Showing 9001 words to 12000 words out of 38330 words

Chapter 4 - AUREN WATA TARA Book Complete By Hajara L Sdiq.txt

27 Dec 2024

2887

Hafiz badan ranshi ya soba ya juya.




Zarah na d'akinta ta na karatu taji Asmy ta Banko k'ofar batayi aune ba saiji tayi ta Rungumeta cikin farinciki ta ce "Sis ki tayamu murna ina applying da Mukayi a wayar Mama kwanaki na A B U zaria to yanzunnan sukayo message sun amshemu sannan daman kinga ita ce first choice dinmu s jamb Ranar Monday ma zamuje muyi PUMB kai sis Kinga farincikin da nake ciki"




"Wow Zarah ta fad'a ta ce " Gaskiya ni kaina nayi farinciki Sai kuma tayi sanyi ta ce "Sis nadai tayaki murna ammani kinsan bamu da halin da zantafi wata makarantar gaba primary da secondry dinma a yaya na yita ina da burin karatu mai zurfi amma dole na hakura saboda karatun yanxu na masu da shi ne "






Lokaci guda asmy ta hade rai Tare da cewa "Insha Allah tare zamu tafi yanda muka fara tun daga pri tare haka zamu cigaba har university ai idan babuke nima wlh Saidai na hakura da makarantar kuma bari naje nayiwa Baba Bayani "




sakin firar Zarah tayi ta Kama wata sun jima suna Hira kafin Asmy ta tafi.




Babansu Asmy ya samu Baba da maganar makarantar da su Zarah suka samu Inda Baba ya nuna masa baida ra'ayin tura Zarah karatun gaba Aure yake da burin yi mata tayi a gidan mijin ta "




shi kanshi babansu asmy baiji dadiba ace yanda yarinyar nan take da tsabar kokari da baiwa Ta tsaya iya sec Dan shi kanshi yasan Asma'u ma Zarah ta taka rawar gani sosai a rayuwarta Dan yasan ba wani kokarin kirki gareta ba Amma tare da Zarah ya sanya itama take dagewa take kokari saboda kunsan ance shi abokin mai sayar da turare Shima kullum cikin k'amshi yake gashi yarinyar ya yaba da tarbiyarta 100%yasan ko makarantar suka tafi baida shakka a kansu saboda bazata bari Asmy tayi wani abun da bai kamata ba.




Koda yaje ya fad'awa Mama yanda sukayi da baban Zarah itama bataji dad'i ba Asmy ko hada kukanta nan ta tubure ta ce itama ta fasa zuwa makarantar.




gidansu Zarah taje tayi ta mata kuka akan dan Allah ta lallaba Baba ya barta sutafi tare idan kuma ba haka ba Itama ta hakura da karatun itama Zarah saida tayi hawayen d'an ba k'aramun so takeyiwa karatu ba.




Da dare duk tayi sanyi baba ya shigo gaisheshi tayi ya amsa tare da cewa .




" Dazu baban su Asma'u yake samuna da wata magana Wai ta karatu to Gaskiya na nuna masa Rashin amincewata saboda Har kullum burina Zarah bai wuce naga ranar Auranki ba naga na sauke nauyin da Allah ya doramun a kanki sannan na cikama mahaifiyarki burinta na Aurar dake sannan na had'aki da danginta kiyi hakuri Zarah bazan barki kije karatu har wani gari ba Kuma ma a halin yanzu bani da k'arfin wannan kiyi hakuri idan Allah ya sanya kinyi Aure sai kici gaba da karatunki gidan mijinki hankali kwance kinji"






Duk yanda hankalin Zarah ya tashi bata yarda ta nunawa Baba ba kasa tayi da kanta ta na mayar da hawayen da suka zubo mata ta ce.




