Showing 30001 words to 33000 words out of 38330 words

Chapter 11 - AUREN WATA TARA Book Complete By Hajara L Sdiq.txt

27 Dec 2024

2881

ta ko ina Shima ya na da irin larurarki Kinga Abu yazo daidai kenan"


"Tab'e baki Zarah tayi ta ce " please ki daina had'ani dashi tunda dai ni yanzu na kama ya hafiz dina daurin aure kawai ya rage Ki hada sa da Asmy ta fad'a ta na Dariya "


Dariya Chuchu tayi ta ce "Ai kece halinku yazo d'aya Kinga Ko dake yafi dacewa sannan ya Hafiz din da kike magana Ai ba daura Aure akayi ba sa Aure ba Aure bane kika sani ma ko ke rabon Yayan nawa ce"


Nanndai sukaci gaba da Gardandaminsu suna Dariya Asmy ce ta ce "nikam zanso naga wannan yayan da ake fad'a sannan baki fad'a mana sunansa ba ?


Gaban Chuchu ne ya fad'i tunowa da MD din da Zarah ta tsana Wani tunani yazo mata Ai basusan sunansa na Gaskiya ba hakan ya sanyata cewa.


" sunansa yaya Mustapha"Nice name Asmy ta fad'a Zarah ko bama ta saurari sunanba Inda Chuchu tayi saurin barin zancen Dan kar suce ta nuna musu hotonshi dukda basu sanshi ba wata rana zasu iya cin karo da hoton a wani wajen ko media kuma Su gane ita Kanwarsa ce.





Daga ranar nan MD bai Kara zuwa gidansu ba Dan Ya ce Sai Hajiya ta tafi saida ya kira Ammy kullum ya gaishe ta.


Amera ma suna y'ar waya akai akai kewarta bata wani damesa ba Dan Inda sabo sun saba Suna ma aurata amma wani time d'in saisuyi wata hud'u basu hadu ba ita ala dole batason zuwa 9ja Wanda shikuma bazai juri hakan ba Dan family dinsa sun fiye masa komai a rayuwa .




sannan wani karinma in ta tafiyarta yawo kashashe sai anganta shi kanshi wani Karin mamaki yake shin wani irin zaman aurene suke da Amira? Kowa haka yake da matarsa daman(nikam na ce MD ka tambayeni😆)


Kira ne ya shigo wayarsa dubawa yayi ya ga Chuchu d'auka yayi Inda yaji sautin muryarta cikin shagwaba ta ce "I really miss you yaya please yaushe zaka kawo mani ziyara nayi missing naka sosai " numfashi yaja kamar bazai magana ba saikuma ya Ce .


"ke meyasa bazaki zo duka ina Kaduna ina Zaria " Ta na shagwaba ta ce "Yaya wlh lectures ce ta dau zafi kasan level 3 akwai azabar karatu yanzu haka ko weekend din da nake samun zuwa ba Dama saboda yanzu har Saturday muna da lectures Friday da Sunday ne kad'ai ba ma lectures"




"Okay Zan duba naga cikin week d'innan idan zan samu dama me kike buk'atar nazo miki dashi" tsalle ta daka tare da buga ihu su Zarah dake gefenta saida suka done kunne ta ce "Thnks so yaya na bana buk'atar komai kai kawai nake buk'atar gani"


Kayataccen murmushi ya saki Dan a rayuwarsa ba abunda yakeso sama da farincikin ahalinsa musamman Chuchu da yake mugun ji da ita ya ce.


"Zaki fasa mun kunne fa chuchun yaya " Dariya tayi ta ce "Sorry yaya duk murnar zakazo ne ta zautar da ni please yaushe zaka shigo"


"Yau yaushe " Friday "okay to Sunday zanshigo insha Allah " Cikin d'okin farinciki ta ce Allah ya kaimu yaya na I love you so much".


.suna gama wayar ta shiga d'okin murna nan Duk ta ishi su Zarah da zancen Yayanta zaizo ya kawo mata ziyara Dariya ma su Suka dinga mata Dan yanda duk ta rikice musu.




