Showing 18001 words to 21000 words out of 38330 words
Chapter 7 - AUREN WATA TARA Book Complete By Hajara L Sdiq.txt
zama Malama Zarah " Dagowa tayi tare da Kallonshi class mate d'insu ne amma tayi mamakin yanda yasan sunanta "
"Matsa masa tayi tare da cewa zaka iya zama mana" Bayan ya zauna Har lokacin karatunta take "cike da burgewa ya ce
" Gaskiya Malama Zarah kin burgeni wlh Tunda kika shigo makarantar nan na lura da kwazo da nutsuwarki Da yawan dalibai ba karatu ke.kawosu ba makaranta amma ke yanda kike dagewa yasanya nayi sha'awar Ko zakiyi abota dani Dan nima na k'aru saboda course d'inmu d'aya kuma math tana bani wahala sosai "
Murmushi Zarah tayi masa tare da kallonta ta lura yana da nutsuwa daga ganinsa kasan d'an Babban gidane ta ce "Badamuwa Allah sa mu karu da juna Saidai bansan sunan malamin nawa ba "
Cikin barkwanci ya ce "Ah dalibinki dai ai kece malamar sunana Yusuf muna zaune a garin Abuja tare da iyaye na karatu ya kawoni Zaria bansan kowaba"
"Ah kace Babana ne Saidai na kiraka da Baba " Dariya Yusuf yayi ya ce "Wow kice da y'ata nake tare Gaskiya nayi sa'ar haihuwar wannan santaleliyar d'iya Kinga dole ayimun biyayya Sannan Abban na zaki dinga Cemun ba Baba ba "
Duk yanda Zarah taso ta fusge saida ya sanyata Dariya ta ce "Eh Gaskiya ne Abba na Amma naga Abban nawa akwai iyayi da surutu fa "
Dariya yayi tare da bude book dinsa ya ce "Wlh daughter karatun da akayi yau kwata kwata bangane ba idan kin gane ki koyamun please"
“bari na duba naga ko zan iya ta fad'a ta na amsa tare da Fara gwada masa dalla_dalla kamar ita ce lecturar sosai Yusuf ya gane fiye da yanda Malam ma ya koya a aji shi kanshi ya sake da baiwar kokari irin na Zarah gashi dai tare aka koya musu amma saika rantse malamin ma a Wajenta ya koya.
Saida ta gama koya masa komai "wow amma daughter nagode Wlh daga yau kinzama malamata ki godewa Allah yayi miki baiwar da ba kowa ya sameta ba Kyau Ilimi tarbiya uwa uba addini "
"Muje dai yanzu class za a shiga wata lectures ba surutun ba Abba na" ta fad'a tana Mikewa Shima Mikewa yayi yana Dariya tare da Amsar jakar dake hannunta "wara idanu tayi ta ce .
" so kake ace y'a ta sanya uba rik'e jaka ai sai a sanyamu a news "Shima dariyar yayi tare da amsar jakar ya ce " Kinga sai muyi suna yanda za ayi ta zancenmu muzama cele".
Har suka isa Class din suna Hirar barkwanci duk miskilancin Zarah har mamaki nayi yanda ta sakarwa Yusuf kodan ance Gamon jini daban yake.
Da suka gama lecture ma tare suka fito Inda sukaje capteria sukaci abinci kafin Zarah ta wuce hostel Bayan ya amshi numberta.
Shakuwa ce da abokantaka ta shiga tsakanin Zarah da Yusuf yazama closed fried d'inta Asmy har mamaki ta ke yanda Zarah ta sakarwa Yusuf fuska duk sanda bai gane wani Abu ba ita take zaunawa ta fahimtar dashi sosai yake amfanuwa da Zarah.
Cikin sati guda da Fara lecture a makarantar har amfara sanin Zarah saboda kokarinta Inda tayi wasu kawaye su biyu hibba da Jamila suma yabawa da tarbiyarsu ta sanya Zarah fara abuta dasu amma fa ba wai Chan ba saboda Har yanzu miskilancin ta ya na nan na Rashin son magana idan y'an maganar sukazo saikayi mamakin yanda take magana .