"To shikenan Baba daman bansa haka a raina ba Allah sa haka shi yafi zama Alkhairi"




Ameeeeern y'ar Amanata Allah ya yi maki albarka ya jikan mahaifiyarki"


"Ameen ta fad'a kasa kasa saboda kar ya gane rawar da muryarta keyi ta na shirin fashewa da kuka Baba na fita daga d'akin ta fashe da matsanancin kukan da take rikewa .




batasan ya akayi ba da bata sa burin karatu a ranta ba Amma daga lokacin da Asmy tazo da maganar taji yanzu duk duniya bata da burin da ya wuce Karatu Sosai take kuka har saida kanta ya fara ciwo sai wajen 2 wahalallen bacci ya kwasheta.




washegari da ciwon kai ta tashi saboda kukan da tasha ranar sukuku ta yini ba walwala .




da Yamma koda Hafiz yazo yana kallonta yasan akwai abunda ke damunta da damuwa a fuskarsa ya ce .




"Me yake damunki ne my Zarah naga kamar kinyi kuka " Kamar jira take take nan ta fashe da wani kukan da batasan yazo mata ba.




"subhanalla Zarah me yake damunki wani abun aka maki " Saida ta tsagaita kukan tukwana cikin muryarta ta shagwabar da batasanma tayi ba ta ce.....โœ๐Ÿฟ


*Hmm Kudai muje zuwa fans ba a fara komai ba wannan shi ake kira somin tab'i bama mu shiga cikin wasan ba wannan duk Bayan fagene*
_07026166536 domin magana da marubuciyar_




*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*




1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300


*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡


0810 433 5144


Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡


0814 179 9224


ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


~Share please~


_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/22, 14:35] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ’‘ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ


MALLAKAR


*Hajara L Sadeq*


*TEAM GAWURTATTU BIYAR*๐Ÿ’ƒ


๐Ÿ…ฟ๏ธ.........*9 & 10*




"Baba ne ya ce Wai bazanci gaba da karatu ba Aure yakeson yayi mun"


Yanayin yanda tayi maganar ne ya bashi Dariya saida ya Dan dara tukwana ya ce "My Zarah kenan rigima to meye a ciki ba saimuyi Auren mu ba Kinga ni bazan hanaki karatu ba daga degree har masters.


Turo baki tayi gaba ta ce " nidai banason Auren karatu nake so"To kwantar da hankalinki gimbiyar mata anjima zanje na samu Baba da maganar insha Allahu zai amince.




Cikin Sauri ta d'ago ta ce "da gaske ya Hafiz" saboda haka take ce masa"murmushi ya sakar mata ya ce .




"Insha Allahu" zokuga murnar da Zarah tayi kamar ance Baba ya amince.Aiko ranar Duk miskilancinta ajeshi tayi itace hada Hira da Hafiz Wanda hakan ba karamun mamaki ya bashi ba.


Da daddare Hafiz yaje ya samu Baba da maganar karatun Zarah Inda ya nuna Rashin amincewarshi sosai Hafiz ya dinga yiwa Baba magiya akan dan Allah ya amince Zarah ta tafi karatun tunda ta na da hankali nutsuwa uwa uba Ilimi Sannan ya ce "Insha Allahu kuma Baba ni zan d'auki nauyin karatunta har ta gama".




Shiru Baba yayi kamar mai nazari kafin ya d'ago ya ce "




"bank'i taka ba yaro kozan iya Amincewa Zarah ta tafi karatu tofa Indai da gaske kake sonta ka turo magabatanka a tsaida maganar Aure duk lokacin da ta gama amma haka kawai sakaka bazanbar y'ata ta tafi karatu ba sannan Ko kana fara d'aukar nauyin ta tofa sainaji magana jinjina daga magabatanka"




"Alhmdllh Hafiz ya fad'a a ranshi daman wajen da yake jira akai kenan " Nan take ya ce "Baba na Amince insha Allahu gobe magabatana zasuzo wajenka yanzu zanje na samesu da maganar".




Ajiyar zuciya Baba ya sauke ya ce " ba laifi"Ranar Hafiz cikin farinciki ya koma gida Koda ya samu iyayenshi da maganar basu wani kin Amincewa ba saboda sunsan Malam Yusuf Babban limamine da garin d'aid'aine basu sanshiba kuma sunsan mutumin kirki ne duk y'ar data fito daga wannan gidan tofa za a sameta da tarbiya.




a washegari magabatan Hafiz sukaje wajen Baba Bayan an mutunta juna Inda suka tsaida magana akan Lokacin gama karatunta za ayi Auren shi ma lokacin sannan ya gama masters dinsa hakan yayiwa kowa dadi musamman baba.




