Showing 33001 words to 36000 words out of 38330 words
Chapter 12 - AUREN WATA TARA Book Complete By Hajara L Sdiq.txt
wata matsala insha Allahu idan muka fad'a musu Gaskiya ba lalle su yarda ba amma kaga haka sun yarda cikin sauki"
Zai sake magana Jaber ya Mike ya ce"is okay bloody ka tashi muje a d'aura kawai"Harararsa MD yayi tare da Jan tsaki ya Mike Dan haushinshi yake ji na lika masa koma wacece da zaiyi baima ganta ba Tsaki yaja Dan baidama buk'atar ganinta.
Kai tsaye Unguwar su Dr Aliyu suka nufa Bayan MD ya rufe fuskarsa da face marks mahaifinshi sukayi sallama dashi ya fito Bayan sun gaisheshi ya amsa Dr Aliyu ya ce.
" baba kaga wannan ya fad'a ya na nuna masa MD Baba ya ce Eh na gansa "yawwa to Abokina ne zaiyi jahadi na Auren wata y'ar gudun hijira to iyayensa sunki su amince da Auren shine ya taho wajena Dan mu taimaka a daura musu Aure inyaso daga baya Ya nemu yafiyarsu"
"Kabbara mahaifinshi yayi ya ce " Allahu akhbar da ace ana samun irin wadannan ai da anzauna lafiya Gaskiya ne wannan jahadi ne zaiyi babba Sannan ya kalli MD ya ce .
"yaro Allah yayi maka albarka Tabbas kaid'in da ne na kwarai insha Allahu a yanzu yanzunnan ba anjima ba za a daura muku Aure " murmushin k'arfin hali MD yayi jaber ko Hamdala kawai yake yanda komai yazo musu yanda basuyi zato ba.
Bayan kammala Sallar la'asr Mahaifin Dr Aliyu ya bada sanarwa da akwai d'aurin auren da za ayi Nan ko mutane suka tattaru aka cika masallacin harda wajensa Dan Malam ashiru sananan mutum ne Bayan an kawo Goro Inda Liman ya zama wakilin Zarah shi kuma mahaifin Dr aliyu Malam ashiru ya zama waliyin MD.
ganin An fara d'aurin Auren ya sanya Jabir saurin d'auko wayarsa tare da Fara yin video a take a nan aka Daura Auren *Zarah Yusuf* tare da Angonta *Mustapha dikko* Akan sadaki Naira Dubu d'ari biyar.......โ๐ฟ
*๐๐yanzu salon wasan zai soma wakana fans wancen duk sharan fagene yanzu muka shiga chakwakiyar Auren wata Tara Kudai ku kasance dani miss hajjo danjin karashin wannan K'ayaitaccen littafin da yazo da salo mai rikitarwa*
*kamar yanda kuka sani littafin nan d'aya yake daga cikin gawurtattu biyar page d'aya ya rage mana mu gama free page daga page 30 zan tsaya da free page Wanda ya biya ne kad'ai yake da daman k'arasa karanta wannan zazzakan labarin da yazo daga zazzakan alkalamin miss hajo ga tsarin yanda biyan nan yake a kasa idan kun duba don neman karin bayani ku tuntube ni Akan number wayata kamar haka 07026166536*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐ฏโโ๏ธ๐๐๐*
1, *MU GANI A ฦASA...*๐ฅ
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ฦWAI..*๐ฅ
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*๐ฅ
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*๐ฉโโค๏ธโ๐จ
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huษu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษaya N300
*DOMIN TURA KUฦIN KAI TSAYE*๐
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya๐
0810 433 5144
Masu tura katin MTN๐
0814 179 9224
ฦณan ฦasar Niger zasu tura nasu anan.๐
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huษu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐๐ฉโโค๏ธโ๐จ
_*Miss Hajo ce*_๐ค๐ฟ
[8/30, 23:21] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐จโโค๏ธโ๐จ *AUREN WATA TARA* ๐จโโค๏ธโ๐จ
```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*
๐
ฟ๏ธ............*29 & 30*
Daga wajen d'aurin Auren MD ko jaber bai Kara waiwaya ba ya wuce Gidanshi dake nan low-cost Zaria Dan kanshi duk Sara masa yake.