A yanzu Hankalinta kwance yake Hartama fara mancewa da su Mama Rabi Saidai tunanin babanta da take.
Suna waya da Hafiz Ya ce "Dear wai bazakije ku bud'e account ba Yaci ace kun bud'e ko Dan saboda scholarship sannan idan za ayi muku aike fa account yafi sauki akan Sai an Aiko muku"
"A rufda cikin da take a kwance ta ce " To ya Hafiz Insha Allahu gobe Monday sai muje mu bud'e ko"
"Yawwa matas Shiyasa nake sonki gobe kuje ku bud'e Ki bud'e a access "
"To ta fad'a tare da cewa gashi ba musan ko ina ba bamu tab'a fita ba "
"Ina abokin naki da kike bani labari Abba ko to shi zai iya sani kice ya rakaki "
"To " ta fad'a sun tab'a Hira Kad'an kafin ta kashe wayar a yanzu Hafiz ya Riga ya fara zama wani bangare na jikinta tun bata sonshi yanzu har taji ta fara sonshi saboda soyayya da kulawa da yake nuna mata.
Washegari Bayan fitowarsu daga lecture suka shirya Fita domin Suje su bud'e account around 1 suka tafi Yusuf yayi musu rakiya Napep suka hau su Ukku Inda shi Yusuf ya hau gaba.
Nan napep d'insu ta fara tafiya Yusuf ne ya jiyo cikin barkwanci ya ce "Daugher Kinga kuwa Yanda kikayi kyau na jima banga macen da hijab ke yiwa kyau kamarki ba ked'in ta musamman ce fa "
"Dariya tayi tare da cewa " baka rabo da barkwanci Abba na Kana uba amma ka maida y'ar jikarka"
"Y'ar Dariya yayi ya ce " Ai Gaskiya Ce dole a fad'a y'artawa ta daban ce Shiyasa idan na tashi Aurar da ita mutum na daban zan aurawa saboda ked'in Matar manya ce ba yara ba wlh daughter "
"Murmushi tayi tare da girgiza kai ta ce " kadai kalli gabanka karka fad'i kaja mana "
Bayan Asmy ta gama waya Ta ce "Ai Gaskiya ka fad'a ko Abbanmu"Dariya yayi tare da cewa " Eh mana Bestynmu "nan suka cigaba da hirarsu su Ukku yawaici duk ta barkwanci ce.
Sunzo daidai round din da zasubi ya kaisu Banki Sukaji mai napep d'in ya tsaya " Abun hankalinsu duk yana dumin da suke "Asmy ta ce Lafiya Malam yanaga ka tsaya"
Mai napep d'in ya ce "Kuyi hakuri Hajiya Inajin wani Babban mutum ne zai wuce a wajen shiyasa chunkoso yayi yawa sai motocinsu sun gama wucewa tukwana a bamu hanya".
Cikin jin Haushi Zarah ta ce " Yanzu haka zamuyi ta tsayuwa a titi saboda kawai wani zai wuce dan fin arziki za a tsaida mu".
"Kuyi hakuri Hajiya ya muka iya " Daidai lokacin da wulfa_wulfam motocin suka fara gittawa ta wajen "Kallon motocin da tunda uwarta ta haifeta Bata tab'a gani ba Asmy ta gani wara idanu tayi tare da cewa " Kan uban Chan waiko shugaban k'asane ya shigo garin?
Yusuf ne dake gaba ya ce "Kan ube Wlh MD ne ya shigo garin nan Chab dole a tsaida mutane Innalillahi inama zan gansa ido da ido MD a Zaria to me ya kawosa"
"Zarah ce ta ja tsaki Ta ce " Shi waye da za ace sabodashi za a tsaida mutane saboda shi yanzu fa Banki suna gab da tashi ta fad'a ta na duba Agogon hannunta "
"Yusuf ya jiwo ya ce "
"Wai kina nufin bakisan MD ba kina Nigeria Amma baki Kallon Television da labarai ko? "
Tab'e zarah tayi ta ce "nidai ban wani sansa ba Asmy ma ta ce nima kam "
Yusuf sarkin bada labari juyowa yayi yare da cewa aiko yau zan baku labarinshi saboda ni fans dinsa ne ina karanta tarihinshi sosai".