Zarah da bata San wainar da ake toyawa ba "saida dare Baba ya fad'a mata yanda sukayi " Baka iya Tantance yanayin da ta shiga farinciki ko akasin haka Amma kuma idan ta tuno da makarantar da Baba ya amince saitaji dadi a ranta batasan ya akayi ba dai maganar Auren bata kwanta mata a rai ba.




Asmy ko koda ta samu labari hada tsallen murnar ta dan babanta dashi aka tsaida lokacin cikin farinciki ta je gidansu Zarah tare da Rungume juna suna murna ta ce.




"Gaskiya nayi farinciki wlh sis bantaba tunanin Baba zai sauko haka ba inye kaga amarya a gidan Hafiz d'inta" turo baki Zarah tayi tare da "Kai mata Bugu a baya ta ce ".




" kinsan bansan zolaya "Ranar kusa raba dare sukayi suna Hirar yanda Tafiyarsu makaranta zai kasance.


Hafiz ko koda yazo Zarah kin fita tayi Dan kunyarshi take ji shiko sai fara a da farinciki ya ke ji yake kamar anmasa Albishir da gidan Aljanna bai tab'a tunanin zai samu Zarah ba cikin Sauk'i haka ba.




Ranar Monday su Zarah suka shirya tafiya Zaria domin zana jarabawarsu ta FUMB Hafiz shi ya kaisu Har Zaria Inda ya jira saida suka gama tukwana Ya juyo dasu A hanya sai kallon Zarah yake yanda take sisinna kai a gaba "




murmushi yayi tare da Kallon Asmy ya ce "Bestynmu yau fa mutuniyar Naga sarautar takeji "


murmushi Asmy tayi ta ce "Naga alama kam inaga kunyarka takejifa "


Harara Zarah ta watso mata daga gaban da take Wanda hakan ya sanya Asmy da Hafiz yi mata Dariya "Turo baki gaba tayi tare da Kallon hanya "


har suka isa funtua suna Hira jefi jefi kasancewar ba wani nisa ke akwai ba tsakanin funtua da Zaria gidan su Asmy suka sauka Dan huce gajiya kafin ta wuce gidansu Ta na isa ta samu Mama Rabi na Surfa bala i ta na cewa.




"Aikin banza aikin hofi ko anzata bamusan iskanci da karuwancin.da ake a jami'ar ba To ayi mugani idan tusa zata hura wuta Aikin banza aikin hofi " Sosai take jifar Zarah da mugayen kalamai Inda ita ko a kanta Dan itadai burinta bai wuce tabar gidan nan ta huta ba.




Cikin ikon Allah jarabawar su ta fito Kuma duka sunci sun samu admission Inda Zarah mass com suka bata saboda daman shi ta cike ita kuma Asmy suka bata Biology education .




zokuga farincikin da suka shiga Daga ranar suka fara sayayyar Tafiyarsu makaranta sun amshi kudin da Zarah ta samu a wajen sauka Inda suka sassayi kayan sawa dasu Komai iri daya suka saya da Asmy kala biyar biyar sukayi atamfofi suka saya Zane bibbiyu suka Kai d'inki ita kuma Mama ta d'inka musu manyan hijabai hurhudu saboda su Kara da nasu.




baban su Asmy shi yayi musu registration ba yanda Baba baiyi dashi ba akan ya bari zai sayar da tumakishi a kauye ya rage masa ya ce




"a.a daman shi yayi niyyar ni musu ai anzama daya " Sosai Baba yaji dadi kuma yayiwa babansu asmy Godiya sosai Zarah ma tayi mashi Godiya kwarai da gaske yanzu zaman gidansu ma gagararta yake saboda koda yaushe suna gidan su Asmy suna shirye_shiryen tafiya saboda Abun na tunkarowa Dan yanzu wata Guda ya rage musu su fara lectures Wanda ji suke kamar su jawo ranakun"
*Wacece zarah*
*Zarah Yusuf* shine cikakken sunanta mahaifinta Malam Yusuf haifaffen garin Batsari ne Noma da kasuwanci shi ya kawoshi garin funtua kasancewarshi malamin addini .




