waccen amma har yanzu an rasa na aure guda d'aya gaisuwa ma suzo abun ya gagara".




Kwana a tashi ba wuya a wurin Allah a yaune ranar saukar su Zarah Duka daliban makarantar sanye suke da ankon atamfa tare da hijab Blue Sabbi sai tag din shaidar su a wuya manyan malamai sosai aka gayyato a walimar .






Wanda wurin ya cika sosai kowa da d'an uwanshi iyaye da abokan arziki sunzo Zarah na zaune ita da Asmy Dan Mamansu Asmy ma tayi musu ankon kayan A gidansu Babu Wanda yazo Sai Baba Dan tanajinsu khairat da tace ma.zatazo Mama Rabi ta hanata .






Hakan bai dameta ba Dan daman ba buk'atar zuwan nasu take ba Fuskarta rufe take da nikab nan aka shiga kiraye kirayen dalibai Bayan sunyi karatu a basu kyaututtuka har akazo kan sunanta.






*Zarah yusuf*Gaban Zarah saida ya bada daram saboda sosai takejin kunyar ratsa mutanen nan Saida aka k'ara kiran sunanta sau biyu tukwana ta mik'e Shima saida Asmy ta zungureta tana mata Dariya kamar wacce batason ta taka kasa Haka take ratsa wajen Wanda duk Inda ta gitta sai an bita da Kallo dukda kwayar idanunta kadai ake gani fuskarta rufe take bai hana Kyaunta bayyanuwa ba .






a haka harta isa kan step din mik'a mata abun karatu akayi amsa tayi tare da Fara rero qir'a cikin zazzak'ar muryarta Mai dadin sauraro tsakiyar suratun bak'ara take karantawa babu mahalukin dake wajen da zaice karatun Zarah bai ratsa sa ba Mutane har wani lumshe ido suke iyaye da dama sunajin inama y'arsu ce jin irin yanda take fitar da tajwidi.




Baba ko wani farinciki da annashuwa ce yakeji na shigarsa yana Godiya ga Allah da ya mallakamai Zarah a matsayin y'a tayi minti ashirin tana karatu batare da gargadaba tukwana Aka amshi abun maganar tare da yi mata kabbara .






Duka wajen kabbara ya d'auka Inda manya daga cikin bak'i suka mik'e tare da Fara yiwa Zarah kyauta Bayan ta amsa tayi musu Godiya Malam ta mik'awa jinjina mata Malam yayi da hannu Dan daman sunsan Zarah zata fiddasu kunya a taron nan






Bayan nan Aka shiga bada kyautar karramawa ga d'alibai Inda yawaici Duka Zarah ta amshe kyaututtukan saboda duk fagen da akazo ita d'ince saida taci kyauta ukku d'aya ta wacce tafi kowa kokari a ajin ta biyu kuma Wacce bata fashi ,ta Ukku nutsuwa da girmama malamai.






,itama Asmy ta amshi kyauta biyu d'aya ta maida hankali a karatu d'aya kuma ta Rashin makara Bayan nan suma sauran dalibai aka shiga basu nasu kyaututtukan sai around 2:pm aka k'are taro Bayan baki sun tafi Ya rage daga dalibai sai malamai .




nan Malaman suka bawa Zarah kyaututtukan da ta samu duk a emblem ne wasu Ba yanda batayi ba akan malaman su rik'e sukace a a a nata ne Sosai Malaman sukeson Zarah saboda kwazo da kokarinta Tabbas Zarah tabar makarantar zasuyi Babban rashi Dan duk musabaqar da ta tashi da ita ake turawa kuma ita ke ciyo musu na daya.






Bayan sun taho daga Makaranta kai tsaye gidansu Asmy suka nufa a kofar gida Zarah ta tarda Baba Dan ya rigasu tahowa Wajenshi suka nufa Kallonsu yayi ya ce "Allah yayi muku albarka Zarah ked'in y'a ce ta gari da kowani uba zaiyi sha'awar kasancewar ki y'arshi ina matuk'ar alfahari dake Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari mai tausayi da jin k'ai".






murmushi Zarah tayi tanajin dad'in addu'ar Baba ta ce "Ameen Baba nagode mik'a masa kyaututtukan da ta samu tayi " nan ya shiga d'agawa emblem na farko kud'ine tsabarsu dubu Hamsin na biyu kuma turmin atamfa na Ukku alqur'an ne sai sallaya a ciki da charbi"Cikin fara a Baba ya ce........โœ๐Ÿฟ


Ga masu buk'atar a tallata musu hajarsu su tuntub'eni akan number wayata kamar haka 07026166526
Ko masu buk'atar shiga grp sharhi ko tambaya hanya a bude take


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*




1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300


*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡


0810 433 5144


Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡


0814 179 9224


ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ








_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/21, 15:53] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ’‘ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


MALLAKAR


*Hajara L Sadeq*






๐Ÿ…ฟ๏ธ.........*5 & 6*


"Masha Allah natayaki murna y'ata Allah sanyawa karatunku albarka "




Ameen suka fad'a ita da asmy Mik'a mata kyaututtukan Baba yayi da niyar ta amsa.




"girgiza kai tayi ta ce " a a a Baba banason komai a ciki komai na sama na sameshine ta dalilin tarbiya da jajircewar da kayi a gareni ".




girgiza mata kai yayi ya ce " na sani Zarah ta amma Bazan amsar miki Komai ba nasan kina da buk'atar abubuwa da dama bakya tambayata Dan haka ki biya bukatunki dasu .