wani shahararren matashin mai kud'i ne iyayenshi suna zaune a garin Kaduna Mahaifiyarshi asalinta y'ar India ce a Chan mahaifinshi ya ganta ya auro ta shiyasa da kin gansa zakiga asalin ba indiye kannansa biyu mata sosai yake sonsu da ji dasu na manta sunansu , Compononyn da gayen nan ya mallaka nan Nigeria da ma k'asashen k'etare da kadarori gidajen mai kudade na ban mamaki ke kanki saikinyi mamaki gashi matashi Dan bazai wuce 38 years ba Amma wlh Inajin gayen nan shi yazo na biyu a kudi a negeria su kansu manyan durkusa masa suke Dan wasu Mahaukatan kud'ine ke garesa duk wajen Da kikaje kikaga an rubuta MD to mallakinsa ne wajen Shopping mall ko da park_park babu jahar da baya dasu a wannan k'asar tamu Ga shi ya had'u Iya had'uwa y'an mata da dama karkiga yanda suke rudewa a kansa Kwanaki a labarai da nagani Wata tana shirin kashe kanta saboda iyayenta zasu aura mata wani Dan uwanta shegiyar yarinyar nan wai MD takeson mutumin da baisan da zaman ta ba Mutum ne mai matuk'ar ji da kansa d'an gayu ne na Bugawa a jarida miskili ne na karshe Dan Ance a waje saiya yini baiyiwa mutane magana ba Amma ance yana magana da family dinsa sosai nidai tunda nake bantaba ga dariyar MD ba a hotunan da nake gani nasa Dan bantaba ganinsa ido da ido ba yana da manyan company a Abuja Amma ance mafi yawan harkokinsa a America ya ke yinsu yanzu haka a Chan yake da zama Saidai Naji ance Allah yayiwa mahaifinshi rasuwa shekaruun baya sosai Wanda ake zargin kashesa akayi to kunji takaitaccen Tarihin MD matashi da kudi Wannan shine kirarinsa".
Tunda ya fara maganar Zarah take Jan tsaki Inda yana gamawa ta kuma Jan wani tsakin tare da cewa "To waya tambayeka Tarihinsa ina ruwanmu dashi ka zauna sai zuba kake mana akan wani chan banza "
wara idanu Yusuf yayi ya ce "MD dinne banza Zarah"
Tsaki taja Dan sosai takejin zafin tsayuwar nan tasu ta ce.
"To me zankirashi dashi Bayan ya tsaida mu a titi yanzu haka Ina tunanin Banki sun tashi"
ta fad'a ta na Jan tsaki tare da kauda kai tanajin haushin wannan banzan MD din da aka fad'a Wanda ya tsaida su kusan Awa guda a titi"
"Chab ba ruwana wlh security dinsa suka jiki Saidai kiji ina cewa A mota muka hadu "
"Asmy ce ta kwashe da Dariya tare da cewa " lallai Abbanmu kace duk uba da d'iyar da ake ajesa za ayi"
"Chab ina ake ta uba idan ta fito lafiya sai acigaba da ubantakan"
"Dariya Asmy tayi ta ce " Kaidai anyi matsoraci wlh nima saida ka fad'a na tuna da shopping mall d'insa da na tab'a gani a kano sannan a funtua ma ai akwai gidajen mansa har biyu Saida ka fad'a nagesu"
"Chab ai yana da Mahaukatan gidajen mai kalli Chan ya fad'a yana nuna mata wani had'adden gidan mai sabo mai d'aukar kai Ashirin Ya ce " Karanta Chan ma me aka rubuta wancen ma nasa ne"dagawa Asmy tayi ta Kalla ta ce "Aikuwa wlh amma dai nima nayi mamakin Mahaukatan kudin matashin nan ya na da mata amma?
" Wara hannu Yusuf yayi ya ce "wannanne dai bansaniba Anya ya rasa mata ma kuwa Amma dai ko wacece Matar zatasha miskilanci"
Dariya asmy tayi ta ce "Gaskiya kam " sai sannan motocin MD suka gama wucewa Mai napep d'insu ya tada suka isa Zarah ta cika tayi Fam Asmy na mata Dariya ta ce.