Ran Sunday tun asuba Zarah ta dinga jin ciwon Mara Alamun zuwan perioud dinta sosai cikinta ke murda mata.




su Asmy basu sani ba saida safe suka ganta ta na juyi wayyo cikina kawai take cewa duk Sannu suka shiga jera mata Zarah iya ciwon cikin da take bata tabajin irin na yau ba fashewa tayi da kuka ta ce.


"Zan mutu ku taimakamun Mara ta ciki na wayyo Allah Baba "


Cikin tashin hankali su Asmy suka sanya hijab d'insu Tare da kamata Chuchu ma duk ta rude fito da ita sukayi ta na murkashi kamar mai nakuda




"Asmy taje ta taro napep Bayan sun fito daga hostel Chuchu na shirin shiga Asmy ta ce " ki koma kiyi mana Girki sis zata samu sauk'i zamu dawo ba jimawa"


Badan Chuchu ba taso ta koma Dan ta tsorata da yanda ta ga Zarah




Kai tsaye asibitin da ake kaita suka nufa Gado aka basu danshi kanshi Dr d'in dake duba ta wannan Karin yayi mamakin yanda take.


allura yayi mata amma kamarma Kara ciwon ake Asmy duk ta rude banda hawaye ba abunda ta ke "Bayan Dr ya fito kallon Asmy yayi ya ce " me yasa tun farko bakuyi amfani da shawarar da na bayar ba Akwai fa matsala sperm ne ya tarar mata Wanda inba sa a ba sai anyi mata Aiki "




"Ta na hawaye ta ce " Dr ba yanda zamuyi ne sannan Shi Wanda zata Aurar saura shekara bikinsu yanzu ya jikin nata"dage kafada yayi ya ce "nadai fad'a muku Gaskiya ta na ciki ki shiga munmayi mata allurar da ake mata ta daina yi mata Aiki ki shiga muga abunda Allah zaiyi.




Ta na kuka Asmy ta shiga d'akin Inda ta samu Zarah a bakin toilet sai sheka amai take ita ta taimaka mata ta gyara wurin kafin ta koma gadon ta na kukan ciwon cikin Dan yanzu ta ma fara fita daga hayyacinta Ita kanta ji take yau kuma kila sunyi bankwana da duniya sabbatu kawai take yayinda Asmy na rik'e da hannunta ta na hawaye.




Shigowarsu kenan garin zaria Inda suka nufi hanyar A B U da mota d'aya suka taho Dan baisan duk Inda yaje asan yazo gari wayar Jaber ce ta yi ringing ,dubawa yayi yaga number mahaifiyarsa cikin Sauri ya dauka cikin muryar tashin hankali ta ce " kana ina jabir kayi Sauri ka wuce Zaria mahaifinka yayi assident yanzu aka kirani aka shaidamun suna asibitin Zaria ina ma hanyar Zaria yanzu haka nayi ta Kiran layinka tun d'azu bata shiga "




Cikin tashin hankali jaber ya ce "Subhanallahi Umma wani asibitin ai ina Zaria ma yanzu haka" bansan sunan asibitin ba Amma bari na baka Aisha ta fad'a maka kila ita ta rik'e wayar Umma ta bawa Aisha Inda ta fad'a masa sunan asibitin kafin ya katse kiran "


Kallonta MD yayi ya ce "Lafiya" da damuwa a fuskar jaber ya ce "Ina fa lafiya wai Abbanmu yayi assident a hanyarsa yanzu haka ya na nan Zaria asibiti kawai ka wuce makarantar ni bari na sauka na wuce Asibitin"


Da damuwa MD ya ce "Subhanallahi Allah ya takaita wahala mu wuce tare kawai ina ai tafiya ta zama biyu kuma" juyar da motar sukayi suka nufi asibitin.


Sunsamu jikin na Abban da sauki raunuka ne ya d'anji kuma harma anyi masa d'inki tare da treatment a lokacin ma har ya samu bacci duk Ajiyar zuciya suka sauke Office d'in Dr d'in suka wuce kafin Su jira farkawarshi .




suna nan harsu mamansu Jabir da Kanwarsa sukazo Inda su suka tsaya wajen Abban nasu su kuma sukayi zaune a office d'in Dr Aliyu kasancewar abokin jaber ne da jaber da Dr Aliyu suna Hira banda MD da yayi shiru ya na latsa waya haka nan yau d'innan yake jinsa wani iri.