"Girgiza kai tayi ta ce " a a Baba wlh bana buk'atar komai kafini bukatarsu Dan Allah ka amsa ".




Duk yanda Zarah tayi Baba ya amsa kin amsa yayi saida Asmy tasa baki dak'yal ya Anshi Dubu ashirin Inda ya mik'awa Asma'u sauran kudin ya ce "




"Amshi ku tafi Sannan ya kalli Asmy ya ce "kiyiwa mamanki Godiya kice nagode Allah ya saka da alkhairi Tabbas Saratu ta cika y'ar mutunci kuma ta cika Alkawarin aminiyarta mariganyiya Kinga yarinyar nan saboda kawaici bata fad'amun akwai maganar Anko ba Allah sarki ashe har tayi muku saida safe take fad'amun angode Allah bada lada".






Murmushi Asmy tayi ta ce "To Baba " Barwa Baba sallayar sukayi tare da Qur'an din Inda suka koma gidan su Asmy sai tayasu murna ake nan y'an uwa da abokan arziki suka shiga shigowa tayasu murna da Yamma suma sukayi y'ar k'aramar walimar su Wanda mamansu Asmy ce ta shirya hakan.




Bayan magriba isha'i Asmy ta kalli Zarah ta ce "Wai kudinnan sis me za ayi miki dasu" ki bawa Mama kawai ni ba abunda zanyi dasu"Mama ce dake jinsu ta ce "Har ance babu abunda za a yi da kudi Zarah zandai Aje miki " .




Girgiza kai Zarah tayi ta ce "Mama Dan Allah ki rik'e wlh babu abunda zanyi dasu ke ai tamkar uwa kike a gareni Dan Allah Mama ki rike " .






girgiza kai Mama tayi ta ce "a a fa Zarah Aje miki kawai zanyi karki k'ara cewa wani Abu "




shiru Zarah tayi badan taso ba Dan a abunda maman asmy take mata ko jininta ce ita sai haka .




"Asmy ce ta ce " Mama babansu zarah yace nayi maki Godiya "girgiza kai tayi ta ce "




" Ai Tsakani na dasu ba Godiya Komai nayiwa Zarah Ban fad'i ba irin zaman mutuncin da mukayi da mariganyiya da amintar da mukayi a lokacin bamu da hali amma Matar nan bata ci banci ba akwai lokacin da saimun kwanta bacci haka zata buga mana gida na bud'e naga abinci ne ta kawomun a lokacin muna cikin wani hali da haka zamu kwana bamuci ba muna halin Rashin babu Amma Matar nan bata tab'a cin Abu Bancishi ba Munyi zama na amana da mutunci da mahaifiyar Yarinyar nan ".






Goge hawayenta tayi ta ce Har yau idan ina tuno da zahara'u bazan daina kukan rashinta ba mace mai kirki hakuri da juriya Allah dai ya jikanta yasa ta huta".




Sosai sukayi sanyi Cikin k'asa da murya Zarah ta ce Ameen ganin ta na shirin yin kuka ne ya sanya Mama barin maganar tare da kama musu hirar duniya Har ta samu ta d'an warware




Bayan sunci abinci Cire kayanta Zarah tayi tare da sanya rigar baccin Asmy Dan daman nan gidan take Aje sabbin kayanta saboda su Habiba suke lalata mata su sanye mata kuma bata isa tayi magana ba hakan yasa take ajewa gidansu Asmy .






nan gidan kawai take samun walwala da farinciki Sai wajen 10pm ta wuce gidansu har bakin kofar gidan Asmy ta rakata tukwana ta Koma Zarah koda ta shiga Zaune ta tarar da Mama Rabi na girgiza k'afa tana ganinta ta taso tare da Wanke da Mari Dan da bakincikin kyaututtukan da akace Zarah ta samu ta yini hakan ya sanyata huce haushinta na dalili marar ma ana da tushe nan tahau dukanta tana bala i tana cewa .






"Y'ar iska tun safe rabonki da gidan nan Sanadin mutane su dinga zagina suna kin lalace a hannu na Bayan duk yanda zanyi inayi iya kokari na Amma kullum baki da aiki sai jamun Zagi cikin unguwa Itakuma saratun in gidanta zaki koma saitazo ta daukeki Dan kazar kazarta kuma daga yau bazaki kara fita ba daga gidan bare ki fake da islamiya na kara ganinki gidan saratu wlh duk tsiyar da na shuka maki ke kikaja shine kikayi zaune gidanta yau babu aikin da kikamun uban wani kike tunanin zai maki aikin gidan Dan matacciyar uwarki " .






Zarah kuka take sosai ta durkushe tana bawa Mama hakuri anma bata Rabu da itaba da hannu take jibgarta Baba ne ya shigo tun a soro yaji kukan y'ar lelen nashi .




cikin b'acin rai Baba ya shigo Tare da wanke Mama Rabi da Mari cikin b'acin ran da idan kaga yayishi tofa rai ya b'aci ya ce "Duk iskancin da kike kikaga ina kyaleki ba tsoronki nake ba Rabi gudun tashin hankali ne me marainiyar Allah tayi miki da Zaki hauta da duka daman an fad'amun irin zalincin da kikewa yarinyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login