ya samu karbuwa sosai a garin kasancewar lokacin Su ilimin addini bai wadatu ba Sosai sai ya kasance yana koyar da wasu manya magidanta karatu a masallaci Bayan kammala Sallar isha i kasancewar shine limamin masallacin Unguwar da masallacin juma'ar yankin"




wannan dalilin ya k'ara sanyawa mutane da dama suka sanshi a lokacin sosai Malam Yusuf yake da rufin asiri saboda gona guda ya ke amsar haya yayi shukar masara da wake Wanda alkhairi da yake samu ba Kad'an bane .




Bayan nan kuma daman yana kiwo a kauye ganin irin cigabar da yake samu a garin ya sanyashi sayan fili a unguwar jabiri Inda a hankali a hankali ya fara gininsa cikin ikon ubangiji har ya gama .




ana haka ne wata rana yaje Noma Ya hadu da wata matashiyar budurwa sai gudu take ta na hak'i sosai hankalinshi ya tashi kuma yayi mamakin daga dajin da ta b'ullo ga Saran maciji jikinta cikin Sauri ya taimaka mata Inda anan take ta sume kai tsaye Asibiti ya nufa da ita bayan an duba Saran da macijin yayi mata nan akayi mata allura aka bata magani.




Gidanshi ya koma da ita nan ya cigaba da kula da ita ganin har lokacin Bata farka ba gudun zargin mutane ya sanyashi daukarta ya tafi da ita garinsu Batsari Inda ya ajeta gidan baffanshi dan mahaifanshi sunjima da rasuwa a hannun kanin mahaifinshi ya taso nan aka cigaba da kula da ita harta farka Saidai me koda ta farka.




bata iya magana Saidai ta kalli mutane Cikin ikon Allah da addua da komai aka samu harta fara magana Saidai me duk tambayar da akayi mata game da Iyayenta ko y'an uwanta bata iya tuna komai duk yanda taso tunawa sai ta kasa.






hakan yana damun Malam sosai kuma yana tausaya mata gata dai ba wata babba ba Dan a lokacin bazata wuce 18 years ba Saidai abunda ya basu mamaki ta rik'e sunanta Zarah.




Saida Zarah ta shekara guda gidansu Malam batare da ta tuna kowa nata ba ga kuma karfaffar soyayyar da ta shiga tsakanin ta da Malam sosai suke San junansu Wanda lura da hakan ya sanya Baffa jin dad'i kanin mahaifinshi kenan Wanda shi ya tsaye musu har aka daura musu Aure.




ranar wannan masoyan sun shiga farincikin marar musaltuwa A funtua suka tare sabon gidan Malam da ke jabiri zamansu yaci gaba da wakana cikin soyayya da k'aunar juna saboda Zarah macece mai biyayya hakuri uwa uba Kirki Dan a zamanta da mutanen unguwar sai dai Sam barka Dan kowa Santa yake da kaunarta






aminiyarta d'aya a unguwar Saratu watau maman su Asmy a lokacin yarinyarsu d'aya Hauwa'u a lokacin suna cikin halin talauci Wanda hakan sosai ke damun Zarah hakan yasa bata iyacin Abu bata bata ba sunyi zama cikin mutunci da amintaka dukda Saratu ta girmi Zarah amma haka take girmamata kuma suke girmama juna.


"ana haka ne Zarah ta samu ciki Wanda tunda ta samu cikin takeshan wahala ta ke jin a jikinta cikin kamar shine ajalinta A tattare suka samu ciki da Saratu Inda lokacin mijinta ya samu warwara saboda daman yayi karatu Inda ya samu aiki a Bangaren agric saboda daman karatun malamin gona yayi .




kwana a tashi ba wuya wajen Allah a yanzu cikin Zarah ya shiga wata Tara Inda ranar wata Juma a ta tashi da nakuda kai tsaye Asibiti aka wuce da ita sosai take shan wahala tasan rayuwarta tazo karshe a lokacin ne kuma ta tuno da rayuwarta Ta baya Tana cikin halin nakuda ta ce " .


a kira mata Malam "haka ko akayi shigowarshi d'akin tayi daidai da haifo santaleliyar y'arta sak mai kama da Ita kamar an tsaga Kara an karya.