"Ran manya ya b'aci ayi hakuri ya muka iya k'asar nan Indai kai talaka ne Ai saida kayi hakuri"
"koda suka isa Banki harsun tashi sosai Zarah ta k'ara k'uluwa tana tsinewa wannan shegen MD din da ya tsaidasu ji take kamar ta kurma ihu Dan Haushi
Wata napep din suka Tara tare da komawa Zarah sai cika take batsewa Dan taji haushin b'ata lokaci ta da sukayi a banza a hofi.
Dan ita tana daraja lokaci da ace tsawon lokacin da suka 'bata a tsaye da ko karatu ta tsaya tayi bata amfana ba.
saida suka tsaya kasuwa sukayi sayayyar kayan miya da Abubuwan da zasu buk'ata Dan karsuyi fitowar banza sune basu koma makaranta ba sai wajen magriba .
Koda isarsu makaranta sosai sukayi mamakin chinchirindon student wasu ana wawwatsewa ita dai Zarah bata tsaya ma kallonsu ba .
Cikin jin Haushi ta isa hostel d'insu Asmy na mata fad'an akan ita da ta sani da hakuri yanzu kuma itace take mita akan Abunda baikai ya kawoba Ta ce " gobe ba saimuje mu bud'e ba Tunda safe ba"
"Zarah bata kula taba saboda ita kanta batasan ya akayi ba takejin haushin b'ata lokacin da sukayi suna isa hostel sunyi mamaki ganin bak'in kaya a Bangaren da ba kowa Uban jibgin kaya akwatuna kamar Lefe banda uban provison Kallon juna sukayi da mamaki Asmy ta ce " to fa ko bakuwa muka samu a d'akin namu '".
Basu k'arasa magana ba sukaji shigowarta dukansu Juyawa sukayi tare da Kallon matashiyar budurwar da baza wuce sa'anninsuba sanye da Doguwar Riga mai shegen tsada da kyau sai fara'a take sosai daga ganinta kasan tana da tsananin fara'a Murmushi ta sakar musu tare da karasa shigowa d'akin saurin fusgewa sukayi da Kallon da suke mata suka zauna bakin gadon su suna huta gajiyar da suka kwaso cikin girmamawa ta ce sannunku ko kune Wanda muke d'aki d'aya"......✍🏿
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[8/29, 14:32] ❤️❤️❤️: 👨❤️👨 *AUREN WATA TARA* 👨❤️👨
```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*
🅿️............*17 & 18*
Murmushin suka mayar mata Asmy ta ce "Eh mune Sannu da zuwa" Yawwa Chuchu ta fad'a tare da cewa.
"suna na Maryam Dikko ana cemun Chuchu ko kuma ku kirani da chuchun yaya dan nafison a kirani da haka kufa".
"Ni suna nan Asma'u ana Cemun Asmy ita kuma wannan " Zarah y'ar uwata ce"Asmy ta fad'a ta na nuna Zarah
"Wow nice name Sunan Ammy na ne Fatima Zarah" Saidai na kirata da momcy "Chuchu ta fad'a cikin iyayinta da ya zame mata jiki.
" Murmushin da batayi niya ba Zarah ta sakar mata tare da cire hijab Dan taje tayi sallah "Asmy ta ce " Wow kice ke y'ar gata ce Gaki ga mom d'inki"
"Ah sosai ma a gatana nazo school d'innan Saidai naga momcyn nawa kamar batason magana dani?
"An d'an bata mata rai ne shiyasa " cewar Asmy Zarah ko Smile ta sakar mata tare da cewa"Ba haka bane Daughter Ykk anzo lafiya "
"Alhmdllh momcy sorry ko Naji ance an bata maki rai ko waye dai Wanda ko wacce ta bata miki ran nan bata kyauta ba gsky kiyi hakuri ko"
"Dariyar da bata shirya ba Zarah tayi Dan ta lura akwaita da surutu ta ce " shikenan na hakura daughter sunci arzikinki"
"Wayar Chuchu ce ta yi ringing Cikin Sauri ta d'aga kiran Ganin ammynta ce ya sanyata " murna ta ce.