Bayan komawarsu jaber asibitin kiran Asmy Dr yasa akayi a office d'inshi jaber ya mik'a mata wayarsa tare nuna mata video din amsa tayi ta na Kalla gabanta na fad'uwa Dan batasan yanda zasu wanshe da Zarah ba "
Tura video din tayi a wayarta itama Dan ya zame.mata hujja sadakin a embleme ya mik'a mata tare da cewa .
"ga sadakin dubu d'ari biyar ne chif" Amsa Asmy tayi tare da Sanyawa jaka duk tayi sanyi ta kalli Dr ta ce "Sai Abu na gaba da bamuyi ba takardar yarjejeniya " girgiza mata kai sukayi jaber ya ce "Ba ma buk'atar wannan ma'u sannan ki bani numberki mun k'arasa sauran maganganun a waya"
Kwafe masa numberta tayi Bayan yayi save tata Shima tayi save a sanyaye ta koma d'akin da Zarah take har lokacin Bacci take tagumi tayi hawayen tausayin aminiyar tata na zubo mata Zarah ita ce bata farka ba sai Asuba koda ta tashi jikin nata Alhmdllh ba ciwon cikin sosai.
A hankali ta mik'e ganin Asmy gefenta ta na bacci toilet ta nufa ta gyara jikinta ta na fitowa ta iske Asmy ta mik'e ta na mika Kallon juna sukayi Asmy ta ce.
"Harkin tashi kenan ya jikin to" Alhmdllh kenan saida muka kwana Asibiti"Wlhko ai ciwon nan naki ya tsoratani Zarah ta fad'a tana shiga toilet Dan yin alwala Bayan ta fito tayi salla ita dai zarah ta yi tagumi Tun lokacin Asmy take son yiwa Zarah bayani amma ta kasa Sai tazo zata mata bayani sai ta kasa Wajen 7:00 Zarah ta ce "waike meye kikeson ki fad'amun tun asuba kin kasa karkija inyi zaton ko wani abun ne ya faru".
Numfasawa Asmy tayi dak'yal ta iya d'aga baki ta ce " daman Zarah "saikuma tayi shiru daman me?ta fad'a ta na tsatsareta da ido" Dak'yal ta iya jarumta ta ce "ta ce .
"Daman Dr ne ya ce ciwon cikin naki yayi worse sosai sannan Allurar da ake maki ta daina maki aiki muddin next month yazo a haka batare da wani Abu ya shiga tsakaninki da wani ba to dole sai anyi miki aikin 30 millions kuma aikin ya na da hatsarin gaske"
Sosai tashin hankali ya bayyana k'arara a fuskarsa Zarah ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Wannan wace irin jarabawa ce Asmy yanzu ni me.zai had'ani da wani namiji kafin one months Ni da ba Aure gareni ba Sannan Aikin 30 millions fa kikace Asmy wani irin aiki ne wannan".
Numfasawa Asmy tayi ta ce " Eh Zarah haka Dr ya ce Saidai akwai mafita "cikin sauri ta d'ago ta ce " wace mafita Asmy?Wani abokin Dr ne da yazo ya tausaya halin da kike ciki shine ya ce Wai idan zaki amince zai Aureki na wata Tara kafin lokacin bikinki da ya Hafiz saiya sakeki Kinga Asiri ya rufu hankali kwance".
Wani banzan kallo ta dinga bin Asmy dashi kafin ta d'ago ta ce "bantaba sanin baki da hankali ba Asmy sai yanzu wannan wace irin banzar magana ne angaya miki Aure abun wasa ne ko kuma ciwo hauka ne to Bari kiji ko zan mutu bazan tab'a yarda da wannan shirmen banzan ba ko a garin gab'a gab'a anyi haka wlh ni kinma b'atamun rai yanda baki tunani " ta fad'a ta na Jan dogon tsaki.
Sosai gaba Asmy ya bada daram hankalinta in yayi dubu ya tashi ta ce "Amma Zarah...daga mata hannu tayi ta ce " ya isa indai akan wannan banzar maganar ce Karki sake mun maganarta "
Ta fad'a ta na mik'ewa tare da sanya Hijab d'inta ta ce "Kinja Asibitinma ya fita a raina tashi mu tafi " Amma aikin bari Dr d'in yazo ya sallamesu"Ke saiki jira har ya zo ya sallameki ni na tafi ta fad'a ta na nufar hanyar kofa.