Banko k'ofar office d'in Asmy tayi cikin tsananin tashin hankali ta na kuka ta ce "dan girman Allah Dr kazo ka gani ka taimakamun kar y'ar uwata ta mutu yanzu haka ta suma bata cikin hayyacinta na shiga ukku na Dr ka taimakamun.......✍🏿


*Domin magana da marubuciyar sharhi tambaya ko kuma Karin bayani 07026166536*




*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*




1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




_*Miss Hajo ce*_🤙🏿
[8/30, 20:44] ❤️❤️❤️: 👨‍❤️‍👨 *AUREN WATA TARA* 👨‍❤️‍👨


```MALLAKAR```


*Hajara L Sadeq*


🅿️............*27 & 28*




Ta k'arasa fad'a ta na fashewa da kuka"kallonta Dr yayi tare da cewa .


"kiyi hakuri y'ar uwa Nifa ba abunda zan iya yiwa yar uwarki na Riga na fad'a maki maganin ciwon ta muddin ba Aure tayi ba ba zata rabu da wannan larurar ba sannan dukta karema ta kai next month's batare da tayi Aure ba to Tabbas sai anyi mata Aiki Dan sperm din ya tarar mata yanda ba aso"




Durk'ushewa Asmy tayi ta na kuka ta ce "Na shiga ukku ni Asma'u yanzu Dr Dan girman Allah muje kayi wani Abu a sume take fa".




Mikewa dr yayi tare da cewa "muje " cikin Sauri Asmy ta mik'e ta bi bayansa "Kallon juna MD da jaber sukayi Sai kuma yayi k'asa da kansa ya na Danna waya Jaber ko shiru yayi ya na nazarin wani irin ciwo ne wannan?




Dan ta samu reliep ya sanya dr yi mata allurar bacci Bayan ta farfado anyi sa a allurar tayi aiki harma bacci ya d'auke ta zaune Asmy tayi a gadon tayi tagumi Ta na tunanin mafita.




Bayan komawar Dr office Bayan ya zauna Jaber ne ya kallesa ya ce " nikam na tambayeka mana Aliyu wace matsala ce Ke damun y'ar uwar yarinyar nan Naji kana maganar sai tayi aure ?




Numfasawa Dr yayi ya ce "Ciwon mara ne take fama dashi lokacin period yanda na lura yarinyar Nada tsananin sha'awa kuma wlh abun mamaki karka ganta yarinya k'arama ,




" shekara Ukku kenan kusan duk wata sai ankawota nayi mata allura to a halin yanzu allurar da nake mata ta daina karbarta Sperm ne ya tarar mata Wanda indai ba wani Abu ya shiga tsakanin ta da namiji ba tofa ba wani magani da zamu iya mata Dan yanzu haka abun yayi worse dukta kare saima anyi mata Aiki nan gaba inhar basuyi abunda na fad'a ba"




Numfashi jaber ya ja ya ce "Allah mai iko amma fa Gaskiya na tausayawa yarinyar nan Saidai kuma ina ga tafiya tazo daidai da zama "




Dagowa yayi ya kalli MD dake Danna wayarsa dukda yanajin duk maganar da suke ya ce " Aboki me zai hana ka auri yarinyar nan kaga Kayi taimako kuma kaima ka yi solution matsalarka "




Wani banzan kallo na ka rainamun hankali MD yayi masa tare da cewa "ka gama rainamun wayau Jaber ohh tunda taimakon zakayi kai me zai ha na ka aure ta " ya fad'a ya na Jan tsaki.


"Look bloody ba haka ba ne Wlh Gaskiya nake fad'a maka baka da mafutar da ta wuce wacce na baka Kuma ka duba ka gani a yanda naga Y'ar uwar wannan yarinyar ta firgita zasu iya Amincewa da bukatarmu sannan kaga anyi Abu biyu ka biya bukatarka itama an biya mata tata kayi tunani"






Tsaki MD yaja tare da cigaba da Danna wayarsa Dan shi a ganinshi jaber ya ma gama raina masa wayau.