Ajiyar zuciya Ta sauke Kallon nurse tayi dake shirin Tafiya don a shirya d'iyar tayi cikin k'arfin ta ce " mik'omun naga kyautar da Allah yayi mun"


mik'a mata y'ar akayi Inda ta tsaya tana kallonta hawayen tausayin y'ar na zubo mata shafa kanta Tayi Tare da kissing din goshinta ta ce "Allah yayi maki Albarka Zarah ya sa mai taimakon Addini ce Ina sonki Sosai y'ata saidai Allah bai nufa Ba zamu rayu tare Allah ya shirya munke yayi miki albarka Albarkata taci gaba da bibiyarki har k'arshen rayuwarki "


tari ne yaci karfinta Mik'awa Malam y'ar tayi tuni harta fara fita daga hayyacinta Tare da cewa " ga Amanar y'ata na a hannunka Malam ka kula mun da ita ka bata tarbiya ka zame mata uwa da uba ka bata duk kulawar da zan bata ka bata tarbiya harka Aurar da ita Malam ga Amanar yata nan "




a lokacin ne maman asmy ta shigo ita ma cikin kid'imewa ta nufi gadon tana hawaye ta ce "me kike cewa haka Zarah ai cuta ba mutuwa bace haka haihuwar take kowa haka yakeji"




Murmushin yake tayi tare da girgiza kai ta ce "bakisan irin abunda nakejiba shiyasa wannan ba zafin nakuda bane sannan ta kamo hannunta tana hawaye ta ce "Ga Amanar y'ata nan A hannunku ku rik'emun ita amana sannan ku bata tarbiya nasan zaku iya ".




" Malam ne da har zuciyarshi ta karye Ya fara hawaye ya ce "Bazaki mutu ba Zarah ta Insha Allah muna nan tare Harsaikinga auran Zarah da kanki zaki Riki y'arki" .




Kallon y'ar kawai take tana tari cikin k'arfin hali ta Ciro wata zoben gold dake hannunta Tare da awarwaron zinaren da dukansu tare aka tsinceta da su ta mik'awa Malam ta ce .




"idan y'ata ta girma har lokacin Aurenta ku bata wannan shine Babban abunda zai taimaka mata wajen gano Dangina lokacin da zan maku Bayani ya K'ure sannan ku sanya mata suna na Fatima Zarah sosai tarinta ya k'ara tsananta kafin kuma daga karshe suji ta fara Salati ta na Salati har ta cika.


Allahsrk mutuwa kenan mutuwar zarah ba Malam kadaiba hatta mutanen dake unguwar ta Girgiza su Malam ko Kullum kamar ba namiji ba haka zai zauna yayi ta kukan mutuwar zarah danma idan ya kalli y'arta sai yaji wani sanyi a ranshi tunda bata mutu ba har saida ta bar masa Jininta kuma photocopy d'inta Dan sak Zarah mahaifiyarta ce har dimple dinta sai kyau ma da tafi mahaifiyarta.




Kasancewar maman asmy itama ranar ta haihu saboda tashin hankalin mutuwar aminiyarta itama nakudar tazo mata Tasha kukan wannan Babban Rashin da sukayi ita ta Shayar da Zarah tare da y'arta da taci suna Asma'u ita kuma Zarah daman tun ranar da aka haifeta kamar yanda mahaifiyarta ta fad'a haka Baba ya sanya mata sunan mahaifiyarta Zarah ".




kulawa ta musamman maman asmy ta dinga bawa Zarah tare da Asma'u ta had'u ta dinga renonsu Malam ko yanzu baida wata jinjinar sana a saboda tundaga mutuwar zarah komai ya tsaya masa baya iya Zuwa ko ina koda akayi shekara biyu da mutuwan da zai koma harkar nomansa Ya samu Mai gonar har ya bawa wani haya nan ya dawo gida yaci gaba da tawakkali da Allah harya samu Aikin bakanikanci a wani garrage gyaran mashina da motoci Inda ya fara aikin A lokacin ne kuma danginshi suka fara korafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login