Daidai fitarta yayi da daidai da shigowar Jaber d'akin da Kallo ya bita harta fice daga Ward din wanda ko fuskarta bai gani ba juya Kallonshi yayi ga Asmy da tayi tsuru a d'akin ya ce .
"hartaji sauki kenan naga fitarta ina zata?hostel wlh ya jaber taki amincewa nan ta fad'a masa yanda sukayi da ita " kallonta yayi ya ce "Karki damu sannan karki fad'a mata ki barta a haka din duk abunda zai wakana ya zamana muna shiryasa ni Dake tunda na lura Amaryar tamu kamar ta na da taurin kai".
Murmushi kawai tayi ta ce " haka take in ta burkuce amma tana da saukin kai bari na bita "Ledar da ya shigo da ita ya mik'a mata ya ce " daman break fast ne na shigo muku dashi"Da farko kin amsa Asmy tayi saida taga yana ta mata magiya kafin ta amsa Bayan taje tayiwa Dr bankwana ta bar asibitin kafin ma ta isa wajen asibitin har Zarah ta tafi wata napep din ta tsaida ta wuce makaranta.
koda ta isa kwance ta tarar da Zarah Chuchu na gefenta ta na bata ruwan tea ta na shigowa Zarah ta kauda kai ta na kunbure kunbure girgiza kai kawai Asmy tayi tare da zama Chuchu ta Kalleta ta ce .
"ya mai jikin jiya nayi ta Kiranki ki fad'amun asibitin da kuke nazo amma kashe " wlhko chaji ne bandashi har yanzu wayar tawa ta mace gashi tata Kinga bamu tafi da ita ba "
"ayya shiya sanya Ai da sauki ma wlh karkiga jiya banyi barcin kirki ba duk hankali na na wajenku sannan Yaya na ma da yace zaizo nayi ta kiranshi Shima kashe duk raina ya gama b'aci jiya da kadaici na yini na kwana".
Murmushi akwai Asmy tayi ta ce " kilan wani uzurin ne ya rikeshi"Wama ya sani kuma fa wlh yaya baya magana biyu abun yaban mamaki sosai "duk maganar da suke Zarah bata ce uffan ba saima Kallon Chuchu da tayi ta ce " kin sanyamun wayata chaji?eh ta fad'a tare da tashi ta miko mata ta ce "anyi ta Kiranki ganin kiran yayi yawa ya sanya na ma kashe ".
bud'e wayar Zarah tayi ta ga missed call d'in ya Hafiz Kusan goma cikin Sauri ta Danna masa kira Ring biyu ya d'auka ta na jin Ajiyar zuciyar da ya sauke tare da cewa .
"ina kika sanya wayarki my love jiya na yini da darura " Ajiyar zuciya ta sauke ta na lumshe ido ta ce "ta mutu ne ba chaji ya Hafiz ina kwana ya sch din" .
Alhmdllh Habibaty har Naji sanyi kinsan na d'auka ko ba lafiya ba sai tunaninki nake"murmushi tayi ta ce "Lafiya qalau nima da tunaninka na yini" ta fad'a ta na rufe fuska ".
Daga bangarensa yayi Dariya ya ce " ai dai nesa ta kusa zuwa kusa nan da one year munzama mata da miji"rufe fuska Zarah tayi kamar ya na gabanta tare da katse kiran Dan ya bata kunya ma .
Ganin yinin ranar yanda Zarah ta share Asmy ya sanya bataji dad'i ba Ta ce "Na ce Kiyi Hakuri Zarah Daman zaki iya fushi dani tunda maganar ta wuce ba shikenan ba" murmushi Zarah tayi ta ce "Ya wuce Asmy kinban Haushi ne nayi mamaki da maganar ta fito daga bakinki saikace baki da hankalii" .
turo baki Asmy tayi ya ce "Naji dai yanzu abar maganar" a take suka shirya sukaci gaba da hirarsu Wanda asmy hankalinta duk baya gurin.