Dr ne ya ce "tsaya wai akanme kuke magana bangane ba" kallonsa jabir yayi ya ce.


"Bari nayi maka bayani aboki Shi wannan da kake gani nasan ka sansa ba boyayyan mutum ba ne, to shekararsa Tara da Aure matarsa bata tab'a haihuwa ba a halin yanzu kuma iyayenshi sun bashi nan da shekara guda Idan matarsa bata haihu ba Kuma bata samu ciki ba to zasu masa aure Wanda shi kuma baida ra ayin mata biyu sannan ya na son matarsa bayasan abunda zai bata mata rai saboda ta na da tsananin kishi Wanda yakai har ta na ikirarin ya k'ara Aure zata iya kashe kanta ta kashe kishiyar kuma matsalar rashin haihuwar daga matar ne duk inda sukaje an aunasa anga lafiyarsa qalau to shine na bashi shawarar me zai hana yayi aure a b'oye na Wata Tara yayiwa Matar ciki harta haihu asirrance Sai ya saketa bayan anyi mata karyar abunda ta haifa ya rasu sai ya amshi abunda ta Haifa ya kai matsayin matarsa ta Haifa ita kuma ya biya ta da mak'udan kudi to ganin matsalar yarinyar nan ta kawomun wani tunani,me zai hana suyi yarjejeniya ya Aure ta na Wata taran idan ta haihu saiya saketa kaga kowannansu yayiwa kowa Amfani shine wai yaki Amincewa banda hakan taimakon kansa ne".




Numfasawa dr din yayi ya na nazarin maganganun jaber kafin ya d'ago ya Ce" Tabbas kayi tunani mai kyau Abokina Saidai matsalar ka na ga zasu amince kuwa?.




jinjina kai Jaber yayi ya ce "Ai gwada sa'a ce " dage kafada dr yayi ya ce "indai zasu amince nima zan taimaka muku ta bangarena wajen tsoratar dasu akan ciwon yanda zasu amince idan ya amince amma fa bro ina baka shawarar ka bi shawarar abokinka Indai muddin bazaka k'ara Aure ba to wannan ce kawai Mafita a gareka ".






Numfashi mai k'arfi MD ya fesar tare da Dagowa ya kallesu Shima su d'in suke kallo Dafe kanshi yayi saboda sara masan da yake tunani yayi yaga Tabbas wannace mafitar ta k'arshe Cikin husky voice dinsa ya ce " Na amince"


"Ajiyar zuciya Jaber ya sauke tare da Kallon Dr ya ce " Alhmdllh to yanzu ta ina zamu fara Dr"Shiru yayi dr kamar mai nazari kafin ya d'ago ya ce "Ku barmun sauran aikin bari kuga ta yanda zan fara".


MD ko zafi yakeji acikin ransa ya na ayyana wannan chakwakiya da zasu fad'a.


Nurse dinsa Dr ya kira a waya tare da fad'a mata Ta shigo masa da budurwar nan da tashigo dazu ta na kuka ta amsa da okay .


Suna nan sunyi shiru Nurse ta shigo Tare da Asmy dake hawaye har lokacin " Umartar nurse din yayi da ta fita kafin ya duba kallonshi ga Asmy da murmsuhi ya nuna mata chairs din da ke gefenshi ya ce "zauna a nan zamuyi magana"




Zama tayi Jaber ko tunda ta shigo ya ke kallonta sosai ta burgesa Numfasawa dr yayi tare da cewa.


"kinsan abunda ya sanya na ce a kiraki Hakikanin Gaskiya Akwai matsala dangane da larurar y'ar uwarki,wanda muddin wani watan ya zagayo ba tare da Wani Abu ya shiga tsakanin ta da wani ba kamar yanda na fad'a tofa cikin biyun nan dole sai d'aya ya faru na farko dai ko dai ta rasa ranta saboda sanin kanki ne ciwon cikin nan ya sha kashewa na biyu kuma dole ne sai anyi mata Aiki Wanda aikin Shima ya na da matuk'ar matsala Dan kila wa kala ne ko a tashi ko a mutu sannan kudin aikin kanshi Ba anan ake ba sai anje India Wanda a k'alla zaku kashe sama da 30 millions"