"Hello my Ammy na " Daga bangaren Ammy ta ce "Na am Autar Ammy kinganni nan daga tafiyarki har na fara kewa"
"Dariya Chuchu tayi tare da cewa" Wayyo Ammy na tun ba Aje ko ina ba har kin fara missing Nima da banjima ba Amma kadaicinki duk ya isheni "ta fad'a ta na turo baki.
Sun tab'a Hira da Ammy cikin so da k'aunar juna Daga nan kuma ta kira Yayanta Bayan ya d'auka ta ce " yaya Ya hanya kunkoma lfy"
"Alhmdllh ya fad'a tare da cewa " ki tsaya kiyi karatun kirki karki sake na kamaki da matsala na sanya a sa miki ido sosai banda biyewa kawayen banza da samarin banza na sameki da haka cireki zanyi"
"toh yaya bazanyi ko d'aya ba daga ciki "
Shima sun tab'a Hira tukwana ta kashe.
Washe gari tare da Asmy suka wuce lectures saboda course d'insu d'aya itakuma Zarah ta tsaya tayi musu girki saboda sai 10 take da lectures.
Cikin k'ank'anin lokaci Su Asmy suka saba da Chuchu Wanda duk ita Chuchu din take shishige musu ita dai tunda taga Zarah taji ta kwanta mata a rai.
Itama Zarah din Chuchu ta kwanta mata a rai Saidai Abunda ke bata Haushi game da ita irin shigar da take kullum da k'aramun gyle bata tab'a ganinta da hijab ba sannan bata tab'a ganin ta dauki Alquran da sunan wai tayi karatu kullum cikin jin kid'a take ta lura yarinyar sangartattace ta Bugawa a jarida Saidai Inda take burge ta ta na da kamun kai sosai.
Sosai y'an mata keson abokantaka da Chuchu saboda lokacin da MD ya kawota sunsan Kanwarsa ce ta bangarenta ko bata kula kowa saboda ita daman haka take bata fiya mu amula da mutane ba sai Wanda jininsu ya zo d'aya.
Da Yamma suna zaune a Harabar hostel din suna shan daddad'an iskan dake kadawa Yayinda Alquran ke hannun Zarah cikin zazzak'ar muryarta Mai dadin sauraro ta ke rerawa ".
" Chuchu ce dake sauraronta sosai ta burgeta yanda take zuba kiri'a shiru tayi ta na sauraronta wayarta ce Tayi ringing saurin dubawa tayi ta ga yaya MD aiko cikin farinciki ta daga tare da cewa.
"Yaya na I really miss you so much yaya " Daga bangaren MD yaja numfashi tare da cewa "miss you too chuchun yaya Ya kike ya school d'in kina dai maida hankali kuma ba wata matsala ba abunda kike bukata"
"alhmdllh yaya na ba wata matsala kuma ina maida hankali sosai " good girl haka nakesonji wani karatu nake ji daga gefenki ko?
"Eh yaya momcy ce Ke yin karatu sunan Ammy gareta yaya karka ganta ta had'u da kyau Ga Ilimi Ko na baka ku gaisa" Tsaki yaja daga bangarensa tare da cewa "kin fara rainani ko ni zaki cewa zaki bawa wata mu gaisa " yana gama fad'ar haka ya kashe wayar .
Chuchu ko Dariya tayi ta ce "Allah barmun kai yaya na " Asmy ce ta ce "Na lura dai kina ji da wannan Yayan naki sosai fa"
"Kamar mai jira Chuchu ta gyara zama tare da cewa .
" kaiii ai fin sosai ma ina son yaya sosai shidin ba matsayin yaya kadai yake a wajena ba shi din uba ne ya na sona da kaunata sosai nima ina sonshi sosai matsayi biyu yake a wajena yaya kuma uba Dan tun wata na biyu a ciki mahaifina ya rasu bansansa ba yaya na kadai ya mayemun gurbinshi shidin na musamman ne a cikin mutane"
"Allahsrk Allah ya jikan Baba ya mishi Rahama Gaskiya dole kiso Yayan nan naki da yawa Allah ya k'ara had'a kanku" Cewar Asmy "
"amen Chuchu ta amsa ta na cigaba da sauraron karatun Zarah"
Dukda karatu