***
"To ba saurin nake ba bloody kaifa komai kafison ayishi cikin ujila ba ina hanyar zuwa gidan ba minti biyu yayi yawa na iso "
" jaber ya fad'a daga wayar "tsaki MD yaja tare da katse kiran ya na tsaye harabar gidan flat house ne Me kyau baida wani girma sosai Saida ya tsaru parking space d'in gidan zai d'auki mota Ukku ya na tsaye motar jaber ta shigo gidan Bayan yayi parking shiga gaba yayi da zasu fita ya tsaya ya mik'awa me gadin kudi tare da cewa .
" A cigaba da kula da tsaftar gidan yanda ya kamata "to ranka ya dad'e insha Allahu Nagode Allah ya k'ara girma" kai tsaye Hanyar kd suka nufa jaber ya Kalleshi ya ce "bazamuje mu gaisa da Chuchu ba" Bana ra'ayin hakan "ya fad'a yana cigaba da latsa wayarsa " Girgiza kai kawai jaber yayi tare da cigaba da driving Dan ya lura ranshi kamar bace tafiyar 30 minutes ta kaisu garin kd Wanda kai tsaye gidan sa suka nufa Bayan ya saukesa jaber ya wuce gidansu Dan tun safe aka Sallami babanshi shi kuma md ciki ya shiga Dan ya huta.
Kwance yayi kan makeken Royal bed dinsa mai matuk'ar d'aukar hankali ya yi pillow da hannayenshi biyu bacci yake so ya daukesa amma ya rasa dalilin da muryar qiri'arta yarinyar ke dawo masa a kunne lumshe idonsa yayi.
Jin ringing d'in wayarsa da ya bude ba jimawa ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya Lula d'aukar wayar yayi ganin Chuchu ce ya sanyashi d'auka "yaya na jiya shine ka shanyani nayi ta jiranka har girki mai dadi nayi maka amma bakazo ba " ta k'arasa fad'a cikin shagwaba "
Cikin muryarsa da bayason yin magana ya ce "wani uziri ne ya hanani zuwa chuchun yaya next time na tashi zuwa Saidai kawai ki ganni kwatsam"
Yana jin ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "To shikenan yaya Ai Inajin next week ma zanzo gida saboda munyi waya da Ruky tace next week zasu tafi Dan naje muyi bankwana " to shikenan Allah ya kawoki lafiya "ya fad'a Dan bayason hayaniya.
Kiran Amera ne ya biyo baya Bayan gama wayarsa da Chuchu kamar bazai daga ba saikuma ya d'auka " kuka yaji ta fashe dashi Wanda yakejinshi har cikin ransa tsayawa yayi ya na sauraronta har saida ta gama kafin ta tsagaita cike da kissa ta ce.
"Haba Honey Bayan kasan nayi missing naka shine zakayi zamanka anan please yaushe zaka dawo kasan banason zamanka a Nigeria ko wace banza ta dinga kallemunkai please mijina ka dawo kewarka duk ta isheni.
" Ke me zai hana bazaki taho ba Inda nake Dan in kin ganni a America to fa saina gama muhimmin aikin da ya kawoni "
"Haba honey yanzu ka na nufin bazaka dawo ba yanzu akwai muhimmin aikin da ya fini daman me zai hana bazaka k'arasa aikin a nan America ba dole sai Nigeria " ta k'arasa fad'a ya na jin shashekar kukanta".
Don son kwantar mata da hankali ya sanyashi kasa da murya ya ce "Aikin bazaiyu ba a Chan my meera ki taho kawai nima ina bukatarki kusa dani kinfi kowa sanin haka Gobe ki taho saiki sauka Abuja"
"Ni wlh honey bazanzo Nigeria yanzu ba idan nazo dinma in banda chazamun kai ba abunda ake sannan a isheni da maganar Rashin haihuwa Bayan ta Allah ce Nifa tun last time da nazo Sunan Daddyn Zey karkaga irin Rashin mutuncin da tsohuwar nan tayimun Hada cewa wai Aure zata sanyaka kayi na shanyeka na gama dakai sannan itama Ammy Ai Naji kwanaki kus_kus din so take kayi Aure to wlh ba abunda zai maidoni Nigeria kusa wancen zuwan ma da kaga nayi Dan nayi kewar iyaye na ne kawai akanme zanzo Bayan family dinka ba k'aunata suke ba dan wlh tsohuwa ko yarinya ta kawomun wargi ba kyalewa zanyi ba Hakanan kawai a doramun hawan jini da yarintata"
Sosai ran MD ya b'aci Cikin b'acin rai ya ce "Da Allah iya mutane shiru stupid kawai iyayen nawa kike fad'awa haka Dan baki da kunya kar alasa kizo din kiyi shekara ta Annabi nuhu tunda America din garin ubanki ce " ya k'arasa fad'a ya na Jan tsaki.