Tashin hankali ba agwada maka rana d'ora hannu a ka Asmy tayi ta ce "Na shiga ukku wayyo Allah na Dr ka taimakamun kar y'ar uwata ta mutu wlh bamu da kud'in aikin nan sannan Taya za ayi Ace Tayi mu'amula da wani namiji kafin lokacin nan Bayan ba Aure gareta ba Dr inba zina akeso tayi ba " ta k'arasa fad'a ta na kuka.




Murmushin Gefen baki Dr yayi Dan Shirinshi ya hau kenan kafin ya ce .


"Calm down mana sister ai akwai mafita da aka samu yanzunnan amma sai inkun amince idan baku amince ba Kuma saiku jirayi abunda zai faru gaba" cikin Sauri ta d'ago ta ce "Wace mafita ce dr wlh munma amince "




"Kinga waddan biyun da ke zaune " ya fad'a ya na nuna mata su MD "Juyawa tayi ta kallesu sai yanzu ma ta San da wasu a office d'in ta juya ta kalli Dr ta ce.


" na gansu Dr "yawwa to Kinga wancen ya shirya taimakon y'ar uwarki Shikuma ya na da larurar tsananin sha'awa ne matarsa bata k'asar ta na k'asar waje karo karatu saura wata Tara ta gama sch shine ya ce " zai taimaka ya Aure ta *Auren wata Tara* saiya saketa Kinga an taimaki juna ya taimaketa ta taimakeshi"




Kallon MD dake zaune Asmy tayi saida ta zaro ido cin karo da kyakykyawan gaske a iya rayuwarta zata iya cewa bata tab'a cin karo da mutum Mai kyau kamarsa ba Ai ba indiye ne ma sak take gani a gabanta control d'in kanta tayi Dan karsu lura tayi kauyanci sannan ta kalli Dr ta ce.


"Na amince indai hakan zai zama.silar ceton Rayuwar yar uwata Dr Saidai akwai baikon wani akanta Saura shekara guda Shima karatu yaje karawa ya na gamawa itama sannan ta gama sch d'inta za ayi Aurensu idan akaje da wannan Maganar mahaifinta bazasu amince ba Gaskiya "




"Ai babu d'aya daga cikin iyayensu da zasu San da maganar nan Abu ne za ayi na sirri idan lokacin ya cika saiya saketa ta tafi tayi auranta Kinga asiri ya rufo ansamu mafita ba tare da ta fad'a halaka ba"




D'agowa tayi ta ce "To wa zai wakilceta Dr " wannan ba matsala bace y'ar y'ar uwa indai kun amice a take a yau d'innan za a daura Auren "




Jinjina kai tayi ta ce "Na amince duk Ajiyar zuciya suka sauke banda MD da duk Haushi ya isheshi yasan Hajiya kaka ce kawai ta jawo masa matsalar nan " Jabir ne ya ce .




"to saimu jirayi farkawarta muji Amincewa daga gareta " Girgiza masa kai Asmy tayi ta ce.


"a a a Karku jirayeta kawai a D'aura Bayan an daura zansan yanda zanyi na shawo kanta har ta amince amma yanzu kawai a daura ba matsala "




"To alhmdllh komai yazo cikin Sauki yanzu zamuje masallaci a daura Auren Bayan fitowar Sallar La'asr sannan zanyi muku video din d'aurin Auren Dan ya zama hujja da shaida a garemu"




"to mungode Allah saka da alkhairi Asmy ta fad'a tare da mik'ewa tace bari na koma Wajenta"


murmushi Dr d'in yayi mata ya ce"muke da Godiya sis " ta na fita MD ya kalli Dr ya ce .


"me yasa ka boye musu Gaskiya Dr da ka fad'a musu bukatarmu idan sun amince idan kuma basu amince ba a hakura kar ashiga hakkinsu fa"


Mikewa dr yayi tare da cewa "karka damu Aboki ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login