Kuka Amera ta fashe dashi ta ce "ni kake zagin uba na MD yau Ni ka zaga" tsaki ya ja tare da katse kiran Dan ta bata masa rai ya jima ya na Jan tsoka.
Kasancewar ya rike ranar da chuchu ta fada masa su hajiya zasu tafi around 11am ya shiga da motarsa harabar gidansu Hango motar Adil tare da su Hajiya da su Chuchu a wajen ya sanyashi karasawa"Ina kwana hajiya "Lafiya qalau Mustapha mu kuma muntafi sai Allah yayi mana dawowa ko kuma kunje dukda Bason zuwa kuke cikin dangin Ku ba kowa gareku ba a Kaduna in banda Aikin gwamnati da kasuwanci da ya kawo mahaifinku duk dangin mahaifinku suna Maiduguri amma tsabar shak'iyanci saiku Shekara biyu ko Ukku baku taka garinba Dan lalacewa Ai wlh duk laifin Fatima ne Ai lokacin da ran Mariganyi yana tiso keyarku kuna zuwa"
Murmushi yayi ya ce "za a gyara Hajjajunah " itama Ammy murmushi tayi ta ce "Insha Allah Hajiya zamuzo nan kusa " Allah yasa Hajiya ta fad'a ta na sanya akwatinta cikin boot da Adil ya fito mata da ita tare da Chuchu hannu Adil ya mikawa MD sukayi musabaha ya ce "Yaya zamu wuce "
"Okay Allah ya kiyaye Ya tsare hanya yanzu tundaga Chan Saida Hajiya ta tiso ka Dan Kawai ka d'aukesu maimakon A musu booking Fly hankali kwance".
murmushi Adil yayi ya ce "Wlhko ya na iya na musa cibi ya zama Kari" Hajiya ce ta ce "Naji dai Komai zakace kace amma banga tukin da zan hau ba idan ba naka ba Sauran duk y,an kasada ne ka maza ka shigo mu tafi maiduguri ba zuwa kano bace karmuyi dare hanyar nan da ba kyau gareta ba".
Ruky ta fara shiga Bayan sunyi hug din juna da Chuchu da takejin kamar tayi kuka Bye bye tayiwa Adil ta na narkewa jikin Ammy murmushi yayi mata na so da k'auna ya ce " Bye Dear sai munyi waya"itama mayar masa tayi ta ce "Allah ya maidaku lafiya " .
Har zasu tafi Hajiya ta juyo ta kalli MD ta ce"kai kuma Ka fara lissafi yanzu saura wata sha d'aya ka bari lokacin da zan dawo garin nan zakayi mamakin d'anyen aikin da zanyi "ta na gama fad'a ta shiga Mota Adil ya ja har suka bar gidan suna daga musu hannu".
Cikin suka koma Chuchu ta zauna gefen Ammy ta d'ora kanta bisa kafadarta " Gaishe da Ammy MD.yayi Bayan ta amsa Kallonnshi Chuchu tayi ta ce "Ina kwana yaya" Lafiya qalau "ya bata amsa tare da cewa jeki hadoman break fast " "to" ta amsa tare da wucewa kitchen.
Kallonshi Ammy tayi ta ce "yaushe zaka koma ka baro Matarka ita kadai kayi zaune a nan" Ba yanxu ba Ammy bazan bar k'asar nan ba har sainagano Wanda sukayi kisan Alhaji sammani saboda sak irin harin da suka kawowa Abba Shima daidai zai shiga gidanshi da mota aka harbeshi akwai binciken da nake saina k'arasa tukwana".
Saida Ammy ta Goge hawayenta tunowa da uban Yayan nata ta ce "Tabbas Wanda yayi kisan Alh sammani shi ya kashemun miji saboda alh sammani da Mahaifinku aminai ne bashi da aminin da